Showing 75001 words to 78000 words out of 382072 words
sam basu sin zancen shi a cikin mu ko kadan.
Ajiyan zuciya ya sauke tare da mikewa tsaye yana gyara rigan shi yake fadin nizan tafi don ba dadewa zanyi ba na dai shigone kawai.
Don a yanzu ya kara tabbatarwa kanshi cewa akwai wani al,amari dake boye tsakanin wanan ahalin dasu yara basu sani ba.
Haka ya tafi cike da mamakin yadda hjyn ta nuna mai nan take inda ya doshi gidan shi kai tsaye har ya shigo Nazifa na kan waya don bata dauka zai dawo a lokacin ba .
Don shigowan safe yayi masu a bazata kuma hakan bai hana shi sauke mata hakkin ta ba dake kanshi a lokacin.
Shine take waya da yar uwanta kuma aminiyarta tana fada mata irin yadda suka kasance a tsakanin da yazo din duk a kunnen shi tsab yaji komai haka yasa ya juya zuwa dakin shi ba tare da tasan da ya shigo gidan ba lokacin.
Dakin shi ya shiga ya kwanta cike da takaici da jin haushin wanan yarinyar mai tonon asiri haka garesu.
Haba abu yayi mai yawa a zuciyar shi da zancen hjyn su zaiji da shi da sukayi dazun nan ko da zancen wanan sakaran yarinyar da take wai matsayin mata a gareshi yanzu.
Wani iri yake ji a zuciyar shi haka yasa ya dauko wayan shi ya kunna kira,a a cikin shi ko zai rage jin abinda yake ji a ranshi din lokacin.
Cikin ikon Allah kuwa ya fara jin zuciyar shi tana sauka masa har zai iya yin tunanen mafita a kan mu a lokaci don duk wani zafi a yanzu ya daina jin shi kuma.
Baida wani manufa a yanzu daya wuce ya tunkari daddy su da wanan zancen yaji ra,ayin shi akan hakan.
Wayan shi ya dauko ya kira layin mahaifin nasa duk da yasan ba lalai bane ya sameshi a yanzu don yasan lokacin aikine a lokacin.
Sai gashi cikin sa,a daddy din ya dauki wayan nasa suka gaisa bayan sallama dashi suka dan taba hira kafin ya jefo mashi tambaya da fadin.
Wai daddy wanan zancen iyalan Abba sambo da suka bata a ina ya kwana yanzu ne don gaskiya bai kamata ace an fita batun su haka ba suna can cikin duniya suna wahala.
Tun bayan da mukaje neman su din nan wanan zancen yake damuna daddy sosai wallahi ya fada cikin sanyin rai.
Mahaifin nasa ya tare shi da fadin ka samu wani labarine game dasu a yanzu ya tambayi dan nasa cikin kaguwa Abubakar din yace.
No daddy naji kawai ka daina wanan zancen ne kuma shine na tambaue ka ya fadawa daddy din a sanyayye kamar bai damu ba.
Watau Abubakar idan har bamu taimaki ahalin nan ba nasan sai Allah ya tambaye mu gobe kiyama don yadda alhakin neman nasu ya rataya yanzu a kan mu .
Sai dai nasan da yawa daga cikin mu basu damu da hakan ba ni kuma yanzu abubuwa sun hanani wanan binciken a kansu yanzu.
Daddy ka ban baki tun ban bar lagos ba na nemo makasu a garin nan idan suna nan cikin sa don wanan yarinyar da na gani gaskiya tana mugun kama da jinin gidan namadi daddy sosai.
Moddibbo kabi sannu kada wani yasan da wanan zancen koda mahaifiyar kane don sanin hakan yana iya jawo maka matsala da yan uwana a yanzu.
Duk da nasan kai din namijine jan gwarzo zaka iya komai kace zakayi a rayuwan ka a yanzu saidai ina kara fadama da kabi wanan maganan a sannu har in zaka iya hakan .
Don nasan ba banza suka bar duk wani wanda yayi yunkurin dawo dasu a cikin muba a yanzu din don muggan mutane masu amfani da al,ada bisaga addini shine kawai akidar da suka rike don jahilci.
Kada kaji komai daddy a yanzu a kaina insha Allahu adduan ku yana amfani a gareni a kullun dan guntun murmushi mahaifin nasa ya sake mai don jin abinda ya fada a lokacin.
Wai rikici ya fada a fili bayan ya kashe wayan yana mamaki kan wani shirka can zasu jefa wa yan nan mutane haka a cikin wanan ukuban rayuwa.
Abu na farko da zai fara shine ya tabbatar da mun samu mun murmure kafin mu koma a cikin yan uwa din sai kuma zancen karatun yara idan bai manta ba ai ya taba ganin yarinyar saye da uniform a tsohon unguwar su da suka baro.
Jin an shigo mai dakin yasashi kara daure fuskan shi sosai a lokacin don yau zai nuna mata ko shi waye don taji dadin gulma da tushe.
Har kwana uku bamu ji duriyan shi ba a wanan lokacin gaskiya ba umma ba har mu din mun fara shiga halin damuwa ga hakan.
Muna zaune dakin munyi shiru tv kawai da nayi karanbanin kunawa a dakin ke aiki don hankalun mu baya wurin saboda bamu saba da wanan kalle kallen ba a rayuwan mu.
Shiyasa ko yanzun ma din muka barshi yana aiki shi kadai don amar ya fara kallo sai barci ya dauke shi a hakan.
Sahiba tsoro fa kar mutanen wurin nan su kai ga koran mu nake ji gashi yaron nan tun shekaran jiya rabon shi damu a wurin nan.
Kardai ace ya gudu ya barmu don nasani dama ba zasu barshi ya mayar damu gida ba kamar yadda muma gidan ya fice a ranmu ga baki daya.
Idan ko har haka din ne har yanzu tsugune bata kare muna ba don gara mu tattara inamu inamu mubar wurin nan baki a lekum idan bai dawo ba gobe.
Wani irin ba dadi naji har kasan raina saidai ba yadda na iya ga hakan shiru nayiwa umma din nake hango abin kamar shirine hakan sukai muna dama.
Bana fatan goben yayi don abinda umma din ta fada a kan zaman mu a cikin wanan gidan da bamu san kanshi ba muna dai cikin sa zaune kawai ana kawo muna abinci muna ci ga kuma kulawan da muke samu din a wanan wurin.
Haka din kuwa Allah yai dare gari ya waye ina ta tunane da zullumin akan zancen mukaji anyi sallama a kofan dakin namu za a shigo.
A Yanzu kan na sheda muryan shi ko a ina naji don saurin fahintar da nake dashi din a kaina, ummace ta amsa mai ya karaso ciki ya samemu.
Muna zaune a cikin kayan da dai ya san mu dashi har lokacin don ba wanda yai amfani da nasa kayan da ya sawo muna din.
Da alaman baiji dadin hakan ba daya gani ya dai daure suka gaisa da umma yana bata hakkuri kan rashin ganin shi da bamuyi ba na yan kwanakin wai tafiya ya kamashi ya tafi kuma ga ba waya a hannun mu yasa bai sanar damu ba.
Umma tana fadin ba komai ai tunda Allah ya dawo muna dakai lafiya nika har na yanke shawaran yau idan bamu ganka ba sai mu bar wurin nan a yau din.
Haba umma ai ba zan kawoku nan in tafi in barku a nan din ba cikin hotel koda bansan darajan ku ba nikan hausan da sukeyi sai nake jin shi a kunne na wani bakon hausa ne ba wanda muka dan koya a wurin umma din bane muka iya.
Sai lokacin na samu daman gaidashi da wuni ya amsa min a takaice yadda ya saba ba sakin fuska a gareni ko kadan .
Magana sukeyi da umma din wanda bana fahinta kan me suke maganan yayin dana dan saci kallon shi da kyau a lokacin ne kuma na fara tunanen a inda nasan shi farkon ganina dashi.
Sannu a hankali nake tunawa har na gane ai shine wanda ya zo wurun gasa masarana a lokacin wani tunane nayi nace watau ke nan tun a lokacin ya fara bibiyata ke nan.
Nidai ko ma meye ya kaimu gida shine bukatana a yanzu don banda wani buri daya wuce in ganni a gaban yan uwana in san su su sanni abar kira muna da bamu da dangi.
Muna yawan samun wanan matsalan tun dai zaman mu a Ajagule gidab su iya wale suna yawan yi muna wanan gorin kuma hakan yakan dameni sosai.
Don haka na kwamacewa komawan mu gida a yanzu din wirin dangi zaifi muna ko dan tsare mutuncin muna zaman diya mata dagani har umma din da maza ke kawowa harin tayawa ko wani lokaci da sunan iskaci.
Zancen kararun mu sukeyi da umma ta fada mashi komai kan dakatar da kararun mu din da mukayi a yanzu bama zuwa boko saidai neman abinda zamuciwa cikin da nakeyi a yanzu.
Ya nuna rashin jin dadin shi ga hakan yake fadin ba zamu bar garin nan ba sai ya karbo muna transfer din mu ga hannun shi zamu tafi.
Naji dadin jin wanan zance na karatun don a gaskya ina son yin kararu sosai a lokacin nan dai da yadda zanyi ne kawai yasa na daina zuwa din.
Sun dan jima da umma suna hira kafin yayi mata sallama ya barmu sai a lokacin nake fadawa umma ko shi waye shine wanda ya ke ban kudin nan dana fara kawo mata a lokacin.
Ummake fadin mena fada maki tun farko zuciyana ya bani run a lokacin cewa akwai abinda ke shirin faruwa damu a lokacin.
Baki yarda da hakan ba yanzu ko kin yarda ko to hakana ma a can gidan da kuke son zuwa abubuwa zasu faru da dama kan komawan mu din cikin su da zamuyi a yanzu.
Jikina nayi sanyu don na fara fahinta cewa dai akwai abinda umma ke nufi da hakan da take yawan fadi ko wani lokaci niko wanan wani irin matsala ne haka da zamu fuskanta gun dangin mu din kuma.
Kwana biyu sai ga ya Abubakar yana fadin mu shirya zai tafi damu school din da muka bari mu an so transfer din mu.
Dole muka bude wanan akwatin mu saka kayan daya saya muna din sai dai duka kayan bazan iya sakasu a jikina ba don ban saba da saka irin su din ba.
Duk yadda umma taso in saka na kasa sakawa don ko zanin ban iya daurawa ba haka ya shigo ya samemu muna wanan rikici da umma din.
Take fada mai yayi dan shiru kafin ya juya ya fita sai can gashi ya shigo da kaya masu yawa dogayen riguna masu kyau daidai size dina da wasu wando da riga sune daidai dani ba wanan daya sayo din da farko ba.
Na saka wandon jeans da yar riga daya dace mai dogon hannu na kawo hijjab dina na dora sama sai naji wata daban can dani ga zafi da naji atake ya fara rufeni don hijjab din.
Haka dai na daure muka tafi ba wani wahalan da muka samu don dan bayanin dayai masu kan rashin ganina din da basuyi ba .
Sun taimaka sun bamu ba tare da yi min repeat ba din sun fada mai i can make it saboda ina da kokari sosai a karatuna din.
A hakan muka barsu muka nufi makarantar su Amar can madin ba wani matsalan da aka samu sun bayar da transfer din yadda ya dace.
Muka dawo inda yai muna masaukin dole din muka samu umma duk ta damu da dadewan da muka danyi bamu dawo ba a dakin.
Kai zan iya cewa wanan bawan Allah yana da saukin kai don sai idan baka zauna dashi bane ganin farko zaka daukeshi wani maijiji dakai ko wani mugu can.
Amma a gaskiya ba hakan yake ba sam don halin shi a sanyayye yake komai nasa don na dauka da umma tace dashi akwai abinda take son dauka a can dakin mu na semi na dauka ba zai yarda da hakan ba sam.
Sai gashi tana fadi a cikin irin ladabi sa yace ba matsala zai kaimu mu dauko duk abinda mukeson dauka a can din kafin mu wuce.
Wanan tafiyan ni yaiwa dadi don akwai inda nake ajiyan kudi a dakin ko umma bata san da hakan ba sai ni kadai nasan wanan abin.
Haka aka kwashe mu zuwa semi din mukayi sallama da duk abokan arzikin mu na nan kan cewa zamu tafi muga gida wata kila mu dawo ko ba zamu dawo ba idan mun tafi din.
An dan nuna jimamen hakan don sabon da muka danyi dasu nikan na faki ido na hako kudina da nake binnewa a dakin cikin kyalen da nake daurewa a cikin sa.
Kudin na nan kamar yadda na barsu ba a taba ko kwandalaba a cikin shi duk da mun samu an dan taba kayan dankin an binciki dakin ga baki dayan shi.
Duk da wanan halin ba bakon abu bane a wanan garin don da zaran kadan daga na kwana biyu hakane ke kasancewa ga mutum dama.
Mukai sallama tare da amsan laban wayoyi idan munje zamu kirasu yadda mukace dasu ke nan a lokacin.
Haka muka rabu dasu ba dadin rai don sabon da akayi da juna na dan lokaci.
Mun dawo hotel din da muke ne da kwana biyu ya gama duk wani shirin tafiyan mu din zuwa arewa a daidai lokavin mahaifinsu daddy ke nan shima ya dawo kasan da kwana biyu.
Zo kaga murna kan don ma umma ta hireni da abubuwa da dama kafin mu fito tayi warning dina sosai kan na kama kaina da kowa don kada a samu a cuta min ga hakan.
Karfe shida na yamma muka bar lagos zuwa kaduna state din da nake jin labadin shi a cikin tarihi ashe dama nan ne state dinmu ashe.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA, , , , , , , , , , ,
2️⃣3️⃣
BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MUTAKABBIR, , , , , , , , ,
ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA NA FADA MAKI NA FITAR DA HAKKIN RASHIN SANI A GAREKI, , , , ,
WASA YA FARA, , , , , , , , , ,
Bin ko ina na airport din nakeyi da kallo da yanayin wurin duk da garin ba zafi amma naji bambamci yanayi da can din don lagos akwai ruwa saidai akwai zafi sosai a can din idan an tashi yi hakan.
Wasu lafiyayyun motocine guda biyu suka dauke mu daga airport din zuwa inda zamu don nan san ko ina ba ni kila gara umma idan bata manta ba ta sani ita.
Unguwar su ya kaimu kai tsaye don motan mu daban ce da wace ya shiga shi saidai abinda na kula dashi tun shigan mub motan umma batai magana da kowan mu ba sai addu,an da take faman yi a bakin ta.
Haka yasa nima nayi shiru ina yan adduan dana saba a bakina na neman tsari ga abinki da dan adam yakeyi don neman kariya.
Daga can cikin motan da yaya Abubakar yake yake waya tare da tambayan daddy da fadin daddy na shigo kaduna kana gidane yanzu ?
Daddy din ya bashi amsa da eh moddibbo ina gida ai kasan baja fita da dare ni bayan magariba ina gida ko wani lokaci.
Na sani daddy zamu karaso yanzu mu sameka a falo ya fada kai tsaye yana kashe waya yabar mahaifin nasa da mamaki don sam bai kawo da mu din yake tafe ba saidai tunajen shi da wasu bakin abokan aikin shine kila yazo don yadda yaji yana masa magana a gurguje da alaman dai akwai wani abu.
Don haka daddy din ya mike zuwa falo inda suke karban bakin su a gidan hjy karima da zata shigo da ruwan zafi a flask ta tsaya tana mamakin ganin ya fito take tambayan shi don a zaton shi wurin hjy zai tafi.
Ina kuma zaka a wanan lokacin ta tambayeshi wucewa yayi inda zai tafi kai tsaye ta juya ta shiga da flask din dakin ta aje.
Wani get da sojoji ke gadin gidan aka bude motoci suka shiga lokaci guda darene a lokacin don haka kowa na cikin gidan sa a lokacin.
Saida yayi magana da umma kafin ya juya ya fara tafiya zuwa ciki muka fito daga cikin motan kai tsaye duk da tafiyan dadi mukayi ba mota muka bi ba jirgine kuma daga airport zuwa gidane a yanzu.
A hankali muka fara bin bayan shi zuwa cikin gidan daya dosa din muna binshi a baya ya rigamu shiga ciki yake fadin daddy ashe ka fito falon ko ga bakin naka nan na kawo maka zasu shigo.
Baki daddy ya tambaya a cikin mamaki don bai fahinci dan nasa ba sallama umma data daga labule tana shiga dakin tayi muna biye a bayan ta muka shigo.
Da wanan bakon yaren da naji umma tayi nan ma din shi take magana dashi da wanan daddy din a cikin yaren filatanci.
Naga ya daga kamar a firgice da mamaki karara a