Showing 363001 words to 366000 words out of 382072 words

Chapter 122 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28350

, , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AN, NUR , , , , , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257

ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U 👋

Bata wuri ta shiga mota ya fada a fusace daga bayan mu sai ta jaye da sauri tana kallon fuskanshi na bude motar na shiga Fatima ma haka ta shigo sai gashi ya iso bakin motan nan ya duko yana fadin.
Ki kula da kanki sahiba zan zo gida yanzun nan idan na gama dasu a nan kai kawai na iya gyada mashi a lokacin driver yaja mota muka tafi raina ba dadi ga abinda nagano.
Allah yaga zuciyana naso na zauna lafiya da kowa amma wanan matar ba zata bari hakan ya faru ba amma zan bita a sannu inga iya gudunta.
A gidan hjy kuma andai kwasa ba dadi bayan wucewan mu dasu don nan ta fara kafa mai tujara wai ya kawota gidan sune dama suci mata mutunci ita da yan uwanta ko me ?
Nan dai suka kwashi jidali bayan an samu da kyar ya tafi ance ya barta tunda taki shiga mota ta tafi ita da yan uwanta.
Rashi bace ya bar gidan sai mugun magana take fadi da iya abinda zata iya min na sheri karshe dai har yakai saida hjyn su mukhatar din tafito da kanta ta tsawata mata don dole tabi umurnin ta ta wuce.
Saboda hjyn tace mata matukar bata bar gidan ba zata nuna mata ita ta haifi mukhatar din kuma ta umurceshi daya aureta a lokacin.
Shin falmata kishi haukane ba,a aure nasa shi don dole sai ya aureki ke dole kuma yabi umurnina har ya aure ki din don yanzu kina ganin kin samu wuri yasa zakizo nan ki muna diban albarka.
Daga kuzo a sulhunta a zauna lafiya ba fitina kowa ya rike girman shi ya tsaya a matsayin shi mijin ku yakara samun kwanciyan hankali a rayuwanshi amma zakizo min gida kina diban albarka haka ?
Falmata me kika takane kike takama dashi wanda banice asalin samuwan haka gareki ba ko kin dauka tsoron ki nake ji nake kyaleki kinawa diyana da yan uwa wulkacin wai ?
To kishiga hankali daga yau aurene dai mukhutar yayi sai kije kiyi abinda zakiyiwa amaryan yanzu saidai ki sani kemafa ba kyaleki za,ayi ba haka.
Ehh hjy dama ba yau ba nasan zamana da mukhutar yana ci miki rai kina bakin ciki da hakan yanzu saidai a yanzu babu yadda zakuyi don jini ya rigada ya gauraya da ruwa tun tuntuni kin makara a yanzu.
Tana fadin hakan ta shiga mota da sauri yan uwanta suka shiga suma ta figi motar da karfi tabar gidan a cikin zafin rai.
Mun isa gida ban tsaya falo ba a daki na nufa na cire gyalen kaina tare da rataye jakkana na fada bandaki don lokacin magariba daya gabato.
Na idar da sallah har lokacin raina a bace saiga Fatima ta shigo tana fadin wai anty wanan matar akwai masifa.
Ashe bayan wucewan mu an kwasa sosai da ita har yakai saida hjy tayi mata tas tana ramawa.
Idanuna na lumshe tare da fadin nagani naga komai Fatima saidai wanan haukan nata bai dameni ba sam idan ba tashigo rayuwana ba ba abinda zaisa na kulata.
Zan barta na manna mata karamin hauka da duniya zasu sanda ita sugane mai gaskiya a tsakanin mu.
Haka naso mami tayi a gidan mu amma sai a barta tana fada a dinga dora mata laifi ko yaushe magana ya tashi da tana kyalewa itama tayi na karkashin kasa ko banza za a dan zauna lafiya a gidan da kowa.
Amma yanzu mu daban su daban da kashigo gida zaka fahinci akwai matsala a gidan kenan mutane su fita damu a baki.
Nan mukayi ta tatauna matsalan kafin muji dawowan shi mun fito falo baya falin yasa muka samu wuri falon muka zauna a nan.
Saida ya dan dauki lokaci kafin ya fito da alama wanka yayi a lokacin ya fito jikin shi saye da jallabiya ta maza brown colour sai kamshi yakeyi jikin shi.
Nan muka shiga gaidasu muna mashi sannu da dawowa ya samu wuri ya amsa muna kafin ya fara fadin.
Iam sorry da abindaya faru daku dazun nagode da kuka bar wurin baku tsaya anyi wani fitina ba daku tunda haka sukaso.
Nerve mind wanan ba komai bane ai na fada tare da kawar da zancen nake fadin ya Abubakar ya sameka a waya ?
Kallon mamaki yayi min na shareshi don na fahinci baya son zancen ya Abubakar din daga bakina niko kaf din mu nafi sabawa dashi don shine mutum na farko daya jamu zuwa gida ya nunamu a dangin mu saidai daddy ya boye hakan.
Don shi kuma nake ragawa duk wani ahalin mu tunda abin ya shafi duka bangarenshi idan nayi ba daidai ba dole ranshi ya baci duk da yana nuna muna rashin damuwa akan bangarensu din.
Yanzun ma akan maganan su ummace da Ammar da yan uwa sukai shawaran waisu zauna a kaduna umma ta bugo min tana fada min shine nakirashi yace zan tambayi mijina yaji ra,ayin shi kan hakan shine na fada mai yanzu din.
Bai kirani ba ya fada yana ci gaba da bata fuska dan lokaci guda nake fada mai cewa akan zancen su ummace wai ba zasu koma lagos ba shine takirani tana fada min na kirashi yace sai yayi magana dakai yaji ra,ayin ka.
A kan me zasu hanasu komawa can din yanzu tunda a can suka saba da zama ko banza ba zasu yarda dasu ba aikuma yanzu don wanda ya kashe maka naka baka taba mantawa dashi ai.
Ko suna ganin kun manta da zancen ne a rayuwan ku kawai dai ban san ra,ayinki na yafe masu da sauri irin haka ba shiyasa nabiki da hakan.
Ba komai bafa na dai share zancen ne don kawai rayuwan na baya ya gyaru nan gaba don kada hakan yazo yaci gaba.
Wanan halin da matarka ta nuna a yau a gabana irinsa ne ya jawo har wanan matsalan ya faru da iyayyen mu tsananin kishi ga uwa yana saka zuciyar diyanta ya gurbata su dauki dan uwa a mastsayin makiyi a garesu.
Shine dalilin da yasa nake son zaman lafiya da kowa a yanzu gaba da kadan da kadan yake fara a zuciya har ya girma yashafi duk wanda ke kewaye da masu shi.
Kallona yakeyi a cikin mamaki har lokacin da nayi shiru kana ya nisa hannu kawai ya miko min alaman nazo wurin shi.
Kallon hannun nasa nayi kafin na rarafa zuwa inda yake duk da bamu da nisa dama dashi amma da dan sasarfa na karasa inda yake din ina zuwa ya karasa jawoni ya manna da jikin shi yana sauke ajiyan zuciya tare da dan murza bayana a hankali.
Kedin karamace amma kina da zuciyar manya Sahiba zuciyarki tankar ta mahaifin kine akan imani da sanin yakamata saidai ina tsoron abinda hakkurin ki zai iya jawo maki nan gaba .
Jin hakan yasa na dago kai na dan kalleshi lokaci guda na dukar da kaina kasa dan ban iya jure hada ido dashi wanan lokacin.
A daidai wanan lokacin kuma wani irin ciwon mara ya soko min lokaci guda har saidana dan zabura na rike maran tare da fadin innalillahi.
Da sauri ya tambayeni ko lafiya nace maratace ya rike min sai gashi wasa wasa abu na shirin zama babba a gareni haka yasa bai tsaya ba muka nufi asibiti Fatima tana daki sai jin yana kwala mata kira tayi ta fito a gigice ganin yanayin da nake ciki yasa ta rudewa lokaci guda itama.
Tashin hankali da fargaba ne fal a ranshi har muka isa asibitin aka dubani a iya bincken su sam basuga wani aibu a jikina ba daya kawo hakan.
Wanan yasa ya shi bai tafi ba a lokacin daya shirya tafiyan shi har ya cika min satin dayan da Allah ya wajabta akan budurwa ai mata amma babu abin daya shiga tsakanina dashi.
Gashi na fahinci cewa matsalan yana faruwane idan mun kebe tsakanin nidashi a nawa fahintar ke nan a yanzu don haka matsalata bana asibiti bane na kuma hana fatima ta fadawa kowa a gida game da wanan matsalan nawa din.
Zaune suke a falon su tunda ya dawo sai wanan lokacin yafito falon suka zauna da Aisha da mahaifiyar shi suna hira.
Wayan shi ya dauki kara ya dauka ganin wanda ke kiranshi din a lokacin yana dauka da sallama saidai jin muryan me magana kamar yana kuka a cikin tashin hankali ya daga mai hankalin shi.
Tambayan shi yake hankali tashe kome ke faruwa abinda ya jawo hankalin uwar da kanwarsa ke nan suke kallonshi suma.
Oga we don die woo all our goods is lost nan ya fara mai bayanin cewa conteners sun nutse a ruwan cottono.
What ya fada da karfi saida wayan ya fadi daga hannun shi bai damu da hakan ba sai kasa dayayi ya kai zaune kawai tare da dafe kanshi.
Tambayen shi take a cikin yaren da takai kala biyar lokaci guda saidai ba amsa hakan sai can ya dago ya kalli Alajan dake durkushe a gaban shi.
Mami shike nan kin rabani da silar dawowan arzikina na fada maki itace rayuwana amma kinki ki gane hakan saida kika rabani da ita mami ?
Wana rabaka dashi daya kunshi arzikin ka ta kara tambayan shi shima ido cikin ido ya bata amsa da fadin Sahiba.
Sahiba ta kara ambatan sunan yace yes mami malamai da yawa sun fada min hakan na lurar dake hakan baki gane nufina ba.
Ita din zaman tadani alherine a gareni sosai mami yanzu rashinta a tare damu ga abinda yake samuna akai akai ina hasaran duk abindana tara.
Komawa tayi zaune dirsha lokaci guda tana mai kallon mamaki tare da kura mashi idanu kafin tace dashi sahiba dince arzikin ka shaaban ?
Kwarai mami mutane da yawa suna fada min hakan saidai ban yarda ba sai da naga yadda arzikina ya hadu da nata sosai haduwan mu da ita yasa na yarda da hakan.
Yanzu kuma da kika rabani da ita na kara gaskanta hakan don irin abin dake bibiyata a yanzu din na hasara da rashi.
Yanzu kinji jirgi ya nutse da kayan da muka odo na mashinu ko daya ba a tsira dashi ba wanda duk rabin arzikina yana a wurin kayan nan.
Innalillahi ta fara tafawa da hannayen ta lokaci guda kafin ta fadi cewa Sahiba ta asirce min yaro da har ka iya yarda da hakan gareta.
Haba haba Alaja wanan baiyi ba wallahi mutum yana a cikin halin gigita kan hasaran da yayi a yanzu kuma zaki kawo mai wanan irin maganan mai cin zuciya.
Aishace daga gefen su take fadin wannan maganan a fusace tana kallon uwar kafin ta juya ta koma inda dan uwan nata yake zaune tana fadin.
Yayana meye abin yi yanzu can inda abin ya faru zamu tafi ko kuwa sahiba din zamu fara nema ta dawo gareka by all means.
Wani kallo ya jefo mata na kina da hankali kuwa Aisha kafin ya bude baki da kyar yace matar auren cefa a yanzu a ina zamu nemo ta .
Idan ma mun samota muce da ita me a yanzu duk wanan zancen bata sanda shi ba ita ni kadai na sanda zancen yasa nake daukaka rayuwanta akoda yaushe ta yadda ba zata iya rabuwa dani ba sai gashi mami ta rabamu da rana tsaka a lokacin da ban taba zaton yin hakan ba.
Ta kara juyawa inda Alaja take zaune tana kallon su a cikin mamaki don a yanzu tasan abinda zancen shi ke nufi don yarbawa basu zama ba tare da irin wanan bincken ba a rayuwan su.
Balleshi mutum mai gwagwalmaya irin haka dole saida tambaya a lamarin su muryan yartane ya katse mata tunanen da tafadayi tana fadin.
Kin gani Alaja kinga abinda kika jawo wa danki yanzu saboda son zuciya irin naki ki barshi yayi rayuwanshi a yadda ya tsara tunda ke kinyi naki a yadda kike so a baya ba a hanaki ba.
Hannu ya daga mata da sauri kan tayi shiru ga abinda take fadi din dan kalamin yayi tsauri ga mahaifiyar su din.
Dana sani da nadamane fam a zuciyar Alaja saidai bata son diyan nata su fahinci hakan daga gareta a lokacin.
Shima ya fahinci ciwon nawa a yanzu saidai bai tsammani nima din nagane wani abu bane na sihiri ke damuna haka ba don ban yarda na nuna mashi komai ba har ya tafi.
Saidai mun samu labari a wurin su sister cewa hjy Falmata bata koma ba kamar yadda mijinta ya fada zata koma itama can inda yaranta suke karatu.
Wai ta tsaya yin wani abune a nan shine ya tafi ya barta nan din wanan labarin bai dameni ba a lokacin amma sai naga kamar ita fatima ta damu da hakan.
Kwana uku da wucewan shi da yamma muna zaune a falo har mai aikin mu don tun bayan tafiyan shi sai aiki ya rage muna a gidan yanzu.
Itama taji dadin hakan don ta fara sakewa tare damu har in ana kallona aika tazo ta zauna zata zo so yanzu ta daina yawan takurawa kanta da labewa sosai.
Nocking din kofa akeyi yasa Suwaiba mai aiki mike zuwa duba ko yawaye saidai tana bude kofan aka turo ta baya da karfi har saida taja dan baya kadan zata fadi kasa.
Abinda ya jawo hankalin mu ke nan muka maida kallon mu a kofan muga mai shigowa a lokacin sune su hudu kamar yadda sukaje gidan hjyn su mukhutar din a ranan.

Suna cikin wani shiga na iskanci saidai sun samu shigan da yafi karfin nasu a jikina don dagani sai dan wandon jean guntu daya tsaya iya wuyan kafana.
Sai riga yar karama mara hannu mai dan kwala a wuyan shi ta yadda zasu iya kare min kallo da kyau ke nan don nasan babu kowa a gidan kuma ba wanda zai shigo yasani wanan shigar sai gasu sunzo sun sameni a hakan.
Ehh lalai tun ba a je turai din ba an koma yin shigarsu koda yake ba mamaki ga hakan don zaman mutum a cikin daban lagos zai iya yin komai a rayuwan shi.
Haba don Allah zaku shigowa mutane gida a haka kuna fitsara fatima ta fada a dan hasale na daga mata hannu alaman ta bari.


ANA DARA, , , , , , , , ,

BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , ,

1️⃣0️⃣9️⃣

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM, , , , AL, HADI

YAR UWA KIJI TSORON ALLAH KI DAINA FITAR MIN DA NOVEL DON KIN BIYA KI BARI WANI YA BIYA SABODA ALLAH👋👋

Komawa tayi ta zauna tana binsu da kallo basu zo inda muke zaune ba sai yawo suka fara a falon suna tabe tabe da yatsune fuska haka yasa nasan ba arziki ya kawosu gidan ba lokacin.
Har zuwa lokacin da suka nufi dakunan kwanan dake cikin gidan suna iskanci in ka debe daya daga cikin su da taja ta tsaya a bayan su .
Juyawa nayi na kalli fatima nace go and close the door for me, ki kawo min key nan ta juyo da sauri tana kallona bansan meta gani a kwayan idona ba ta mike da sauri ta wucesu zuwa kofan tayi abinda nace tayi din jikinta sai kaduwa yakeyi a lokacin don tsoro.
Suna wani tafiyan isa da takama suna harare harare suka karaso tsakiyan falon suka tsaya.
Ganin hakan yasa na mike tsaye remote na dauka na rage karan tv dake aiki kallona sukayi tare da fadin ehh lalai samun wuri anga komai abanza dole ayi yadda akeso ba a saba da ganin daula haka ba ba.
Dan murmushi na sake a fuskana ina dan karkada farin kafana da duk rabinshi yana waje sai takalman zaman gida na roba shima pink kalar wandon dake jikina anyi mai addo daga sama kamar gashi an rufeshi.
Dama kwadayin arzikin ne ya kawota cin banza saidai yarinya kin tabka babban kuskure da kika yarda kika shigo gidan mijin yar uwan mu da sunan kishi da ita.
Ohh Realy na kalleta na fada naci gaba da fadin ita yar uwar taku diyar waye a kasan nan da ba,a shiga gidan mijinta itama din ba shiga tayiba.
Ji wanan banza muna fadi kina fadi ke din yar waye diyar bararon daji kawai kilama rufa rufa akaiwa mutane ba a san asalin ubanki ba.
Keko taga arziki ido


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login