Showing 138001 words to 141000 words out of 382072 words

Chapter 47 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28338

inda nake zaune mutumin daya umurce ni a gidan mahaifan shi cewa kada in fara in nuna cewa nasan shi koda wasa don me yanzu zai dawo ya dinga kokarin son kulla zumunci damu kuma ?
Yarinya nake tabasa a gareshi amma zan gwada mashi don bamu da gata yanzu ba shine zaisa har su takamu yadda suke so ba.
Ban fito ba saida zai tafi umma ta kwala min kira na ki amsawa Amar ya leko dakin da dokin shi ya samu na tayar da sallah da bansan kan shiba bama lokacin.
Ina ji ya koma yana fadi wai ina sallah ne lokacin haka suka kwasa ta dan rakashi ta dawo ta tayar da sallah itama ban yarda na fito ba son nasan kwanan wasa dole sai umma tayi min fada kanshi.
Sai karfe tara na fito a cikin shirina na kwanciya barci suna falo zaune inda Allah ya taimakeni kafin takai ga yi min magana saiga Muniya matar Abdulhamid ta shigo tana fadin .
Tazone ta fadawa umma bakon da yazo yabawa yaran su dubu goma tafito da kudin tana nunawa umma tare da ajewa a gaban ta.
Ban dago kai na kallesu ba na mayar da hannkalina a wurin wakan da akeyi a cikin tv din kafin can na mike jin suna hira tana fadawa umma maigidan ta da yaran sun fita zuwa asalatu wurin daukan karatu ke nan suke nufi da hakan.
Abinci na debo na fito ban zauna falo din ba na shige dakina dashisun dan dade tare kafin mijin nata da yaran su dawo tayima umma saida safe ta shiga gidan ta.
Haka yasa bamu hadu da umma ba a ranan sai washe gari na gama aiyukana da nakayi kafin in tafi school na dan zauna ina kurba rwan zafi don ga dabian bayerabe baka fita daga gidan ka ba tare daka saka wani abu a bakin ka ba koda kuwa kurbi dayane.
A cewan su koda wani mugun abu zai sameka Allah zai kawo saukin abin da kariya bazai sameka yadda akeso ba ba ku koyawa diyan ku sabawa da dan cin koda wani abune kadan kafin su fita makaranta mata Allah ya tsare ya karemu baki daya amin.
Umma ta fito daga daki tana gyara daurin zanin dake jikin ta tace dani bayan takai zaune tace sahiba na dago kai da sauri na kalleta.
Abinda kikayiwa dan uwan ki jiya kin kyauta ke nan umma dan uwana wake nan ta watso min harara daga inda take na sake dukar da kai kasa.
Ki matsa idan nuna kula shi a garemun da yakeyi shima laifine yin hakan kin dai san bamu da kowa a duniyan nan sai wanda ya tausaya muna yazo ya rabemi kafin shima kwana biyu ai masa aiki ya gujemu.
Dan murmushin bakin ciki na sake a fuskana kafin ince umma kema kin fada da bakin ki yanzu bazan taba yarda da duk wani daya shafi wanan zuri,an ba kuma a yanzu.
Balle wanan din da tun farko ya iya fada min kada in yarda in sake nuna cewa nasan koda a mafalki ni kuma zan nuna mashi cewa ba shegiya aka haifeni ba ai.
Ina fadin hakan na mike ban tsaya sauraren ta ba na fita zuwa school ranan ko Amar ban tsaya jira ba na sa kai na fice a gidan ni kadai.
A school ma ban sake jiki ba don abinda ya faru dani da umma da safe haka kawai zai zoya haddasa muna fitina a tsakanin mu.
Dole akwai abinda abinda yake dashi a zuciyan shi game damu na nasa a raina amma ko me haka ke nufi wata rana zai fito filine ni dai komai umma zatayi min bazan taba yarda in nuna wai nasan shi ko muna da wani alaka dashi ma.
Har na koma gida ban yarda na sake ba har lokacin haka itama umma din hakane ya faru da ita don nayi mata abinda take gani saboda na girma nake ganin har zan iya kin bin dokan ta akaina.
Shima din dai haka ya koma yana mamaki yadda yarinya karama ta iya masa duk a lokacin bai gano cewa wai saboda wanan maganan bane daya fada min nayi hakan.
Me yarinyar nan take nufi ne wai ko ta dauka takai wata mace ce da har zai nuna ra,ayinsa a kanta yaja guntun tsuki tare da daukan cup din glass din dake gaban shi cike da ruwan lemo ya kurba kafin ya aje cup din yana furzo iska daga bakin shi.
Me yarinyar nan ta dauki kanta a yanzu yarinyar dake yawo kwararo kwararo a cikin garin nan da kayan talla a kanta.
Da badan maman shi data matsa akan ya binciko wani alakane tsakanin daddy damu ba ba abinda zaisa ya sake kula wa yan nan mutanem ya fada a fili shi daya kamar mahaukaci a falonshi.
Shi shi ya fada wai bata sanshi ba a lokacin ne kuma warning din da yai min a baya ya fado mashi a zuciya tabbas wanan maganan yar ficiciyar yarinyar nan ta rike.
Da badon tafiyan dake gabab shi ba gobe daya koma yaciwa yarinyar nan mutunci ko a gaban uwar natane kuwa don shi baida shayin kowa idan ya tashi tsula tsiyar shi shi yasa bai kula kowa kaf dangin shi saboda bahagon zuciyar shi da take mai baudai shiru shirun muguntane gareshi don ya tsotsina fulani a jinin shi.
Abdulhamid ne ya shigo har falon mu bayan sallah isha,i suka gaisa da umma ina daki ina jin muryan shi tunda yayi sallama don kwana biyu ke nan muna haka da umma.
Bawai bama magana ba a,a kawai dai tana fushi dani sama sama ne dana ga haka na rage zama a kusa da ita nafi zama a dakina idan ina gida.
Ina kokarin shafa maganin nan da suka amaso baki amfani dashi ba duk dare ina shafawa kafin in kwanta barci tunda saboda ni aka karbo
Sahiba fa naji Abdulhamid ya ambata don ya kamata ta koma aikin ta hakanavnaji muryan shi yana fadi yaci gaba da fadin.
Don yau sun tambayeni ita nace ta samu lafiya sosai don naga tana shiga school.
Eh to Sahibace yanzu Abdulhamid ta dauko wani sallo kuma bari dai a kira maka ita kuyi magana idan tana ra,ayin komawa nan din.
Sam banji dadin jin kalamin umma ba datayi mai a kaina don dai itace zance ta dauki abindaya faru da zafi ai kan almustpha din da yazo dawata manufa garemu yanzu.
Amar ya shigo ya fada min umma na kirana nace gani tafe bai dade da fita ba na fito saye da dogon rigan barci na daura zani a sama sai yar hula dana daure gashina na dunkule a ciki.
Gaida shi nayi kafin ya ce dani gobe ki fara fita aikin ki Sahiba don aikin yana da muhinmanci a kanki sosai sai dai ba lalai bane ki gane hakan yanzu.
Idan kinyi hakkuru nan gaba zakiji dadin hakan da alama ya fada yana kallona dan shiru nayi kafin nace bawai bana son komawa bane sai dai yanzu irin kallon da mutanen wajen sasuyi min shine kawai.
Ba wanda zai kalleki dawata manufa yanzu don duk su san ke din ta dabance so suna tsoron yadda zasu tunkare ki ko su wani tsaya a gabab ki balle mu manyane muka san da abinda ya faru din.
Ganin yadda umma tayi yasa nace shike nan zan shiriya gobe na fara fita idan Allah ya kaimu na kara da fadan nagode uncle yace shima ya gode.
Ya juya zuwa part din su ya fita daga part din mu sai naji wani iri a raina yadda na bi umurnin shi kuma yaji dadin hakan ko ba komai na fahinci suna kokarin maida mu wasu na jikin su .
Duk da banyi mamakin hakan ba don irin halarcin da umma tayi masu a cikin yan kwanaki da sanin mu dasu wanda hakan na hango zai zama muna alheri nan gaba watakila
Lokacin mai tsawo na dauka ranan banyi barci ba koda na koma daki ina tunanen yadda zan kasance da abokan aikina idan naje aikin .
Ba komai nake guduba sai sanin da nayi masu akan camfa abu yanzun zasu iya cewa da wani juju nake aiki ko wani kungiya nakeyi nake gane abinda mutum yake ciki.
Washe garin da zan fita gun aikine muke magana da umma kan Almustapha wai na daina abinda nayi mashi ranan don bashi nayiwa hakan ba kamar ita na tozarta a gaban shi ai.
Umma kin manta da warning din da yayi min kan kada na nuna nasan shi ko a wani wajen umma nafa fada maki yadda mukayi dashi lokacin.
Yanzu ma din da wata manufa yake zuwa nan umma sai kiyi hankali kisan yadda zaku zauna dashi ki kama bakin ki dako mu waye a wurin daddy don abinda yazo ya sani ke nan ina fadin hakan na dauki jakkana tare da gyara hijabina nace sai na dawo umma.
Shiru tayi ta bini da ido kawai har nakai kofa na murda zan bude naja na tsaya na juyo ina fadin shi din kin sani mai laifine da yansanda suke nema ruwa a jallo a cikin su harda yaya Abubakar ki kula umma kar zuwan shi ya jawo muna matsala muma a nan.
Kofan na bude na fita ta sake bina da kallo don jikin ta ya mutu da abinda na fada kafin na fita amma idan har hakan gaskiyane dole tayi taka tsatsan a wurin zancen ta yanzu.
Na isa wurin aiki tun a kofa da zan shiga na fara haduwa da wani babban ma,aikacin a wurin yayi wani irin ja baya da sauri ya kauce min tun a nan na fara kaduwa da kalubalin dazan fuskanta a wurin.
Nayi signging kamar yadda kowa keyi ina kokarin zuwa inda nake tsaro naji muryan Abdulhamid a bayana yana fadin ba a nan zanyi aiki yanzu ba .
Sun canza min wuri zan koma wurin accounter muyi aiki tare dasu a a ciki mamaki da kaduwa ne ya kamani lokaci daya najin hakan.
Nasan wurin don haka na nufi wurin da suke na samu suna bakin aikin su muka gaisa suka nuna min wurin zamana kenan zan zauna zaman saka ido a komai har kudin dake shigowa da jama,an dake zirga zirga muna gani a wurin.
Gaskiya na sani matsayina da komai baikai in kai wanan matakin da suka ban a yanzu ba a wurin don kosassun mutane da suka kwarai da aikin suke wanan wurun suna aiki.
Nawa dai saka idone idan suna aikin da sauran abubuwa don haka mai min bayani yana dagawa daga wurin na sauke ajiyan zuciya tare da bin wurin da kallo.
Gashi su kaf duk da manyane amma bai hana suyi wani haba haba dani ba mu biyu ne mata a wurin saidai dayan gaskiya ta girme min ga komai irin wayayyun matan nan ne na lagos masu ji da kansu do haka take zuba wani sallo da yauki a wurin.
Aiki kan ranan anyi an tashi lafiya lokacin tashi yana yi na fito daga wuein bam saba da zama a cikin irin wanan sayin haka ba.
Ina fitowa muka hade da Abdulhamid yake fadin ni yake jira nazo na ya kaini wurin motana dake aje a waje don yasan ban sanma kalar motan ba har lokacin.
Dan yajayin fuskana na sauya kafin nace ya bari watarana zan ganta na san hakan amma yanzu muje kiga motar kawai kafin mu saka ranan da zaku fara koyon motan.
Irin kallon da yan wajen ke min suna kus kus a kaina yasa na fara tsarguwa da hakan zan tafine na bashi amsa na fara tafiya don fita daga wanan wajen.
Ya sake fadin zaki jira mu koma gida a tare don yanzu zan fito mu tafi daga nan sai kiga motan sai kuma ya dan juya ya kalli inda nake kallo yayi dan murmushi yana fadin.
Yana juyawa ya nufi inda suke aiki ya dago jakkar aijin sa ya nufoni muka fita bamu bar wajen ba saida ya nuna min motan dake matsayin nawa yana rufe a wuri sabuwa dal da ita.
Mun kama hanya duk jikina yayi sanyi ga tsarguwa da tunane da ya addabi zuciyana a lokacin ya dan kalleni yana fadin.
Wanan sai ya faru dama suna zancene kan yaushe kikazo nan kika samesu har a kaiki wanan wurin aikin wasu kuma kan abinda ya farune suke shakkan ki a yanzu.
Saidai dole sai kin kara taka tsatsan da kowa mu saman wanan wurin da oga yace a mayar dake yanzu don duk wanda ke wanan wurin sun san kan aikin su sun kuma karanta aikin tun farko keko haye kikayi.
Don haka ki kula ki sa ido dama ina zargin don hakan oga yasa akaiki wanan wurin ki aiki dasu don abubuwan da ake masa a wanan wurin ba kadan bane wallahi.
Zaki canza yanzu dole zaki zama big girl a cikin dubu komai har dabiun ki dole ya kara canzawa a yanzu don hakane ma ya karasa ya bayar da wanan motan.
Godiya nayi mai bayan hakan ban samu bakin kara furta mashi komai ba har muka kai gida inda muka samu su umma a waje tare da matar shi suna muna sannu da dawowa.
Na tsaya mun gaisa dasu kafin na shiga ciki itama matar muniya tashi tayi tabishi zuwa nasu part din suka bar umma tana hada kaya zata rufe shagon don yamma yayi a lokaci.
Ranan ban samu sukuni ba don ni abin kamar a mafaki nake ganin shi lokacin wai yau nice a wanan matsayin anya kuwa zan iya kuwa.

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , ,


WwwANA DARA GA, , , , , , , , ,

4️⃣2️⃣ BY, , , , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL, ADL, , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL DON ALLAH YAR UWA KI BIYA KAFIN KI KARANTA NA SAUKE HAKKIN RASHIN SANI A GAREKI, , , , ,

Akwana biyun da nake aiki a wanan wurin baifi sati biyu da fara aikin ba duk da ba fulltime nake zuwa ba sai yamma idan na dawo daga school in taso goma dare sai kuma gobe idan Allah ya kaimu zan fito.
Amma hakan bai hana jikina canzawa ba don nayi wani itrn kyau na murje haskena na boye ya kara fitowa yanayina kanshi ga baki daya ya sauya a yanzu.
Dole ina gilma mutane su bini da ido ga uniform din official din ya karbi jikina don bujena har kasa yake sai dan hijab da nake dorawa a sama.wanda iya fuskana zaka iya gani.
Zan iya cewa a yanzu kam masha Allah zamana shagon nan don kudi baya katse muna gaskiya don akwai alwas da ake bamu don suturorin aikin mu kawai shine lissafi idan ko wani part na kaya sun shigo da kudin su.
Anyi gulma anyi jininin hakan don ban isa wanan matakin ba tsakani da Allah sai manager yace wanan umurnin oga mai wurin ne dawa dani wanan part din.
Don har kungiya akayi aka samu manager da zancen yayi masu bayanin irin umurnin daya samu daga samane dole sukai hakkuri suka saka ido don ba mai ikon zuwa wurin maishagon koshi manager da yake jin kanshi yana hura hanci idan yana gaban shi dole ya kwanta kasa don biyayya a gareshi.
Bayerabe bai raina abin jifa dan uwan shi, kan dan abu kadan don hakan saida suka gwada sa,ansu gareni sai dai sun makaro don akwai tsarin Allah a tare dani badai mutum ba saidai Allah.
Suit din aikin baki ke jikina na dufaro kamfani a cikin motana a karo na farko da Abdulhamid ya matsa min da hakan dole na koya na fara tuki har yakai ranan na fita school a cikin ta na dawo kuma na shirya zuwa wirin aiki duk a cikin motan.
Umma kan tana jin dadin hakan ganin irin baiwan da Allah yayiwa yar ta irin wanda bamu taba zaton samun shi ba a rayuwa .
Yau gashi Allah ya tarfawa garin mu nono Allah ya gwada mata yar ta a wanan matsayin da bata taba zato a garemu mu ba rayuwa ke nan inda ranka baka debe tsamani a wurin ubangiji.
Na fito na kulle motar kamar yadda Abdulhamid yayi warning dina dayi akan in kula in dinga rufe kofa idan na fita daga ciki zan shiga wani wajen.
Abinda nayi mafalki da darene na fara cin karo dashi duk yana cikin alamomin iskana zanga abu a mafalki washe gari kuma sai ingashi zahiri.
Nasan akwai masu wanan baiwan da yawa a cikin al,umma duk alamane na farfarun mabiya ga mutum da wuya aiwa irin su asiri ya kama mutum irin masu wanan yanayin.
Funke ne tsaye kamar dama ni take jira ina shiga sai gata da fara,anta ta nufoni tana washe min baki tare da fadin hello miss Sahiba.
Na dan ce hi ina tafiya take fadin you about to let todaya sai kuma ta miko min hannu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login