Showing 303001 words to 306000 words out of 382072 words
yaran sunyi tunanen irin haka ba ai da bata san yadda zasuyi a rayuwan su duk da modibbo na iya taimaka masu sosai tun ranan da mijin nasu ya tafi.
Saidai duba ga yanayi da kuma yawan su ba lalai bane komai ya wadatace su a yanzu yadda suke so don dole kudin da yake bata tayi wani lalura dashi ai.
Gashi kamar yadda sukayo mata sayayya haka suka dan kwatanta suka sayowa hjy karima da yaranta itama suka kai mata.
A zaton mommy din hjy karima ba zata karba sai gashi sun dawo suna fada mata cewa ta karba a cikin jin dadi kuma har da godiya ga hakan da sukai mata.
Da alama kuma sun bata kudi duk da basu fada mata hakan ba amma tunda suka iya aje mata kudi itama tasan zasu kwatanta hakan ga abokiyar zaman nata.
Ashe ko wani mutum da Allah ya hadaka dashi yana da ranan shi a duniyan nan yau itace ta sanadin Sahiba alheri ya shigo mata ya part din ta haka ta juya tana kallon kayan dake gaban ta a cikin babban leda guda hudu wanda sayayyan Faiza yafi yawa daga ciki.
Sahiba yarinya ta kwaso halin mahaifin ta ke nan da halarci za a ce bata fahinci irin rikon da nake mata a zuciyana ba ?
Wayan tane yai kara ta dan juya a kasalance tana duban wayan da wanda ke kiranta a lokaci guda sunan hjy harira ta gani da hjy Hari ta mika hannu ta dauki wayan tana karawa a kunnen ta.
Gaisawa sukayi tare da jajanta zancen rashin dawowan daddy cikin su har tsawon mako biyun nan kafin hjy hari din a bangarenta tace wai kinsan me tace sai kin fada.
Yarinyar nan Sahiba fa ina ganin ranan duk abinda muke fadi a kunnen tane saida ta gama sauraren mu tayi sallama ta shigo gidan ku.
Meyasa kikace haka hjy hari ta fada tana gyara zaman ta tace bari kedai sako ta bani ta wurin Alh cewa ya tambayani abinda na fasa kanta da the boy ranan a gidan ku ?
Ita sahiban ta fadi hakan da bakin ta hjy hari ta amsa da wallahi abinda ya fada min ke nan yau da safen nan don gaba daya yaron nan yaki daukan wayan mu sam tun ranan daya bar kasan nan.
Shine shi Alh yace yasan abinda zaiyi nasan ya kira layin ita sahiban ne sukai magana kan shi boy din ta nuna masa hakan.
Idan ko har haka wallahi abinda ake fadi kan yarinyar nan na shu,imanci gaskiyace hjy hari wai kode da gaskene ta mugun kungiyan mayu ne irin na kudu bamu sani ba ?
Yarinya kamar aljana kowa yasata a gaba sai taga bayan shi hjy hari tace aina gani don ni abin ya ban tsoro sosai wallahi.
Wai mema muka fada a ranan game da itane wai don ni har na mata da anyi wanan zancen shi nake son tunawa a yanzu ?
Ba wani abu bane illa man ta kara tuna mata abinda kowa ya fada game da sahiba sai kuma suka koma kame kame a tsakanin su.
Bayan na gama shiri na na juya zan filo wurin umma wayan ta sake daukan kara na juyo zuwa inda take na dauka Sir oga Shaaban ne a layin lokacin.
Sai lokacin na tuna da yace zai kirani da kuma zancen motan dana bari da sauri nayi receiving din wayan karya katse.
Muryan shi naji a dan sanyaye yana mun sallama na amsa tare da fara gaidashi ya amsa har lokacin muryan shi yana a yadda najita da farko.
Bayan mun gaisa dan shiru ya gitta a lokacin kafin yace dani naso nazo da kaina saidai hakan bai samu ba don nazo family house din mune da yamman nan.
Ya zancen maganan mu ya tsaya dake don ina son yin aure a cikin dan kwanakin nan kada koda yake wanan ba zancen yi a cikin waya bane zanzo har gida in sameki muyi shi don aure nake son yi dake Sahiba.
Nervetheles motan ki na a waje yanzun nan a kofan gidan ku idan kin fito zaki gani zan saka subada key a hannun Abdul.
Ok nace a cikin wani yanayin dana shiga saboda zancen daya gama yi yanzu daya zo min a bazata don sam ban taba tsanmanin irin wanan maganan ba a bakin shi.
Wai dama da gaske sir Shaaban yakeyi ne da wasan da muka hadawa mommy shi a can kasan da mukaje komu ita din ta dauka kusan gaskiyane zance.
To wai ko a kanshine yanzu yake son juye abin ya zama gaskiya a idon jama, a ko kuma wani abin ne ya sashi haka gareni.
Don sam ban taba jin wani mahalunki da namiji a cikin raina da sunan so ba har wanan rana ta yaya zancen aure har mutum biyu zaizo min a rana daya kusan lokaci guda kuma.
Fitan da banyi ba ke nan zuwa wirin umma na dinga jin bacin rai a zuciyana dole na samu wuri na kwanta na share zancen ga baki daya don ina son natsuwa.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA , , , , , , , ,
9️⃣1️⃣BY, , , , , , , , , , , ,
ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL BATIN , , , , , , , , , ,
ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257
ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋
Affuwan yan uwa kwana biyu bakujini ba wallahi ba laifina bane matsala wutan neper ne da muka samu har tsawon kwana hudu dan Allah ai min affuwan yan uwa.
Ina zaune sakon ya Abubakar ya shigo min na duba naga lambane da sunan maishi na dade ina maimaita sunan a raina kafin na aje wayan don nasan a lokacin dare can a kasan da mai layin wayan yake yanzu.
Don akwai wanda zan iya samun shi a nan idan yana Nigeria saidai ban gwada kiran wanan layin ba tunda yace baya kasan yanzu yana kasan waje.
Washegari kan kona ce ina da karfin gwiwa a tare dani nasan karya na fada don bana jin wani lakka a tare dani har yakai umma ta fahinci hakan a gareni .
Take tambayana abinda ya sameni nace nima haka na tashi ina jin raina yana baci sosai a ranan gashi kuma dama na boye mata zancen wayoyin kowa da nayi jiyan don fada mata zai iya saka umma tace zata ban wani shawara dagane da hakan.
Kallona umma tayi ta sake fadin anya kuwa ba abinda ke damun ki ga haka don yanayin ki gaba daya ya nuna kina cikin damuwa gaskiya.
In kuma wacan zancen ne kika saka a ranki haka ai gara ki fitar da rai zaifi don su yanzu suke fuskantar nasu hukuncin abinda suka shuka din.
Ba zancen su bane a raina kawai dai hakan na kwanta na tashi ina zama lokaci guda nake fadin hakan kafin na tambayi umma Ammar ko ya fitane lokacin ?
Ta dan dago tana fadin koya fita bai wuce ya shiga part din Abdul bane don yau ba school ake zuwa ba balle ya fita haka da safen nan.
Bata rufe baki ba ya turo kofan ya shigo falon mu nan ya fara min ina kwana na amsa a kasalance yake fadin jiya ban fito ba mun yi hira da dare lafiya nake kuwa ?
Nace kalau jin suna yawan tambayana hakan yasa nayi kokarin nakai kwance a daidai lokacin da wayana ya dauki kara kira na shigo min a lokacin ke nan.
Hannu na mika daga kwancen ina gyara kwanciya na dauki wayan na kara a kunne na ina fadin morning brother jin haka yasa Ammar ya matso kusa dani.
Bayan mun gaisa ya tambayeni gida nace suna lafiya lokacin Ammar yace na bashi waya zaiyi magana dashi shi kuma din yana tambayana yadda mukayi da mutumin da alama zancen tsare daddy din yana damun rayuwan shi sosai a lokacin.
Zankirshi ai na bashi amsa tare da fadin na bari time yayi daidaine da yadda nake son na kirashi kada muyi mai girshi.
Ok kawai ya amsa min dashi nan ammar ya cabe wayan ya mike zuwa waje suna magana da bansan kona maye ba a lokacin.
Saida suka gama magana da Ammar din kafin ya dawo min da wayan hannuna na karba naci gaba da magana yake fadin in ba Ammar kudi kafin yazo yayi registration din football team yake son shiga.
Hararan inda Ammar yake nayi ina fadin shi da bai faye lafiya ba zaije shiga wasan kwallon kafa a yanzu.
Nan dai ya din ya kara min magana na amsa da zan bashi nayi dan mamakin abinda ya hana ya turo maahi din ya amma kuma sai dan tunane yazo min lokaci guda na kodai ya dan shiga matsalane rashin daddy din nan na dan lokaci sai kuma shi ya Abubakar din naji tausayin sa sosai kan hakan.
Bayan gama wayan mu na dannawa wanan layin kira har sai dayayi ta ringing ya kusa katsewa aka daga a cikin wani muryan maza mai amon wani sauti dake kada zuciyan ya mace lokaci guda.
Hellow2 yake fadi daga ban garena na amsa nima da kya kafin nace i am Sahibat from lagos calling now.
I know miss sahiba where d you get my number nace daga wani na sama kafin na juye zancen da fadin ya kake ya family din ka.
Well, anyway duk muna lafiya nagode ya fada a gurguje kafin yake fadin ya mahaifiyar mu da dan uwana nan ma na bashi amsa da suna lafiya.
Sai dan shiru ya biyo baya kafin yace dani anything else miss sahiba na nisa kadan tare da fadin nothing much dama akan case din su yan uwan mahaifina dakasa aka tsare a Abuja yasa na kiraka yanzu.
I know saboda shi kika kirani din don idan bashi ba ba zaki kirani don mu gaisa ba ai ina da labarin cewa wanan dan iskan yaron yana neman layina ninace a bashi ai.
Amma ban dauka take zaibi yai amfani da layin ba na dauka shida kanshine zai kirani kan barawon mahaifin shi da baida imani idanuna na dan runtse don jin zagin da yakewa iyayyena din da a yanzu su nake gani a matsayin iyayyena a duniya kaf.
Enough mr mukhatar wanan matsalan mu ya shafa family din daddy mu bakai ba banga dalilin da yanzu zaka saka kanka a cikin family issue din mu ba.
Dan murmushi ya sake kafin yace good ashe kuna da family yanzu har kin sanda dasu suma sun san dake da kike ikirari a kansu.
Amma suka wullakantaku suka barku a cikin duniya kuna yawo ba wanda ya tausaya maku sai yanzun ne da sukaga bayi suke son ku har kike ganin su a yan uwanku yanzu ?
Good idan wanan ne ai basu kade bane da irin laifin nan naga wa yanda ma sukeda karfi fiye dasu basuyi yunkurin neman mu ba sai wanan lokacin.
And beside mu musulmaine musan cewa bawa bai wuce kaddaran ubangijin shi dan haka mun yarda da wanan a yanzu munyi imani da hakan.
A takaice dai na gane kamar neman jin dadin yan uwa a yanzu ya rufe maki idanu har kina ganin kowa mai laifine a wajen ki don kawai , , , ,
Look mr ban kiraka don dogon zance ba a yanzu kawai kayi abinda ya dace kasa a sako masu mutanen su final mu mun barsu ga Allah understand na kashe wayan.
Duk da umma bata jin turanci amma ta fahinci ba maganan dadin rai mukeyi da sunan wanda taji nakira din wanda tun lokacin ta dago kai ta mayar da hankali garemu.
Meya hadaki dashi koba mukhatar din maiduguri bane kuke waya dashi yanzu na gyada kai alaman eh shidin daine .
Maimaita tambayan ta gareni tayi ta sake jefo min tambayan da tayi min da farko meya hadaki dashi yanzu kuma ?
Akan case din su daddy daine ya Abubakar ya matsa sai nayi magana dashi don a san abinyi don hankalinsu a tashe yake nan dai na fada mata yadda mukayi dashi din a cikin yare yadda zata gane.
Wanda tun kan na kai karshe nake ganin wani irin kallo a fuskan umma din da take jefo min na takaici da jin zafin abinda nake fada mata din.
Yanzun Sahiba kinga kin kyauta ke nan yadda kike kokarin watsa mai kasa a ido haka kan kokarin da yakeyi don mu ?
No umma idan ba hakan nayi maiba a yanzu ba zai dauki maganan da muhinmanci ba sosai don kinga ya Abubakar a yadda ya daukemu bai dace muki nuna mashi goyon bayan hakan ba.
Dan shiru tayi kamar tana nazarin zancen nawa kafin tace nasan da hakan amma shima bai kamata ace kin masa magana haka tsatsaye ba a yanzu.
Shiru nayi don an riga an gama ko yanzu saura naga ranshi zai baci ya fitar da hannun shi a case din ko kuwa don yadda naji ya kira daddy da macuci yana da wuya idan bai saka anyi masu wullakanci ba fiye da yadda bamu zata ba ma.
Shiru falon yayi kowa da abinda zuciyar shi ke raya masa lokacin kafin wayana ya dauki kara lokaci guda banyi saurin dubawa ba sai kusan ya katse na dauka ya Abubakar din ne ya kara kira wanan karon muryan shi da rauni yake magana wanan karon.
Sahiba wanan guy din ya kirani kece kika bashi layina nace bani bace dama ya fada min yasan kana neman layinshi shi yace a baka.
A zaton shi kaine ka turoni nayi masa magana sai naji ya Abubakar din ya dan sake murmushi kafin yace dani yace zai saka a daure ga baki dayan mu idan bamu fitar da baki cikin wanan zancen ba a yanzu.
Ko muka kara matsa maku kuka kirashi zaici muna mutunci fiye da zaton mu kawai dai shike nan yanzu ai ku barshi yayi abinda zaiyi a yanzu din.
Kada ki kara kiranshi a kan zancen ki barshi tunda har yake zargin mune muka turoki wai kici masa mutunci muna ganin idan munyi hakan zamuyi nasara kanshi don baida karfi kome a cikin zancen ko ?
To mu sani ba wani barazana da yanzu zai dakatar dashi kan matakin da yake shirin dauka ku kyaleshi shida bakin shi zai furta ya janye akan zancen.
Ok kawai ya iya ce min lokacin naji ya kashe wayan don wani murya dayazo wurin shi suna magana tunda na kwanta na juya ban kara magana da kowa ba don raina daya baci da maganganun dayayi din gun su yaya.
Kai duniya bata da tabbas abinda baffah hamza ya fada ke nan kafin ya kai zaune yaci gaba da fadin dama na fada maku ai da wuya yadda mukayi da yarinyar nan ta canza magana kuma yanzu.
Eh yanzun dai ai gara da mukaji daga bakin ta kaga mun fitar da zargin komai nasu a zuciyan mu, dama ai nasan Sahiba ba zata fada mai komai ba.
Ya dai yine kawai yaji idan mun tursasatane kan haka kawai kowa ya kyaleshi yanzu a zuba mai ido.
Ayi hakan mu dai dan saurara mu gani nan da dan wani lokaci kafin mu kara tuntubanshi da kan mu wanan karon.
Da wanan shawaran har suka isa Abuja da yanzu zuwa abuja ya kamasu a cikin mota don dole ya Abubakar da bai saba da wanan harkan tafiya da mota ba ya kowa don dole.
Saidai duk yadda sukayi don a bari suga su daddy din sun kasa ganin su don tausararan matakan da aka dauka a kansu.
Wanan yasa dole suka juyo zuwa gida duk rayukan su a baci zuwa wanan lokacin sun saduda da cewa lamarin a yanzu yafi karfin su.
Wanan dawowan ya kara tayar da hankalin kowa a family din mu kowa da irin abinda yake fada yanzu kan zancen wasu suce aima har an sa ranan kashesu.
Wasu kuma suna fadin cewa a a ai yanzune ma za,a fara sharia dasu don wani cargo na kayan zinare da suka dulmuye a tsakanin su na dan uwan nasu da suka kashe.
Hakana dai wanan zancen yayi ta yawo a tsakanin ba wanda ke fadan daidai da abinda ya faru dasu don ko wanda suka tafi don ganin su Abujan ba zasuce ga halin da suke ciki ba.
A bangarena kuma dai duk da naso na kyale zancen na kasa hakan ranan da faiza ta kira wayana tana kuka take fada min wai ashe su daddy ance rateyesu za ayi ?
Naji wani iri a lokacin amma tausayinta yasa na daure nake fadin ba gaskiya