Showing 234001 words to 237000 words out of 382072 words

Chapter 79 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28341

mune kayan irin kallon da yaiwa kayan lokacin kafin ya nisa yace aikin banza ke nan har inma gaskiyane kowan ku nan ai yasan Sambo baida da namiji ko ?
Alh ba wanan zancen a yanzu kamata yayi mu fara sanin waye wanan yarinyar wai kuma a ina take zaune amma kafin nan dole muga Ali dcp muji komai.
Kuna bani mamaki wallahi matar nan da yarta fa wurin malamai bakwai sun sheda muna sun mutu kuma malaman nan ba wai hadin baki bane sukayi tunda ba wanda yasan wani a cikin su kuna nufin hakan karyane ke nan.
Saidai dama idan ya zauna da watace acan daban irin zaman bariki tunda kunce yarinyar kamar kabilace ai haka yake don gaskiya shiganta kamar na kabilune nagani buhari din ya fada a sanyaye kafin ya fada cikin tunane.
Falon ya kara shiru na tsawon lokaci karan wayan Alh sani ne yasa kowa ya daga ya kara wayan a kunnen shi yana amsa sallama tare da sauraren bayanin maishi din wanda ya kirashi a lokacin.
Abinda ya fada tun kafa wayan a kunnen yasa su kara mayar da hankalin su wurin Sani din da yake fadin dama nima nayi zargin shi dcp Aliyu din don in bata da alaka dasu tun farko me zaisa har tazo bukin yar su yanzu?
Ya kashe wayan bayan ya gama sauraren na cikin wayan yana fadin kuji a yadda ake fada yanzu wai yarinyar ta zauna a gidan Ali dcp na wani lokaci kafin su koma inda suka fito.
Yanzu kuma wata babbace ake gani ko wani babban mutum a can kudu take aure amma dai za a binciko min ko yar Sambo dince ta asali.
Shirmen banza ke nan shirmen wofi nifa duk wanan zancem a shirme na daukeshi a wurina sam ba zai yuyu ba son wanan rudani da kuke nuwa sai a gane da wata a kasa .
Idan har yar Sambo dinne tazo mana mu kawar da ubantama balle ita me zata iya yi damu yanzu kuma ?
Ina abinda dai kuke tunane ke nan sannan shi Alin har in shiya kulla wani makarkashi na zuwan wanan yar aiko shi bai tsira ba a cikin zancen Alh Nuhu ke wanan maganan rai bace.
Falon yai shiru yaci gaba da fadin yanzu dare yayi koma me ke nan sai a bari har zuwa safe ba sai muga shi Aliyun muji gaskiyan maganan a bakin shi ba.
Kallon shi Buhari yayi don jin abinda ya fada na a gaja dashi Aliyun aji me zai fada game da zancen don su san matakin da zasu dauka.
Karfe biyu saura sai alokacin suka fito kowa ya shiga motar shi ta alfarma da sukazo gidan dashi zuwa gidajen su ciki da zargi da tunanen wani ne keson ya kulla masu shiri kaqai da hakan.
Yadan dade a zaune yana tunane kafin ya mike zuwa wani daki dake part din nasa ya rufo kofa ya fara abinda yake sonyi a dakin lokacin


ZAINAB IDRIS MAKAWA


ANA DARA GA , , , , , , , ,

6️⃣9️⃣BY, , , , , , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL WALAIE, , , , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257

ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋

Bayan mun firfito daga motan na tsaya nayi masu godiya sosai tare da basu abin rabo ba tare da sun san abinda ke faru ba don Abdul ya fake ga fadin ba,a son asan inda nake zaune yasa zamu nuna hakan a wurin.
Kowa ya nufi bangaren shi kafin na juya muka shiga ciki nida Amar muka rufo gida su umma suna falo yaran duk sunyi barci saman jikin ta muka samu wuri muka zauna har lokacin sai sannu da zuwa take muna.
Ammar ne ya fara bata labari yana tambayan ta da umman mu duk taron nan ana nufin su din yan uwan mune wai ?
Haba dai na fada daga inda nake zaune ina cire sarkan wuyana don na riga na cire dan kunne ko alokacin .
Nace duk wanda kaga na gayar sune yan uwan mu na jini saura kuma abokan arzikine da suka zo tayasu murna kafin na juyo ina fadin amma umma nayi mamaki da daddy ya aura wa karamar yarinya kamar baby wanan mashayin haka ?
Jam ta fada mashayi kuma nace kwarai umma don har ta hudashi ma zaki gane hakan a jikin shi kinsan ni bana shiri da maishan wanan abin sam don haka naganeshi da sauri.
Allah ya kyauta ta fada a karshe muka amsa da amin sai tace yanzu dai saura mu saurari abinda zai biyo baya ke nan don nasan dole su nememu yanzu kan ruwa a jallo.
Zasu nema sosai ma amma ba yanzun ba sai an daura aure gobe wanan zance zaiyi boosting ga kowa don zasu hadu a wurin ne za a fara wanan maganan daya shafemu din don kowa yanzu haka yana cikin wasiwasin ne a zuciyar shi kan mu.
Waya ta na mika hannu na dauko daga cikin jakata na kunna sako suka fara shigo min da sauri na dauko na duba ina karanta sakon da nagani daga oga sha,aban ce yasa na bude sakon da sauri ina karantawa.
Katin gaiyatane na bukin kammala karatun kanwarshi tilo daya da yake da ita wand za ayi a Oxford.
Wanan kan ai sai manya zuwan shi na fada a fili meke nan fa umma ta tambayeni tana kallona jin abinda nake fadi a loka nan nake fada mata abinda sakon ya kumsa.
Shiru tayi kafin tace dani au a can ke nan zasuyi taron nayi mata bayani dalla dalla yadda zata fahinta a daidai lokacin ne kuma wayana ya dauki kara lokaci guda.
Na duba ya Abubakar ne a layin yana gab da katsewa nadaga da sallama ya amsa yana jefo min tambaya kuna inane nace gida sai naji ya sake wani nauyayyan ajiyan zuciya.
Kafin yace OKey kawai ya amsa dashi yayi shiru sai kuma naji yace ki kula don kin tayar da hankalin manya sosai a wurin nan yanzu haka nemaku suke ruwa a jallo.
Karo na farko da zaice yaji farin cikina har nayi dariya a fili haka yadda yaji a lokacin tun bayan dawowan shi garemu kafin nace sai su matsa idan suna son ganoni a yanzu ai da safe zan shigo gidan ki gaida umma.
Don sam baiyi zancen yaran shi koda yake yadda yake magana yanayin ya nuna cewa shima dai hankalin shi a tashe yake a lokacin.
Daddy tun safe ya fita daga gidan gidan amin sa ya nufa kai tsaye wanan fitan shine sauki a gare shi ranan don bai dawo ba sai gab da daurin aure Abubakar da suke waya dashine ya gudanar da komai har aka gama tsara komai yadda suke so.
Hankali kan ba a kwance ba don duk taron yan uwa da zaka gani a gidan bukin suyi gungu gungu kowa da abinda yake fada inda a nan hjy karima take tsuntar wani zance ga jama, a.
Hakan sai ya lankwasar da ita ga gagarumin shirin da tayi don taba mommy da diyan ta takaici a ranan don itama hankalinta bai kwanta ba ai a wurin.
Saidai duk da hakan yan uwa da abokanta sunyi dan kide kide da raye raye wanda sukasa niyar yi don turawa mommy haushi da yayan ta.
An daura aure an tashi lafiya baki suna watsewa ne baffan su nan biyu suka kira taron gagawa a tsakanin su yan family din.
Bayan kusan duk wanda aka gaiyata sun isone sai yan kalilan ne basu wurin aka fara da addua kafin ya fara magana da fadin.
Tau sallamu Alaikum jama, a duk da nasan wasun ku da dama nan sun san makasudin wanan kira na gagawa da ya hadamu nan wasu kuma basu sani ba dai.
Kamar kullun kusan sai wani abu na muhinmin ya farune na musanman muke wanan haduwan irin haka a nan .
Daidai lokacin Alh Nuhu ya tura hannu a cikin Aljihun shi na riga ya ciro kwankwan shaken shi ya balle ya diba ya tura a duka hancin shi biyu yana turmuzawa da kyau don ya dauki caji.
Jiya zance ko shekaran jiya baiyanan wata yarinya da wasu a nan cikin ku suka kawo muna labari tazo da barazana a gare mu cewa ita din da kanin ta yaya ne ga dan mu kuma dan uwanku marigayi sambo daya rasu a shekarun baya daya shude.
Nan aka fara dan hayani a falon tsohon lokaci guda kowa da abinda yake fadi a lokacin don wanan bakon lamarin da akazo dashi din.
Ko tana da hujjan fadan hakan ko baiyanar da kanta da take kokarin yi yanzu a gaban mu idan tana da hujjan hakan sai tazo muna dashi don mu gamsu da bayanin ta Alh Nuhu ya fada a kausashe.
Yana bin kowa dake falon da kallo idanun sa sun kada sunyi ja sosai a lokacin kowa yai shiru a falon yana sauraren shi don bai magana wani nayi ko don dole a kyaleshi ya gama.
Yaci gaba da fadin wanan zancen banza da wofine ai ta bijiro muna yanzu wai ita din yace ga dan uwan mu a sanin nan kowa yasan Sambo ai ya dayace gareshi sai matar daya bari daya.
Ita kuma akarshe tabi dare ta gudu a ranan da abin ya faru yasa muka fara zargin ko itace ta kashe shima ta gudu kuma.
A iya bincke mu gano inda take har malamai bakwai mun gani kan hakan wurare daban daban suna sheda muna duhu suke gani ma,ana dai bata duniyan nan daga ita har yarta kuwa.
Don me yanzu wata yarinyar banza can yar duniya ga yadda akace ai wanan din kamar kabilace ma ita to a waje ya haife ta ko me bamu sani ba ?
Wanan kuma ka fadi ba daidai ba yaya don ba zamuyi saurin sheganta yar nan a yanzu sai idan mun tabbatar da hakan baffa Hamza ya fada wani mai ra,ayin rikau ne shi ba ruwan shi da kowa a cikin su.
Wani kallon shi Alh Nuhun yayi kafin yace duba Hamza kada kayi kokarin kawo muna zancen da baida hujja a nan ko kadan abinda muka sani shine Sambo dai ya rasu haka kuma iyalin shi duk munsan basu raye a yanzu.
Wanan ba gaskiya bane kan don har in kana tunanen hakan ka daina komai mai iya yuyuwane a yanzu idan yarinyar nan tazo da hujja mai karfi ya tabbata ita din da kanin ta din yayan marigayi din ne ke nan.
Ta kawo hujjan mana ko ta baiyana nan agaban mu idan ta isa ita din tsagerace muna sauraron ta ya sake fada rai bace kowa dai nan yasan mairoce matar sambo yau ina mairo din take.
Zata ko zo har mairo din baffa Abdullahi da tun dazun yake son yin magana yana shakkan abinda zai fada din a wurin sai yanzu Allah ya bashi ikon fadin hakan kowa ya kallo shi.
Kwarai zata zo har mairo din da kuke fadi a yanzu mairo bata mutu ba tana raye don ance kwanakin baya suna cikin harin nan ita da yaran kusan shekaran biyu a nan kaduna gidan dcp zaune.
Meka fada yace kwarai yau da safen nan Addah ke fada min komai don tayi shirune da bakinta bisa bin umurnin shirin mijinta da yace kada ta nuna kosu din waye a gare su taja bakin ta tayi shiru bata fada ba.
Ta fada muna duk yadda a yanzu kuke tsamanin wasan ya wuce nan sin ashe mairo ta tafi da ciki a jikin ta wanan cikin shine wanan yaron da kuke tantama akan shi.
Ita Addah ta fada maka hakan yace kwarai da gaske kuwa bani kadai ba dani da Hamza da sani da Hari da Asiya yau da safen nan a falon ta.
Lalai kuwa zamu zauna da Addah kai zancen nan fa yafi shafuwan mu a nan nake gani baku kadai ne zaku nuna damuwan ku a kai ba kawai.
Amma dai muna da hakkin cikin wanan zancen kuma kamar yadda kowan mu nan idan ya mutu ya bar baya kowa zaiyi hakki a kai don kula da abinda dan uwa ya bari hamza din da yake karami cikin su ya fada.
Kwarai kuwa baffa Buhari ya fada wanan maganan haka shike hamza don haka yanzu ya kamata ace mun samo ita mairo da yaran nata don samun gamsashen sheda a wurin ita mairon.
Abinda nagani ke nan baffa Abdullahi ya fada don zancen manya sunyi shiru sun bar matasan kannen su suna magana a lokacin.
Samun su yanzu shine shawara na gaba baffa hamza ya fada sai Abdullahi yace baida wani wahala don wanan yaron moddibo da dan wajen hari sun san da ida suke zaune a can ikko.
Ikko fa Alh Nuhu ya fada a cikin mamaki yace kwarai a ikko suke zaune ashe duk wanan dadewan haka tana ikko zaune ashe.
Amma indai hakane Ali dcp ya munafunce mu ai ba haka mukayi dashi ba ya fada a cikin subutan baki baffa hamza ne ya dawo mai da tunanen shi yace yaya kukayi dashi muji ?
Wani banzan kallo ya jefawa kanin nasa yace baka isa ba kuma in fada maka don kai hamza da nake gani nake hango zallan bakin ciki a idon ka baka isa ka titsiyene nan in fada maka ba yanzu.
Dan dariya hamza din da suke daki daya da hjy Addah ya kwashe dashi don shi lectura ne a A b u zaria a lokacin boko ya gama ratsashi ko sosai shi yasan abinda yakeyi sosai.
Maganan shi sam baiyi wa wasun su dadi ba amma kuma manyan sun tsaya ga maganan shi hakan yasa Alh nuhu rufe kowa da fada har yana fadin shine dai babba a nasu zauren don haka ko anki anso dole abi anbinda ya fada don haka bai yarda da zancen wai mairo ta dawo da iyalin ta ba ai dama ba wanda ya koreta don kawai tana zargin kanta ai tagudu ta shiga duniya.
Jin hakan matasan daga cikin su suka mike suna fadin maganan shi zancen banza ne shima ai ina ya taba jin haka idan diyan cikan kane zakace mu wofintar dasu a cikin duniya ne ?
Ranan dai an fara kaiwa inda ba a son akai don dama matasan hudu sun dade suna jin zafin irin cin zarafin da yakeyi a cikin Family.
Ranan kan gaskiya an tashi wanan taron ana kaiwa kaiwa abinda bai taba faru dashi ba ya fadi har wasu tsageran kanansa suna mayar mashi da amsa bako manyansu ba a cikin su.
Haka sukayi wanan satin a cikin rigima sai kus kus sukeyi a tsakanin ba wanda ya isa ya fito fili ya fadi don basu samu kan daddy da iyalan shi ba balle suji wani abu a wurin su suna fama da sallaman bakin su da sukazo buki lokacin.
Safiyan litini kuma a wurin aiki tun safe bello yana get din ma, aikatan dake shigowa yana sane dasu idan zaka shiga sai kayi signed idan sunan ka na cikin wa yan da aka dakatar ya baka takardan dakatarwa ba bayanin komai sai idan kaje ka karantane zakaga abinda aka rubuta ma a ciki.
Karfe tara saiga Oga Bala ya shigotun daga nisa yake mamakin ganin an rufe get din ma,aikatan yau haka ya karaso har get din zai hau maigadin da fada yaga bakon fuskane a ranan don bai sanshi bama kwata kwata a cikin ma,aikatan nasu.
Malam ka fito ka duba can indan an yarda ka shiga sai a bude ma ka shiga mutumin ya fada cikin rashin ko inkula da abinda ya fada.
Fitowa yayi daga motan yazo yana kokarin bude get din a cikin fada sai ga wasu majiya karfi sun mike mutum biyar dole yaja da baya yana fadin meye hakan wai ?
Meke faruwane a cikin nan yau ne ni zaku hana shiga ciki ubanwa yasamu wanan aikin duk garin nan ?
Yallabai barka da zuwa aka fada daga gefen shi Bello ya kuma shedashi wurin barka da kwana rankai dade bai tsaya amsawa bellon ba yake fadin kai me ke faruwane wirin nan har banzan mutanen can suna min barazana da shiga ciki.
Rankaidade ba laifin su bane umurnin hakan aka bayar daga sama cewa duk wanda sunan shi bai fito a wanan takardan ba kada yashiga ma,aikatan .
Me ake nufi da hakan ya tambayi bello din a wani irin yanayi na bacin rai rankai dade gadai takardan ka karanta zaifi kyau nake gani.
Zuwan chairman ne ya hana


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login