Showing 198001 words to 201000 words out of 382072 words

Chapter 67 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28371

files din da kike gani a gabana ya kumshi duk wani bayanin da muke nema.
Saidai nayi mamakin ganun haka saboda wasu fliles din da suka boye suna zaton wa yan nan ne a wurin sauri ikon Allah gagara musali ta fada .
Kafin ta nisa tace baida alhakin sune shiya sosu da alheri sun nuna masa halin yan Adam yanzu gashi abinda basu zata ba yana shirin faruwa dasu kuma.
Bawa akwaishi da matuwa sosai akan dukiya sai ya shagala ya manta da komai balle dukiyan daba nakaba yau ina laifin wanda ya jawoka cin arziki a karkashin shi ?
Nisawa nayi ina dagowa tare da aje takardin a gefen wurin sallah na nasan don ban fito naci abinci bane yakai har umma ta biyoni dakina dan tun zuwan mu bata leka dakin da nake zaune a cikin sa ba sai ranan.
Tare muka fito zuwa falon nako samu an jera abinci saman dan karamin dining table din dake aje a gefen falon Amar yana kwance yana kwashe rubutu a littafi shi yana jin motsin mu yake gaidani na amsa na zauna umma ta zauna a gefena.
Muka fara cin abinci cibi uku nayi na wani irin zabura na mike tsaye da sauri kamar an tsikareni lafiya umma ta tambaya banyi magana ba nasa kai na fita daga falon kai tsaye na nufi hanyar get din shigowa haraban gidajen namu.
Ganin haka hankalin umma ya tashi sosai Abudulhamid ta kira hankali tashe tana fada mashi ya fito daga shi sai dan gajeren wandon daya saka a jikin shi na zaman gida.
Ina kaiwa kofan na tsaya na dan lokaci kafin na duka na dauki duwatsu kwara uku nayi addu,a na jefa a ta wajen get din duk kusurwan wurin hudu nayi haka na juyo na dawo part din mu duk su umma da Adnan da Abdul suna bina a baya.
Daidai tsakiyan gidajen naja na tsaya na dade a wurin ina dan waige waige kafin nayi tako biyu na tsugunna a wurin na dade kamar ina ginan wani abu kafin na mayar da kasan na rufe.
Tare muka koma ciki dasu a lokacin ina shiga falon na fada kan kujera basu ankara ba sai ji sukayi ina barci cikin abinda baifi mintuna biyar ba da shigowan mu.
Abdul ne ya kallesu yana fadin nasan ba ita bace dama akwai matsalan da suka hango sukai wanan abin haka duk yadda akayi.
Ke nan dai tana da sprit a kanta masu karfi Adnan ya tambaya kwarai kuwa ya bashi amsa sun dade a wajen gidan mu suna magana kafin suyi sallama da umma su shige gidajen su don dai suna mazane amma sun dan firgita don basu san meya kawo hakan ba.
Washe gari jumma,a ban iya fita da wuri ba don sun dauka ma bazan fito ba a ranan sun fada da aka tambayeni cewa banjin dadin jikinane.
Abin yai masu dadi sosai da sauri Inusa ya nufi office din manager ya samu malam bala a ciki ana faman kulawa yake fada masu abinda yaji a bakin abokan tafiyana.
Suke fadin mu din dama na wasane an fada mata mu yan iskane da zatayi wa kutse kudi daine munci ba yadda za ayi damu fakat yana wani bude hannayen shi biyu yake magana a cikin isa da izza.
Zubur na mike ganin lokacin a gurguje na fada ban daki nayi wanka na dauro alwala na fito na tayar da sallah.
Shiryawa nayi cikin bakar abaya nagyara tsab zaka dauka balarabiyace ni din na fito na dauki files dina da laptop na shiga motan sai ganina kawai sukayi na shigo wanda yakai gulman banda lafiya ranan shiya kawo masu tsegumin zuwana kuma.
Kallon juna sukayi da mamaki kafin suce ga yar iska shu,uma kada fa yarinyar nan taso juyamuna hankali fa.
Ban zauna ba sai yawatawan da muka kama dasu Adnan bayan inda ya rifto muna jiya na nufa tare dasu ba abinda ya faru da saman rufin din wurin to amma ya akayi cikin ya rusa Adnan ya tambaya.
Wurin na dan kurawa ido na dan lokaci na sauke ajiyan zuciya muka koma ciki bayani na fara yi masu kan abinda nayi nazari kowa ya duba abin yadda ya dace sauran zancen zami barshi sai monday mu karasa nace dasu.
Da biyu nayi hakan don nasan zasuji wanan zaman namu na ranan don haka nake son hanin kullin da zasuyi muna kuma nan gaba.
Motana na nufa don tafiya gida saidai tun kan na kaso inda take in shiga naji gabana yayi wani irin faduwa sosai addua nayi na sa kai na shiga don zuciyana ta ban na shiga kawai .
Hakana tuka zuwa gida ba abinda ya sameni saidai ina fita ban jima ba ake fadin akawo agaji motar na fitar da hayaki a cikin ta.
Aka dai samu aka tsayar da taimakon mazan site din namu abin yabawa kowa mamaki Amar yabi Abdul da Adnan tare da iyalin shi zuwa sallah jumma, a sai ya rage dagani sai umma a gidan ban yarda na kwanta ba don kada sallah ya wuceni.
An sako jumma,a ke nan ya fito ya shiga mota ya dauki waya kira layin umma muna zaune kiran ya shi ya shigo a wayan umma nike kusa don umma na sallah na dauka don ganin shine mai kira.
Haka kawai naji yanzu ya kamata na daina nuna mai komai tunda yace ba laifin shi bane hakan don shima baiso haka din ba da aka kyalemu din.
Sallamu Alaikum na fada ya amsa min tare da fasin so you are at home Sahiba nace eh yaya good afternoon ya amsa da afternoon.
Ya kuke ya mama nace lafiya tana sallah ne yace ok kuna dai lafiya ko kwana biyu ban zo na duba kuba aiki yayi min yawa a nan ina kaduna.
Ayyah yasu Faiza dasu Amira na tambaye shi yace lafiya suke suna tambayan ki sosai da alama shima yaji dadin yadda na sake ranan muna magana dashi din.
Idan mama ta idar zan kira ki gaida Ammar ya fada yana kokarin kashe wayan dake hannun shi din ina fadin umma ta idar amma ya kashe wayan baiji ba.
Umma na idar da sallah take fadin Abubakar ne ko na gyada kai tace ya kirani jiya yana fadin akwai tambayan da yakeson yayi min bansan ko na menene ba dai don bai fada ba tukun.
Mwku yake son tambayan ki kuma na fada shigowan Amar yasa muka bar wanan zancen da mukeyi din yana bamu labarin wai yaga hanyar da muke zuwa school da muna gidan daddy zaune.
Ni dai kallon shi nayi umma ko cewa tayi dashi haba Amar koni bazance ga hanyar da zamubi zuwa gidan daddy daga nan ba don gaba daya garin nan ya juye min ban san a wani barin muke ba.
Dariya abin ya ban nace bamu da wani nisa sosai dasu a nan don muna New GRA ne nan kinga ba nisa sosai dasu ba daga nan.
Wayan tane ya sake daukan kara ya kira ko ta fada ina mika mata wayan dake hannun nawa ta karba bayan tayi receive.
Sun gaisa yake fadin ko kin san filaye nawa Uncle ya bari a duniya kafin ya rasu mama don naga kamar ba wanan case din a cikin case din shi yadda wani makwabcin shi yaba da shedu shekarun da suka wuce.
Shiru umma ta danyi kafin tace ba zance na sani ba gaskiya amma dan littafin da yake rubuta komai na samu daman daukan shi yana wurina kafin na bargida .
Wata kila zaka iya ganin komai a cikin sa da kake so yanzu ban baku bane a baya don ganin zancem bai tashi ba lokaci.
Da kyau mama haka yayi yana nan a hannin ki yanzu haka ko tace yana wurina yanzu haka bana yarda nayi nida dashi ko kadan ai.
Zan shigo lagos wani sati zanzo har gida na karba in duba don Allah a ajeshi da kyau don nasan akwai bayanan da zan iya samu a cikin sa.
Basu gama wayan ba layi ya katse lokaci guda kallon umma din nayi ina fadin bana son su san cewa muna garin nan umma.
Dama saida nayi wanan tunanen hakan zaizo bai samemu a nan din ba kawai a kyaleshi mana idan har ya samu zuwa din bai samemu ba zaiyi zaton mun tafi wani wurine don ba zai taba zaton muna garin nan ba ai saboda Abdul dai yayiwa kanin gargadi kada ya fadawa kowa ga inda muka tafi.
Shiru nayi ina tunane a raina yadda abubuwa ke son tikice muna kuma gana aikin da mukazo yi na gane zamu kwasa dasu sosai inba gyaran Allah ba.
Shi kuma yanzu yaya ya fito da wani zance wai akan matsalan mahaifin da kawai ya share zancem kamar yadda kowa ma ya share har sai an je gaban ubangiji.
Olawede ya kira waya yana min bayani kan sai an buga waya a kawo mai kaya nace ya bari idan kin dawo zan fada maki.
Sai lokacin na nisa ina fadin yaushe ya kira umma wallahi banso ya kai ga kira ba naso na tura kudine a tura masa kaya tun bai nema ba.
Sai kuma zancen aikin nan ya dauke min hankali umma kinga mutanen nan basu tsoron Allah sam wallahi wai yanzu kokari sukeyi su koremu da asiri ko su shafa muna mantuwa mu bar garin nan a rikice.
Yaushe tsoron Allah zai shiga zuciyar mutanene sun Allah ba karya bane wai mutuwan nan fa kullun yita akeyi ana nunawa mutane ishara akan shagala da duniya.
Amma maimakon tsoron Allah ya shiga zuciyoyin yan Adam sai kuma kara dulmiya da son duniya akeyi musanman musulman mu na wanan nahiyar na yanzu.
Waya na dauka na turawa wa kamfani kudi tare da kiran su nayi masu bayanin abubuwan da zasu kawo muna.
Mikewa nayi na kwaso takarduna ina dubawa kafin nayi wani zabura da sauri don ganin sunan wanda ban zata ba a cikin jerin sunan da nike lissafowa a lokaci.
Kafa ma sunan ido nayi na dan lokaci kafin na saci kallon umma inda take zaune na kara mayar da kallona kan sunan ina kallo.
Jikina ne yayi sanyi sosai na kasa aikin da nakeyi din na zurfafa a cikin tunane mai nisa lokaci guda.
Barci na shige da wuri ranan umma tana daukan duk hakan gajiyane a nasu fahintar basu san abinda na gani bane a takardan yasani a cikin damuwa don sunan wanda ban taba zato ko tsamani ba da nagani a cikin wanan jerin sunayen.
Saidai kuma zuciya na taki yarda da hakan cewa shi din ne saidai idan mai kama da sunan shi ne na gani din acikin masu ruwa da tsakin maida kamfanin baya a yanzu.
Sam zuciyar shi bai yarda da abinda yake gani a wayan shi ba don haka washe gari ya dauki wayan ya saita shi ta yadda zai kaishi har inda yake bashi location din wayan umma din.
Ganin inda ya kaishi a GRA din na kaduna ya tsaya yana mamaki hakan kuma signal din yaci gaba da nuna mai green kundunbala yayi ya shiga compound din wurin yana bin ko ina da kallo.
Har inda computer din nasa ya tsaya wuri daya yana dan halbawa ya dago kai ya kalli kofan gidan da kyau mamakine ya kamashi lokaci daya amma cikin karfin hali irin nasa yasa ya fito don tabbatarwa kanshi ganin dalilin kasancewar hakan.
Gyara tsayi yayi tare da dan gyaran kwalan rigan shi nocking din kofan gidan yayi tayi lokaci guda kusan sau uku ba wanda ya bude gidan.
Kallin gidan ya kara yi na dan wani lokaci kafin ya juya ya na kokarin shiga motan shi jin an bude kofon yasashi juyowa ya dan waigo don ganin ko waye ya fito.
Nice tsaye dagani sai dan rigan barci mara hannu har kasa duk dantsen hannuna sun bai yano a waje.
Sai gashin kaina dana daure daga baya yay dan tuntu babu hula a saman kan nawa din.
Sunan shi na dan kira ina fadun sannu da zuwa kayi hakkuri barci mukeyi bamuji nocking din kofan naka ba tun dazun.
Tsaye yayi ya dan kuramin ido na dan lokaci kafin yace wai Sahiba kece din dama kina garin nan bamu da labarin hakan ?
Ehto tafiyan ne dai yazo muna a hakan bawai munzo nan din bane da shiri bare mu fadawa wani zamu zo din .
Bissimillah mana shigo umma na ciki barin tayar maka da ita na fads ina shigewa ciki shikan imanine ya kasheshi a wurin lokaci guda.
Umma na sama a daki na fada mata zuwan shi mamakine kwarai ya kama umma ban tsaya mata wani bayani ba don sallaman shi da mukaji ya shigo falon lokacin .
Haka yasa ta fito daga dakin a cikin hijab din ta mai ruwan siminti har kasa tana mashi sannu da zuwa ya amsa ta nuna mai kujera ya zauna.
Sun gaisa duk umma tana a kunya da ganin shi tunda bata samu fada mai cewa muna kaduna ba ita da bakin ta saida ya gano hakan da kanshi.
Dan shirune ya biyo bayan gaisuwa kafin can ya kawar da shirun da fadin gaskiya mama banji dadin hakan ba ace kuna cikin garin nan banda masaniya saida na,urana ya nuna min hakan ta hanyarshi har nazo nan inda kuke yanzu ?
Bayan munyi waya dake mama koda ka sani ai sanin baida amfani yaya don ba lalai bane bayan kai wani dan uwa ya neme mu a garin nan tunda ba ruwan kowa damu .
Juyowa yayi ya kallo inda nake fitowa ina maganan wanan karon na dora jacket din rigan a sama na daure a tsakiyan kwakwasona .
Ba tsoro ko wani darr dinshi a fuskana lokacin ga wani gogewa da wayewa irin na matan goggagu da ya baiyana a fuskana alaman dai jiya ba yau bane a wurina.
Amma ta yaya yarinyar nan idon ta yai sauri budewa hakane ya tambayi kanshi lokaci daya kuma ya ba kanshi amsa da fadi ba abin mamaki bane kuma ga yarinyar data tashi lagos kuma tayi karatu a cikkn sa ga aiki kuma duk a lokaci daya haka.
Sahiba ni kike fadawa wanan maganan haka na dan kai zaune ina murmushi na kara fadin sorry to say tun jiyan da kuke waya na hana umma ta fada ma hakan.
Don aikin daya kawomune kawai zamuyi mu koma inda mukafi karfi da wayau don haka ba lalai bane sai ka sani.
Dan murmushi bakin ciki ya sake kafin ya dago kai ya dan kalleni yana
fadin, , , , , ,


ZAINAB IDRIS MAKAWA

ANA DARA GA , , , , , , , ,

5️⃣9️⃣BY, , , , , , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL HAKIM, , , , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257

ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋

Don haka kawai naji gara in fada mai hakan don su sanda sanin cewa bawai surin su mukazo ba lokacin namu ne ya kawomu garin.
Masangalin kujera na dafa ina kallon shi kanshi ya dan dukar a kasa kamar yana nazarin abinda na fada mai a lokaci.
A kujara na zauna gami da ciro wayata dake ringing a daidai lokacin dan basarwa nayi har kiran ya katse na dago kai ina fadin .
Wallahi ninace kada umma ta fada ma haka kada mu sakaka a cikin matsala kuma don aikine na yan watani ya kawo mu nan ba wai munzo zama bane nan kaduna kaji dalilin dayasa nace kada umma ta fadawa kowa muna nan.
Abin mamaki ya bashi yadda na zauna nake maganan zakace wata babban mace ce a lokacin.
Kafin ya juya wurin umma din yana tambaya tun yaushe kuks zo garin nan ke nan umma har ban sani ba ?
Kafin umma ta fada mai nace shekaran jiya nan a takaice ya dan kara kallo inda nake saini kaina amsar bata bada ma,ana a gareni ba amma kuma hakan ne na shirya dama tun baizo gidab namu din har idan sun gano muna cikin kaduna.
Kanshi kawai ya girgiza cikin wayancewa don yanayin yadda yaga ina masa a yanzu yace I na Ammar yake ?
Wayata ta fara kara kafin ni ko umma mu iya cewa wani don idon daya zubo min na mamaki komai da nakeyi a yanzu din.
Daga kano suka kirani suna min bayanin irin abinda suka sama a wurin da wullakancin da manager da suka sama yayi masu don bai ko yarda an zauna dashi ba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login