Showing 225001 words to 228000 words out of 382072 words

Chapter 76 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28354

Abdul sun saba idan na dawo su tareni bazan shiga gida ba sai na raba masu dan abinda na tsaya hanya na sawo masu ranan da ban sayo ba kuma kudine zan basu ince suje school dashi da safe.
Yauma shiryawa nayi zamu fita kasancewan weekend ne ranan zamu fita sayayya don washe gari sunday ne yawancin shaguna basu budewa a ranan.
Nida muniyace a gaba ta dauki yar ya Abubakar karaman a jikinta babban kuma rabin jikinta yana akan jikina ina tuka motar .
Wani babban shagon sayar da kaya na tsaya muniya ta kalloni tana mamaki na sake mata murmushi kafin ince zan dan duba abune na juya wurin samarin dake baya su hudu ina fadin banda garaje sun san nan ba wasa yanzu a yankewa mutum hannuwa idan ya taba masu kaya.
Daga cikin motanshi ya kura muna ido sosai har muka fito muka shiga shagon shima fitowa yayi yabi bayan mu zuwa cikin shagon.
Yar banci mukeyi a lokacin yana tsaye yana mamakin ina na samu diya saidai abinda ya tsayar mai da mamakin nasa shine gabnin yarinya tana son zuwa wurin .
Ajiyan zuciya ya sauke ganin uwar yarinyar ta karbi abinta daga hannuna sunyi gaba sai lokacin ya iya motsawa daga inda yake tsaye din.
Kayan yaran nake zabe mata kaina a duke naga hannu ya tabo wani daga bayana yana fadin ki zabi wanan yana da kyau sosai.
Ya sallam na fada a raina ina lumshe idanuna duk da ban juyo ba nasan muryan dake min magana a lokacin don muryan Almustaphane a bayana yake maganan.
Gane hakan baisa na juyo na fuskance shiba naci gaba da abinda nakeyi wurin dubawa karamin yaron muniya kayan sakawan shi.
Sahiba dake nake don nasan kin sheda ko waye a bayan ki ke nan wanan kin juyowan naki da kikayi a yanzu ya nuna min hakan.
Kwarai na shedaka kokai waye saidai bai zama dole gareni ba in nuna nasanka a ko ina na ganka kona ji muryan ka din.
Murmushi mai sauti naji ya sake tare da gyara tsayuwar shi da kyau yana fadin har yanzu zancen haka na cikin zuciyar ki ashe ?
Magana daya zanyi da mutum na rikeshi har mutuwa ta bana mance Alheri hakama bana mance gargadin ko wani zancen danayi da wani.
Ina munyi wanan zancen dake a baya na dauka komai ya wuce a yanzu ai na dago kai na watsa mashi wani irin kallo da dukkan idona.
Murmushi ya sake yana saka hannayen shi cikim aljihun wanson shi dukka biyu yace ba wanan ba me kika zoyi a kaduna yanzu ?
Kwanaki na ganki a by pass sai na dauka bake bace don ban taba zaton cewa kedin bace a kaduna a wanan lokaci daga baya kuma sai banyi mamakin hakan ba don tunawan da nayi cewa kedin dama kin taba zama a nan din.
Me ya kawoki nan ina kuma mama da Ammar suke ban rufe baki ba saiga yaran sun dawo hannayen su dauke da alawan da nace kowa ya zabo a lokacin.
Amar yana ganin shi ya dan so zuwa wurin shi sai kuma ya tsaya yana kallona a cikin dan shakkan hakan a fili.
Zo mana abokina ya fada yana kallon Amar din da murmushi a fuskan shi ya sake mikawa amar din hannu nayi mai alaman ya tafi inda yaken.
Da sauri ya karasa wurin shi banda wani dar din komai akan Amar din don mun riga da mun koyar dashi abinda duk wani zai tabayeshi game da zuwan mu din.
Gaba daya yaran suka bishi a baya yake tambayan shi yaushe kukazo garin nan yace this week muka zo muna zuwa ganin likitane mu koma lagos.
Har a ranshi ya gamsu da hakan da yaron yace don ba wani shaku a fuskan yaron na fadin hakan ya sake tambayan shi wani unguwa kuke yace a hotel a can muka hadu da wa yan nan suma sunzo bukine sukace.
Daukan yaran yayi yaci gaba da yi masu sayyayya har na fitan arziki mu dai muna jiran su a madakata muka fito tare dashi.
A bakin motan mu ya tsaya nayi dabaran ba muniya makulin motar tun kan mu fito akan itace zata ja motar kada ya gane hakan don tun wurin biyan kudun Amar yai min signal da cewa ya fadamai hakan.
Duk sun shiga motar sun zauna saini naji yyace gaskiya sahiba baki da kirki kin shigo garin nan keda Amar amma baki nemi yan gida sun san kina nan ba.
Ba wani abu nazo nan nema wurin wani ba asibiti mukazo kawai kuma jirgin safe zamubi gobe din wanan makwabciyar tamuce ta matsa mu shigo ko zamu dan saki jiki dama Amar ya fada min yace.
Ka gaida gwaggo na fada ina kokarin shiga motar dana bude tako kije da kanki idan kin damu da ita ya fada.
Nashige mota bance dashi komai ba a lokacin mukaja muka tafi muka dauki wani hanya don batar mai da sawu saida naga bai biyo mu bane na sauke ajiyan zuciya.
Mun koma gida nake ba umma bayanin haduwan mu dashi lokacin muka bude abinda ya sayo ma yaran muna mamakin hakan.
Ammar kuma ya bamu bayanin duk yadda sukayi dashi lokacin dayaja su yana masu sayayya.
Wai yar nan kinyi dubara tun farko kamar kin san hakan zai faru din nace na sani tunda munzo garin su man ai dole mu hadu da wanin su gashi ko duk mun hadu dasu din.
Kayan da nayi oda lagos don halattan bukin baby suka iso gareni a daidai lokacin da kuma nake wasi wasin zuwa bukin yanzu don ni kadai nasan shirin da nakeyi a bangarena yanzu boyo dai ya isa hakanan kuma garemu na fada a raina.
Shiri nayi sosai da ba tare da kowa yasan da hakan ba sai wa yanda na shirya hakan dasu da zamu tafi tare.
Shiru dakin yayi lokaci guda ba wanda ya iya magana a cikin su bayan mahaifiyar nasu tagama wayan da hjy Addah.
Tasiu ne ya kawar da shirun falon yana fadin ba shike nan ba tunda wurin kakansu suke yanzu meye na damuwa kuma ?
Kai dan Allah rufa min baki in yaran na wurin Addah ita fa me yake nufi da ita ko a nan kake son ta zauna muna a samu abun fada kan mu.
Ban fita wani ba yanzun kuma wani na shirin tunkara duk a kan yaya wanan abin dame yai kamane wai ?
Ni Abba ma nakejiwa wallahi don idan yasan da zacen nan komawan ki yanzu sai Allah gidan nan.
Wa zai fadawa Abba ina gidan nan ta fada tana dauko wayanta tana neman layin mijin nata lokaci guda.
Ai dole Alh ya san kina gidan nan ke kin dauka zancen wasane wai kinyi wauta babba da kibar yaran nan a gidanshi koda baizo donke ba dole yazo don yayan shi ai.
Dolene mana Nura ya fada yana mikewa tsaye yace ita anty ma duk mata suna son dangin mijin su amma ke kullun kina cikin fada da naki ko banza ai gwaggo Addah kanwar mahaifin mune kuma muna jin dadin ta duk wanda yaje daga gidan nan.
Ya fada yana gunguni ya fita daga dakin rai bace uwar nasu ta kwala mashi kira don kada ya fita ya fadawa wani.
Da kyat yaron ya dawo dakin ya zauna yana cicika yana batsewa har lokacin yana jin zafin yar uwan nasu sosai a zuciyar shi.
Ya kara fadin ke baki tausayin mamace ki duba dan iskan nan idan baida hankaline ai suna da yan mata a part din meyasa baije can ba sai nan don suna jin haushin mu mana su barna muna suna ga banza.
Kan uwar na suke abin duniya ya dameta lokaci guda kafin tayi magana uwargidan su tayi sallama ta shigo da sunan gaida Aina,u da jiki.
Amma tana ganin Nazifa sai kuma ta buge da fadin kina nan ne ashe ta juya ta kalli mai aikin nata tana fadin ina yaran suke ?
Suna gida tare da baban su ta fada Allah sarki sai basu biyo kuba kuma ashe sun saba da uban nasune har haka.
Aina ya karfin jikin naki tace naji sauki a wani irin yanayi na nuna rashin jin dadi a lokacin.
Ta juya tana fadin idan kun tafi a gaida muna su ta fice a cikin tsarguwa ganin yadda suke zaune zugun zugun a falon kamar an masu mutuwa.
Dole dai yadda ba a son din hakan akayi don an nemi wayan Abubakar din ba, a samuba don baya shiga yana fadin a kashe wayan yake.
Dole uwargidan nasu tafadawa halinda ake ciki ta samu mijin nasu da zancen bayan ta gama yiwa nazifan fada sosai na irin rashin jankalin da takeyi.
Har tana fadin idan baki hankali ba sai iyayyen shi ko shi sun saka ya kara aure mace da zatazo ta mamaye mKi gida kina ji kin gani kuwa.
Shi kuma Alh ya gama jin tana gida modibbo y kwashe yaran ya rufe gida ba a san inda yaje da yaran ba yanzu haka ko an kira wayan nasa baya shiga sam.
Dago kan Alh din sai cewa yayi to shine me ke nifa sam bani son zancen yaron nan a gabana kwata kwata wallahi na tsani wanan dan iskan yaron a rayuwana mai kafiya kamar irin na ubansa.
Hakkuri za ayi Alh tunda aure ya hada harda zuri,a uwargidan nasa ta fada a sanyaye ya mere baki yana fadin to tunda ya hada ai sai ta koma can wirin su baffa Amadu su mayar da ita.
A daiyi hakkuri Alh abi abin a sannu zaifi hannun ka baya ruba ka yanke aure ya riga daya gama yanzu kuma kaga dama kuma ga zumunci a tsakani.
Bai kara magana ba don bacin rai har ta karasa zaman ta tashi ba tare daya iya furta komai ba a lokacin don yakai wuya makura da zancen.
Wasa wasa sai gashi ana share kwanaki ba wanda ya biyo bayanta daga can gidan shima ba, a jishi balle a san inda suke da yaran.
Wanan ya tayar da hankalin mommy sosai ga zancen bukin su daya doso kai sai abin ya taru ya zame mata biyu lokaci guda.
Anty Amarya taji komai amma tunda ba a fada mata ba sai ta share saida tana gulma da mutanen ta idan sunzo su kuma in zasu fita hjy Addah na falo zasu sake mata haibaici da cewa aikin huta ki aurar da yarki ki huta ba sai ta girma maki a gida kuna gwada sa, a ba.
Wanan irin zancen yakan dagawa mommy hankali sosai saidai bata nuna tasan dasu akeyi don kada ta biye masu a tafi da ita ana yadawa a gari.
Daddy ko a waya mommy ta kirashi ta fara fada mai abindake faruwa da Abubakar din tun cikin wayan ya fara sababi dasu .
Daya dawo kuma ya dora a inda ya tsaya inda yake shiga ba nan yake fita ba dama uwa itace mai daukan kwaram ko yaushe.
Bukin kan an farashi gadan gadan ba kama hannun yaro saidai kuma dan cikasa din da aka samu daga bangaren ango don yaki sake hannu yadda uwar yar keson ayi a bukin.
Gidan baffa Abdullahi kanin daddy za, ayi kamu ban samu zuwa ranan ba yadda naso saboda na dade a wuein aiki sai washe gari da za ai mother's day a gidan gwaggo hari ne na samu halartan taron .
Mun isa musalin biyar da rabi duk girman gidan ya cika da mutane tun daga waje har cikin shi da jamma,a wuri na samu nayi parking din motana na fito tare da Ammar da babban dan Abdul sai muniya da mukazo tare.
Dogon riga ne dark blue har kasa yaji duwatsu daga sama zuwa kusan cibiyan rigan muniya ma ba a barta a baya ba tayi shiga na abaya mai kyau sosai.
Shigan mu kawai zai nunawa mutum cewa mun banbanta da yanayin yan wurin dole wanan idan na gitta a sau anjuyo ankara kallon mu karo na biyu don shigan yai min kyau sosai a ranan don ko takalmana da jakkana abun tsayawa a kallane a wurin.
Wayata na jawo iphone thirty ina kiran layin Faiza dake can cikin taron jama,a a lokacin sai can taji ana kiranta ta dauki wayan tana dubawa taga sunana da mamaki take kallin kiran ta fita daga wajen taron zuwa cikin gidan tana daukan kiran.
Kwana biyu sahiba ina ta kira bani samun ki nace ayyah kina ina yanzu tace kin san an fara bukin baby muna wurin mother's day yanzun haka .
Ki fito gamu a waje ki shigo damu nace mata a takaice don bana jin ta sosai a lokacin kai abin sherine aida nasan hanyar lagos wallahi da kin gani watarana.
Ki fito mana na fada a dan tsawace ta sake fadin wai iskaci sheri wai zaki min don kinki zuwa ko ke wata iri ce wallahi zan koma donke fa nazo wurin nan .
Waida gaske kikeyi ko wasa nace ke bakiji kidan wurun nan na tashi a wayana ba aiko inaga taji din don wani irin ihu data sake lokaci guda.
Baifi yan mintina ba tafito waje tana raba ido gamu a gabanta ta wuce tana basarwa na kara danna wayana nace wai kinyi haukane zaki wuce duk a cikin turanci muke magana don shi na shirya yi a wurin .
Juyowa tayi inda muke ta kara kallin mu saida ta tsaya tayi min kallin tsab kafin ta yanko da gudu ta rugumeni nima din rugumeta nayi muna murnan ganin juna.
Wai sahiba kece nan ko gizau idona ke min kece kika koma wata lady dake haka don Allah ?
Murmushin cikin aji wanda a yanzu ya zame min jiki na sake mata ganin hankalin mutane yana dawowa garemu muniya na gefe tana muna murmushin ganin yadda mukeyi.
Ina Ammar da umma na nuna mata Ammar a gefena dake tsaye Ammar kaine ta fada tana nufar shi ta rugumeshi gaisuwa irin na yaran lagos yayi mata.
Goodevening ya fada tare da dan rankwafo kai yana dan daga kafa daga baya itakan mamakin wanan sauyin namu takeyi har kasan ranta.
A tare muka jera zuwa cikin wurin taron da ita sai hankali ya dawo garemu don yadda aka jera kujerun na zaune zasu iya hango masu shigowa gidan.
Tun kofa naji an fara tambayan ta su waye wa yan nan faiza sister din mu ce take fadawa mutane kawai.
Murna yayiwa faiza yawa bakinta bai rufuwa a lokacin sai yankawa mommy kira takeyi alokacin cikin taro tana rungume dani mommy ta juyo tana fadi mommy ga Sahiba.
Fatima dake can tana magana taji ana fadin sahiba ta juyo ai muna arba ta sake kara ta kama bangaje mutane tayo wurina tana ihu jin dadi tare da kiran sunana.
Hakan saiya kara jawo hankalin mutane garemu sosai kowa na kallon mu Amira ce tasani kaiwa da dan sasarfa muka rungume juna a wurin .
Mommy ta taso anty amarya ma taso ina binsu muna rungumar juna ina gaidasu saiga Nabila da hauwa muka rugumi juna gaba daya yan gidan sun nuna inada ma,ana a wurin su.
Kafin muka dan zauna na dan lokaci dana dago kai zanga yadda mata ke kallon mu suna magana muka dan juyowa nayi ina fada mata muje motana su kwaso kayan gift suna a bayan mota mu zamu tafi.
Ina zaki ta tambayeni nace inda muka sauka fatima ce aka tura ta fadawa Anty Amarya sai gata da kanta lokaci guda muka mike don barin wurin idone ya bine caaaa.
Takawa nayi inda mommy suke zaune tare dasu gwaggo hari har kasa nakai ina sallaman su don ladabi ban damu da idon mutane dake kanmu ba a lokacin.
Hakan ya kara nunawa taron cewa suna da ma,ana a wurina sosai yadda nayi masu din lokacin kuma anty Amarya ta iso tana fadin Sahiba kuyi hakkuri ance zaku tafi ba a gida zaku saukabane ?.
Kaina girgiza ina fadin akwai inda muka sauka ko tunda nan za ayi yawa ta kara fadin fatima tace kince azo a kwaso serbeniya ko nace eh Anty na kara juyawa nayiwasu gwaggo sallama muka tafi harda anty din son rashin yarda da bata dashi.
An bude ta cika da mamaki sosai manyan kwalaye ne na jug masu kyau tun gida umma tasa na ware ma mimmy nasu da yanzu naga kunya a idon ta karara don ganin mu da tayi.
Faiza na dankawa nasu naba mommy saura haka aka kwaso zuwa cikin gidan gwaggo hari gaba daya don anty tace basu rabuwa a wurin lokacin.
Ido caaaa suna tsaye har na tayar da mota muka barsu cike da mamakin ganin mu a ciki bakon yanayin da mukai masu na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login