Showing 12001 words to 15000 words out of 382072 words
kada ki kara yarda da kalaman sa a gareki .
Don dan adam mugun ice ne wanda ka yarda dashi ka amince masa shine zai dawo ya cuce ka akarshe.
Koda kuwa dan uwankane a wanan zamanin zai iya cutama idan ba,yi dace da dan uwa na gari ba sai a hada dashi a cutama.
Tashi mu fita naga maishi ta fada tana mikewa tsaye sahiba ce ta fara fita a dakin umma tabi bayan ta zuwa wajen saidai suna zuwa babu kowa a wurin sai mutane dake dan gittawa a lokacin.
A nan na barshi fa umna na fada kafin in sake cewa na barahi a bayana tafe na shigo in fada maki nan dai ta kara kwashe yadda sukayi har ya bata kudin da tafiyan shi.
Yazo neman wanine a garin nan umma ta sake tambayan sahiba wanan kalmam daga ida take tsaye da sauri a cikin yanayin damuwa da tsoro na,amsa da haka yace umma .
Don dai ni bai min magana ba ban iyaka yaga wani zai mun rashin mutuncine yazo inda naken ya kori mai shi.
Shige ciki mu tafi umma ta fada da sauri suna shiga suka hango Amar a tsaye yana kallon iya wale dake fada a kofan su ta dauki tsohon abin gashin masaranta data arawa sahiba din a cikin masifa irin nata maineman nayi a kullun.
Bayan sun shi aka kara gwaucewa da wani ruwa mai karfi dole kowa ya nemi mafaka saidai hakan baisa sahiba ta zauna ba.
Nan ta shiga gyaran dakin su da tara masu ruwan amfani ga yan kayan dake garesu na aiki sai yamma sosai aka dakatar da ruwan zuwa lokacin yunwa yaga halaka haka ta fito neman abinda zasuci a cikin duhun nan bread da shayi ta dauki kudin jiya ta sayo don wanan kan da aka bata ta gama tsorata dasu a zuciyan ta.
Kodata dawo ta samu Amar har ya soma barci a lokacin ta tayat dashi suka sha suka kwanta bafon sun koshi ba.
Washe gari bata so fita school ba amma umma ta gargadata dole ta tafi har lokacin data dawo bata sake jiki ba a gidan.
Wajen gidan su ta fita ta samu dan karafuna tayi dubaran hada hada abin da zata gasa sauran masaranta na jiya ta fita dashi duk da umma bata so hakan ba sai dai don kada ayi hasaran kudin da aka saya ta barta ta fita dashi hakana .
Allah ya taimaketa ta sayar da wuri don haka taje kuma ta sari katin waya tana bin motoci dashi har zuwa magariba ta dawo gidan da abincin data sayo masu don tasan ba wani abin kwarai a cikin su tun jiya.
Bayan sun gamane suna zaune ta kwaso littafanta tana assignment din su na makatanta,
Muryan ummane yadaki kunnuwan ta tana fadin ina kudin da mutumin nan ya baki taji gabanta ya fadi don tsoro a sanyayye ta dago kai tana fadin yana a cikin jakar kayana na boye.
Dauko mu kirga nawane a gani ta mike da sauri ta dauko kudin suka kirga tayi wani irin zabura lokaci guda don ganin yawan kudin dake hannun ta a mike sabbi fil dasu.
Dubu saba,in ne cif a hannun ta ta dago kai da sauri ta kalli mahaifiyarta dake kallon ta daga gefe itama a tsorace.
Wanan kudin ya baki su duka zama guda Sahiba da alama wanan yana so ya shigo rayuwan mu da yaudara dole akwai abin da yake so a gurin ki.
Tsorone ya kara kama Sahiban don zancen akwai abinda yake nema a wurinta da umma ke yawan fada din nan ko yaushe.
Zaune yake bayan motan yana bin ko ina na unguwanin da kallo yana mamakin yadda garin yake bunkasa a kullun yake kara girma da fadi.
Nisawa yayi kadan yana gyara kwanciyan balance din da yayi a lokacin a bayan motan driver najan shi zuwa gidan shi don dawowan shi ke nan kasan daga tafiya.
Alh Ibrahim Nagwoggo tsohon ke nan tsohon jami,in tsaro da yayi ritaya ga aikin shi yanzu ya kama kasuwanci gadan gadan.
Alh Ibrahim ustazu ne babba yasan addini sosai kuma yana amfani da sanin nasa a yanzu matan shi biyu bayan dadewan shekaru da yayi da matarsa daya hjy Addah.
Dashi da ita duka yan uwane aure ne hadin iyayye a tsakanin su dukkan su din sun fito a tsatso dayane mutanen Adamawane Amma mazauna garin kaduna don a yanzu kowa nasu na kusa yana zaunane a cikin garin kaduna.
Saidai duk da hakan basu bar gida ba don har yanzu suna kai ziyara a wurin yan uwansu dake can suma kuma suna zuwa idan sha,anin su ya tashi.
Don iyayyen su basu rasu ba saida sukai dabaran aurar da wasu yayan su ga danginsu dake can don kada zumunci ya yanke a bayan su.
Zaman hjy Addah auren hadi na dangi a gareshi baisa ya gaza nuna kaunata a gareta ba itama hjyn ta iya tattalin mijin ta don tasan abinda yake so da wanda baya so sai suka zauna lafiya saboda kiyayyewan da yakeyi din a kan hakan.
Yayan su ukku yanzu dake raye a duniya don haihuwan ta biyar maza uku mata biyu amma mazan na farko sun rasu sai kan Abubakar da suke kira modibo diyan suka fara tsayawa a duniya.
Kasancewan Abubakar da daya tilo garesu bai hana su bashi tarbiya isalama yadda ya dace ba dashi da sauran yan uwanshi mata Nabila da Aisha ke nan kanne a gareshi.
Ya auro hjy karima shekuru goma da suka wuce ita din ma,aikaciyar jinyace a baya irin matan kaduna din nan yan kwalisa na kwarai.
Daga baya ta aje aikin dataga abinda yai mata a gidan don gaskiya ba laifi akwai hutu sosai a gidan nasa.
Da farko hjy karima taso ta wuce gona da iri ga zaman su da hjy Addah din sai shi Alh Ibrahim din ya nuna mata bata isa ba don dama maigida shike fara bada daman a raina masa matan da aka sama a gida wani lokaci.
Ganin idan ta matsa daman ta zai tafi a banza yasa ta aje duk wani makaman data shigo dashi na yakar hjy din a gefe aka zauna lafiya a yanzu da har takai ga haihuwan nata yaran uku duka mata.
Ita hjy Addah kusan iyayyen su daya za a ce don wa da kane suke da mijin nata Alh Ibrahim din don haka zumuncine mai karfi a tsakanin su.
Duk da akwai kishi na boye a tsakanin su da hjy karima sin hakan bai hana hjy Addah rungumarta kamar yar uwa ba agareta don yayan ta gaba daya tana nuna masu kyauna har cikin ranta kuwa.
Yanzu Abubakar shi babban da ga Alh ibrahim din yayi karatun shi na secondary ne a FGC porthercort dake kasan ibo don Allah ya bashi baiwan ilimi tin yana karamin shi.
Yana gamawa saboda kwazon shi mahaifin shi ya kaishi waje yayi sauran karatu shi a can har ya zama yana aiki a karkashin malisan dinki duniya na tararyan kasa da kasa a matsayin dan leken asirin su dai wasu aiyuka a wurin.
Sai Nabila da Aisha da yanzune suka shiga matakin farko a univesty kaduna suna karatun kimiya da fasaha dukkan su.
Tarbiya iya tarbiya yaran gidan kaf dinsu suna dashi don iyayyen idanun su yana a kansu wurin ganin sun basu ingattacen tarbiyan daya dace da islama a gidan.
Wanan ke nan daga dan cikin tarahin ahalin Abubakar dashi kan shi Abubukar modibo dayanzu yazo lagos neman wani mutum dayayo ta,asa a can waje din wurin shara da yaudaran mutane yana cin kudi tare da sayar da miyagun kwayoyi yana kuma safaran makamai a kasashen Africa.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA, , , , , , ,
BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM MALIK, YUU,MMIDEEN, , , ,
KIBIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DA AMINCI BA TARE DA DAUKAN HAKKIN KOWA AKANKI BA YAR UWA ALLAH YASA MUFI KARFIN ZUCIYAR MU AMIN, , , , ,
Motar dake dauke da Alh lbrahim ta danna kai shiga gidan nasa sai lokacin ya sauke ajiyan zuciya yana gyara zaman shi.
Kananan yaran yan wirin hjy karima ne a waje su biyu suna saye da dogon wandon jean blue da riguna ja riga haka take masu shiga kamar su din tagwayene don ta hada kansu tun suna kanana a nata hikimar.
Murmushi ya sake ganin yaran daga kofan glass din gidan suna yan tsale tsalen a waje gida ke nan da iyali sai a lokacin yaji dan farin ciki ya sauka mai a zuciyar shi.
Hankalin yaran ne ya koma wurin motan mahaifin nasu da sukai kwana biyu basu ganshi ba, yana wurin yafiya.
Ya kuma dawo a yanzu a daidai lokacin da kowa nagidan bai tsamaci dawowan shi ba a ranan tsaye sukayi suna kallon motan suna jiran suga wanda zai fito daga cikin motan a lokacin.
Driver ne ya fara fitowa da sauri ya zagoyo dayan gefen ya budewa ogan nasa mota a cikin mutunci a daidai lokacin yaran suka sheko suna ihun eh daddy daddy da gudun su.
Hakan ya ankarar da hjy Addah dake zaune falo tana waya sai su Nabila da suma a zaunen suke suna tsabgogin su a lokacin.
Nabila ta dan zabura tana fadin kamar daddy suke kira fa zai yuyu shidin nema don ba abin mamaki bane son a cikin satin nan yace zai dawo dama.
Jin dan shirun da yaran sukayine yasa su daukan wasan sune kawai sukeyi a lokacin don kewan shi da suke ji a yanzu din.
Kofa a katuro driver shine yake kokarin shigo da kayan shi ciki shi kuma yana bayan shi tafe da yaran kanana daya rike daya ako wani gefen shi suna dan hira.
Mikewa yan matan sukayi suka hari mahaifin nasu suna mashi sannu da zuwa dukkansu su uku da yar kanwar hjy da riko a yanzu.
Hjy ta mike a cikin kwaliyan da take na atampan super tana murmushi take fadin kwatsam haka babu sanarwan zuwa.
Gida yayi kira banda saurin uzuri bayan hakan sannu da zuwa tayi mai a cikin ladabi duk yayan nasa na baibaiye dashi ya amsa.
Zama yayi yaran suka zube kasa kamar yadda suka saba suna gaidaashi a lokacin hjy ta juya tana fadin bari a kawo abin sha bata tsaya ba ta shige ciki.
Wayan ta dake hannun ta ta kalla ta dan fara neman layi a gagauce ta samu layin hjy karima data fita gidan tun dazun.
Har ya katse ba,a dauka ba bata hakkura ba ta sake kira a karo na biyu kusan ya katse aka daga tare da fadin hjy Addah lafiya dai ko ?
Duk inda kike ki dawo gida yanzun nan don Alh ya dawo yanzu haka yana cikin gidan nan ko ta fada a dan gagauce tana katse kiran a daidai lokacin da hjy karima ke fadin dama yau zai, , , ,
Munafuka wai Alh ne ya dawo ta fadawa kawayen nata da suke tare ai dama yau zai dawo ne kika fito dayan kawar ta tambaye ta.
Ina fa nasan da zancen dawowan shi a yanzu din na a gaban ta fa nafito bata fada min zai dawo ba don nasan tunda munafukine shima ba zai rasa fada mata zancen dawowan shi yau din.
Wai karima me kike jira da wanan matar har yanzu baki taka mata burki ba tun farko saida nace a fitar da ita kafin ki shiga kice wai ita din me wanan tsohuwar ba zata zama maki matsala ba sai dai uwarshi itace matsalan ki.
Yanzu gaahi tana son ta zama maki ciwon ido tsakanin ki da mijin ki don tana munafuka wai zata kiraki tana kashe murya hjy karima kiyi sauri ki dawo duk inda kike Alh ya dawo.
Mikewa tayi tana fadin ai ki barni dasu sai nayi maganin su dagashi har ita din zasu gane kuren su dan shimfida nayi masu inga iya gudun su yanzu ko nagani.
Tabe baki yar dogowan daga cikin su tayi tana fadin na yaushe kuma wai an cuci na kauye yanzu ai ki mike din ki daina kwana kina sake AC kega wace ta samu wuri.
Alhalin mai miji tana can rike da mijin ta sai abinda ta fada kuma ta shimfida akeyi a gidan ke kin koma yar kallo kawai.
Binsu tayi da kallo don suna kara mata takaicine kawai da wanan maganan a yanzu don takai iya kuluwa da zancen yau.
Boyar Allah hjy Addah kuwa tana can tana kokarin kare kariman don da tafito dauke da kayan ta mufo falon har lokacin yana zaune da yayan shi suna surutu.
Tana direwa yake fadin wai ina karima ne ban ganta ba me yuyuwa tana bandakine ko tana barci bata ji shigowan ka ba sai kawai taga ya dan saki murmushi a fuskan shi.
A daidai lokacin ne kuma karamar yar hjy kariman dake saman cinyan shi zaune ta sake fadin daddy I told you she went somewhare tunda safe wanka ma anty Nabilace tayi muna.
A take ya kara daure fuska a hankali ya sauke yarinyar daga jikin shi kafin ya mike ya dago kai yana fadin kin gani keda ke kareta zaki koyawa yara karya,
Wai ma yaushe kika fara karyane Addah ya tambaye ta yana tsure ta da idonun shi kafin ya juya yana girgiza kai.
Kayi hakkuri Alh fitan ne ya kamata in bashi ba babu inda take zuwa ai tana gida baiyi magana ba sai hanyar part din shi daya dosa kawai.
Ya barta tsaye kafin ta juyo tana fadin Amira waya tambaye ki sai mamin ku ta murde bakin nan mai surutu idan ta dawo.
Fuska yarinyar ta tabe tana make hannu alaman kuka a lokacin daga haka hjy tabi bayan shi cike da fargaba don sanin halin shi da tayi.
Ta sameshi zaune saman gado ya kwabe babban rigan shi dake saman jikin shi kamar yana tunane a lokacin.
Tashigo da sallama tana fadin Alh kayi hakkuri ya dago tare da dakatar da ita yana fadin ki fita a cikin zancen nan don nafiki sanin waye karima .
Ba yau ba nasan tana wanan halin da zaran na daga kafa nabar gadin nan zaman gida ya kare a gareta ita kuma ko kina dauka bansan da hakan bane wai har zaki wani tare kina rufe min.
Ku daiyi hakkuri kowa da halinsa ake zama dashi inda sabo aika saba da halinta tunda yanzu an zama daya.
Hada min ruwa in watsa ya umurce ta kai tsaye don haka ta juya zuwa bandakin don ta hada mai ruwan wankan.
A daidai wanan lokacin kuma hjy karima ta shigo gidan su Nabila ta sama a falo ko kallon su batayi ba sai Aisha da zakiya ke fadin sannu da dawowa Anty .
Ciki ciki ta amsa ta nufi part din ta kai tsaye saida ta shige Nabila taja dan guntun tsuki tana fadin Allah ya kara ai gwai kuma da har kuka tare ta ai.
Ta shigo ta kallemu ta kawar da kai kune masu wani taron ta can ai kun gani yanzu wa zata zo tana budawa taje can ta hadu da daddy yau yar rainin wayau kawai.
Hjy karima tana shiga dakinta ta wurgar da jakkan hannun ta da gyalen data yafa saman gado kafin takai zaune a hankali saman gadon tana tunanen abinyi.
Yaran tane suka shigo dakin suna hayaniya mami kin sayo muna Sweet suna kokarin bude hand bag din ta su duba su gani.
Hey Amira stop it bana hanaki wanan halin ba kina bude min jaka idan na dawo sai dayan ta biyun tace kada ki bata mami.
Itace ta fadawa daddy wai kin fita tunda safe bayan mommy tace kina daki kina wanka ko kuma barci ya daukeki.
Wani kallo ta watsawa yaran kafin ta kai hannu tana jan bakin yarinyar karama tana fada sai kuma taja tsuki tana fadin ita kuma munafukan wayace tace inayin wanka ?
Ai daddy yayi fada yace wai ta fara karya ko yayi fushi ya wuce part nasa.
Mommy ku tana ina yanzu tana part din daddy what ta fada tana mikewa yaushe ne daddy ku ya dawo ta tambayi yar babban dake magana ita kan Amira kuka ta saka.
Don babban yarta tana makarantan kwana a lokacin tana jss one don ba babba bace sosai shikuma a ka,idan gidan shi makarantar kwana yara suke zuwa bai yarda da jekaka dawo ba a lokacin.
Yarinyar kan bata san time ba don haka tace da uwar tun safe daddy ya dawo hakan ya harzuka karima din sosai watau tun safe ya dawo shine saida suka gama cin amanan ta yanzu zata kirata do munafunci wai tana fada mata dawowan shi a yanzu.