Showing 72001 words to 75000 words out of 382072 words

Chapter 25 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28445

da mamaki a ranta na ashe umma din dai mai gatace haka tazo nan ta zauna a cikin rashin galihu.
Kai koma meye wanan dalilinn yana da zafi da daure kai gashi sun dsakartar da zancen data so taji don umma taki furta komai ga kowa tun ranan da ta shigo lagos din ta zauna dasu har wanam rana.
Yazun kan maggi ya kama kan zabo don hjy karima ta samu gidan a yadda take so don a dan kankanin lokaci ta samu kan kowa na gidan kamar yadda take son samu din.
Yanzu kan daga ita sai diyan ta kaje ji bakin Alh din abu kadan ya hau hjy Adda da fada ko zagi ido rufe.
A takaice dai yanzu gidan yana kamar under control din hjy karima ne a yanzu duk biye suke da ita a gidan abinda wasu mata da dama suke butin samu a rayuwan su ke nan saboda dan zaman duniya na lokaci kadan mace zata iya sayar da lahiran ta kan hakan a banza.
Abida komai yawan shekarun ki a duniya ba zaki tsufa irin na duniya ba a rayuwan ki akan wanan dan zama na lokaci yar uwa zaki yarda ki halaka kanki da kanki don kawai huduban shedan da shedanun yan adam ?
Ya Allah kasa mufi karfin zuciyar mu akoda yaushe mu tuna kidhin nan fa na dan lokacine don baki san abinda kika debowa rayuwan ki ba zaman ki na duniya.
Shin yar uwa idan har kin mulki kishiya da miji da yayansu zaki fitane ki mulki duniya ko garin ku baki daya ?
Kin gani muyi kishi irin na wayewan kai mai ma,ana da fahinta kada ki yarda a cutar dake ke kuma kada ki cutar da abokan zaman naki don rayuwan yar kalilance a tare dake.
A irin wanan halin ne da daman da ta samu sa,a gun bokanta a yanzu take taka kambon ta a dakin tafito tana tako daya daya daga part din ta a cikin shirin kwaliyan ta na fita unguwa wanda a yanzu kusan kullun sai ta fita a gidan.
Ga idan akace gari ya waye da sabon iya shegen da zata tsiro wa mutane na iskancin kada dai a zauna lafiya don kawai ta musgunawa yan gidan ta nuna ita din itace dai a gaban komai.
Har yakai yanzu yan uwan miji da suke yan uwa ga ita hjy Addah suna kokarin juyawa addah din baya don sai su shigo gidan ba tare da sun shiga part din hjy Addah din ba harsu fita.
Don kawai a nasu zaton ita zata iya sa mijin su yai masu abinda suke so ko ya biya masu wani bukatan da suke dashi da sauri.
Saidai kaiya yan adam basu gane hakan ba don irin matan nan da kansu kawai suka sani sai yayan su akarshema sune masu hana miji yaiwa yan uwasa alheri din don tsaban bakim ciki dake cin su a jini.
Wasu kuma zasu dinga amfani da yan uwan mijin suna tatsar dan uwan su wurin ya bayar idan an bayar din sai su rage su tura a aljihun su.
Su Nabilane zaune da kawayen su da suka zo gaida dija da bata da lafiya satin nan duk bata fita school na don fever dake damunta a lokacin.
Gaida ita suka fara a cikin dan shaku tare da fargaba suma dai kawayen hakan har ta dan wucesu tana karbawa sai kuma ta juyo taja ta tsaya tana fadin.
Amma dai baku da hankali duba yadda kuka bata falon nan kamar anyi fada a gidan gala kalo kalo suka fara a tsakanin su.
Ta sake fadin ke kuma Dija daga ke har uwar ku da baku san ciwon kanku ba yanzu kin zauna a gida kince baki da lafiya baki fita school .
Amma gashi yanzu muryan ki yana tashi har kofan gidan nan don kawai baku san zafin kudin da ake kashewa a kan ku ba ko me ?
Oya yanzun nan ku gyara falon nan tasa ku kuma ta juya wurin abokan nasu da fada tana fadin maza kuzo ku fice a gidan nan tunda ba gidan holewa bane nan din.
Tashi sukayi a cikin fushi don zagin barnan sunan da tayi masu din ransu a bace Nabila ta dago kai a cikin takaici ta kalleta tana fadin.
Anty sunzo gaida Dija ne ba wani abu suka zo yi ba dama nace su fita ta dakawa yar mijin nata tsawa don kawai ta disgasu a gaban kawayen nasu ta nuna su din ba kowa bane a gidan nasu.
Nabila da zata bisu ta basu hakkuri itama wani ashar din zagi da ta samu a wurin ta din jin hakan yasa hjy Addah cikin dakewan zuciya ta fito daga dakinta dayafi kusa da falon tana tambayan meke faruwa ne hakan ?
Saida tayiwa hjy din wani kallon raini take fadin wani abu zaki tambaya bayan baku iya tsawata wa yaran ku idan suna abinda ba daidai ba.
Karima ni din kike fadawa hakan tace an fada kewa da baza a fada maki hakan ba wai dama daurin gindin ki suke samu ta zauna a gida tace bata da lafiya amma yanzu ta dawo falo da kawaye suna muna shewa a gida haka .
Shewa kuma wani irin shewa ne da banjiyosu ba a dakina af dama ai ba zaki taba jinsu ba ai tunda da sanin ki suke komai da sukeyi ai.
Anan fada yaso ya kara kaurewa sai su Nabila din suka ja mahaifiyar su a cikin takaici suka shige part din su ransu na masu zafi ga wanan disgawan da hjy karima din tai masu a gaban kawayen su
Da kuma nema ta raina wa uwansu wayau da take son yi a gaban kawayen su din a yanzu don basu karasa fita gidan ba a lokacin.
Duk da saurin da takeyi saida ta tsaya ta batawa kanta lokaci wirin fadan da baida dalili ko nasaba don kawai neman nayi a gidan.
Irjn haka take masu koda kallo sukeyi duk da akwai kayan kallo a ko wani part amma basu isa su bushi iska su fito main falo suce zasuyi kallo ba a yanzu kamar yadda suka saba yi a baya yanzun ne zata korasu zuwa ciki.
Su dai a takaice wanan ahalin a halin yanzu nasu ya samesu basu da kwanciyan hankali idan garin Allah ya waye suna sauraron da wace zata bullo masu dashi na bacin rai a garesu.
Zaune nake nayi tagumi gashi na fada sosai a cikin dan kwana ukkun da nayi a kulle a dakin ina cikin fargaba da tashin hankali wanda ba zan iya musulta shi ba a lokacin.
Hakan yasa na zauna nayi tagumi ina zulumin halin da umman mu zata shiga a wanan lokacin na kiyasta abubuwa kala kala a zuciyana kan hakan karshe kuma na shiga jero addua a bakina.
Naji an tur kofan dakin duk da ban gane lokaci ga hakan amma ina iya amgani da lokaci in fahinci lokavin da ake ciki a wuni.
Hakan yasa na fahinci cewa lokacin dai bayan karfe ukun rana ne la, asar bata karasa yi ba a lokacin.
Kofan naji anturo nayi mamakin jin hakan don ba lokacin da ake budewa bane a shigo min da abinci don da safe zasu kawo min abinci lafiyaye da drinks sai kuma karfe dayan rana zasu kawo min shi da yamma kuma karfe bakwai daidai suke kawowa .
Ban dagoba ban juya ba don ganin mai shigowa din ina zaune takure a inda nake azaune din muryan da ban taba zaton ji a wanan wurin ba shi naji a lokacin .
Umma ce ke fadin mun gode daga kofan na juya a cikin wani irin juyi na firgice lokaci guda ina kallon kofan na mike da gudu zuwa wirin kofan da umma din suke suna shigowa dakin da nake ciki din.
Umma i miss you dey carry me come here, i don no wetin i do for dem dey kidnap me here sai na fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya ina fadawa jikin umma din lokaci guda.
Har lokacin yana tsaye a kofa tare da harde kafa yana kallon haukan da nakewa umma din sai da umma ta dafa ni tace stop crying he be ur brother Abubakar son of ur aunti nd his father is ur baba broda.
Jin haka yasa na dago kai daga jikin umma da sauri na dan kalle ta kafin na juya gun da yake tsaye ina mashi wani irin kallo kamar na tsoro a lokacin.
Ta kara fadin a cikin yarbanci da fatan baki masa rashin kunya ba dai na girgiza kai tare da fadin ban ma ganshi ba tunda suka kawoni nan sai mai ban abinci kawai ke shigowa dakin nan ya kawo min.
Naji ta sauke ajiyan zuciya a hankali ta juya gareshi tare datin wani yaren da ban taba tsamanin umma jinsa a bakinta ba, ya amsa mata shima a cikin yaren irin wanda tayi mai din .
Wurin shi na nufa na bayan umma din tayi min yaren yarabawa akan in gaida shi a matsayin dan uwana kuma yayana.
Na duka har kasa a cikin ladabi na fara gaidashi yana mamaki ya amsa min a takaice yana fadawa umma shi zai dan fita don Allah mu saki jiki kamar muna gida a nan.
Ya rufo kofan sai lokacin umma tabi dakin da kallo ta ko ina sai kuma ta fashe da wani irin kuka da ban san dalilin yin shi ba a lokacin.
Saida tayi mai isan ta don kanta tabari tara fadin sahiba na rabaku da gatan ku da yan uwan ku kan wani dalili da na zabawa kaina daku hakan a rayuwan mu.
Ko yanzu ina nadaman komawa a cikin dakin ku da zakuyi don ban san ko dukane suke da akidan dake rike a zuciyar su ba akan ku.
Ku yaranane a yanzu fada maku wanan labadin baida amfani a gareku yanzu don ba zaku taba fahintar me hakan da nayi yake nufi ba.
Suma din zasu dauka ra,ayunane na son in shakata wata kila ya fitar dani a cikin su bar kowa nawa zuwa nan inda bamu da kowa na jini a nan din.
Kallon kaina nayi jin umma tace ba zamu iya fahintar abinda zancen ta yake nufi ba a yanzu idan ta sanar damu niko gani nake ai na girma nakai munzalin da zan fahinci wani abu yanzu ai .
Yanzu ba zan iya cewa mahaifin ku yana raye ko baya raye ba sai dai ga maganan Abubakar din yanzu da muka hadu na fahinci dai mahaifin ku shima baya tare dasu.
A kullun zancen mahaifin ku shine makomar ku a cikin yan uwan shi don hakane yake taka tsatsak da ke a lokacin baya yarda ki rabi kowa idan ba niba ko shi saiko wasu daga cikin dangina kuma.
Yanzu wanan mutumin ya min alkawarin ba abinda zai samu rayuwan mu dagani har ku muddin yana a raye a duniya.
Haka kuma ya ban zabi akan idan ba zamu iya zama a can gida ba zamu iya dawowa nan din mu zauna tunda nan muka saba dashi din.
Wanan ya kara ban kwarin gwiwan da har na yarda na amince zan je gidan kodan naga halin da mahaifana da yan uwana sule ciki a bayan mu.
Tana fadin haka tayi shiru tare da shiga cikin tunane kafin ta mike tana fadin inane ban daki zata kewaya tayi sallah nan ta barmu zaune munyi shiru shi dai Amar yana bin fakin hotel din da kallin mamaki.
Kafin nace dashi ban san ko inane nan ba don bansan lokacin da suka kawoni wirin nan daga shiga mota na tsunci kaina a dakin nan.
Na fara bashi labdin yadda abin ya farune umma ta fito bayin tace in tashi inje inyi sallah in roki Allah tsari ga duk wani abin ki a gare mu.
Bayan mun idar ne umma nake tambayan umma yadda har ya gane cewa ni din yar uwarshine haka.
Murmushi umma tayi kafin tace kuna da kama na asali da zai iya gane hakan idan dama yasa da bacewan mu kuma ina zaton ya sani din dama.
Umma ban fada bane ya dade yana bibiyata tun baro wancan unguwar da mukayi har zuwa yanzun da Allah ya bashi sa,a akaina yanzu din.
Dakin fada min da wuri zamu gusa daga garin nan muje can nisa dasu ko yanzu din bawai zan yarda in bishi haka kawai bane sai na kalli hankalin shi na gane manufan hakan a garemu da yake son yi.
Umma idan hakane ni zan bishi naje naga yan uwanmu in yaso indawo in fada maki irin taron da sukai min a can din.
Tsawa umma ta daka min tare da fadun ke yarinyace sahiba kina zuwa rayuwan ki zasuyi kokarin nema su kashe ki.
Su kasheni umma na fada a cikin mamaki ina kallon umma din don mamakin abinda umma din ta fada game da zuwan namu wurin yan uwan mu din.
Kafin umma ta bani amsa aka turo kofan shine wani na biye dashi a baya da wasu trolers guda biyu ya shigo dakin misalin biyar da rabi na yamma.
Kaya sawa ne namu dana umma a cikin akwatin don mutumin ya koma ya dauko daya ya dawo dashi nan yake nunawa umma nata sai nawa da na amar yake fadin zamu iya amfani dasu din mu sa ya sayo muna su din don Allah mu saki jiki dashi don bai daukomu da niyar wani ya cutar damu ba a yanzu kuma.


ZAINAB IDRIS MAKAWA



:ANA DARA GA, , , , , , ,

2️⃣2️⃣

BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL JABBAR, , , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA KI KARANTA A CIKIN SALAMA NA FADA MAKI NA FITAR DA HAKKIN HAKA GAREKI, , , ,

Ummace kawai ta iya budan kayan da aka shigo muna dashi din nikan ina zaune ina faman tunanen rayuwa a zuciyana.
Ina tunanen wai wani irin kiyayyane tsakanin mu da yan uwan mahaifin mu haka da har yasa umma ke gudun mu dasu haka ?
Idan ita ummace basa so aimu ba zasu kimu ba tunda sune mahaifan mu ai dole ko su so yayan dan uwan nasu ai na fada.
Abinci mai lafiya aka kawo muna wanan daren kan naci nasha na koshi na kuma yi barci mai dadi a ransn duk da tunanen yadda zan ga yan uwana ganin farko a rayuwana.
Asuba mun tashi lafiya bamu kara barci ba sai mudin ganin yan uwa da zamuyi mukeyi a tsakanin mu inda nake cewa Amar ai suna da kama da wanan boda din namu sosai.
Umma dai dake jin shirmen mu kamar almara wai muna zumudin zuwa ganin yan uwan mu a cikin ranmu muke wanan shirmen haka don tasan shirmene sai anje can gida mun ganewa idon mu abubuwa zasu rikice muna a can din ai wanda bata fatan komai ya samu wani daga cikin mu kuma.
Shiru shiru a ranan bamuga wanan boda din namu ba kuma bai leko mu ba tun hakan yana damun umma a zuciya har dai takai ga yin magana a fili game dashi.
Nace umma ba zai manta da muba ai tunda kinga ya kawo muna abinci da safe munci don haka muna a ransa wata kila akwai abinda ya tsare shi ga zuwa ne.
Wasa wasa har magariba babu almanan shigowan shi dakin da muke din har zuwa lokacin da muka shiga barci.
Abubakar din ne zaune a dakin mahaifiyan su bayan sun gaisa sun dan taba hira ya jefo mata tambaya da fadin.
Wai umma meye dalilin barin gidan iyalan Abba sambo ne da har yanzu naji ba wanda ke zance a kansu.
Wani irn juyowa hjy din tayi kamar ta kadu da jin sunan daya ambata din yanzu a gabanta din tace ina ruwan ka da wanan zance na manya ta fada a cikin daure fuskan ta gareshi.
Shiru yayi ya dukar da kanshi kasa kamar mai tunane muryan mahaifiyar nasa ne ya katse shi tana fadin kada ma ka kuskura kace zaka tsoma bakin ka a cikin zancensu a yanzu.
Koma ka tsoma din dawa zakayi mutanen da da suka bata cikin duniya ga baki daya babu labarin su har yanzu ina ruwan ka da zancen su kuma.
Tunda yake bai taba mamakin kalaman daga bakin hjyn tasu ba irin yau din nan don bai taba zaton zaiji hakan daga bakin ta ba ma.
Sai gashi ita da kanta take masa warning kan hakan da ya fitar da bakin sa a cikin rikicin gidan su ya rufa masu asiri.
Idan har yaya Nuhu yaji wanan zance ai sai ka lalata komai a tsakanin mu kuma a yanzu gashi Addah Dada daga ranan da tayi zancen su a gaban shi tun ranan ya rufe da ita dashi da wasu yan uwa namu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login