Showing 51001 words to 54000 words out of 382072 words
don lamarin bukin .
Wanda tun bayan wucewan Abubakar sau daya yazo gida koshi sai da daddy yayi masa fadan hakan bayan hjy ta fadawa daddy din dalilin fushin shi dasu da yakeyi.
Cikin fushi daddy ya mike yana fadin wanan wace irin maganace bayan mun tsayar da zance yazo zai kawo wani magana daga baya.
Dama kin san baku shirya hakan da dan naki ba kika bari har nakai ga zuwa na tsayar da magana gaban manya.
Hjy a cikin lumana ta kalli mijin nata tana fadin menene na tayar da hankali haka Alh ina dai dani da modibbo duk a karkashin ka muke.
Auren nan kuma haka akaiwa kowa shi ko yana so ko baka so aka kuma hakkura aka zauna mutum nawa a cikin family din nan suka nuna basa so daga baya kuma bayan anyi aure a zauna lafiya.
Alh ya dago kai ya kalleta kafun ya zauna dakyau yadda yake zaune ada yana sauke ajiyan zuciya yana fadin shike nan ai na dauka kema zaki mara masa ne ku mayar dani mutumin banza a idon mutane.
Tace ni na isa in hakan tunda nasan wanan abin ba fashi tunda yaki nemowa da kanshi a wuce wurin .
Ya gyada kai cikin zafin zuciya har lokacin yace ki fada mai ya tabbatar da yazo garin nan kafin satin daurin auren yaji bukatan da suke dashi a bangaren yan matan dashi da abokan shi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA , , , , , , , , , , , ,
1️⃣6️⃣
BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL- MALIK, , , , , ,
PAID ONLINE NOVEL YAR UWA KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA DON GIRMAN ALLAH, , , , , , ,
Yar uwa ina bukatan adduan ku da bakunan ku masu albarka Allah ya yaye min duk abinda ke damuna dani daku duka baki dataya don Allah kice amin yar uwa Allah ya amsa muna tare dake.
Ko kafin ya isa har anyu jere a sabin gida sa daya gina kuma daddy ya taimaka mai da wasu abubuwa.
Wanda hakan ya kara jawo mai bakin jini a wurin hjy karima tun tana fadan hakan a lokacin a zuciyar ta dakuma aminta har dai yakai ta fito fili ta tukari Alh da zancen tana fadin moddibo fa bashi kadai bane akwai yan uwanshi suma suna da hakki a cikin dukiyan shi.
Murmushi ya dan yi yana zaune kamar badashi take magana ba sai da yaji tayi shiru ya dago kai da hasals yana fadin kin gama abinda ya kawo ki ?
Tace aini ba fada nazo yi ba gaskiya na fada don bashi kadai bane akwai wasu yace oh niki dabaran ke nan ke to ina wasu din suke ki nuna min su a yanzu ?
Ta dago itama a cikin mamaki tana kallon shi don jin abinda ya fada yana huci yace nace ki fada min ina wasun suke a yanzu din don ni shina fara gani a yanzu.
Itama a cikin fushi ta fara fadin wa yan nan matan daka raina don suma mutane ne ai kuma dasu nake alfahari.
Amma kuma dake dasu dani gaba dayan ku kuke tunkaho a garin nan ko sai tayi shiru karima kina da matsala wallahi.
Moddibo da kike gani wata rana ko ina raye ko ban raye shine gatan ku daga ke har diyan naki da a yanzu kikewa wanan fadan.
Kuma kada ki manta ba rashi ko wani abu yasa nakewa yaron nan haka saudan shima yana da hakki hakan a kaina kamar yadda kikewa diyan ki fada a yanzu.
Kin ban mamaki karima halaiyan ki na banza a yanzu suke kara fita fili ko can ace wani yana cin albarkancin wani da badon darajan mahaifin ki ba dana nuna maki ko wa nake nima kingani.
Ai dama haka fadan gaskiya yake saukin abin dai yadda kowa ya iya shige da fice nima zan iya hakan ta juya ta fita tabar dakin cikin kunya ya bita da kallo.
Zuciyan Alh kan cike yake da zafin wanan maganan da matar tasa ta sameshi dashi wai yana kashe zarahi akan mutum daya kamar shi kadai ya haifa.
A karshe mikewa yayi yana kai kawo a dakin shi daya har hjy ta shigo ta sameshi hakan kallo tsoro tayi mai don ta fahinci akwai wani abu mai zafi dake damun mijin nata a lokacin.
A haka hjy ta sameshi a dakin binshi ta fara yi da kallo don ta fanci akwai abinda ya faru da maigidan nasu na bacin rai a lokacin.
Alh lafiya dai ta fada tana kallon inda mijin nata yake tsaye ya dan juyo ya kalleta tare da kawar da kai ba tare data iya furta komai a gareta ba.
Ido ta kura mai na dan lokaci kafin ta nisa tana fadin Allah ya sauwa har lokacin bai iya bude bakin shi ya bata amsan abinda take so ba.
Lokacin da hjy tashigo dakin shi bayan kwana biyu da hakan da turamen zani a hannun ta guda biyar tana fadin ga abin arziki Alh ta zube turamen a gaban shi saman table din dake gaban shi a falon shi din tace.
Gashi hjy karima ta bada a zuba a cikin akwatin modibbo da za akai gobe Alh ya dago kai a hankali ya dan kalli hjy ya girgiza kai tare da bin kayan da kallo yace ita karima din tabada wa yan nan kayan ?
Tace yanzu ina daki Ladi ta shigo min dasu sai kawai ya sake murmushi a fuskan shi yana girgiza kai yace angode ai.
Tun wanan lokacin hjy Addah ta fahinci akwai wani abu daya faru mijin nasu yace hakan kan kayan don ta dauka hakan zaisa yai farinciki a fili.
Sai taga sabanin hakan gareshi shiru hjy ta danyi na dan lokaci kafin ta mike tana daukan kayan data zube din a gaban shi.
Haka ta fita gwiwa a sanyaye ta kasa furta komai saidai zuciyata yana cike tab da zargi kan haka.
Bukin ya taso din hjy karima din ita ta jagoranci komai da akayi a ranan ta boye komai dake cikin zuciyan ta an tafi da ita a cikin sha,anin akan shawaran da kawayenta suka bata na ta daure a tafi hakanan da ita kada ta bari a gane akwai wani abu a kasan zuciyar ta.
Ganin har za,a fara sha,anin buki Abubakar bai shigo ba baiyi waya da kowa ba kuma sai hankalin iyayyen shi ya tashi sosai.
Daddy ya soma neman layin Abubakar din wayan ba ringing ba a daga va sai hakan ya kara tayar da hankalin daddy din sosai.
Ya kara kira karo na biyu akaci sa,a ya dauka daman ya kewayane a lokacin.
A cikin girmamawa ya fara gaida daddy din da daddy ina wuni, ya amsa da lafiya kalau shin ba zaka samu zuwa bane har za a fara buki.
A dan maraice yadda yaji muryan daddy din a cikin fushi yace dashi aimun hakkuri daddy ina tafe akwai abinda ya tsayar danine a nan ne daddy zan shigo kwanan nan insha Allahu
Daddy yace dashi a hasale zancen aure kafa akeyi nan da kwana biyu mai zuwa in Allah ya kaimu don haka idan kaga dama ka shigo idaman ba zaka shigo ba ruwan ka.
Yace daddy ayi min hakkuri ina sane zan shigo insha Allahu kada ma ka shigo aure daine ba fashi a cikin zuwa jibin ya kashe wayan
Abubakar din ya tsorata da fushin mahaifin nasa don baya fushi irin haka dasu har ya kashe mai waya idan suna sai gashi yau din ya kashe.
Don haka ya yanke shawaran kiran abokan shi a lokacin ya fara sanar dasu halin da yake ciki don mutum daya ya kira yace afadawa sauran don shi ba tarun abokai yake dasu ba.
Sai daren da aka fara sha,anin buki ne yazo da abokan shi da basufi uku ba suka diro garin a cikin dare a lokacin har hankalin hjy Addah ya fara tashi tana gudun dan ya aikata wani abin da zai bar masu abin fade ga mutane.
WwYayin da hjy karima aakuma duk take sane da komai dake wakana wanda take ganin duk alhakintane dana diyanta Allah zai fitar masu a nan.
Gida har ya fara cika da wasu yan uwan su da sukazo daga wasu auraren na daban a bagaren daddy ma shine tare da yan uwan shi dasuka tsure shi da korafi wai yaki hadin da suka so ayi a tsakanin yayan hjy Altine da Abubakar din.
Ya biyewa hjy Addah ta hada da diyar dan uwanta taki nasu din yanzu ga yarinya ta shiga wani hali don ta kwallafa rai ga hadin su da Abubakar din a rayuwan ta.
Daddy din yana zaune yana jin su kafin yayi murmushi ya kalli kannen nasa mata yana fadin kai kudai mata kuna da matsala.
Yau kuma har muna da bambanci ashe a tsakanin mu da gidan babfa namadi ashe a wurin ku ?
Yau ashe har kuna da bakin da zaku fadi hakan kuda bakin ku har kun manta da irin halalarci wanan tsohon a gare ku har zaku fadi hakan don kasa ya rufewa tsofin mu ido.
Kallon juna sukayi kafin hajiya Asiya tace mu ba hakan muke nufi ba yaya kawai dai don ganin yadda in anyi da ita hamida zumuncin zai kara karfi a tsakanin mu ne kuma yanzu.
Can din bazai kara ba ke nan ya fada cikin daure fuska kafin ya gyara zama yana dan dagowa saman kujeran tare da fadin.
Ina sin ku saurareni da kyau kuji kada ku manta ba haka tsufin mu suka koyar damu ba kan zumunci.
Har ma udan laifi shi Nuhu yayi aiba yar shi bane tayi laifin don kuma yar kuce yar Nuhu idan kun dauki hakan.
Yaya yanzu dai ai zancen ya kare dama mun fada mane kasan abinda Addah tayi muna bata kyauta ba tunda tasan akwai soyayya a tsakanin yaran nan tun farko amma ta nuna muna sin kai ga hakan.
To kuji nan wanan zancen shirmen ina son duk a barshi a nan kada inii wanan zancen ya fito idan da Allah ya nufi hamida ce matar modibbo.
Babu fashi ita dince zata kasance matar ba wanan din ba don haka na kashe wanan zancen tun a wurin nan ya fada yana komawa saman kujeran.
Dole ba fuska a wurin su suka bar falon yayan nasu rai bace don a yadda suka shirya sun so suba hjy Addah mamaki a wanan karon.
Haka dai akai sha,anin bukin hjy Addah na tsaka mai wuya ita bata tsira ba a gurin yan uwanta dake ganin laifin ta kanta daurewa modibbo gidi yake kokarin kunyata su.
A bangaren mijin ta kuma sun hade mata kai gaba dayan su taga canji a wurun su kan sha,anin bukin .
Duk kan da namiji daya tilo da Allah ya bata ake mata wanan abun da take gani yanzu gun dangin nata.
Anyi buki an watse lafiya kowani bangare sun nuna ba komai saidai na ciki na ciki a zuciyar kowan su a lokacin.
Alhamdullahi taro ya watse lafiya an kai amarya dakin ta uwarta tanuna yar yar dangi ce ita don uwar tayi mata goma shatara bayan wanda mahaifinta yayi mata kuma.
Kasancewan itace ya ta farko a wurin ta yasa ta nuna nata bajintan a dakin yar kowa nata sa albarka masu zagi kuma suna bi da zagi da gulma.
Agege lagos yau can abin ya daukeni yakai na sari doya ina bin layi shiga biyu nayi sa,a kamar na kifar ganin rana yayi sanyi yasa na dauki kati da kudina ina bin masu motan dashi don nasan zan sayar ko da zuwa gobene idan na kara fitowa.
Motace na hango lafiyayya a gabana sai walkiya takeyi na nufi wurin motan da sauri ina fadin buy credit buy rechage card .
Aka zuge glass din motan a hankali maishi bai min magana ba sai ga wani dan mashin a baya yace rechage card na sheka da sauri nakai mai card din ya karbi mtn na dari biyar yace give me five hundred change na bashi sai yake kuma kokarin wucewa da card din da kudin duka nace.
Olay give me my money nd my card u de call me thief becouse of ur money ?
no be thief u are ? U own my card nd my money u wan run with ur nape sai fada ya barke a tsakanin mu dashi a wurin.
Kaya kaya ya sauko ni kuma na fara gyara kayana da kyau ina shirin fada dashi murya mukaji a bayan mu ana fadin waitin de happen ?
Na juyo da sauri ina fadin na my money he wan run with bayeraben ya kara fadin oga i go nak dis yeye girl if she call me thief again.
No be thief u be na sake fada nima a hasale oya give her d money dan sandan dake da kayan kaki a jikin shi ya fada..
Mutumin ya kara kallona a shasale sai gashi ya miko min dari biyar biyar da sanda na bashi da kuma eani daga cikin aljihun shi yana nace olesi omo buruku, buruku dadani.
Ina tura kudin a cikin katon aljihun rigana mai zip na fada cikin dan hasala akai horn daga cikon motan nan na farko duk muka juya muna kallon motan.
Naji dan sandan nan yace bring card for my oga na juya da sauri zuwa wurin mitan farko data tsaya kwadayin ciniki ya kaini ga mai keken kuma.
Na isa wurin motan ba tare dana tsaya na kalli na ciki ba na fara fadin mtn zain etisalat, an glo five hundred two hundred own de.
Jin anyi shiru daga cikin motan yasa na dago kai a dan hasale don dama kaina yana kasa ina gyara katin dake rataye a wuyana.
Don haka ban kalli na ciki motan a lokacin saida na gaba na dago ina fadin oga talk naw me i wan go ina dago kai sai mukai arba dashi na dan so in razana don na kadu da ganin shi saboda na sheda fuskan a yanzu .
Sai dai gani biyu ne yasa ja she da hakan na farko zuwa kama mai laifi a gidan hayan mu sai na biyun da yazo karban wayan shi da ya fadi a hannuna.
Shine dalilin gane fuskan shi a yanzu da nayi har na sheda shi a wanan ganin da nayi mashi a yanzu.
A cikin dan rudewa nace oga u na good evening woo how much own u wan na dan fada a sanyaye yana zaune ido kawai ya kura min daga inda yake sin.
Sai na dan tsargu da hakan ga kuma irin kallon da yake minnna mamaki nikan ina ganin hakan sai na juya zan bar wurin da sauri.
Naji ance wait cak naja na tsaya a wuri daya ban kuma motsa ba ban juyo ba sai bayan yan dakiku naji murya na fadin come back my oga wan see u.
Na sheda muryan mai magana a lokacin dan samdam nan ne na tare dassu wanda ya rabani da mai Nape fada.
Na nuna kaina ina fadin emi ina tambaya ya kada min kai a hankali na fara dan takowa a hankali ina nufar su.
Nace oga na di card mtn eirtel glo which one u want na fada ina dago kai na dan kallesu .
Yace yana nunani da yatsa yace you where is your mother na dan kalli bayana da mamaki koda wani yake yi badani ba, a bayana .
Sai naga dai dani din yake magana nace she de for house ya sake fadin where ?
Nace In surelere side, yace from there you come here nace yes cikin gyada mai kai ya kura min ido na dan wani lokaci.
Kafin yace oya inter d car now take me to your mother place i want to see her wani irin mamakine ya baiyana a fuskana lokaci guda.
Nace a cikin rudewa da tashin hankali lokaci guda i de come let me pack my tins na fada cikin juyawa da sauri yana magana ai ban tsaya ba da sauri na shige cikin mutane kafin ai haka na shige wani kwarkwada na gudu .
Har ya tura dansandan yabini sai kuma ya sa ya dawo ya barni don yaga alaman ba zai sameni ba koda ya bini yadda wurin keda cun koson mutane da yawa haka.
Kai tsaye wani titin na bula na dauki shatan mai Nape sai gida duk da kayana da kudin wani dana dauki kayan shi ban sayar ba a lokacin.
Sai gani na iso gidan da wuri har umma na mamakin hakan gareni sai dai naki yarda in fadawa kowa wanan zancen nabarwa zuciyana hakan.
Sai dai na yanke shawara a raina cewa zan canza wuri ne nisa dasu