Showing 321001 words to 324000 words out of 382072 words

Chapter 108 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28405

kwanciya na kwanta.
Washe gari ya kama jumma,a da wuri muke shirin fita zuwa masalaci don mu samu sallah a lokacin cikin masallacin.
Kowan mu yana shirin umma ta shigo dakin da wani leda mai kyau ta miko min tana fadin yau jumma,ane mu saka fararen kaya mu fito.
Na bude ledan wani dogon rigane mai kyau da daukan ido kafin ma nayi magana take fadin in saka ba lokaci idan mun dawo zatai min bayani ta fita.
Ni dai na bita da mamaki faiza ta bude rigan tace na saka yana da kyau sosai gashi yau jumma,a dama ban so ba amma na daure na saka don umma.
Saidai ina jin don me zata kashe kudinta ta saya min riga haka ni ban saya mata ba haka muka fito dole motan dake kwasan su zamu shiga mu bisu kada mu rasa sallah a haram din.
Har mun zauna cikin motan na hangoshi ya fito shi da wasu mutum biyu shima fararen kayan ne na yan Pakistan a jikin shi sun karbeshi sun masa kyau sosai.
Suka shigo motan ya tashi ban yarda na dago kaina ba a lokacin don kada mu hada ido dashi tun kallon dana jefa mai lokacin da suka fito din na kawar da kaina gefe ina karatun wani addua a cikin wayana.
Har muka isa masallacin muka nufi wurin mata suma maza suka nufi nasu wurin har dare muna ciki muna ibada kafin mu dawo masaukin mu.
Duk dai gani nan banjin dadin kaina a ranan gaba daya tun safe ina jin bakin rai muna sauka mota su mama Amina suka tareni da fadin yar nan ashe abin arziki ya samemu haka yau ?
Ban fahinci me take fadi ba a lokacin don haka murmushi kawai nayi mata na wuce zuwa ciki na barsu suna tafe bayana suna fadin wanan abin da mamaki yake babu abinda bai iya faruwa ga bawa idan Allah ya nufa dama ?


ZAINAB IDRIS MAKAWA




ANA DARA GA , , , , , , , ,

9️⃣7️⃣BY, , , , , , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL AFUWW, , , , , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257

ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋

A hankali yake saukowa daga matakalan ya na tsikayo muryan mahaifiyar shi a waya tana yanka salati tare da fadin aure fa wani irin aurene haka kowa bai san da shirin saba ?
Kafin ya karaso wurin yaji tayi shiru tana saurare wanda suke wayan dashi lokacin har ya iso ya zauna ba tare da yayi mata magana ba yana dan tunanen shi.
Kalman data fada yasa shi dago kai da sauri yana kallon ta taci gaba da fadin dolema ai ita Sahiba din tasan da shirin auren ta dama sukaje can watau sun raina damu nan har zasu gwada muna mu bamu isa ba ko bamu kaiba.
Da ansan abindata shirya ke nan da aiko su hamza din kada su tafi balle su dauki wanan rainin hankalin nata.
Nina dauka a yanzu muna da kima da darajan da zata kawo miji nan a daura mata aure amma don ta gwada muna bariki auren ma a can saudiya zasu daura shi.
Wai sahiba ce tayi aure kowa mami yake tambayanta da zalla tashin hankali a idon shi karara don wanan zuwan ya dawo da niyar yin yadda ya dace dashi da mahaifin shi koda mami din bata soba kuwa.
Sai gashi tunda faran safiyan ranan da yake saka ran dawowan mahaifin shi suyi zaman karshe da mami din kan kudirin shi kunnen shi ya tareshi da wanan zancen a bakin mahaifiyar shi.
Zubur ya mike yana fadin sahiba fa kika ce mami Sahiba din itace tayi aure a can saudiyan dama aure sukaje yi a can bata sanar da kowa ba sai kuma ya juya ya fita kafin ta bashi amsa.
A rude ta kashe wayan tana kwals mashi kira saidai ko juyowa baiyi ba balle ya amsa kiran da take mashi da the boy boy fa dakai nake bakaji bane wai.
Don sam ta manta da wani zancen so da yake min abaya motan shi ya nufa kai tsaye bai tsaya ko ina ba sai gidan ya Abubakar da yake zaton da sanin shi akai komai.
Wanda baisan shima sai bayan daurin auren da baffah suka nuna isa sukai min ya samu labari ba duk da su baffah sun fada mai yadda zancen ya kasance amma yaji ba dadin rashin sanar mai da kuma rashin tambayan ra,ayina da basu samuyi ba.
Don ya fada masu cewa su fara tambayana ra,ayina kan hakan da mahaifiyar mukhutar din tazo masu da bukatan tana son hadin iri a tsakanin mu dasu don abinda danta kawai zai muna ke nan ya rama halarcin mahaifin mu gareshi a cewan ta.
Yace su tambayeni suji ra,ayina don yasan halina fiye dasu zan iya tara masu jama,a a can ayi yadda ba,a so a tsakanin amma kuma da suka zauna dasu umma sai a karshe shawara ya tsaya kan cewa gara dai ayi din kamar yadda suka bukata tunda su sun isar min ai suke gani.
Da wanan shawaran suka tafi masalacin bada niyar daura aure a ranan ba amma sai kanin mahaifin shi mukhutar din dake cikin su yace ga sadaki gaba daya tunda suna wuri mafi tsarki a duniya a lokacin ai gara kawai ayi komai daga baya sai ayi duk shagalin da za ayi in an koma gida.
Wanda ba bata lokaci kuma bayan idar da sallah suka gaiyaci mutanen dake wurin aka tsaya aka daura aure akan sadakin dubu dari kacal a musulunce.
Horn ya dinga yi da karfi saida maigadin gidan ya fito a gigice yazo ya bude mai zan iya cewa wanan ne zuwan shi na farko duk tsawon zama shi dan uwan shi a lokacin baisan yadda gidan shi yake ba .
Don abinda ke tsakanin su na rashin jittuwa da basayi ra,ayinsu yasha bambam dana juna a yanzu din ma magana yazo ya fadawa dan uwan nasa akan burin shi ya cika sai ya zuba ruwa a kasa yasha.
Horn din motan yayi ta dannawa hakan yasa ya Abubakar din fitowa dagashi sai dogon jallabiyan dake jikin shi a lokacin.
Yayi mamakin ganin Al, mustapha din gidan shi sam bai kawo akan wanan zancen yazo mashi gida ba a lokacin sai gashi yana dan kakaro murmushin dole a fuskan shi don ganin dan uwan nasa a gidan sa duk da baisan abinda ya kawo shi gidan ba lokacin yasan dai dole akwai wani dalilin zuwan shi gidan wurin shi.
Haka ya karaso zuwa inda yake kokarin fitowa a cikin motan shi a fusace shima sai ya daure fuskan shi yadda ya ganshi din.
Salamu alaikum ya fada tun kan ya karasa isowa inda yaken rike wanan salaman munafuncin nazo nayi murnane kan sherin da kake bina dashi.
Har ya fito a fili haka kayi nasaran rabani da Sahiba a wanan karon saidai ba zaka iya raba zumuncin dake tsakanin mu ba ai.
Kaifa baka da hankali duk da nasan ba yinka bane wata kila a buge kake ma yasa har ka fadi hakan in bashi ba nine zan rabaka da sahiba ko wanda ya aure ta a yanzu .
Juyawa yayi ya kalli yan sandan dake kofan gidan suna gadi wanda suma din su suke kallo daga inda suke kafin ya juyo yana murmushi ya kalli dan uwan nasa yana fadin.
Kaci arzikin a gidan ka na sameka da ba haka ba yau dana nuna ma dan drugs nake na gaske saidai ni shana ba kowa ne yasani ba ai don banyi shan da nake zuwa mashaya kamar na wasu tsofin a baya ba.
Ido Abubakar din ya runtse tare da hade dantsen hannun shi kamar mai alaman shirin kai masa naushi a lokacin.
Ashe kana da wanan labarin kaima saidai wanda ya fadama koya baka labarin cewa tare suke zuwa da manemin matan da har tsufa ya kasa daina gara wanda yayi da kurciya ya daina yanzu ai.
Wa kake nufi da hakan ke nan yace wanda ka fada abokin cin mushen sa nake fada na kurciyan da sukai sha,shanci tare ya daina shiko yana ruwa har yanzun.
Wani kallo ya kureshi dashi kamar zai dukeshi kafin ya kuta ya juya ya bude mota zai shiga sai kuma yaja ya tsaya yana fadin .
Kaci bashin wanan kalman daka fada a yanzu sahibs kuma ka rubuta ka aje cewa saina aureta muddin ina raye.
Shirme ke nan don a yanzu Sahiba tafi karfin ka fiye da yadda kake zato don wanda ya dauki garabasan ba sa,an jan wanda ma kake takama dashi bane balle kai a yanzu.
Shima jan idon shi ya zubo mai kafin ya kuta yana kokarin murda key din motan ya kara fadin zancen bashi kuma ni Abubakar bana cin bashin kowa a rayuwa.
Nan yaja mota a haukace Allah ya taimaka ba kura a gidan dake malale da inter lock a ko ina na haraban gidan daya bata mashi jiki a lokacin da kura.
Binshi yayi da kallo tare da furta mahaukacin banza kawai da wofi ka dauka zaka zo min da hauka na kyalekane .
Ya shiga ciki yana mai jin zafin kalaman dan uwan nasa a kansa inda yake nasa irin matakin da zai dauka kan mustapha din nan gaba da sai ya raina kanshi.
Da sauri saurina dawo dakin mu don haka kawai naji jikina ya mutu kwanciya nakeso kawai gomama batayi ba na bi lafiyan gado tare da kashe wayana na kwanta sai barci.
Can cikin dare ba mike na tashi ban daki na shiga na fito da alwala nazo duk suna barci basu san ma na falka ba a lokacin.
Na dade zaune ina sallah a wurin kamar yadda na saba yi ko a gida tun lokacin dana samu dakin kaina ina yawan yawaita nafila da dare kamar yadda naga umma na yawan yi a baya can da muke kwana daki daya dasu.
Har na idar na dan kishingida a wurin ina tunanen mafalkin da nayi har ya falkar dani lokacin ido na mayar na rufe saiga hawaye yana zubo min a hankali.
Yauni da bansan Abbana ba a fili nice ke mafalki dashi har na samu albarka daga bakin shi nasan akan dai zancen yadda na dage na bankado asirin yan uwan shi har na ganshi a cikin mafalkin nawa na yau.
Har lokacin da zamu tafi sallah yayi alam ya buga hakan yasa na dan dago na bubuga gado su faiza suka tashi mikewa nayi nima na kara yo alwala zuwa lokacin da muka fita gashi washegari zamu bar madina ina jin wani iri a raina wanda bani kadai ke jin wanan din ba lokacin.
Munje an taso kamar kullun inda maza sukazo suna fadin mu shirya kayan mu karfetakwas na safe zamu dauki hanyar zuwa makka da faiza da fatima duk a kage suke aje makkan a lokacin.
Kowa sai faman har hada kayan shi yakeyi lokacin su sister kamar yadda suke kiranta har manyan su suka shigo dakin namu.
Kallon inda nake kwance ta fara yi tana fadin a, a ina dake akace za a fita yanzu kuma na ganki a kwance haka hankalin ki kwance.
Tana kallona take wanan maganan idonta a kaina har ta zauna faiza ce take fadin wai dani take magana fa na dan juyo ina dan murmushi nake fadin.
No bani ba sai kuma na juya da turanci ina fadin ba inda zan sake fita sau anjima idan mun fita sallah dai na fada ina gyara kwanciya.
Kai matar yaya ba dai izza ba da takama kin kumayi dace kinzo inda ya dace zanso ganin ki keda Anty Battula a gidan ku.
Waitin she talk na tambayi Faiza ina kallonta kafin takai ga ban amsa aka turo kofan umma ce ta shigo suka gaisa kafin ta juye min harshe da yarbanci tana fadin .
Wallahi wanan tsohuwar ne tazo wai zata fita dake yanzu tana son zaki rakata zaban kaya a wani shago ki daure ku tafi kuma banda , , ,
Haba umma ga yayan ta nan ai babu zaben da bazasu iya ba daba sai naje bani nifa ban son shigewa mutanen nan na fada ina bata raina don Allah ya gani hakan bai mun dadi ba.
Ki tashi kuje tunda ta roka dake zata tafi kina son in fada mata bazaki bane ko in mata rashin kunya kikeso nace ban yarda kije ba tunda kina yata.
Zan tafi naba umma amsa a takaice tace tagode amma kada ki dade ki fito tunda ta shirya tace ta sake fadin in kula da kaina don Allah.
Haka na tashi na shirya raina a bace don dai babbace zan raka din haka kuma umma din da tayi min tsaye sai in tafi yasa na shirya don dole na fita .
Har nakai kofa ina jin wanan din dai da suke kira da sister ita matar auren kenan tana fadin Amarya ke nan a dawo lafiya ban kawo komai a raina ba na dauka don katon hijjabin dana saka take min sherin hakan.
Dakin su umma na fara zuwa muna cikin magana aka turo kofan wanan budurwan yar wancan tawagance ta shigo tana fadin waini suke jira gasu a waje.
Tare muka fita da Rukkaiya din zuwa dakin su sai gasu su fito shine a gaba uwar tana baya tana gyara mayafin jikin ta a cikin hausan da bai zauna mata ba take fadin au ga yar tawa ta fitoma ashe yanzun muke niyar bin bayan ki.
Kafin ta rufe baki nakai kasa irun gaisuwan mu na yarbawa na bar girma gaba dayan naje kasa ina gaida ita da sauri ta dagoni tana fadin kai kai haba dai ke yatace fa yanzun mun kara zama daya sosai daku ki daina hakan kinji.
Yi nayi kamar ban ganshi a wurin ba muka jera muka fita na dauka da Rukkaiya din zamu fita dukan mu ashe dagani sai sune kawai fitan.
Wani motane lafiyayye a waje muka sama ita muka shiga shida driver suna gaba muna baya da tsohuwar sai yaren su sukeyi da banji aikina kawai bin garin da kallo yadda aka tsarashi.
Wani katafaren ajen sayar da gwala gwalai mukaje motan ya tsaya muka fifito muna kallo wajen amma shi baiko damu da kallon da mukeyi ba din.
Yake fadin bissimillah hjy mu shiga ko zamu shiga din ta juye mai da yare ya dan juyo ya kalleni yana min guntun murmushi.
Nan muka shiga wajen har kasa a kwai gina na shagunan gwalagwalan gasunan kowa na kira kazo ka saya sai binshi mukeyi zuwa wani babban waje.
Bayan an bamu wajen zamane mun zauna suka shiga kawo irin kayan da suke dashi a wajen muna dubawa da kudin su .
Wanine ya dauke min hankali na rike na dan juyashi har bayan shi zubin shi yaimin kyau sosai ga gani da nice zan saya wanan din zan zaba saidai ban san ra,ayin maishi ba.
Ban kuma san wace zasu saiwa ba a lokacin muryan shi naji yana tambayana da wanan dai yana da kyau ke nan ko naga kin rikeshi.
Kamar ba zan bashi amsa ba sai can nace eh yana da kyau sosai design din yayi min baida girma ko nauyi saidai kudin shi yayi yawa sosai nake gani.
Idan yana da kyau kawai a dauka ya fada ba tare da damuwa ba sai kuma yakai hannun shi ga wani shima dai zubin shi gaskiya kamar yafi wanda na zaba din yace wanan fa ?
Sai lokacin zaice yaga murmushina kadan har diple dina yana dan lutsawa nace kamar yaso yafi wanan din ma kyau din ban gashi ba sai yanzu duk a harshen turanci dole muke magana.
Ai is ok uwar ta fada shida kanshi ya zabo wasu awarwaro ya hada da kayan sai mamaki su nakeyi a raina don nasan uban kudi suka tara a wana wuri lokacin.
Bayan yan canza magana kawai naga ya tura masu kudin su a take muka fito zuwa lokacin ashe har yamma yayi ke nan na fada a raina ba zamu samu zuwa sallah ba a haram ke nan.
Wanda banso hakan ya kasance dani ba a lokacin muka dauki hanya a zatona masalaci zamu ko gida sai gamu wani wajen kuma nan kan sayayya sukayi sosai ina mamakin tana da wasu yara ne dai haka ashe bayan su sai gab da sallah magariba muka nufi masalaci a can muka hade da yan uwa.
Bayan mun dawo ne faiza taso bugun cikina da ina kayan da muka sayo nace suna wajen masushi a can na barsu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login