Showing 9001 words to 12000 words out of 382072 words
Amma saukin abin haka mutane suke zirga zirgansu ba tare da andamu da yanayin da garin yake ciki ba.
Wuri ta samu a gefen titi tabi jerin masu sayar da kaya saman titin itama sai dai tana dan nisa dasu kadan don kiran kasuwa kowa a wurin kusan haka ake tsayi a wurin.
Sai da ta gama shirya komai yadda ya dace ta zauna tare da aje ledan da zata rufa idan ruwan ya gwauce ta fara hura wutan gason masaran.
Dan yayafi aka fara a hankalin a daidai lokacin data dago kai tana wani tsaye a gefe dan tako kadan ta ita yana kallon duk abinda takeyi a wurin.
Ta dago don daukan leda ta gyara koda ruwan zai zo da karfi ta rufa suka hada ido dashi daga inda yake tsaye din.
Tun data zauna din take kula dashi tsaye a wurin ci gaba tayi da abinda takeyi na gaso tana fadin azo a saya.
Ruwane mai karfin gaskene ya dauko lokaci daya hakan yasa kowa ya gyara kayan sana,ar shi a wurin hakan kuma bai hana masu son saya su tsaya ba.
Wani ne yazo kamar zai saya sai kuma ya tsaya yana son ya kawowa Sahiban iskanci a wurin ta dinga masifa dashi .
Ganin haka yasa ya dan matso daga inda yake tsaye din a cikin turancin shi dake nuna shu din ba mazauni lagos bane na gidi ya kore mutumin a wurin ta.
Jin dadin hakan yasa ta dan cewa dashi ta gode taci gaba da abinda takeyi a wurin na sayar da masara din ba tare data kara kulashi ba.
Kallon yarinyar yake daga nisa ta bashi matukar tausayi don wanan bata koyi sa,an hafsa babban yar hjy karima ba balle su Nabila da suke ciki daya davewa kannen shi dake gida.
Ya lumshe ido gami dajin tausayin tallaka yana ratsa mashi a zuciuyar shi shidai wanan yarinyar Allah na yawan hadasu da ita tun shigowan shi garin lagos din.
Muryan ta yaji tana yare a cikin yarbanci tana kallon shi kafin ta juya da turanci tana tambayan u no sebi yaruba ?
Kai kawai ya gyada mata tace o i see if no worry meka help u stay under my ledda .
Kafada ya dan daga don wanan din ma mai kama da yare da tayi sai da kyat ya iya gane me take nufi da hakan.
Haka suka dan shiga ledan kusan duk haka wasu suka samu suka dan laba ga ledojin masu talla a gefen titi din wa yanda basu son ruwa ya tabasu ke nan.
Hankalin shi naga titi yana kallon masu suce a surin ita kuma tana faman gyaran kayan ta kada su jike da ruwan saman.
But u are new here ba ta tambayeshi ya gyada mata kai kaiwa don duk a kage yake ya gaji da wanan yanayin da suke ciki gara da itama a dan tsugune take saman wani roban penti karami.
Wuta ta dan taba da hannun ta a take ta furta subbahanallah wai Allah na da sauri ya dan kallota kafin yace kin iya hausa ne dama ?
Ita fadi take lah kai bahaushe ne kaima saidai yanayin hausan nata duk da ta iya yana dan surki da harshen yare alokacin.
Mamakine ya kama shi sosai na yadda ta saje da yan garin har ba a iya bambamta ta dasu ya kara dan satan kallon yanayin yarinyar ba inda tayi kama da hausawa ko kadan.
A nata dabi,an shine idan taga bahaushe kamar taga dan uwanta najini ne a garin don haka ta dauki masara daya mai zafi ta mika masa.
Kai ya girgiza mata don bai saba da irin wanan ciye ciye din ba tace take zakaji dadin shi ya karba dole yana fadin nagode.
Ba damuwa taci gaba da abinda takeyi fuskanta a dan sake ke yar inace ya tambaye ta ba tare daya sake kallon ta ba.
Ni nidai hausace amma ban san sunan garin mu ba amma umman mu tace garin mu arewa ne .
Arewa wani gari ke nan a cikin arewan tace ban sani ba tana dan jera masaran data samu ta gasa a lokacin .
Mamakine ya kamashi shi ya sake jefo mata tambaya mahaifin ku fa take fuskanta ya sake a lokaci guda har saida gaban shi ta fadi.
A zuciyar shi yace ko dai irin shegun yayan nan da ake shigowa bariki a haifane su tashi a garin lagos din a wahalce karshe su zama yan daba masu batawa arewa suna.
Don yanayin ta da yaga ya canza da tambayan da yayi mata din sai can ta bude baki tace umman mu tace tun kafin a haifi Amar kanina mahaifin mu ya rasu iya abinda ta fada min ke nan kawai.
Allah ya jikan shi yace ya mayar da kanshi gun masu wucewa harkan gaban su yana kuma kula da yanayin su don abinda yazo nema wurin.
Meye sunan garin ku ta jefo mashi tambayan sunan garin mu kaduna kin taba jin kaduna ko tace kwarai kuwa a cikin history ko ba a stete din queen Amina take ba ?
Tambayan yaso ya bashi dariya don yadda ta fada din sai a lokacin ya kara kallonta ya fahinci iya shekarun ta.
Wata rana zaki kai ziyara ke nan tace umman mu tace akwai nisa sosai a nan kaga kuwa bazanje ba tunda kudin motan shi ba da yawa da naje naga garin da tayi mulki da ake fada.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA, , , , , , , ,
BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AR, RAHHAMANIN RAHIM, , , , , , , , , ,
LITTAFIN NAN NA KUDINE YAR UWA KI BIYA DON ALLAH KADA MU RIKI JUNA DON TSORON ALLAH A ZUCIYA YAKE BA A BAKI BA, , , ,
Idan ke me tsoron Allah ce zaki gane hakan da kanki don zuciyar ki ba zai barki ki aikata abinda ba daidai ba yar uwa Allah yasa mufi karfin zuciyar mu Amin.
Kada ta halaka kanta ta halakaki don kawai karatun da ba,a zuwa dashi lahira iyakar shi nan duniya abarki da nauyi wani a kanki.
Mamakin ikon Allah yakeyi wai yar arewace ita kuma bata san komao game da arewan ba amma tana kurin ita bahaushiyace don yadda ta nuna data ganshi kamar taga wani dan uwanta na jini.
Yanzu idan nace zamu tafi arewa nida umman mu da dan uwana kamar nawa zan kashe ta tambaye shi tana kallon shi ido da ido.
Shima dan kallon ta yayi duk da wahalan da take ciki hakan bai hana shi ganin irin halitan da Allah yaiwa yarinyar ba wanda ba boye yake gareshi ba.
Gaban shine ya fadi ras ras don bala,in kamar da sukayi da Batula diyar baffa kabiru dake karatu a waye.
Haba shi dai yarinyar tana yi masa kama da wani fuskan daya waye dashi da farko amma ya rasa a ina yasan wanan fuskan nata ne ?
Bakaji ba nace nawa zai kaimu arewa mu uku a musali ?
Yace zaku je arewan ne ?
Tace yanzu kan banda kudi tunda umman tace kudin yana da yawa sai dai idan na girma zanta tara kudi sannu a hankali wanda zai kaimu arewa din nida mahaifiyata da dan uwana.
Ji yayi muryan ta yi tankar na diyan gidan su da dan diple din ta dake lutsawa sak irin nasu wani iri yake ji a kirjin shi lokaci guda zuciyar shi ta shiga balaguro a tsakanin iyayyen shi din da ya sani amma ya kasa gano ko yar waye ita kanshi yaba amsa ba kama daine irin na ikon Allah amma hakan bai yuyuwa ai ina sam kamane kawai.
Dagowa yayi yaga hankalinta na gun mai sayen masaran ta a lokacin suna cinikin da baifi naira hamsin zuwa dari ba kallon tarin dan masaran da take gasawa yayi sai yaji wani tausayinta ya kara kamashi lokaci guda.
Ya tuna yanzu yan uwan shi suna can a cikin sanyin AC da jin dadi ita wanan boyar Allah gata a cikin ruwan sama yana dukan ta.
Dan saba,in din da taiyi cinikine take washe baki tana fadin yau na fito a sa,a gashi har na fara ciki a cikin ruwan nan sai kuma ta sauke idon ta ga hannun shi kallon wanda ta bashi tayi baiko ciza ba tace.
Bakaci ba ko wanan din bai maka bane in canzama wani tana kallon shi yace No yayi min zan tafi dashi ne inci anjima.
Leda ta fara nema a cikin kayan ta, ta miko mashi ya saka a cikin zuwa lokacin ruwan saman ya tsaya cak don haka ta yaye ledan data rufamasu din.
Ya mike yana yi mata godiya akan zai tafi tace au baka fada min kudin motan ba zaka tafi yace dubu hamsin zai kaiku har abincin da zakuci ko wani garine zaku a cikin arewa din.
Ido ta kwalalo waje kafin yace ko kuma a jirgi zaku tafi jirgin sama zaki kashewa kowan ku dubu hamsin din akala dai ko kuma a jirgin kasa saidai zaku dan jima a hanya baku kaiba ta jirgin kasan amma yafi saukin kudi gaskiya.
Kila sai idan na girma na fara aiki ko na samu babban shago zan dauki umman mu muje arewa ina son in san yan uwana ina son in san garin mu kuma da kowa nawa.
A ranshi yace idan kina da uba ko amma a fili sai cewa yayi idan kin tara kudin ashe zamu ganku arewa ke nan duk lokacin ya gaji da wanan zuban da take mai maganan dole yake mata don yarinyar na bashi tausayi sosai a cikin dan hiran da tayi mai din yanzu.
Sai anjima yayi mata ya juya zai tafi tace dashi har zaka tafi ke nan ko sana kazo yi kaima a nan kamar yadda yan can ke zuwa nan neman kudi don haka kawai taji ya kwata mata a rai yadda yake magana shi da yanayin shi ya nuna natsuwa a gareshi.
No nazo neman wanine a nan ya fada ta dago a cikin mamaki tana fadin a wanan erea din namu yake da zama tambaye shi.
Ban sani ba ina dai neman shi ko zan dace Allah yasa ka dace ya fada tace amin ya juya ya tafi ita kuma ta dago kai wani uban hadarin aka kada hadawa har yafi na farko haduwa a yadda ya taso din.
Oni yau na shiga uku da iya wale a gidan mu ina zan saka kaina da fitinan iya wale ke nan ta fada tana gyara kayan sana,anta don bata da niyar barin wurin.
Tausayin ta ya kara kamashi don haka ya dan taka zuwa inda take sai gani kawai tayi an miko mata sabbin yan dubu daya zasu kai ashirin ga nata lissafin.
Da sauri ta dago kai tana kallon shi kai ya kada mata alaman ta amshi kudin ya nuna mata hadarin a cikin alaman maganan kurame yayi maganan.
Ga mamakin shi ga yarinyar data fito neman kudi a cikin wanan uban ruwan haka ai zata karbi wanan kudin sabbi haka dasu kar .
Amma sai yaga ta gyada mashi kai tana fadin a,a kabarshi nagode ummana ta hanani karban alherin zama don ba don Allah suke ba mace abin hannun su ba sai da dalili.
Cikin mamaki ya tambaya yana fadin su mazan tace kwarai haka umman mu ta fada kuma umman mu bata taba fadan abu ba daidai ba.
To ki karbi wanan din kicewa umman ku din wani bawan Allah ya baki su sadaka don yaga kina wahala a ruwa haka idan kuma baki yarda da hakan ba sai muje wurun umman naki in bata da hannun ta.
Ai zata karba ko idan ita na ba a hannun ta din sai ta dan tsaya tayi tunane kadan kafin ya ji tace to barin paka kaya sai mu tafi din yace karbi kudin ki rika idan munje sai ki fara bata kafin ta fito din ta karba ta cusa a cikin wani katon aljihu a rigan jikin ta da bai kula dashi ba sai lokacin.
Gidan kusane ko don ni zan wuce na cigaba da duban wanda nazo duba din tace dashi nan kusa ne kadan yace to mutafi don haka ta dauko kayan buuuu tana gaba yana binta a baya yana karayiwa yanayin ta kallo .
Koda tace gidan bai da nisa sai tafiya yaga sunayi a cikin ruwan cabo ga kazanta ko ina irin na lagos amma haka take takawa a cikin rashin damuwa ita.
Shine ke dan tsayawa kaucewa yana kin wani yanayi na bacin rai a gare shi don haka tayi mai nisa sosai dabara ya fado mai yayi kamar yana waya ya hango ta ta shiga wani lungu hakan ya bashi daman jada baya daga nan ya sulale mata ya gudu.
Kamar kullun ta shiga gidan da sallaman ta a baki kamar yadda ta saba shiga idan ta dawo duk da sanin su musulmai basu da yawa a cikin gidan sosai.
Amma hakan bai hanata yin sallama idan zata shiga aiko iya wale na zaune a kofan ta duk wanan sanyin ruwa da sabon hadirun da aka hada din a lokacin bai hanata kasawa ta tsare ba tana sakin habaici ga umma dake dakin su labe ba.
Tana ganin shigowan Sahiba dauke da kaya da sauran tarkace tasan batayi wani ciniki ba don ruwan ranan yaki bari aji dadin sana,a a ranan.
Nan ta miko hannu tana fadin Oya give me my renting money and my property i wan go inside.
Kallon ta sahiba tayi tana fadin i dey come now i no forget with your money now.
No be now i nter d house, i no even see my mama self, your money de for my mind since i cary ur tins.
Look Omo, me i no wan wahala woo just give me d money u promies me.
Dan tsayawa Sahiba tayi da mamaki hali irin na iya wale da son kudi da fitina tace .
Oya cary d money, u tink sey i me no get d money to give u now, if give u dis money now i no go baro your tins again.
Iya wale tace eh make u no baro wan again naw, just qui qui give me d money first.
Duk da uban kayan dake saman kanta a lokacin haka ta tsaya ta tura hannu ta zaro dari biyu ta mikawa iya walem tana jin haushi a zuciyarta ta wuce zuwa dakin su da sauri don abinda ke gabanta.
Allah nagode ma Sahiba kin dawo ke nan nikan nasan wanan hadarin yau da wuya ya barki kiyi wani cinikin kirki a garin nan yau.
Umman mu tare nake da wani mutum a waje ya ban kudi dayaga hadari yace in dawo gida shine naki karba don kin hanani karban kyautan maza shine yace wai muzo wurin ki tare dashi kinga kudin nan yana waje yana jiran ki fito.
Zuwa yanzu fuskar uwar ne ya canza a sanyaye tace Sahiba kin san shi ko kinsan koshi waye.
Da sauri tana girgiza kai tace a,a umma wallahi ban san shi ba asalima ban taba ganin shi bani nidadi kawai tausayi ya bani da ruwa ke dukan shi nace ya shigo ledana ya fake .
Da zai tafi yaga an kara hada hadari ya ban kudi yace in koma gida ruwa yayi yawa yau a garin.
Sahiba yaushe kika fara magana da mutane irin haka har ki fara karbo kayan wasu zuwa gidan nan duk da irin huduban da nake maki a kullun.
Hasbunalah hasbunallahi wani,imal wakil umma don Allah kada ki zargeni ga hakan kada kiyin zato kan abinda ba zan taba aikatawa ba koda a bayan ki.
Jikin uwar ne yayi sanyi lokaci guda don abinda diyar nata ta fada sai dai bata yarda ta nuna sarewan ta akan hakan ba na fada maki kiyi hankali da maza ke dama kowa a cikin garin nan dake din da dan uwan ki amna kuke a wurina duk danice na haife ku.
Ko banza gari irin wanan bariki dole sai ka kula da kanka sahiba yau kaji wanan ya samu wance .
Gobe kaji ai wancen ga abinda ya sameshi shiyasa a kullun nake kafa kafa da rayuwan ku da nawa a garin nake zama wawiya mara wayau ga kowa a garin nan .
Badon komai ba don kawai mu tsira da mutunci mu a garin nan yanzu kinje yau kin karbo kudin wanan mutum gobe kuma da wata zance zaizo maki don ba zai baki abinsa a banza ba.
Yanzu zan fita in masa kashedi a kanki yayi nisa dake kema hakan ki nisance shi