Showing 171001 words to 174000 words out of 382072 words

Chapter 58 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28412

Yasha aure basa haihuwa ko kuma idan sun haihu diyan su mutu sai aka camfashi cewa da diyan kudin shi ke hafbaka don haka aka dinga tsoron auren shi.
Lokacin daya hadu da mahaifiyar Sha,aban bai boye mata komai ba duk abinda ake zarga mashi din ya fada mata da yake bahaushe akwai karfin hali su hakan bai basu tsoro ba ya aureta ta haifa mai diya biyu kuma sunanan raye.
Sai kuma suka juyacewa ai ba diyan shi bane su shiyasa yaran suka tsaya jin haka shikuma lokacin yana raye yace gaba daya duka iyalin shi za,aiwa gwajin jini sai sukaki yarda wacan da diyanta suje tun lokacin yaran suka fita rayuwan shi.
Amma bayan mutuwa shi an raba gado dasu an basu kason su kamar yadda musulunci ya shimfida .
Saidai Allah bai raba daya ba don yanzu su saidai sunan mahaifin nasu dasuke amfani dashi don na komai daga cikin abinda aka raba din nagadon su.
Duk a wanan taron na tsunci maganganun a wurin matan dake gefena ta baya inda Allah ya rufawa Sha,aban da mahaifiyar shi asiri shine kamar su sak da mahaifi nasu har dabi,un shi duk na mahaifin nasu ne .
Lokacin da aka kirasu zuwa wurin babban limamin don suyi addua ne, nabar jin me suke fada don na tashi na barsu a wurin suna hiran su na gulma.
Lokacin da suka tashi din don zuwa gaban liman din banyi niyar tashi na inbi bayansu ba tunda iyalan mamacin akakira zallah.
Amma tun da natuna da worning din da yai min yasa da sauri na mike nabisu a bayan muka fita tare dasu zuwa gaban liman din.
Yadda suka rusunna haka nima na rusunna adan baya dasu kadan ana addu,an ina amsawa da amin amin har na gaji da duki can muka taso muna bin limaman dake zaune muna zuba kudi kamar yadda akeyi dai.
Muka dawo wurin zaman mu muka zauna bamu dade da zama ba aka kawo masu abinsha dana taunawa gaban su aka aje nabi drinks din da kallo na dago kai muka hada ido dashi na girgiza kai alaman kada su taba komai fa.
Zaune nake kawai amma na mayar da hankalina ga abinda ya kawoni tun lokacin da naga an fara yawo da abinci don kada a samu matsala a bangarena.
Zakace hankalina yana gun program din da akeyine a wurin saidai a zahiri ina kallon abindake wakana dasu ne a fakaice a wurin.
Can sai ga wata mata fara tas irin hajiyoyin lagos din nan itama mai jiki kama mahaifiyar oga din daganin ta da yanayin shiganta zaka gane itama hamshakiyace dai tazo ta rungumi mahaifiyar Ogan namu sun dan dade tare haka suna magana.
Sai bayan tafiyan ta matan ta wuce ne na farga da abinda ya faru a lokacin saboda baka dauka yadda sukayi da junan su kadauka akwai wani na mugun nufi a tsakanin su.
Na rasa yadda zan sanar dashi an samu matsala sai dabara ya fado min wayana na tura mashi text da fadin if possible kasa mahaifiyar ka ta canza gyalen jikin ta yanzun nan akwai sherin da aka shafawa gyalen kada ya taba jikin ta .
Sai aka samu akasi bai dauki wayan ba a lokacin don mutanen da sukai yawa a gaban su suna kawo gaisuwa lokacin.
Na rasa yadda zanyi kawai saina danna mai kira ba kakautawa na matsa da kiranshi ina kashewa har yakai ya ciro wayan nasa ya duba sai yaga sakon da sauri ya dan juyo na gyada mashi kai alaman eh.
Rubutu na hangoshi yanayi ga wayan shi ya turo min What would we do now ya aiko min da sako na tura mai da fadin mu tashi zuwa resting room zan kawo mata gyale yanzu kada kowan ku ya bari gyalen ya tabeshi.
Ya gyada min kai bayan na tura mai da sakon sai kuma na turawa Adnan ta wayana nabi bayan su zuwa dakin hutun da zasu jira din.
Muna kai kofan nake jin uwar na masifa don me wai ya dago dasu zuwa nan sai da muka shiga ya kalleta yace akwai matsala don akwai abinda aka shafa maki a jiki ki a wurin rungumar ki yanzun nan shi muke son ki cire wanan gyalen da sauri ba tare da maganin ya taba jikin ki ba .
What ta fada kafin tace Lalalala haram haram ta fada tana yare cikin larabci shima yaren ya fara mata jikin ta yayi sanyi sosai tana fadi kalas kalas yallah yallah.
Ta juya turanci tana fadin shine tsiyata da mutanen nan wallahi baka zuwa sai wani ya nemi da yahalaka yaga bayan ka.
Ganin zata kaiga barin abin ya tabi jikinta yadda take fada na taka zuwa inda suke a cikin ladabi nace dashi zancire gyalen a jikin ta yanzu sai ya yafa mata na jikina kafin akawo wani Adnan zaizo yanzu dashi insha Allah.
Hakan mukayi yaja wanda ke jikina ni kuma na cire nata ya yafa mata nawa din tayi tagumi tana kallon ikon Allah gabanta sai faduwa yake mata anan ya fada mata cewa kada su yarda su taba komai naci a wurin.
Adanan ya kirani ya dawo na fada mai inda muke yashigo ya mika min na walwale kai mata gyalen maikyau dashi ta yafa ledan mukai amfani muka saka wanan a ciki.
Iya tunanen duniya yayi shi a rayuwan shi don ya gano gaskiyar maganan da yaji a bakin Nazifa matar shi don yana son ya dago wanan case din ba tare da sanin kowa daga cikin mahaifan shi ba.
Abune wanda yake son binciken siri don haka gaba daya a yanzu sai bai yarda da yan ahalin shi ba don duk yana zarginsu dayin rubda ciki a gadon uyan maruyun Allah da aka bari bayan kashe masu mahaifi da gangan .
A wanan fanin yasan yana da evidence ko umma ta ishesu shedan komai ga irin bayabar da tabayar a lokaci don an kashe mata miji a gabanta ta kuma san ko suwaye sukayi shi.
Saidai ta ina zai fara wanan binciken nasa yanzu karshe dai yayi tunanen zuwa police station ya binciko wanan case din saidai hakan ba zai yuyu a gareshi ba sai a sirce zai gudanar da komai yadda ya tsara din.
A gidan sa kuma duk wani dabaran da nazifa zatayi mai yaci abinci ya kaucewa wanan zai fita yaje waje ya hada take away ya zauna a motan shi yaci don kada wani ya ganshi girman shi ya fadi.
Yauma zai fitane da safe yana shiri tana zaune gefen gado ta zuba mai ido tana ba yar ta nono take fadin.
Nasan a gidsn hjyn ku kake cin abinci yanzu don baka yarda da girkina ba kana nufin za a hada kai danine a cuta maka ko me koda yake ma ba kaine mai laifin ba mommy din ai tasan hakkina ne yanzu in baka abinci ba ita ba amma take baka don kawai a kuntata min.
Dakatar da abinda yakeyi yayi yana kallon ta tare da fadin Nazifa kanki daya kuwa koda a can nake cin abincin ma laifi ne idan naje can naci abincin ?
Ai kin fi kowa sanin cewa mommy ce mahaifiyata don baki da kunya zaki bude baki kina fadin wanan banzan maganan haka a gabana yanzu.
Ta tabe baki tace dama ai haka akeson ya kasance a tsakanin mu shiya ake kirkiro abubuwan da akasan zanyi magana a kanshi.
Saukin abindai mutum bai iya rabumu saidai yayi sherin shi ya barni wallahi indai nice.
Ya rasa abinyi sai ido daya zuba mata wai uwarshi take fadawa wanan maganan haka yana mamakin rashin iya maganan Nazifa haka
Wace ma bata iya boye sirin uwarta da ubanta ba wajen katobara wa zata ragawa ga duk abinda ya fito a bakin ta wautane ko rashin tarbiya ke damun ta ?
Wani haushi ya shigeshi nata ta ya juya yana saka talkama a kafanshi a cikin kulewa da ita yaji muryan ta tana fadin wai fitan zakayi baka karya ba da gaske ?
Don kawai na fadi gaskiya bai kulata ba sai tura wayan shi da yayi cikin aljihun ya dan juyo ya kalleta a cikin takaci yasa kai ya fita yana jin ta tana mashi masifa har ya bar jiyo muryanta don nisan da yayi da ita lokacin.
Haka muka wuni a wanan wuri Allah ya taimakeni ina fashin sallah a ranan don haka na biyewa abinda sukeyi har aka gama muka kwasa zuwa gida bayan anyi rabe raben gift masu tsada da jawabai daga yan uwa da abokan arziki da suka san mamacin a baya.
Dole saida muka koma gidan nasu tare dasu don haka nakai yamma sosai a ranan ban dawo ba sai dare na shigo gida na samu umma a cikin damuwan rashin dawowa gashi na wuni ban gida a ranan.
Koda nayi sallama a kofa na tsaya ina cire takalmana a cikin gajiya na jingina jikina ga bango ina kallon umma dake amsa min sallaman yaran Avdulhamid ne a falin tare dasu suna kallo suka dago suna kallona tare da yi min sannu da dawowa.
Na karba na nufi cikin dakina ina fadin umma ina zuwa don a matse nake na watsa ruwa don yanayn da nake ciki a lokaci.
Na dade a cikin bayin na fito na zauna na gyara jikina ba zancen yunwa sai barci a tare dani don haka na dai fita naje muka gaisa da umma ban dade ba nayi mata saida safe na dawo dakin na kwanta.
Washegari ban tashi da wuri duk da nasan gidan Oga zan koma a ranan aiki kuma an fada muna mu fito da wuri akwai abinda zamuyi da safe.
Sai dai gaskiya gajiya bai barni nabi umurnan ba a ranan nafito na samu umma tayi alale wanda yaji kwai sosai cikin sa da kifin teku sai kamshi ke tashi suna zaune har yaran Abdulhamid suna ci yaban shawa sosai amma na kasa zama naci ko kadan saboda saurin da nakeyi a lokacin.
Goma ya wuce da yan mintuna a lokacin haka nayi masu sallama a gurguje na fita daga gidan na samu abokan aikina har yemisi suna falon farko zaune muka gaisa suke fadin karfe nawa na fito nida akacewa mu fito tun safe.
Wuri na samu na zauna oga jimone ya fara magana kan aikin mu na jiya da mukayi ya yabawa kowan mu daba,a samu wani kuskure a wurin kowa ba a lokacin.
Yar aikin gidan ce ta fito tana fadi a cikin yaroba ance Sahiba tazo idan tana nan jin hakan yasa na mike nabi bayan ta muka shiga ciki tare.
Bakin su nan nan basu tafi ba son haka gidan yake da jama,a cike gashi kayan aikine a jikina na saka bakin wando da riga fari ta ciki sai corth din mata dana saka baki a sama kayan sun matukar karban jikina sosai.
Suna daki da hjyn shi ta sauka a nan na samesu zaune tare da wasu bakin su suna hira na gaida su a cikin mutunci na mike zan fita hjyn tace oh Allah sarki yarinyar jiyace ashe ?
Na danyi murmushi zan juya in fita muka hade da Ogan mu da zai shigo dakin da suke din don yayi sallama da bakin da sukazo masu daga arewa zasu koma gida jirgij karfe daya na ranan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA




ANA DARA GA, , , , , , , , , , ,

5️⃣1️⃣ BY, , , , , , , , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL HAFIZ, , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA ZAKI TURO DA KATIN WAYA KO BANK TA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959557

Hjy fatima farar macece sol saidai bata da tsayi sosai amma kuma ba za a kirata gajera ba kuma mai tsawo ba tana da kyau don kana ganin ta kasan tayi zamanin kyau irin nata
Tana da dan fada sai dai ba irin sosai din nan ba can don inda tayi nan take barin zancen bazata rike a rayuwan ta ba.
Nagane hakan ne don yanzu a tare dasu nake dan zaman su damu a kasan nan da zasuyi ya azamin nauyin fita dasu ko zama ina kulawa dasu a cikin gidan don ganin masu shigowa da kuma motsin su.
Saidai gaskiya hakan ba a banza zance mukeyin aikin ba don akwai alheri sosai da muke samu ga hakan a kulun daga garesu kinga ko aikin bai zama na banza don baga albashi kawai muka dogara bake nan ai.
Ranan danayi wanka zan fara sallah a gudan su sallah azahar ya riskeni ranan ana sallah na mike na shiga bandakin da nake kewayawa a cikin sa na dauro alwala nazo na tayar da sallah anan falon su Allah da ikon shi hjy ta gitto ta ganni ina sallah anan ta shiga tana mamakin irin halina haka babu sakewa ko zakewa ga sha,anina duk da yanayina ya nuna akwai hutu a tare dani amma ina nuna a karkashin su nake komai a cikin girmamawa zan masu shi.
A, a kece kike sallah anan baki shiga daki ba ta fada kafin ta shige ta kara da fadin idan kin idar zamu fita dake unguwa dan an jima kadan ta fada a karshe.
Na idan na dan zauna nayi addua kafin na jawo jakkana na fito da kayan makeup din dake ciki na gyara fuskana kadan koshi naga duk macen da zata shigo a cikin kwaliyan ta take a fuskanta yasa na dan fara yin make din haka ba dabi,ana bane yin makeup.
Daga driver saisu biyu da yarta muka shiga motan zuwa wani unguwa mai nisa dasu munje gidan wata mata dana gani wurin addu,an ranan so close to her .
Mun zauna a falon matar sun gaisa muma mun gaisa da ita suna dai hiran yaushe rabo a tsakanin a cikin hiran sun ne naji ranan da zasu koma.
Kusan sau biyu muna hada ido da wanan matar sai tayi saurin kawar da idonta daga kallona saina fara zarginta don mugu bai hada ido da mai iska sau uku ko biyu.
Can matar take fadin wanan kyakyawar yar dai tun shekaran jiya nake ganin ku tare da ita hala da ita kuka zo daga can ?
Hjy ta dago ta kalleni tana fadin wai wanan yar a, a anan dai muka sameta danki ne ya hadamu da ita tun zuwan mu yanzun ma rakomu tayi nan kin san shi da rashin yadda .
Haba wanan ai kyauta haka abin tsorone sosai dan tafi kama da yar ruwa saboda kamannin ta ai dariya hjyn oga tayi tana fadin mace maikyau sai ta zama wani abu kuma don kyaun ta matar tace nan lagos nefa hjy fatima.
Sai matar ta kara kollona tana dan murmushi take fadin anya kuwa wanan ba sallon yan zamanin nan bane kuwa ya fito maki dashi don wanan ai batai kama da yan aiki ba sam.
Hjy Fatima mahaifiyar shi bata gane mai matar ke nufi ba tace ai ba aikin gida nake nufi na dahuwa ko wani goge goge ba a ma,akatan su dai take aiki tare dasu.
Yaran nan sun iya bata sau wallahi haka dai ya fada maki shi amma wanan ai ba haka yake ba kema kin sani sabo kawai ya turata kuyi kada daga baya ki nuna baki son zancen.
Anya haka zancen nan yake kuwa don nasan halin sha,aban sosai ke dai mubar zancen matar ta fada saboda bata dauka na iya hausan da sukeyi din ba yasa ta juye yare zuwa hausa sama sama don bata iya yaren sosai ba.
Mikewa tayi zuwa kawo mana wai abin tabawa duk da bata sanda zuwan mu ba haka ya ban daman kallon ko ina na falon nata don hankalina bai kwanta ba a lokacin.
Can idona ya gano min abinda yasani mikewa da sauri don yadda na zabura saida suma suka fitgita dani don tsoro.
We most live now before she come back with her evil act now now na fada cikin fidda idona waje ina umurtan su da hakan.
Aishan tsoron yadda taga mayi taji ta fake a bayan uwarnata don saitin kafanta nake kallo sosai ganin basu tashi ba yasa na nuna abin da hannu ina fadin go back to ut owner don't try to touch any one here again.
Ai Aishan saita mike uwar ma hakan suka fara tafiya ban fita ba saida suka fita nabi bayan su har sun shiga mota na bude na kalli gidan ina fadin back to ur send d evil sprit.
People are saying dis to hajiya ban taba yarda ba har hjy zata iya cuta min duk irin taimakon da nayi mata a duniyan nan ashe.
Mama i told you duk ranan da naganta ko zan ganta sai nayi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login