Showing 354001 words to 357000 words out of 382072 words
tare a gidan yau kuma ace kinje kina masifa ?
Koma meye ai dole ya dawo gidan nan ya sameki babu ruwanki da ita a yanzu don game din ai bai fara ba ko tunda baiko kwana a wirin ta an gani ba amma yanzu da kije an samu abinda ake jira a kanki ke nan ai.
Wani kallon hasala ta watsa masu kafin tace dasu a fada mana na isane idan da ban isa ba aiba zasu fada ba tana magana a hasale cikin yaren kanuri.
Kwat ba zamu bariki ki fita a yanzu ba karamarsu ta fada daga inda take fitan kina nufin zubar da kiman kine a idon mutane ai basai kinje kin sameshi a can ba dole dai ya dawo gidan nan komai tsiyan su eh,heh.
Ranta ne ya kara baci sai kawai ta nemi kujera takai zaune don kafarta bazai iya daukanta ba yadda takeji.
Shima brother wani irin zuwa gidan amaryane yanzu da ranan nan haka aina zata saida darene zai tafi can din yau ko ta kalli yan uwan ?
Shine ai kawai dai halin maza yake son ya fara nunawa tun yanzu waishi ga mai amarya wanan farin fatan yake rudin shi kome a jikinta mace hakama ba wani fasali gareta.
Kallonta yar uwan tayi sai kuma ta kumshe dariyan ta dake cinta kada yayan nasu dake zaune hasale tace bata damu da damuwarta ba ita .
Amma da badon hakan ba data bawa yar uwan nata amsa da cewa ki kalli kanki keda kike baka kirin ba fasaline kike zagin wata haka wace duk da a rufe muka ganta alama ya nuna cewa ita din mace ce har mace fuskantane kawai basu gani da kyau ba.
Gashi duk wani memo din buki iya hannayen su a hade kawai ake nunuwa babu fuskokinsu a jikin abubuwan da aka raba na bukin.
Wanan kuma duk aikon sister ce don bakin sanin da tayiwa hjy falmata din ko a photo zata iya shanmatan mutum karamin aikintane wanan din.
Sanin hakan yasa sister tasa komai da aka buga bata yarda anyi amfani da photun muba a ciki amma duk da hakan saida suka gane dalilin sister din.
Da kyar dai suka samu ta koma daki bayan sun gama surfa muna zagi ta uwa ta uba cikin ma wai basu da tarihina ke nan amma duk da hakan saida nasha zagi iya inda suka tsaya.
Shima a nasa bangaren abinda ya guda ke nan tun farko bai daga wayan ba tunda ina dakin ina barci lokacin yasan zatayi mai fitina sai bai dauki wayan ba don kada injisu.
Hakana rai bace ya fito zuwa sallah daga masalacin bai dawo nan ba gidan mahaifiyarshi ya nufa suka gaisa nan take fada mai su gwaggo sin bugo waya sun isa lafiya suna godiya kan karamcin da akai masu .
Alhamdullahi ya fada dan jin sun sauka lafiya kafin ya mike yana fadin zai karasa gida tun safe daya fito rakiyan su bai koma gida ba.
Har ya bada baya yaji hjyn na fadin kadai san yau a wurin sahibs zaka kwana ko dan ina tsoron halin da falmata ta fito dashi yanzu kan auren nan.
Yanzun ma daga gidan ta nake ya fada tare da dan juyowa yana fuskantar mahaifiyar nasa yaci gaba da fadin tundana raka bakin nan airport ban koma gida ba har yanzu shine ta bugo waya tana surfa min zagi waini dan cin amana azzalumi tun yanzu na fara da hakan dukkan mu zatayi maganin mu ai dagani har sahiban .
Ka gani ko wanan dalilin yasa banso zuwan falmata wanan sha,anin ba tunda bata kasan nan sai gata kamar an jefota saukin abin ma dai anyi an gama lafiya bata tada wani fitina ba a gaban mutane.
Murmushi ya sauke a fuskanshi yace Allah dai ya sauwaka dadin abin ma anty hafsat tana wurin itace ke hanata yin wani abin idan tasoyi.
Nima zuwan hafsat din yayi min daidai tunda na ganta sai naji dadi a raina amma bayan ita ai duk sauran irin su daya da falmata din kamar ba Lamice ta haifesu ba.
Ni zan karasa yacewa mahaifiyar nasa kada ka biyewa shirmen ta don yanzu an tabata komai zata iyayiwa kowa musanman ma kai da kaimata laifin.
Ya kara dan murmushi yana shafo fuskanshi a hakan ya fice daga gidan mahaifiyar nasa tabishi da kallon tausayi don har ya fada ya danyi baki tasan shi shi mutum ne wanda baison yawan hayaniya dama.
Suna falo har ita ya shigo tunda ya hangosu ya daure fuskan shi tafiya yake a natse yayin da duk suka bishi da kallo saidai ita madam din ko kallo bai isheta ba.
Da kyat dayan kawar nata ta iya budan baki tace dashi sannu da dawowa ya amsa mata ciki ciki yana jin madam Falmata najan uban tsoki yasa kai yayi part din shi.
Yana shiga kwanciya yayi a yadda ya shigo dakin takalma kawai ya iya cirewa a lokacin tace ba abinda ke yawo a kunnen shi sai kalman azzalumi data kirashi dashi.
Ta ina ya cuceta har tayi mai furcin wanan kalman mai muni haka amma zai nuna mata tayi babban kuskure kan fadin hakan .
Shi duk sauran babatunshi bai taba damun shiba a yanzu amma wanan kalman na azzalumi shine ya tsaya mashi a rai yanzu.
Yaso ta bashi hadin kai a zauna lafiya a yadda ya fara fahintar sahiba da alama tana da saukin kai tare da biyayya ba kamar yadda ya zata zaisha wahala a kanta ba.
Kofan ta turo a fusace yasan itace don ita kadai ta isa ta shigo mai daki a yanzu kuma koda bayab shine don ds farko ta dauko kannen nata su shiga amma ya takawa hakan burki sun daina a yanzu.
Ka dawo daga cin amanan naka ai sai ka koma can ka karasa don kwananta ya fara ke nan daga lissafina bazan yarda a kawo min wanan cin amanan ba a ha,inceni kan wata can da bata da asali.
Sai lokacin ya dago da mamaki karara a idon shi ya sauke a kanta kafin yace Falmata kada in kara jin kin kira wanan yarinyar da mara asali koda kuwa a gidan karuwai na dauko ta.
Ai kinfi kowa sanin tana da asali asalin ma da yafi nakowa tunda ke din shedane da arzikin mahaifinta nz gina nawa a yanzu.
Kin sanin kinsan gidan mau me nake dashi kome ke akwai a gidan mu dacan baya lokacin da kika fara guduna don bamu da komai ?
Yanzu kan itama din da mamaki ta fara kallon shi kafin tayi karfin halin fadin au ashe don dukiyan mahaifinta ke nan ka aure ta ?
Yes of course don shi na aure ta saboda itama din dorne ce tana da kudin ta tana da kaddarori ga ilimi kinga ashe ba don kudi ta aureni ba sai don biyayya ga iyayye.
And by the way kalman azzalumin na kada in kara jinshi a bakin ki me na rageki dashi a rayuwa ko me na ha,inci rayuwan ki dashi don kawai na kara aure a yanzu shine zaluncin nawa kome ?
Ko nayi maki alkwarin cewa zan zauna dake ke kadaine a rayuwana bazan kara aure ba me kike so a rayuwa da ban maki shiba.
Nakai kowa naki makka na gina maku gida na bawa yan uwanki maza har wanda ban taba sani ba jari yau don na kara abinda zuciyana yake so shine zalunci a gareki ?
Mukhatar yau ni kakewa gori haka akan yar yarbawan da baka san ko ita din wacece bama tukunna ?
Koda bayerabiyace ita haka na ganta ina sonta kuma hakana balle kinga asalinta kin kuma ga yan uwanta kinsan ko waye ita.
Wani kallo ta watsa mashi kafin tace ehh lalai mukhatar wata kila harta dandana maka agumon bujenta na yarbawane ko ka haukace haka lokaci guda ?
Bata dandana min bako zata dai dandana min sai na karasa haukacewa ga baki daya ki kuma iya bakin ki don ba zan dauki wanan sakarcin da kika soma ba a yanzu.
I want piece in my life da kowa kuma kada kiyi kokarin zubar da girman ki da kimarki a idon yarinyar nan don you will regret it later.
Duk kan wanan yarinyar kake fada min magana hakaan fada maki haihuwana kikayi da bazan fada maki ba ki fice min daga daki ya isheki hakana ya fada a hasale sake kallon shi tayi taga da gaske yake a yau kafin ta girgiza kai ta juya ta fice daga dakin rai bace itama ta hau sosai a lokacin saidai ganin yau shima ya hau fiye da tsamanin ta, taba kanta salama.
Jin karan yadda ta bugo kofan yasa yan uwan nata dake zaune zaman jiran jin yadda zata kaya a tsajanin su
Jin yadda ta bugo kofan yayi kara yasa suka kallon kofan da sauri itace ta fito rai bace ko kallon inda suke batayi ba ta wuce zuwa dakinta fuuu a hasale.
Binta sukayi da kallo kafin dayan ta daga hannu alaman meya faru sai dayan tace ni data barshi kawai tunda dole itama ai ya kulata.
Zakice haka mana tunda kin likewa mai mata kada ai maki hakan ta fada tana hararan yar uwan ta mike zuwa dakin yar nasu suma sauran suka bita.
A kwance suka sameta ta kafawa rufin dakin ido tana tunane jin sun shigone yasa ta daga masu hannu alaman su barta kawai a lokacin.
Yasa suka juya suka fice a dakin suma zuciyoyinsu babu dadi a lokacin ganin yanayin da yar uwan nasu take ciki na tashin hankali kan kishiyan da aka kara mata yanzu.
Suna isa falo babban tace wai meye abin yi yanzu ta tambayi sauran sai ta tsakiyan tace meye kuwa mu meye amfanin mu muje gidan kawai mu latsa shegiya tasan ba wurin zamanta bane nan din.
Idan munyi haka fa yana iya shafan mu karshe muma yace zai kore mu kusan halinshi idan ranshi ya baci kodai bamu duke taba muyi mata warning akan antyn mu din zaifi.
Ni dai ban goyi bayan hakan ba yanzu da kawai mu bari muji kan zancen kada muje muyi abinda ba daidai ba dama gashi dangin shi kaf sun tsanemu.
Nan dai sukai ta shawaran yadda abubuwa ke tafiya a yanzu din tare da sgan alwashin zuwa gidan nawa suyi min warning nan gaba kadan.
Bayan na fitone daga part dinshi na shiga daki banga fatima a ciki ba kayan jikina na rage kafin na kewayawa nayi tsarki tare da dauro alwala na fito nafila na fara kafin lokacin sallah na mike na gabatar da sallah farillah din.
Kofa aka turo a zato ko shine fatima ce ta shigo tana ganina take fadin au kin shigo har kinyi sallah ashe yanzun nan fa nake fadin Allah yasa kunga time din sallah yayi ai.
Barci nayi wallahi tun dazun na sani shiyasa na fara aiki a kitchen kafin ki fito aikin me ke nan na tambaye ta aikin abinci mana ba,a nan yau uncle zaici abincin dare ba ?
Cikin ya mutse fuska ina mikewa nake fadin me i don now woo, i no sebi dis kind of wahala, may be na here he go eat ?
Murmushi ta sake a fuskanta tana fadin nan ne mana tunda dama saboda bakine bai zauna nan tun jiya ba ai yanzun ko bakin sun tafi sai ku fara amarci ke nan tana dariya.
Kyale ta nayi naci gaba da nade hijjabin sallah danayi take fadin tun safe fa bakici komai ba nace banajin cin ina kokarin dauko wayana a cikin jakka da tun da zamu fita na saka a ciki ban kara bi ta kanshi ba sai lokacin.
Ina bude wayan misscall nagani ratata a wayan sunayen masu kiran nawa wanda kusan su gwaggone da suka isa gida suke kirana lokacin.
Nan na fara kiran su ina masu ban gajiya tare da godiya suma suna dan kara min da nasiha ha zuwa lokacin da Fatima ta idar da sallah zata fita na kirata da hannu lokacin muna waya da umma.
Tazo tambayanta nayi me take dafawane tace wai tuwo tayi da miyar taushe don taga darene za a fi son shi kai na gyada mata har ta juya zata tafi sai kuma ta juyo tana fadin .
A kwai wata mace da tazo tun dazun tace hjyn su uncle ce ta turo wai ta kama maki aiki muna kitchen din tare da ita tun dazun na gyada kai.
Mikewa nayi nabi bayan ta da wayan a kunne na muka karasa kitchen din dake da dan nisa da part din a nan na samu matar itama ta idar da sallah tana nade dankwalinta data shimfida.
Tun kan mu gaisa da ita nace haba haba dai badai a nan kikai sallah ba ga falo can ga kuma dakuna a ko ina a gidan .
Matar tana dan murmushi ba wata babba bace sosai take fadin nan ma yayi min ai ba laifi ai wurin tana kara kallon wurin kafin tace da Fatima din itace matar gidan ko ?
Eh itace sai gata tana rusunnawa kasa ta fara gaidani da fadin ina wuni hjy da sauri nace da ita no kada ki sake daga haka na fara bude wasu kuloli masu kyau dana gani an rufe.
Tuwone da aka mulmula a cikin farar leda sai nason zufan zafi yakeji gashi ya tuku da kyau gwanin ban sha,awa sun kai leda biyar a ciki.
Sai kuma dayan da aka saka miyar da sukayi tayi kyau sosai kallon sukeyi duka suji me zaice sai ji sukayi ina fadin masha Allah yayi kyau sosai.
Ga drikin nan da ferfesu munayi ta fada nace duk yaushe za a cishi din yau din nan ?
Kusan tare dani suka karrasa girkin muka fito don la,asar yayi a dakin fafima dakin dasu gwaggo suka zauna ne a nan muke har me aikin sai bayan magariba ne naji waya na kira na dauko shine a layin yake fadin.
Kuna lafiya ko lafiya naba da amsa yace ok da fatan an girka min abinci don nan zan kwana yau insha Allah.
The food is ready na fada yace ok ganin tafe idan na fito wurin hjy da sauri naga fatima ta mike bayan na kashe waya tana fadin.
Na tashi na kimsa kada ya sameni hakanan kallon mamaki nake mata sai naga ta dan marairaice tare da fadin wallahi haka akeyi koda zai shigo saiya yasameki a cikin kwaliya zaifi.
Wanan mai aikin ne tazo min sallama wai zata koma gidan hjy don a can kayanta yake mukai sallama da ita nayi mata godiya ta tafi.
A nan don dole na tashi din na shiga wanka ban jima ba na fito na samu fatima har ta fitar min da wasu kayan sakawa wani material ne mekyau yana dan kyalkyali an mashi dinki bubu .
Tsab na shirya a cikin shi fatima tana gyara min sai mamakin yadda akayi tasan irin wanan abubuwa ina mamakin yaran hausa da komai a yanzu sun sani sai gani na fito tsab dani da gani dai kasan amaryace ni din.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA , , , , , , , ,
1️⃣0️⃣6️⃣BY, , , , , , , , , , , ,
ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AD,DARR , , , , , , , , , , ,
ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257
ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U 👋
Ko ina na dakin tsab yake ba dakin ba har gidan duk Fatima tabishi ta gyara ta saka kamshi tare da taimakon wanan matar da hjy ta turo ta taimaka min .
Don haka gidan ya kara haske ga nutsuwa ba wani hayani saina kiran da fatima ta kunna dake fitowa daga dakina a hankali, yana kuma karama mai sauraron shi natsuwa.
Don duk dakin muyi shiru muna bin karantun a lokacin ciki ciki yayi sallama daga kofan tare da dan jira mu amsa mai don yasan ba ni kadai bane a dakin balle ya shigo ciki kai tsaye.
Kamar sallama ko anty haka yasa na dago kai daga kallon wayan da nakeyi lokacin ina mai kallon kofan nima.
Wanan karon nokin yayi don yana zaton bamuji sallaman nasa bane haka yai daidai da budan kofan da fatima tayi da sauri taja baya tana mashi sannu da zuwa.
A cikin fara,a ya amsa yana fadin a a badai tsoro yasa kuka shige daki ba a wanan lokacin dare baiyi ba is just past nine yanzu fa ?
Tana murmushi daga inda take tsaye take fadin muna dai hirane