Showing 216001 words to 219000 words out of 382072 words

Chapter 73 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28433

sun zauna a jikinane koda yayi aikima ba zai gane koni wacece ba a yanzu.
Dama nasan da hakan ya Abubakar ya fada don ni naji da kaina yana waya nayi kuma tunanen hakan tun lokacin
kai kuma a kwai aiki Abubakar din a gabanka ya nunashi da yatsa ya nuna kanshi yana fadin shi shikan ai bai tare da wani aiki a yanzu mai yawa.
Dan murmushi na sake yace abinda kake nema nasu yana karkashin kulawan mahaifin kane don da hannun shi akai komai.
Wani irin zabura ya Abubakar din yayi lokaci guda yace kwarai kuwa amma idan na fada maka zaka yarda ka je office din su na tsohon ajiya bayan bakar kanta can kasa layi na uku daga barin hagun ka idon ka zai sauka a wani tsohon jan file zaka samu duk abinda kake nema kake wanan wahalan haka.
Yace ya gode ba don ya yarda da hakan ba har kasan zuciyarshi ya dauki abin shirmene shi amma a fili ya amsa da to kawai.
Don yana ganin mahaufin shi ba zai taba wanan badalan ba shida ke kawowa mutum ayah kan komai da mutum zaiyi zai sa hannu ga wanan aika aikan haka amma zai gwada don ya tabbatar da gaskiyan lamarin.
Sun dauki lokaci a tare dashi gaba dayan su ya fadawa kowan su matsalan shi wurin ita umma akan yan uwanta akai mata magana kan lalai tayi gagawan zuwa garesu tun lokaci bai kure mata ba sai Abdulhamid shi kuma an fada maicewa yan uwanshi sun masa abinda kada yayi arziki don suma basu tara ba sai don haka idan yana son kanshi da arziki ya daina nuwa ko matarshi yana da budi ko wasu abu suna shigo mashi a lokacin.
Malam akace yayi gagawan komawa akwai mara lafiyan da suka zo daga nisa dake son taimakon shi duk da sun san ba zai iyaba amma ya nemo wani suka fada mai inda zai sameshi wai shine keda makarin ciwon maralafiyan dake jiran shi dain agida lokacin.
AKarshe yayi masu alkawarin cewa zai fita bada dadewa ba in Allah ya yarda hutu kawai suke ba godiyan su a yanzu.
Abu wasa wasa har suka kai goma da rabi a gidan mu ana abu guda zuwa lokacin an kira malam yakai sau biyar wai yazo yayi baki daga katsina.
Haka dai sukaiwa umma sallama suka tafi kowan su cike da mamaki abubuwan daya wakana a wurin a mota malamin ke fadin lalai akwai manyan abubuwa masu karfin gaske akan yarinyat nan .
Nisawa yayi daga inda yake tukin motan din shi tunanen zancen mahaufin shine ya tsaya mashi a rai da baisom ya gaskanta hakan kada ya zamo gaskiya da wani ido zai dubi wa yan nan mutanen idan hakan ya zamo gaskiya.
Bayan ya sauke malam sunyi sallama ya kawo abinda zai bashi ya bashine ya tafi ya samu sunyi barci a falo ya rufe gidan ya tayar dasu haka ya kwana yana tunanen maganan aljanin har yana jan tsuki.
Washegari bayan sallah asuba ya koma ya kwanta don barcin dake idon shi bai falka ba sai bayan tara yayi wanka yana shiryawane umma ta kirashi a waya a daidai lokacin nazifa zata shigo dakin taji yana fadin yaya jikin nata mama da sauki dai ko ?
Bataji me aka fada ba hakan ya tsaya yana sauraren umma dake fada mai yanayin jikin nawa a lokacin yana fadin masha Allah zai shigo anjima idan ya fito.
Sunyi sallama da umma din ya juya yaci gaba da shirin shi jin batayi magana ba yasa shima bai juyo gareta ba tunda bata iya gaidashi da kwana kullun yana mata fadan hakan.
Wai wata mamace kake wanan wayan da ita tun jiya hakane ta tambayeshi tana mai tsureshi da idanu ya juyo a cikon mamaki yana kallon ta tare da tambayanta wata mamace ?
Ina ruwan ki da sanin ko wata mace ko banda ikon waya da kowa sai kin san wanda nake waya dashi kiji da abinda ke gaban ki kafin ki shiga hurumin wani.
Wani kallo tayi mai tana fadin bangane wanan na kamar ya naji da abinda ke gabana meye a gabana din ta sake tambayan shi.
Wani kallo yayi mata tare da fadin ohh ke yanzu halinda yan uwanki ke ciki duk garin nan ya dauki zance ba abin damuwa bane a gareki ko ?
Koda yake banyin mamaki don banga shitin hakan a gareki ba dama ko kadan yaja tsuki kuka ta fashe dashi tana fadib dama shike nan kuma da abin ya shafa kai min gorin hakan balle wani na waje.
Wanan muma ke kika daukeshi a gori tunda suke asibitin nan kin dafa abinci kin kai masu ko ki sai wani abu akai masu daga tambayan dawa kake waya zaka fada min wanan maganan haka.
Ina ruwan ki da wace nake waya kije duk abinda zuciyarki ya naki shine din ya fada ya dauki hular shi daya dora saman gado yakafa a kai tare da daukan agogon shi ya daura a hannun shi yana nufar hanyar fita daga dakin.
Itama mikewa tayi tabi bayan shi tana fadin wallahi idan ma da watace kake waya in fada ma kayi kadan wallahi kace zaka kara min kishiya a yanzu.
Jin hakan yasa ya tsaya a kofan yana kallonta a cikin mamaki yace haka zuciyar ki ya baki dama to haka din ne don kin canka a daidai ya fice daga gidan ga baki daya.
Gidan su ya nufa har lokacin yana jin rashi a bace yake mai sun gaisa da mommy yake tambayanta mahaifin shi tace da safen nan yayi tafiya zuwa ghana daurin auren yar abokin shi.
Ok kawai yace yayi shiru kafin ya kara fadin yaushe zai dawo ke nan tace zuwa jibi nasan don bukin baby ya kawo jiki yanzu ina zai tsaya can kuma.
Hakane ya fada yana mikewa tare da fadin shi zai tafi sukai sallaman da mommy din ya kawo falon sune yaji muryan Faiza na fadin yaya na daina samun sahiba a waya kwanan nan.
Wallahi naso tazo wurin bukin nan ko zan ganta inga yadda ta koma yanzu wallahi yaya naso ace zata zo din.
Murmushi yayi daga inda yake tsaye yana fadin kinsan lagos akwai nisa da nan din kuma aiki takeyi kin sani yanzu.
Kamar wani buki can ta damu mutane Allah yasa sahiba tazo idan sahiban tazo ma waya damu da zuwan ta kin damu mutane.
Ban daiyi dake ba idan ma kowa bai damu da itaba nina damu da ita hakama nasan akwai wa yanda suka damu tazo don nan bayan ni.
Ba wani buki bane bukin yar uwan naki Nabila kadafa ki manta baby yar uwar haihuwan kice look ban son inji ko inga wani abu ya fito daga wurin ku har a kare bukin nan ya nunasu da yatsa duka ukun cikin daure fuskanshi garesu.
Ba zakaji ba brother insha Allahu hauwa ta fada daga inda take zaune cikon ko in kula da zancen da sukeyi mai tun shigowan shi.
Mommy ne tafito daga dakin tana tambayan meya faru kowan su yayi shiru na dan lokaci saishi ne yace na fada masu kada naji wani tashin hankaki daga wurinsu kan lamarin bukin nan da za ayi.
Mommy takai zaune tana fadin me zaikai bakin yaro a ciki iyaka dai ayi a watse lafiya shike nan bukin da ajirace ake damu mu tanka a sauke muna abinda akeson fadamuna dama me zai kaisu fitina nadai fada masu gaskiya ai.
Nima abindana fada masu ke nan yanzu ya fada yana kallon mahaifiyar nasa kafin yai mata sallama ya nufi inda yake son zuwa kai tsaye tsohon office din ya nufa.
Bayan ya nemu izzinin shiga an bashi don sanin koshi waye a wurin su din kwatancen da akai mashine yabi zuwa wurin kantan komai bai mantaba yadda aka fada har yakai daidai wurin files din .
Idon shine ya sauka saman jan file din na kasa ya jawoshi yana kakabe kuran da takardan kedashi yaga an rubuta murder case da kwanan wata da komai a cikin sa.




ZAINAB IDRIS MAKAWA


ANA DARA GA , , , , , , , ,

6️⃣4️⃣ BY, , , , , , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL HAKKUM, , , , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257

ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋


Ranan kan na samu barci sosai yadda na fara hakama saukan shi yazo min don saidana shaki barci kusan wuni daya ina abu daya sai yamma na tashi.
Gidan ne yayi min shiru na mike zaune ina duban wayana da ban gani ba a gefena dana san ina ajewa din a hankali na fito zuwa falon sai dai banji motsin umma ba a falon na bude labulen dakin ta a nan ma bata cikin dakin lokacin.
Haka yasa na nufi kofan gidan namu na bude dagani sai dogon wando light brow da riganshi kala daya kaina a hargitse duk da na daure shi da ribon ta baya.
Ummace a tsaye tare da Abdul suna magana jin budan kofa yasa su juyowa suka kallo inda a cikin mama umma ina wayata na fada.
A cikin dan tsorata da i,iniya take fadin wayan wayaki na wuri a dakina na saka maki chagi jin hakan yasa na juya na barsu tsaye suna mamaki.
Ba komai sukewa mamaki sai tun farkon faruwan ciwona na umurci da adauke wayan a kusa dani bana son ganin ta yasa umma ta boye wayan a wurin ta duk tsawon kwanakin tana kuma saka caji a cikin ta.
Dakin nata na shiga na dauko wayan dake saman filon ta nafito zuwa falo ban zauna ba na nufi kofan sai gasu sun shigo nace umma yunwa nake ji sosai a cikina.
Kallon inda Abdul yake tsaye shima din ni yake kallo a cikin mamaki wai yau nice ke tambayan abinci da bakina wace kwana da kwanaki bana cikin komai sai diyan icce a cikina.
Da sauri umma tace abinci bari a dauko maki abinci kici ta wuce zuwa kitchen da sauri ta hado abinci ta kawo min.
Sune zaune sun zuba min ido har na kusa tashi da leda daya na sakwara da miyan yauki dsyaji nama manyan yanka a cikin sa.
Saida ya saura kadan na dauki goran ruwa na kwankwade shi saura kadan shima na aje tare da lumshe ido sai lokacin ne na tuna da suna tsaye a kaina dan murmushi na sake a cikon kunya kafin kuma na mike zuwa dakina da sauri fitsari nayi sosai a lokacin naga ai gara na watsa ruwa naji dadin jikina a lokacin.
Wanka nayi na dauro alwala kodana shirya na fito nasamu Abdul baya gidan sai umma zaune a falo tana ganina tayi min sannu na amsa Ammar dake kwance shima ya dago yana gaidani.
Wai umma wani abu ya farune halan ina barci kadin umma ta girgiza min kai tana fadin ba komai Ammar ya dago yana fadin .
Baki da lafiyane fa almost one week ke nan yau ni na tambaye shi da sauri sai umma ta mika mai dakuwa da hannu tana zagin shi.
Maida kaina nayi jikin kujera ya dan lumshe idona ina tunane saidai na kasa tuna komai a lokacin yadda ya dace in tuna din.
Ammar dauko min laptop dina a daki na fada don sam bana jin karfin jikina ko kadan ya mike da sauri ya dauko min tana da full charge don haka na fara duba abinda nake son dubawa.
Date din ranan na duba da sauri na dago kaina don ya nuna min rabona da yin aiki ga lokacin kafin in magana muniya ta shigo dauke da cool abinci tana ganina ta washe bakin jin dadin ganina zaune ina aiki.
Ta shigo da murnan ta tana fadin oh mun godewa Allah sahiba kin tashi ogana yayi kuka sosai kan rashin lafiyan nan naki ranan shida Adnan a gidan mu.
Barin aikin nayi na dago kai ina kallon ta cikin mamakin jin abinda ta fada sai kuma na juya na kalli umma na dukar da kaina.
Daga inda yake tsaye yaga yana neman faduwa kasa a lokacin hakan yasa yakai kasa zaune saman dandaman wurin tun baiyi nisa ga karanta abinda ke cikin ba ya fara cin karo da tashi hankali.
Tsab ya gama karanta komai yanayi yana share gumin dayake tartso mashi saman goshin shi da hannu daya kafin ya mayar da file din ya daure kamar yadda ya sameshi a wurin saidai wanan karon bai bar file din haka yadda ya sameshi ba a wurin saida yayi itin nasa dabaran ya musaya komai ya canza wurin sallon ajiyan.
Ya fito ana sara mashi sanin koshi waye a wurin daga nan yayi sallama dasu yafito ya shiga motar shi yabar wurin hankaki tashe Allah ne ya gyara ya isa lafiya don baya ko ganin hanya da kyau a lokacin,
Haka ya shiga gidan suna falo a zaune don uinin ranan bata leks asibiti taga yan uwanta ba acewan ta tagaji da zuwa mutane suna nunata.
Don haka tayi fushi ta daina zuwa da rana a cewab saida dare zata dinga lekasu da niyar yau tayi masu dafuwa taje dashi ko don gorin da akai mata a safiyan yau din.
Saiga mijin nata ya shigo a yanayin data ganshi ta fahinci ba lafiya gareshi amma hakan baisa ta tashi ta bi bayan shi taji meke damun shi a lokacin.
Sanyine ya rufeshi lokaci guda jikin shi har yana karkadawa don tashin hankalin daya tsunci kanshi a ciki ranan.
Yana kwamce shi kadai a dakin sai rawan sanyi yakeyi shi daya yana kuma faman tunane abinda ke karasa hauhawan zazzabin jikin nasa yake kara karuwa a lokacin.
Lalai duniya baki da tabas don mutum gaskiya ba abin yarda bane ashe ko kadan a zamanin nan koda kuwa kun fito tsatso daya dashi kada kayi saurin aminta dashi kai tsaye sai ka fahinci shi waye a zuciyar shi.
Idon ya kara rintsewa lokaci guda yana maijin wani irun zafi a zuciyan shi bayan na jikin shi dake fita a lokacin.
Ba ita tashiga dakin ba sai bayab isha,i data fito wai zata asibiti a lokacinne ta sameshi a dakin ya rufe ruf a cikin wani yanayi na tashin hankali.
Amanatace ta raya hakan a zuciyar ta kafin ta kirashi tare da fadin zan tafi asibiti na dubosu dakyat ya iya budan baki yana fadin.
Don Allah kashe min Ac din nan gaba daya ta wani kalleshi shekeke kafin tace tou fa a cikin wani yanayi ta nufi wuri makunnin wutan ta rage Ac din har ya rufe jikin shi ya kuma bude a daidai lokacin da take fadin na tafi yaran suna gun mai,aiki idan kafito ba tare da nuna damuwa da halin da yake ciki ba a lokacin.
Dan miko min ruwa mara sanyi ya fada a wahalce nan ma saida ta dan kalleshi kamar zatayi magana sai kuma ta wuce tana fadin kada dare fa yayi min ban fita ba.
Takawo ruwan saman table ta dangware mai tun bai dago ya kara fadin wani abu ba ya tsayar da ita don haka ta fice a gidan kai tsaye.
Acan asibitin ma samun mahaifiyar ta tayi ta cika da ita tana jiran zuwan ta don rashin jinta da kuma rashin kirasu su san halin da take ciki kamar ba yar uwan haihuwanta matsala irin haka ya sama ba a lokacin.
Idan sauran yan uwan nata sun nuna ko in kula suna goyon bayan dan uwansu itafa da suka fito ciki daya da yar uwan nata.
Iein fadan da uwar ta dingayi ke nan lokacin tana zaune tana taunan cingan tare da duban wayan ta jin uwar tayi shiru ta karasa da Allah dai ya sauwa irun wanan abin haka kamar masu bakin uwa aka.
Mama konazo din da haka mutane zasu dinga gulma suna nunani ni kuma haushin hakan nake ji wallahi.
Kuka kanwar dake saman gado ta sake lokaci guda don jin zafin abinda yar nata tafada a lokacin ita ke nan taji kunya a nunata a matsayin yar uwanta inaga ita kanta ke nan.
Kiyi hakkuri Allah zai kwato maki hakkin insha Allah in suna ganin kamar kece kika gaiyatoshi zuwa wurin ki kamar yadda suka juye zancen a yanzu gaba dayan su.
Bata kai wani lokaci ba don tagaji dajin irin wanan zancen dake kara mata takaici a zuciyarta ta mike tana fadin tau mama zan tafi nabar yara a gida da mai aikina.
Cikin makoshi uwar ta furta Allah bamu alheri tafice suka bita da kallo alokacine kuma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login