Showing 291001 words to 294000 words out of 382072 words

Chapter 98 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28333

fito da kudin muka rabashi a tsakanin mu har wurin rabon yaso ya kawo muna rikici a tsakanin mu wanda har wanan lokacin muna rike da wanan zancen.
Ko Alh zai iya fada muna abinda kowa ya samu a cikin kason objection my lord dayan lauyan ya fada lokacin dana gimtse idona dake fitar da hawayen bakin ciki.
Wanan wani irin rashin kaunane da rashim imani sukaiwa mahaifin mu haka yan uwanka na jini bako bare ba sai kace basu san inda ya fito ba wanan irin son kai da suka nuna mashi.
Ashe gaskiyane da ake fadin kiyayya ta asali bata goguwa a zukatan makiya kome ko zakai masu sai ranan da sukaga kanka a kasa koshi idan yana motsi basu barin ka sai ya daina matsin.
Saidai su wa yan nan sun kashe macijine basu samu sare kan shiba da ace sun sanda hakan duk inda muka shiga cikin duniyan nan Allah nuhu sai ya nemo umma damu ya halakamu a lokacin.
Dukda abune mai wuya irin nisan shakon da umma tayi zuwa semi boda Allah kadaine ya gyara bata tsalaka kwatano damu ba a lokacin.
Ko can din take zai iya zuwa ko ya tura akashemu da ace yasan da hakan a lokacin Allah ne kawai zai kwacemu a hannun shi.
Duk yadda lauyan mu yaso yakai daddy makura saboda yasan logon sharia ya kasa kayar da daddy a ranan don iya duniyama.
Sai rokom kotu da daddy yayi kan cewa yana son kotu ya bashi dama ya halartawa iyalan mamacin dukiyan su a hannun su dake wajen shi tunda yanzu lokacin hakan yayi.
Jin hakan yasa na dago idona ina kallon daddy din wanda ni kaina bazance ga irin kallon da nake masa ba lokacin kamar ance na duba gefena ya Abubakar ne zaune dasu baffa hamza a kujera guda.
Idona a cikin nasa alaman daga kai yayi man wanda ban fahinci nufin shi ba a lokacin sai muryan mai bayanin kotun dake fadin ko zamuga wace ke kara muji na bakin ta a yanzu.
Duban inda nake mutane keyi ranan dai shiga shigen na hausawane duba da inda muka fito yola yasa nasaka atamfa amma buje da riga matsatsu da suka kame jikina sosai.
Gyalen dake saman cinyana na dauka na dora a kafada don gaskiya babu wani zancen hijjab a gareni don ban saba sakawa ba tun ina karama.
Wanan yasa ko a yanzun niko a jikina hakana tashi tinkis tinkis dani suka bini da kallo masu tausayi na tausayawa masu jin haushi naji hakama masu mamakin mu a wurin.
Daga yanayina zaka gane a gajiye nake ko kuma cikin wani yanayi na daban can mai nuna rashin jin dadi a gareni nazo na tsaya a inda ake tsayawa din lauyan ya kalleni yace dani.
Shabi u hear what he said now ?
Waitin he talk na sake jefo mashi tambayan nima a wahalce yace dani kan dukiyan mahaifin ku dake hannun shi da yake son ya danka maku su a yanzu.
Which kind of wealth he dey talk now i beg may he forget about dem shaaa.
Ni a yanzu kawai bukatana garesu shine su sakar muna mara muyi rayuwa kamar kowa ina son kotu ta kafa muna sheda damu dasu akan duk abinda ya shafi rayuwan mu a yanzu sune.
Aiko nan kotu ya dauki hayaniya masu dariya nayi irin yadda nayi maganan zakace ni din wata tsohuwar bayerabiya dani ga kuma na nuna ba dukiyan bane a gabanmu mu.
Shima kanshi lauyan dariya na bashi sosai yayi dan murmushi yana girgiza kanshi dan abin ya bashi mamaki matuka nace yes now.
We no wan de money and erverything daya fito a wurin kowa daga garin nan tunda ba zasu dawo muna da mahaifin mu ba su rike komai mun yafe mu.
Aikuwa kamar mutane su cinyeni danye don abindana fada ina kuka ina share hawaye har alkali yaita dukan gudumar shi wurin yai shiru ya dukar da kanshi yana rubutu kafin ya dago yayi gyaran murya aka kara natsuwa sosai ana saurarenin.
A nazarin kotu a bisa tsarun da doka ya shimfida ya zama dole wa,yanda ake tuhuma su gagauta dawo da duk abinda suka wawasa na daga dukiyan mamacin ba tare dako kwandala ya bata ba a cikin shi kamar yadda ya rubuta dukiyan shi a tsare ya bari.
Nan aka shiga jero masu abubuwan daga ciki har da gidaje da filaye kiwon shanu motoci da sauran abubuwan amfani na gida.
In boni handi yoooo Alh gyade ya fada yana zubewa kasa tare da fadin Nuhu kai shushe mu ka shuci rayuwan mu kace muci ba a komai ya gashi zan tashi ko kwandala bandashi a duniya.
A take kotun ya rikice da koke koken diyan su dana yan uwa kowa da gefen da yake bi a cikin su yayin da Alh nuhu yayi tsayuwan da baisan inda yake ba a lokacin.
Alkali yaci gaba da bayani bayan haka kotu ta yanke hukuncin Alh Ali dcp taran naira miliyan ashirin ga magadan don kamashi da cin amanan mamacin da kuma sassaucin dauri na shekara daya ko taran naira miliyan biyar ga kotu.
Haka kuma zai iya daga karan idan hakan bai mashi ba yaje gaba iya abinda kotu zata yanke yanzu ke nan kan Ali dcp.
Sai su Alh nuhu da zasu mika komai da suka mallaka ga ko magadan su haka kuma zasu fuskanci daurin mara sassauci da tara ga kotu kan kisan dan uwan su da sukayi.
Shi buhari ya wanke kotu ta bata kamashi da laifi asalima an yaudare shi anyi amfani dashi anje kissa an kuma boye mashi hakan.
Jarrr kaniya Alh nuhu ya fada da karfi kowa dake cikin kotun hankali ya koma akanshi lokaci guda ya fara fadin akan Sambo za ai min daurin rai da rai a gidan wakafi.
Kana da daman daga kara idan sharian mu bai gamsheka ba a nan aka fada Alkali na dagawa daga kujeran shi da yake zaune don an dade a wurin zaune ranan.
Koke koke ne ya tashi a kotun lokacin guda wanda yan uwa keyi na tashin hankali ya dai tabbata ke nan cewa sune suka kashe dan uwan su ashe.
Ga iyalin su kuma suna fadin an tauyesu ba a basu daman kare kansu ba ga kuma cin zarfi wai za a kwace komai da suka mallaka a dankawa yaran nan shine wani sabon tashin hankalin su a lokacin.
Daga nan wurin sharian ko gidan kowa bamu leka ba aka wuce damu airport zamu bi jirgin yamma da zai tashi duk ko son ganin mu da aka turo text cewa daddy yana son yi a lokacin hakan baisa mun dawo ba muka bar masu garin suna a cikin tashin hankalin halin da zukata suka shiga lokacin.
Saukan dare mukayi Abdulne yazo ya dauke mu daga airport ya kaimu gida tun a hanya suke hira da umma ban saka masu baki ba har muka kai gida.
Daga shigan mu dakina na nufa na kwabe kayan jikina da suka dameni na shiga wanka na fito na tayar da sallah don rama sallolin dake kan mu.
Karfe goma da rabi na gama komai duk da banci abinci ba amma wurin kwanciya nake nema in kwanta lokacin don yamayin da nake jin kaina abu ya tsaya min a makoshina lokacin.
Abinci muniya ta kawo muna amma ban iya dagawa naci ba har barci ya dan daukeni ban kara sanin inda nake ba kuma a lokacin.
Washe gari hakan yasa na tashi ina jin yunwa sosai a cikina na fita neman abinda zanci din nan na hada cooker orth na zauna nasha lokacin umma ta fito daga dakin ta zuwa wajena a falon.
Sai bayan ta zauna nake gaida ita ta amsa take fadin wai mutane basu da kunya yau daddy kune ya kirani yake tambayana muna ina zaizo ya same mu.
Kin fada mashi munbar kaduna tun jiya na tambaya a gagauce tace na fada mana nace muna lagos mu tun jiya ai daga kotu airport muka nufa ai.
Wai sai yake fadin don me zamuyi haka bayan ga yadda aka aje magana damu ido na tsurawa umma dake min bayani sai cewa nayi amma yaji abinda kika fada a kotu ai don haka ya rike komai shiri tsakanin shine da mai dukiyan na kashe waya.
Dan murmushine ya baiyana min a fuskana ganin yanzu umma tsoro ko nauyi ya fara fita a idon ta a yanzu.
Mun dan taba hiran abinda daddy ya fada a cikin kotu din kafin mu sauya hiran namu zuwa na yan uwan umma dake yola.
Irin yadda suka nuna muna karamci da jin dadin ganin mu da sukayi a lokacin jin nayi shiru lokacin da take min bayanin yadda suke da kowan su yasa ta dan kura min ido tare da dakatar da maganan da take min din tana kallona .
Nayi zurfi sosai a cikin tunane a lokacin don haka ban gane hakan da wuri ba sai dana sauke ajiyan zuciya na dago kai nake tambayan ta da cewa.
Dama wanancan kauyen shine asalin kauyen iyayyen mu maza da suka fito tace kwarai kuwa kusan duk abu daya ake ai kinsan bafilace da son zaman daji ai.
Badon komai ba ya jawo hakan saboda dabbobin sune suke bin wuraren dake da sanyi don haki saboda dabbobin nasu su koshi kada suyi rama .
Don shi bafilace na asali a rugga aka sanshi da zama ba a cikin gari ba amma cikin garin akwai su idan idon su ya bude zakiga sun baro daji sun dawo gari da zama to alokacin sun camfa idan ba Allah ya gyara ba mutum yakan shiga wasu halin dabana kwarai ba ga hakan.
Asali dai bafilace shi a daji aka san rayuwan shi ba acikin gari ba duk da a cikin garin akwai fulani yan asali da asalin sune garine suma.
A can kaduna kuma an wayi gari kwatsam kotu ta tura a kargame dukkan gidanjen su har wanda iyalan su ke rayuwa a ciki ashe.
Abin bai tsaya a nan ba don duk wani kaddara na Alh nuhu dai na mahaifin mune ashe don haka kotu ta bayar da daman cewa a kwace komai daya mallaka ayi kudin su ko zasu kai adadin abin mu dake hannun shi.
Zancen gidan shi yafi daga hankalin kowa a cikin ahalin namu don har ya Abubakar shima a karshe hankali a tashe ya kira yana fada muna abinda ke faruwa.
Don yanzu shi kanshi sharian namu yana bashi tsoro sosai don ya gano akwai wanda ke izza wutan abin daga sama kuma maishi ya tsaya muna saidai ya kasa gano ko ta inane.
Don dai Alkalin ya fada mai case din babbane sosai don an bashi umurni tundaga sama akan yayi sharia yadda ya dace idan ba haka ba a bakin aikin shine.
Saidai kuma yayi mamakin jin yadda mukai mamakin faruwan hakan don sam bamu sanda wanan zance ba a lokacin mu sai a wurin shine muke ji lokacin.
Ko dai waye wanan din yana da wani alakan hakan daku ko kuma dashi marigayin ke nan tunda yan jarida sun yadda zancen kowa yaji a yanzu.
Ya barmu da mamakin hakan don muma munyi bincke a bagaren mu mun kasa gano ko waye mai wanan danyen aikin yanzu kuma.
Gashi sai waya ke zuwa yana dawowa na yan uwa dake neman mu a layin su don wai a roka mu yarda iyalansu zauna a ciki kafin asan abinyi garesu.
Saida kyat suka samu layin na na dauka mun gaisa su babbaf hamzane suke fadin haba Sahiba bai kamata kiyi hakan ba idan sunyi maki su.
Idanuwa na lumshe a hankali ina rauraren baffah hamza din don abinda yake labarta min lokacin na halin tashin hankalin da kowa ke fuskanta a cikin su.
Baffa ban san waye ya bada wanan umurnin ba don na tambaya a nan bangaren mu babu wani daya saka ai hakan na bashi amsa a sanyayye.
Mukai sallama na fara jin digon tausayin su a kasan zuciyana don wanan yawan iyalan nasu ina zasu zauna wanan korar kai tsaye haka lokaci guda ba zato.
Da sauri wani zuciya ya gargadeni da har kin manta da naku bakin cikin rayuwan da suka jefaku ciki na maraici bayan kisan gillan da sukaiwa mahaifin ku ?
Ko har kin manta da irin kunci da kadaicin rayuwan da kuka kasance na tsawon shekuru masu dama ?
Daga inda yake zaune da sauri yake sarrafa computer din nasa yana son gano abinda yake nema a lokacin koda zargin shi zai iya zama gaskiya .
Idonshine ya sauka ga wani rubutu na shafin mutumin farine dogo saidai ya girmey masu sosai ga shekaru yana tsaye a cikin bakkaken suit da suka karfi jikin shi.
Shigan shi zaka dauka dan shekara ashirin da wani abune lokacin nan ko shekara talatin da biyu yake ma,ana zai iya kaiwa sa,an ya Mustaphan gwaggo hari a wajen shekaru ke nan.
Ga wasu baiti da yayi kasan photon nasa da wanda ke nuna halin kunci takaici suyan zuciya bakin ciki dayayi na rashin ubangida aminin shi a baya .
Sai ya dawo kasa yana nuna cewa duk da kuncin da zuciya ke ciki a yanzu hakan ba zai hanamu tunawa da Allah ba kan amsan adduan mu na tsawon shekaru kan Allah ya baiyana muna azzaluman da sukai maka kashin gillah.
Lokaci yayi da zasu fuskanci hukunci daidai da abinda suka aikata a gareka suma a yanzu sai wani photon da ya sake yana mai murmushin mugunta.



.ANA DARA GA , , , , , , , ,

8️⃣7️⃣BY, , , , , , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL AWWAL, , , , , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257

ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋

Zubur ya mike tsaya lokaci guda ya fara zagaye dakin shi kadai yana tunanem inda yasan wanan sunan ko fuskan wanda yake kallo a screen din laptop din tsawon awa daya da rabi.
Wani irin abu yaji a zuciyan shi lokaci daya yaja ya tsaya yana sauke numfashi a lokaci guda ya dan furzo iska mai zafi daga bakin shi kana yakai hannun shi akanshi ya shafo zuwa fuskan shi.
MUKHATAR USMAN MARWA fittacen dan kasuwan nan mai harka da ma,adanai na kasa kasa matashin da yai saurin fice a wanan harkan lokaci guda kuma yana matsayin basarake daya fito daga nahiyar gabas mai fada aji akasa saboda sun kawowa kasa cigaba sosai ake damawa dasu sosai.
Mukhatar dai kowa yasan ba mutum bane mai lokacin kanshi balle na iyalan shi ko yan uwa mutum ne wanda a yanzu ganin sa ma aikine.
Yayiwa harkan shigan wuri harkan kuma ta karbeshi yashige cikin turawa ya saje dasu ana gwagwalmayan rayuwa tun tasowan shi.
But why ya tsoma kanshi a cikin wanan harkan a yanzu yake tambayan kanshi saidai a halin yanzu ba amsa a gareshi.
A gurguje ya shiga bathroom ya watsa ruwa a jikin shi ya fito ya shirya yana kokarin daura belt din shi a kwankwason shi ta turo kofan da kuka wiwi .
Hakan yasa ya juyo yana kallon ta duk da bata bude baki tayi magana ba yasan kukan ta bai rasa basaba da abinda ke faruwa a gidajen su a yanzu.
Juyowa yayi a fusace yana fadin ke meye hakan meye zaki shigo min dagi a wanan yanayin na tashin hankali haka kuma ?
Haba modibbo kaji wai a kan wanan case din yarinyar nan wai anje gida an fitar dasu mama fitarwan wullakaci gaba dayan su gidan, suna titi a watse da safen nan fa suka dira masu a gida sukai masu wanan wullakacin.
Uhummm ya fada ya juya yana kara saka wandon jikin shi da kyau ita kuma tayi tsaye sororo tana binshi da kallo cike da takaicin ganin rashin damuwan da bai nuna ba ga abinda ta fada mai din.
Wani irin kuka mai sautin tausayi ta sake lokaci guda har ya kare shirin shi yana jinta saida ya fesa turare bayan ya gama tsab ya juyo yana ce mata.
Yanzu kukan nan naki shi zai saka wani abu ko kuma kijawa kanki wani matsala nima kuma ki tayar min da nawa hankalin ?
Dole inyi kuka saboda nina nasan zafin da radadin hakan dana ke ji don kai naga abin bai shafeka ba ka nuna min yanzu.
Kome zaki fada ki fada yanzu don kina da daman fadan hakan saidai kada ki manta da cewa nima abin ya shafeni ai ko kin manta da hakan ne.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login