Showing 21001 words to 24000 words out of 382072 words

Chapter 8 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28420

fahintar wani na rayuwa.
Don wanan zancen na uwar yasa yar ta dan shiga zurfin tunane a lokacin ta fara hango abinda hankalin ta ya kasa hango mata a kan mutanen

Zaune take tana lazumi saman sallaya bayan ta idar da sallah magariba wani kanshi ya ziyarci hancin ta ko ba a fada ba tasab kanahin turaren mijin sune wanan.
Shi din ne ya shigo dakin yana gyara agogon hanunun shi ya dan kalleta yana fadin aroka muna da yawa don Allah .
Ta dan dago kai ta sauke a kanshi tana dan murmushi tana fadin Allah dai ya karba muna wanan kamshin haka sai ina kuma haka ?
Ya dan bata rai kafin yace zanje gidan su wanan mara hankalin ne karima don mahaifita ya dameni da kira tun rana hjy Addah bata bata rai ba shima kuma din bai zaci hakan a gareta ba dama.
Shedab da yake mata na bata taba korafi akan karima din ba tun shigowan ta gidan shi ta zauna kuma a cikin su din a yanzu.
Sai cewan da tayi Alh kaima ai ba zaka biyewa mace irin karima kuna sayar da hali ba haka zama da wanda rayuwan shi san ba kwabo sai sannu a hankali zata shiryu ta gane gaskiya.
Amma irin wanan ina dadin sa ga yara a tsakanin ku, ace ka turata gida haka dolene hankalin mahaifanta ya tashi gaskiya.
Hmmm haka kike gani don ita ai bata da alaman nadama kan abinda tayi din ko dazun an fada min an ganta a by pass su biyu a cikin mota .
Da ace ta damu da hakan ne ai da ko idon fita bata gani ba a halin yanzu din tunda tasan akan shi muka samu matsala dani da ita.
To ai kaji na fada maka sai fa hakuri don yanzu wanda duk ya ganta matarka dai za a ce ba matar wani.
Sai na dawo yace da ita don baida amsan da zai iya bata a lokacin ya sakai ya fice daga dakin ya bar gidan zuwa amsa kiran dattijon dake neman shi din.
Yasamu ankai ruwa rana a tsakanin mahaifan ta din da suka samu sabani a gidan akan yar tasu.
Bayan gaisuwa a tsakanin su sai dan shiru ya biyo baya mahaifin hjy kariman ne ya fara magana yana fadin .
Alh mun san kayi hakkuri da halin yarinyar nan kuma kana kanyi har yanzu don ni kaina ba macen da zata kawo min wanan shegantakan in kyaleta ace mijin ki bainan kisa kafa ki fita ba tare da sanin miji ba.
Alh yace ni abinda ya ban haushi fitan karima baida lokaci duk sanda ta bushi iska fita takeyi tana bin abokan banza suna koya mata shedana.
Yanzu meye laifin hjy Addah a cikin wanan zancen da zata nemi ta zageta matar nan har idona ta faka ta kirata ta dawo gida na dawo.
Wai amma ita, ta dawo gidan tana zargi wai itace munafukanta kuma duk wanan abinda tayi mata din bata gani ba.
Daga can kofan daki inda mahaifiyan nata take zaune tace ai dama na fada maka malam karka da da karka kara akan uwargidan yace tazo gida.
Cikin mamaki Alh ya dago kai yana kallon mahaifiyar matar nasa da bata iya boye shigarwa yarta a fili ba haka.
Shikuma ma haifin na fadin saudatu mena fada maki tun kafin mu zauna wurin nan kikace kinji don haka karki kawo muna zancen ku na mata nan.
Yanzu dai hakkuri zamu baka Alh kayi hakkuri yarinyar nan ta koma dakin ta iidan kunne ya ji jiki ya tsira idan halin ta ne ta koma tunda haka taga matarka ta gida tanayi data shigo.
Nan dai mahaifin yai mata fada suka tattaro suka dawo gidan tare da ita inda suka samu mutanen gidan kaf din su a falo suna murnan zuwan yayan su daya dawo .
Amira tana zaune saman jikin shi cikin rashin damuwa da rashin uwar su a gidan sukai mata sannu da dawowa ta shige part din ta kai tsaye.
Alh ne ya shigo karshe bayan ya gama sallaman driver ya samu dan shi zo wanda suka dade basu hadu ba sai wanan karon daya shigo wanan aikin.
Na neman wanda suke zargi da aikata wani abu na daban sabanin wanda ni ya fada min din alokacin a baya daya fada min dalilin zuwan shi.
Da kyat Abubakar ya iya budan bakin yana fadin sannu da dawowa bai tsanmani amsawan ta ba don haka yana fadi ya kawar da kanshi ga kallonta kamar yadda itama ta kawar ranta na kara baci da ganin shi yazo.
Duk da yakan dan samu abinda ya bata idan yazo sai dai hakan bai mata dadi ita don tana rainawa ita tafi son ya bata daidai da na mahaifiyar shi.
Yaranta ne suka nufo ta da murna suna fadin mami ta dawo mami oyo jin muryan maigidan a falo yanawa dan nasa kirari da sarkin aiki ina ka fito office ina zaka aiki sai hakan kuma ya kara batawa hjy karima rai sosai don yadda yake nunawa diyan shi so a fili.
Sai kishi ya rufe mata ido take ganin ai nata yaran basu samun kulawan mahaifin nasu kamar yadda yake kula diyan hjy Addah.
Kishi ke nan duk halarcin hjy Adda da diyanta kishi ya rufewa hjy kariman ido bata ganin wanan halarci karshe ma sai take daukan hakan da kishi wai na munafunci suke nuna mata..
Saidai duk da hjy Addah tasan da hakan kuma abin yana damunta sosai a ranta saidai bata yarda ta biyewa halin ta sun zama daya ba.
Wanda hakan kuma ya kara haska ta ga mijin don hakkurin ta don shi mutum ne da yasan ya kamata.
Sabanin wasu mazajen da zasuga hakan duk da uwargida tana hakkuri sai kuma subi amarya a taru ana musguna mata.
Irin wanan ke uwar gida idan kinga hakan hakkurin ki zai jawo maki raini da koma baya abinda ya kamata kiyi na farko shine addu,a tare da sakawa kanki hakkuri akai.
Saidai kuma dole ki tanka din shiru wani lokaci yankan kawo raini ga uwargida don haka a rika dan magantawa a cikin hikima.

Nayi mamakin yadda umma ta yarda ana kashe wanan kudin duk data soki wanda ya bamu shi din a lokacin.
Sai gashi naga tana zara ana sayo duk abinda Amar yace yana sonci don iya sayen abin kaiwa baki kawai muke saye a asibitin.
Magani da allurai saidai muga an shigo dasu dakin ana masa amfani dashi ba tare da mun fitar da kwandalan mu ba anyi amfani dashi.
Yamma yayi karfe hudu umma ta turani gida in dauko muna dan abin bukatan da zamu zauna dashi asibitin don irin fitowan da mukayi koma bamu samu dauka ba dakin muma a bude muka barshi.
Inda Allah ya taimaka ga irin wayau na duk da rudewan da nayi a lokacin bayan naga umma ta fita da Amar a rude sai dana koma na kwashe dan kudin mu dake dakin a lokacin.
Don nasan yadda akeyi a gidan da zaran dan tafiya ya kamaka kayi kwanaki masu dan tsawo baka dawo ba sai abi dare a fasa dakin a kwashe ma abin kwarai a dakin masu amfani .
Wanda sanin hakan yasa farga na kwashe kudin na tafi dasu a cikin aljihun rigan dake jikina wanda sai wanan lokacin nake tuna hakan.
Abinda na zata shine ya faru don na samu har dan raggan katifan da umma da Amar ke kwana a sama andaga a dakin kai ba katifan bama har ledan kasa an daga wanda nasan kudi ake nema a dakin don mu bamu da wani abin jin dadi na zamani a dakin na kudi.
Fada na fito waje ina yi a cikin yarbanci ina zage zage ina hadawa da turancin brokin a bakina wanda su suka amshe bakina wajen gwanewa.
Ba wanda ya tanka min don hakan ne wasu ma basu gidan basu dasowa a lokacin daga kasuwa da sauran wajajen balaguron su.
Gidan babban gidane zai mutane saba,in zuwa tamanin ke rayuwa a cikin wanan gifan da baifi mutum goma su zauna suyi rayuwa a cikin saba a arewa.
Na karaci fadana na tsunci yan raggadun mu da yan plate na jawo kofan don bamu da kwado na rufo na nufi titi.
A hanya muka hadu da iya mulika take tambayana abinda ke faruwa na fada mata tace in gaiyar mata da umma da Amar din.
Har take ban shawara tunda muje asibiti muyi kokari umma taga likita asan abinda ke yawan damun ta datake faman ciwo haka.
Naji dadin wanan shawaran na iya mulika din don duk fadin gidan ita kade ta nuna muna damuwanta a kan mu.
Na koma nake ba umma labarin halin dana samu dakin mu a ciki ta bugi kirji tana fadin aiko mun shiga uku dama tayi tunanen hakan tun dazun.
Shike nan an kwashe dan kudin da mutumin can yabaki shekaran jiya kudin bai amfane mu ba na tsaya dogon guri dashi.
Umma ban bar dakin mu ba saida na kwaso duk dan kudin dake garemu na hado da wanan din don nasan akwai matasa a gidan masu shiga dakuna idan mutum bai gida.
Sahiba kin kyauta muna da baki bari an sace wanan kudin ba yau umma ina zan bari tunda shi nake son muyi amfani dashi wuri ganin likitan ki kadin mu bar asibitin nan.
Sahiba yadda nake jin jikin nan yanzu ina mukaga kuflfldin da har zanga likita ko na yaron nan ai Allahne ya kawo muna mafita a kanshi.
Gobe dai sai muje mu yanki kati umma kema a dubaki tunda gamu a cikin asibitin ko iya mulika yanzu saida ta kara ban shawaran hakan kuma tace na gaida ke.
Mun bar wanan zancen a kan gobe zamu ga likita ashe likitan yakan zagayo duba marasa lafiya da dare da rigimana nan na jefo mai zancen umma din.
Saida ya dan kalli umma inda take zaune din yake fadin sai mu yanki kati a goben mubi layi Allah ya kaimu umma ta fada da hausa.
Nan ya barmu ya fita bayan ya gama dan dube dube da tambaya akan jikin Amar din dake kwance yana barci.
Abincin dana sayo muna da zan dawo shi umma tace na diba naci kan na kwanta tunda tasan a gajiye nake dai umma ta mance irin jigilan da nakayi a duk wunin Allah.
Ban kaiga tashi a wurin ba don na tsaya ba umma labarin yadda na samu an burkuce muna daki har ledan kasa.
Wata yar nurse tayi sallama dauke da ledan abinci da abin sha ta shigo dakin duk muka bita da kalkon mamaki.
Tace a cikin yarbanci iya Amar ko ?
Umma tace ahmi tace ga wanan ance na kawo maku inji wanda ya kawo ku ta aje tana fadin manbo, wa ta fita sai gata dauke wani katon kwali mu dai muna binta da kallo kawai har ta aje.
Tace duk shi yace na shigo dashi yana zuwa zaiga likita eh, kwale data juya umma ta fada don nikan nagama shan jinin jikina a lokacin don nasan wani fadan zansha kuma a hakan.
Kodan ance wai yana zuwane bata furta komai ba sai bin kayan take da ido tana ajiyan zuciya ga tagumi data hada tana umm,, , ,
Shiru har dare ya soma yi alokacin nakai kasa na soma barci don yau gamu ga fanka a dakin zamu kwana dashi kamar kowa a dakin nan da nan jikina ya mutu na fara gyangyadi har nakai kwance.
Umma ce ta tayar dani naci abincin duk da taji tsoron cin namu amma saidai kuma zuciya naso don lafiyeyen abincine koda ba a bude ba duk kamshi ya bure dakin ko a lokacin.
Saida ta dan kira sunana kamar sau uku na amsa tace a cikin yarbanci na tashi naci abinci kada inyi barci banci abinci ba.
Na tashi na shiga ban dakin na kurkure baki ba na fito na zauna na dan kali umma nake fadin umma ba zakici abincin bane ke ?
Tace sai zuwa anjima kafin mun kwanta zanci na jawo kedan na fara fito da take away din nan mai tsada na dan kali umma tayi kamar ba kallona takeyi ba.
Saida na debo abincin naji umma na fadin indaici da bisimillah don bzmu san manufar su akan mu ba.
Hakan nayi da murna a zuciyana da yau banji umma tayi wani fada ko maganan da zai ban tsoro naji abincin ya fita min rai ba.
Naji dadin sakwaran da miyan egushi da naman shi kamar yanka duk da yajin da miyan kedashi haka nayi taci don yaji kan mun saba dashi mun tashi a cikin cin sa tunda muna garin yarbawa.
Aka turo kofan da sauri muka dago don ganin waya shigo wata nurse ce dauke da file tace umma ta bata cikakken sunan ta likita yace da safe akwai awon da za ai mata kada taci komai har zuwa safen.
Har zata fita umma take tambayan ta kudi nawa za, a bayar tace maganan likita ne wanan ba nata ta fice ta barmu da mamakin hakan don sanin halin asibiti da mukayi muna jin rashin nasihan da akewa marasa lafiya idan basu da kudin ganin likita.
Mu sai gashi anzo kawai wai umma ta fara shirin za ai mata aune aune zuwa safe din.
Abincin ne yafita min a rai duk da son da nakeyiwa abincin don dadin shi amma haka naji komai ya tsaya min cak lokaci guda.


ZAINAB IDRIS MAKAWA


ANA DARA GA , , , , , , , , , ,

8️⃣

BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM SIRA,ATAL LAZINA AL,AMTA ALAIHIM, , , ,

BARKA DA JUMMA,A YAN UWA

PAID NOVEL BY MAKAWA, , ,

Tunda suka fito sallah asuba hankalin ta ya dauku ga wata macen bahausa da ta gani a dayan dakin dake kusa dasu tana jinyar dan ta.
Sai kuma yanzu da suka sake haduwa da matar a bakin famfo zata dauraye cups da plate da sukai amfani dashi wanda itama shi din tazo yi a wurin.
Yanayin shigar matar ne ya kara daukan hankalinta zani da rigane na atamfa a jikinta sai gyalen da keda ruwa da shigen kayanta data yafa ya rufe mata jiki sai shigan yaiwa Sahiba kyau ainun har ya dauke mata hankali.
Ga kunshin a hannayen ta gwanin ban sha,awa zanen sun fito shar dasu a hannayen ta ga zobbuna dasa a yatsunta hudu a hannun da bangus sai walkiya takeyi shar da ita.
Tana tsaye a gefen su tana kallon rigiman da akeyi a cikin yarbanci wanda bakin sahibace ke tashi tana fada da wace ta fara zagin ta a wurin.
Dan dagowa tayi don ta gyara gaban rigan ta daya dan fado bata son aga tsiraicin ta yasa take ta faman gyaran don rigan Okirki dake jikin tana suka hada ido da wanan matar dake tsaye tun dazun a wurin.
Har ta mayar da kai ta duka sai kuma taga rashin dacewan hakan don ko banza matar yanayin ta ya nuna ita din musulmace kuma bahaushiya.
Gashi har lokacin matar bata motsa ba ga wasu tafe bayan su wanda tasan matar zata dade a wurin nan ke nan don ba mutunci kega mutanen nan ba sai ka nuna masu kaima ka iya zaku zauna daidai.
Roban ta ta tara kafin ta juya zuwa wurin matar ba tare datayi magana da ita ba ta karbi kayan dake hannun ta tun dazun ta juya.
Yanzu kan da aka juya harshe hjy halima taji me suke fada don taji suna fadin Ajayi so na house girl de do dis for us since.
Sai Sahiban data kwarai da zama a cikin su tace eh even house girl na human ben if i no sebe do am , i no go do ta fada ta duka tana zubawa kayan morning fresh din wanke wanken data gani a cikin kayan ta fara wankewa a hankali.
Har ta gama hjy Halima na kallon yadda ta wanke su tsab ta nufo ta dasu ta mika mata bata tsaya jin komai ba ta juya ta dauki kayan ta data riga ta wanke su ko.
Don dokar asibitin ne haka kada a wanke masu komai a ciki akwai famfo a waje idan bukatan hakan ya tasowa mutum a lokacin zama asibitin.
Hanyan daki daya suka nufa tare sai lokacin hjy ta samu bakin yiwa yarinyar da tunanen ta ya addabi zuciyar ta tana fadi a cikin zuciyan ta.
Ga yarinya har yarinya da zubin irin na musulunci amma kuma da gani ba musulma bace ga kyau ga wanan yar kamar ita ta halici kanta sai dai doti ya hana komai ya fito fili.
Sai gashi sun hada hanya da ita zuwa ciki tace da sahiban thank you very much for what you did for me.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login