Showing 306001 words to 309000 words out of 382072 words

Chapter 103 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28452

bane hakan don ko mu ba a nememu ba har yanzu kan zancen don ko nasan ba za ai wani sharia da bamu wajen ba a lokacin.
Koma meye nasan ba zasu rufe sati biyu a can tsare ba don haka ku kwantar da hankalin ku ku daina jin jitajita hakana.
Abinda ya daure min kai shine yanzu sam bana jin alaman mutane kaina a tare dani kamar da can da nake yawan jin su ko suke taso min haka kawai kamar ila har na gama komai da zanyi zan kwanta.
Sai nayi wani tunane kawai na mike na nufi wardrobe din kayana na dauko wani jakkana na koma saman gado dashi na shiga laluben abinda nake nema a lokacin.
Har nayi sa, a na lalubo abinda nake nema na bude kwalban na dan shaka kadan kafin na rufe na mayar ai ban kaiga dawowa bakin gadona ba tun lokacin na fita cikin hayacina.
A wanan daren jumma,an dai abubuwan kaina saida suka taka min saida kyat umma ta samu suka dan lafa min ba tare da wani hayaniya ba kuma.
Washegari ma sai ummace ta kai min dan ruwan tea nasha da kyat na koma na kwanta ba,a dauki lokaci ba wayana ya dauki kara ummace ta dauka tana sallama.
Wanan mutumin mukhatar usman ne a layin yana jin muryan umma ya shedata suka gaisa yake tambayan ta lafiya mu tace Alhamdullahi sai dai Sahiba din ce take fama da laluran ta na jinnu da kan dameta wani lokaci.
Ya danyi shiru na dan lokaci kafin yace dama tana da wanan laluran ne ashe umma tace dashi tana dashi don yanzu sun kai shekara kusan goma data fara irin haka.
Dama nima a nan nayi wani irin mafalkine da ita shine yasa na kiraku yanzu inji idan kuna lafiya don mafalkin ya ban tsoro sosai da sauki umma ta fada.
Bayan dan shirun da yayi can kuma ya sake tambayan ko dai duk a kan case din nan ne don abinda mafalkin ya nuna min ke nan saboda mutanen nan shu,uman mutane ne sosai wallahi.
Umma tace anya zasu iya cin galaba akanta kuwa sai dai abinda ya fito daga Allah amma nina san ba dai suyi mata wani abinda zai iya kamata ba dai da sunan sihiri.
Amma hjy sai nake ganin kamar ba a banza take wasu abubuwa ba a yanzu Allah ya nufa umma tace don hjy da ya kirata da shi a lokacin.
Da zasu iya wani abu da ita da ba a kai wanan lokacin ba kawai dai tana da nata dalilin ne a yanzu na ganin bai kamata duka a hukuntasu a kan laifin da bai shafi wasun su ba dai.
Ok na fahinta yanzu a dan bani lokaci na kara dan bincke wanda ba a kama da wani laifi ba sosai a cikin su zan sakoshi insha Allahu nagode da kuma na sameki mukai maganan fahinta dake.
Ba komai umma ta fada sai dai kunyi hakkuri da wanan yanayin na Sahiba don haka abubuwan suka mayar da ita yanzu sam bata da tsoro ko fargaban komai idan ta tashi magana.
Murmushi ya sakeyi yana fadin ya fahinta kafin ya kashe wayan cike da fargaba da tunanen wani zance da suka tsaya mashi a rai cikin dan maganan da sukayi da umma din na dan lokaci.



ANA DARA GA , , , , , , , ,

9️⃣2️⃣BY, , , , , , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL WALI , , , , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257

ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋

Yau na tashi da wuri don aikin da muke dashi a office yasani sakkon tashi don zuwa wurin aiki na samu na gama da wuri nayiwa umma sallama na fita.
Don dan kwana biyun da nayi ban fita ba koda naje na samu aiki ya taru yana jirana a lokacin bayan na gama gaisawa da duk wanda ya kamata na zauna na fara duba aikin dake gabana lokacin.
Sosai na natsu Ina aiki kafin tsawon wani lokaci wayana ya fara kara ban kula da in dauka ba don aikin dake gabana a lokacin har yakai ga tsunkewa kafin wani lokaci kuma kiran ya sake shigowa again.
Dan tsuke naja a daidai lokacin dana mika hannu cikin jakata ina dauko wayan son duba wanda ke kirana lokacin .
Saidai ganin bakon lamba yayin kasan wajene kuma ban san mai shiba yasa na dana ina karawa a kunne na.
Muryan mace ce yasa na tsaya ina sauraren ta a daidai lokacin da nake kokarin yin sallama ita kuma take fadin ehhe na sahiba a dey talk too?
Naso sheda muryan maishi amma na kasa tuna inda nasan wanan muryan taci gaba da fadin ba zan tsaya wani dogon magana ba dake a yanzu saidai ina son ki fita hanyan dana da kika sihirce min shi saboda arzikin shi.
Dama haka irin ku suke diyan tallakawa da zaran kun kyala ido akan dan mai kudi kukaga yana da arziki lokaci kankani sai ku juye mashi kai ku sace zuciyan shi.
Na fada maki tun farko dana ba ajin ki bane aiki kawaine a tsakani ku aikin ma a yanzu zanso a barshi don nasan izuwa yanzu kin samu karuwa sosai a wurin shi wanan ma kawai ya isheki in kina da godiyan Allah.
Wai waye wanan mara sanin mutunci da adam sai zancen wani dukiya da danki dama ban sani ba kike faman yi min a waya ?
Koke wacece baki da kirkin ko imani dan baki san Allah ba balle Annabi a cikin lamarin ki an fada maki kowaye danki aiki dashi danki din da kike fadi,kina tunanen anayi anaci masa kudin .
Za ai masa aikin banzane ko an fada maki mu bayin shine ko haihuwan mu yayi da zamuyi masa aiki kyauta ?
Ki koma ki tambayi dan naki idan wani abinshi ya taba hadashi dani har kike min wanan zancen daki baya gabana ko waye shi don haka ki dafa abinki kice idan Sahibace .
Mamakine ko me ya hanata ban amsa don ni kaina nayi mamakin jin yadda tayi shiru don da farko tayi niyar cimin mutuncine sosai a kan dan nata saina tare ta da baki na wanke ta tas a wayan.
Tsuki naja naci gaba da aikina raina a bace lokaci guda naji tsanar aikin ga baki daya ya kamani don nasan ba kowa bace sai Alaja zata kirani taso raina min wayau ga danta ji nayi kamar kada na karasa aikin na mike nabar office din a lokacin.
A dadafe na samu na karasa komai office din na mike tare da tattara duk wani abinda nasan cewa nawane na bar office din rai bace.
A sabuwar motana na saka sai bayan na shiga na zauna na dago kai na kalli haraban ma,aikatan lokaci guda na sauke ajiyan zuciya.
Don Allah ya gani banso na daina aiki dasu ba saidai hakan ya zama min dole don in samawa kaina dashi Sha,aban din salama a gun mahaifiyar shi dake nata haukan a kanmu yanzu .
Motar nasa key zan tayar wata zuciya tace bar masa motarshi shima a nan to idan na bari ai taci banza ke nan naba kaina amsa ni kadai .
Jan motar nayi a hasale kamar Alaja din tana tsaye tana kallona a lokacin nake jan motan haka nakai gida zuciyana yana tafasa.
Na dan tsaya mun gaisa da umma dana sama a shago kafin na shige ciki na tube kayan jikina na dan watsa ruwa na fito mm a shiga kitchen abincin dare na dora muna lokacin don dai kawai naga na zama busy na fita zancen dake cin zuciyana lokacin.
Saidai hakan bai samu ba don ina aikin abin yana fado min a rai ina jan dan tsuki daga inda nake har na karasa na kawo falo na ajewa su umma na shige dakina zuwa lokacin an kira sallah magariba ko.
Bandaga wurin ba har saida na idar da isha,i na mike wanka na sakeyi na dawo na kwanta zuwa lokacin lekowan Ammar sau biyu a dakin nawa yana ganina busy.
Har sai lokacin da yazo karona ukku ya sameni kwance ya zauna a bakin gado yana tambayana meke faruwa dani ?
Notin na bashi amsa wayana dake gefe ajiye ya dauka ya bude ya fara latsawa sai naji yace dani you have nine miscall in your phone.
Da sauri na juyo inda yake ina tambaya daga waye yace new number ne yana miko min wayan dake hannun shi din.
Kallon number nayi na wani kasane ba wancan da akakirani dashi bane da farko banza nayi da kiran muka kama hira da brother din har ya dan mantan dani abinda ke damuna din a lokacin.
Muryan ummane ta kira Ammar yazo ya daukan muna abinci idan ba zamu fito zuwa falo ba lokacin muci.
Jin hakan yasa muka fito kamar ana jiran zaman mu a falo wani kiran ya kara shigowa saidai wanan kiran na ya Abubakar ne yasa nayi saurin dagawa.
Gaisawa mukayi yana tambayan lafiyan mu nace dashi duk muna kalau kafin yace yau dai daddy da uncle buhari they free yanzu haka suna gida dazun nan suka dawo daga Abuja.
Thank god na fada tare da fadin yaya sauran kuma saida ya dan nisa kafin yace dani kinsan yadda sharian kashe mutum yake fa.
Ko su din bawai an sakesu ga baki daya bane an dai yardane ayi bellin su a yanzu din kafin lokacin shiga kotu yayi.
Idanuwana na lumshe kamar yana gabana lokacin ina maijin wani iri a raina sainaji muryan shi yana fadin ki fadawa mama duk yadda akayi mun gode duk da munsan ba,a kyauta maku ba ga hakan.
Mukai sallama dashi don akwai hayaniyan da nakeji yana tashi a wurin hakan ya nuna yana wurin jama,ane lokacin ya kirani.
Nayiwa umma bayani kamar yadda yayi min bayani babu wani fara,a a fuskanta ko nuna jin dadi ga labarin sai Allah ya kyauta data fada kawai ta dan nisa a lokacin.
Loma biyu kawai tayiwa abincin sai ta kasa ci gaba da cin abincin dake gabata din a lokacin nima a bangarene hakan ne ya faru dani.
Don na kasa kalon abuncin da sunan ci sai wayan da nake faman dakila a hankali bada niyar yin hakan ba nakeyi don dole.
Shima dai Ammar ya dan taba saidai baci kamar kullun ba don irin yanayin da yaga mun shiga a dan lokacin na damuwa wanda ba zamuce ga dalilin hakan ba a lokacin.
Gidansu daddy kuwa sai shige da fice jama,a keyi suna mashi murnan wai sherin da ake kokarin kula mai don a bata mai suna.
Ai yanzu gashi gaskiya tayi halinta an gane an sakoshi tunda part din anty Amarta hjy karima ba abinda sukeyi sai faman surfa muna zagi iya son ransu.
Wai mun dawo da talauci a haukace munzo mun hargitsa masu kwanciyan hankalin su lokaci guda mun hana mutane zaman lafiya.
Sai goma na dare aka samu rufe gidan daddy din sanan mutane suka tsagaita shigowa badan sun daina zuwa don murnan dawowan nashi ba a lokacin.
Washegarima haka aka dora tun fitowan shi a masalaci jama,a suka dunga shigowa a lokacin nan kuma gidan ya sake dinkewa da jama,a har ma sunfi na jiyan da sukazo mashi tunda shi mutumin jama,ane ga kuma ta fannin matan shi suma don labarin ya bazu gari kowa yaji.
Daddy daya fito gaisawa da gungun wasu maza da mata da sukazo daga fannin anty Amarya bayan sun gaisa din ne akai mashi barka da arziki.
Sai kuma aka shiga jefa min zagi suna aibantani tare da jefa muna mumunan addu,a da sauri daddy din ya dagawa mai maganan hannu lokaci guda.
Tare da fadin haba malam meye laifin yarinyar nan a nan ka kwantata akan ka idan kaine yau aka kasheka yaya iyalinka zasu dauki a bun a zuciyar su.
Ba dadi mutumin ya bada amsa cikin sanyin murya yana gyara zaman shi a hankalin cikin muzanta don wanda yakeyiwa ya katseshi ta hanyar daure jikin shi.
Daddy din yaci gaba da fadin haka din dai nasan zasuyi koma fiye da hakan amma kaga jiyan nan ba,a sakini ba don wani matsayina kona wani saidai don ita wanan yarinyar da kake zance akanta yanzu.
Itace tayi tsaye saida taga an fito damu a yanzu din don wanan kamun bada sanin ta akaimuna shiba yanzu wanine can kuma da yake da alaka da wanan case din yasa akamomu din shari,an da akai a nan wai bai gamsheshi ba.
Au haka zancen yake yace kwarai kuwa babu laifin iyalin marigayin ko kadan a wanan kamun namu na yanzu .
Wanan tsakanin mune dashi wanan mutumin a yanzu ita kuma ta bayar da nata taimakon ta hanyar da zata iya bayarwa din a yanzu kan hakan.
Kowa falon yai shiru dukda tunanen kan wanan zancen na daddy sukeyi a yanzu har dai aka dauko wani zancen suka kaiga watsewa wurin.
Modibbone ya shigo gidan cikin kamala dashi da matarshi nan suka shiga gaida mutane da suka sama kafin ta samu wuri daga kujeran dake da dan nisa da inda daddy din yake zaune ta zauna itama.
Kallonta mommy ta danyi kadan kafin ta mayar da kanta inda take kallo da farko tana maijin zafi a zuciyarta na yarda Nazifa din bata da kunya ko kadan a rayuwan ta.
Don idan tana da kunya ta yaya su suna zaune saman kujera zata shigo itama ta zauna a sama haka wanan ai nuna rashin tarbiyane garesu.
Fuskanta a cikin damuwa yake itama daddy dakewa yan jikokin shi ba a ne ya dago yana fadin suma dai su Alh din muna sa raicewa abin zaizo masu da sauki insha Allahu saidai yadda shari,an ya tsaya dai a yanzu.
Hawaye ta fara sakewa duk kokarin da tayi kada su fito din wurin taushe zuciyarta saiga kuma zancen da daddy din ya karasa dashi a yanzu wanda ya kara tayar mata da hankali.
Dama kuma zuwan nasu saida mijin nata yayi da kyar ta taso sukazo gaida daddy din don a cewan su ana son a nuna masu son kaine a fitar dasu daddy din su kadai abar mahaifinsu a ciki maganan da suka gama da yarta kenan a waya.
Sai gashi kuma yanzu daddy din yana fadi da bakin shi cewa fitowan mahaifin nasu saidai addua ke nan kuma watau dai ba tabbas a garesu.
Bayan sun da jima a zaune an bata hakkurine ta tsagaita kukanta ta turawa mijin waya da su tafi hakana ya sauketa wurin mahaifiyar ta.
Bai tashi a lokacin ba saida ya dan kara lokaci suna magana da mahaifin shi sanan ya tashi ya sauketa a gidan da uwayen nata ke ciki yanzu nan ya tafi inda zai je ya barta wurin su.
Washegari har goma ban leka office ba ga aiki na ugent na jirana haka yasa suke ta kirana daga Felix har oga jimo saidai wayan nawa baya shiga.
A haka dai har karfe biyu ban leko ba har hudu felix daya fito ya biyo ta gidan namu akace dashi na fita lokacin.
Haka kuma washegari shiru har kwana uku babuni babu wayana don idan ban samun zuwa zan bugowa oga jimoh waya in sanar dashi dalilin rashin fitowana ranan.
Gashi ko oga Abdul da muke gida daya ban fada mai dalilin rashin zuwan nawa office din ba dan bamuma haduwa dashi ko a gida.
Hakan yasa daga wurin aikin suka nufo gidanmu su ukku sunyi sa,a ina gida na gama gyaran gida da jikina ina kokarin in fita shagon umma in zauna.
Sai gasu sun shigo tare da umma da suka sama a shagonta na fito muka gaisa nan Filex ke min wasa bayan mun natsu oga jimoh yake tambayana ko lafiya har kwana ukku basu ganni ba.
Dan shiru nayi kafin nace dasu na jaye daga aikina bazan kara shiga aikiba kuma gaba daya suka kalloni don basu zaci jin hakan daga gareni ba lokacin.
A cikin wani yanayi oga jimoh yace ko saboda mey nayi wanan maganan nace ra,ayine hakan ganin ba zan kara magana ba akan hakan yasa suka mike sukai muna sallama suka tafi.
Umma bata dawowa tun fitan su don tasan da dalili dana fadi hakan don haka tasan idan na samu natsuwa zan fada mata ko meye.
A nan gidan kuma komawa nayi saman gado na kwanta ina faman tunane tunda ina son aikina ina samun rufin asiri a cikin sa kuma basumin komai ba wurin.
Saidai dole in barshi don kare mutunci da kima da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login