Showing 153001 words to 156000 words out of 382072 words

Chapter 52 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28343

kuma kaduna zamu tafi meeting mu dawo duk da bani kadai bace mace yanzu dake cikin su akwai Yemisi da ta dawo daga kasan waje tana jin kanta mu shidda ke nan ke tafiya yanzu wuri muna take mai baya kowa da aikin sa kuma.
Sai shawaran umma din yai min dadi a lokacin don shiga ta alfarma shine ya dace da wanan shigan munyi da safe karfe bakwai zasu daukeni mu tafi.
Sai ga zance ya canza aida karfe hudu zamuyi tafiyan ke nan wanan katon kwana zamuyi a can yaya zan tari umma da wanan zancen ta kwana tare da maza haka.
Abdulhamid na sama a gidan shi bayan ya dawo aiki na fada mai abindake faruwa shima din saidai yayi tunanen abinda zai fadawa umma din kafin ni kuma yayi min nasiha da kama kai da mutuncina duk da yasan ba halina bane yin hakan.
Saidai baisha wani wahala wurin fadawa umma din ba sai cewa da tayi ta kama kanta da mutuncin ta nasan halin sahiba amma duk da hakan ta tsare mutuncin ta dai a can don kaduna gidane gareta.
Data shigo kuma take fada min yadda sukayi da Abdulhamid din ta min nasiha tare da cewa na leka gidan daddy koma na kwana a can din ba komai bane din sun watsar damu hakan mu sai mu bisu ai yan uwan mune su.
Allah ya rufa min asiri karfe uku sai ga felix gidan yazo wurin umma yake fada mata don lokacin da suka kirani suna fada min nace ba zan tafi ba ni shine ya fadawa ogan shi kuma ya turo shi wurin umma din akan ya roketa zamu tafi aiki kaduna mu dawo gobe.
Shima din rokon shi umma tayi akan akula mata dani don Allah kuma akwai yan uwa a can don mu din daga kaduna din muke ai.
Karfe uku da rabi muka bargida zuwa airport don jirgin hudu zamu bi ba bata lokaci kuma jirgi ya daga sai kaduna garin gwauna damu.
A wani katafaren hotel muka sauka kowa da dakin shi karfe takwas zasu fara taron nasu ke nan na dare don haka muna da sauran lokaci ke nan sallah nayi na zauna zaman lazumi.
Kafin na mike na shiga nayi wanka a bayin na fito sallah na tayar na fara shirin barin hotel din shiga nayi sosai na alfarma da daya daga cikin rugunan dana sayo din baka mai duwatsu farin ado a jikin shi na zauna gaban mirrow din na daura dan kwali baka ganin komai sai zagayen fuskana sai turaren muzawa mai kwanci daya bi jikina yana tashi a gankali takalma mai hill ne a kafana sai jakka dana dauka shigen kayan jikin nawa kafin na dauko jakkar laptop dina daga baya.
Ni kaina nasan ban taba shiga irin wanan din ba haka zaka rantse da Allah ni din wata balabiyace a lokacin Felix ne ya kwankwasa min kofa a lokacin na bude yake fadin suna jirana a waje fa nasan oga baison latti.
Ashema har yemisi na cikin gidan lokacin tare muka jera mu ukun dukkan mu a cikin bakaken kaya .
Mun samesu a cikin mota sai satan kallon motan nakeyi don kyau ya nuna min inda zan shiga na nufi gaban motan zan bude da sauri wani yace min baya dai na bude bayan na shiga.
Budewa nayi ina mamakin sauyin ranan na shiga na dauka yemisi ma nan zata shiga naga ta nufi wani motan daban ta shiga.
Ina shiga ogan mune a ciki a cikin rikicewa na gaidashi ya amsa min ciki ciki a takure na zauna muka fara hanya motan yana shiru saishi dake aiki a cikin computer din shi yace na bude nawa yana miko min wani abu .
Ganin ba zan iya ba yace dani na miko mai photon mune mu da umma da mukayi ranan sallah na saka a screen din computer din .
Saitin ta yayi min tare da dan fada min abinda zanyi ya miko min tafiya mai dan nisa sai gamu haraban wajen taron tun daga nisa zaka ga irin haske da yawan motocin dake wajen.
Daga can dan nisa kadan muka samu wurin parking din motocin mu bamu fito ba sai da wasu security sukazo aurin aka bada umurnin fita.
A ciki kuma kallo yake don matasan masu kudin zamani ne birjit a wurin sai tsofi da dattawa da kososhin gwaunati masu fada aji a cikin kasa.
Wow ga sha,aban nan ya shigo da nasa tawagan wanan taro yayi albarka sosai da amsa gaiyatan matasan mu dake tasowa da kulada jin dadin kasa.
Idanuwa sukayo kan mu caaaa yana dan daga masu hannu irin na sallama ga yan uwa har muka isa inda akai muna mazaunin mu a wurin.
Daga can baya inda suke zaune da zasu iya ganin masu shigowa yake kallon fuskokin mu daya bayan daya sai dai ya tsayar da kallon shi ne a kaina zuciyar shi na bashi karya a lokacin.

ZAINAB IDRIS MAKAWA



ANA DARA GA , , , , , , , ,

4️⃣6️⃣ BY, , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL AZEEM, , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KADA KI RAINA GIRMAN AIKI MAI KYAU DON HAKA KADA KI RAINA KANKANTAN ZUNUBI A GARE KI KIBIYA KAFIN KI KARANTA, , , , , , ,

Kina daukin a dauko ki karanta a banza bayan kinsan girma da nauyin hakki a wurin Allah kada ki raina girman zunubi a kanki yar uwa ki zama mai gujewa shiga hakkon wani komai kankantan abin Allah yasa mufi karfin zuciyan mu.
Yanayin zaman mu daban dana saura a wurin bamu dade da zama ba aka fara gudanar da taron ba wani abu ake magana akai ba sai yadda abubuwa a yanzu suke tabarbarewa a kasa inda gwaunati ke neman hannun jarin yan kasuwa .
Akan su saka hannu su bayar da gudun mawa a nasu bangaren mai bayani ya kara fadin babu babba ba karami a wurin wanan harkan don gaba daya ci gaban kasa ake nema.
A karshe gwaunati ta kawo tallan wasu abubuwa da gwainatin ke mulka a wurin yan kasu don ya koma karkashin su ko abubuwan zasu gyaru nan gaba saboda gwaunati na ganin ba zata iya ba idan ba hannun yan kasuwan a cikin harkan.
Ko wani abu aka gabatar zamu zauna muyi nazarin sa a tsakanin mu a cikin sytem din dake gaban kowanin mu a turawa juna wanda kusan ko wani dan kasuwa shima yana duban abinda ka fitar dashine a lokacin.
Duk abinda akeyi daga inda yake zaune idon shi na a kan mu ya raba hankalin shi gida biyu zuwa ukku a wurin komai irin na yarinyar ne saidai wayewan da rayuwa ya hanashi yarda da abinda zuciyar shi ke bashi.
Wanda ke bayani a lokacin ya fadi abin ban dariya duk dakin taron aka kwashe da dariya sabanin ni da hakan yasa na dago kai a lokacin ina bin mutanen dake wurin da kallo.
Caraf idona ya sauka kan tsohon dake gefen mu dan nisa kadan damu daga inda muke zaune babu tantama shi dinne dai Alh Nuhu shine makashin mahaifin mu dana taba gani sau biyu a rayuwana don bazan taba mantawa da fuskanshi ba.
Take naji duk ilahirin tsikan jikina ya tashi a wurin ba zan iya kara daga kai in kalli wurin hatare dana shakeshi ba a yadda nake jin zafi a zuciyana ba.
Wurin ya dan kaure da hayaniya don dan hutun da akaje kan ambada dama ayi nazari kan zancen da gwaunati tazo dashi ga yan kasuwan da suka karba sunan su na yan kasuwa a kasa.
Masu hida a wurin ne biyun suka kawo abin sha a taburin mu duk ina jin abinda suke fada sama sama don ban cikin hankalina sosai a lokacin.
Adanan ne yake kokarin bude drink din dake gaban shi da sauri na dago kai ina fadin karku taba komai a cikin abin da aka aje a gaban ku.
Kalloni gaba daya sukayi da mamaki nace kuyi saurin gagauta abinda mukeyi mu bar wurin nan kafin nan da minti talatin don yan kungiyan asiri sunyi yawa a wurin nan akwai abinda zai faru a nan gaba.
Felix ne yace what sahiba are you a wizird how d u know all dis will happened next hannu oga sha,aban ya daga masa akan yayi shiru.
Kafin inji suna zance da Jimoh babban na hannun daman shi ke nan da suke gudanar da aikin su tare don akwaishi da hazaka sosai yau sai gashi na tsoma masu baki ga zancen su ina fadin.
Maida alkama din zasu kada ku canza wani daga wanan din idan kun yarda ba tare dana dago kai na kallesu ba na sake fadin sai semintin don shima ribane a gareku nan gaba baikai second ba sakon haka ya shigo a wayan mu daga gareshi.
Ya fara rufe sytem din shi kafin da sauri gaba dayan mu muka rufe muka mike tsaye don barin wurin bayan ya aika da sakon shi.
Yana gaba muna daga bayan shi gab da zamu fitane aka kwalawa sunana kira da Sahiba abinda yasa yaja ya tsaya cak ke nan ya dan waige .
Ba shi kadai ya tsaya ba don gaba dayan mu munji kiran kafin kuma ya daga kafanshi ya soma tafiya don barin wurin muka bishi a baya .
Zargin shi ya zama gaskiya don ta haka zai gane koni dince dai ya gani ba zargin yakeyi ba a lokacin sai dai ai kuma ban ko juyo ba a lokacin .
Ganin mun fara takawa don barin wurin shima ya tako da sauri zuwa wurin mu din alokacin har mun shiga mota driver ya tayar ya tsaya yana kallon mu da hannu nayi mai wani alaman da bai gane me nake nufi da hakan ba.
Ya juya don komawa dakin taron kafin yakaine ciki yaji fashewan wani abu har mu dake cikin motan a hanya don bamuyu nisa ba munji wanan karan fashewan abin.
Daga can motan da jimo ke ciki ya bugowa oga waya yana fadin yaji abinda sukaji kuwa yace yaji shima direct masaukin mu muka koma daga nan.
Bayan mun fito daga motan tsayawa yayi kamar yana nazari duk muka tsaya a bayan shi muna sauraren me zai fada.
Baiyi magana ba sai kuma ya fara takawa yana tafiya tare da fadin jimo follo me Sahina you too yaci gaba da tafiya zuwa dakin da yake.
Dan tsayawa nayi kafin da sauri nabi bayan su din nan muka bar sauran suka bimu da kallo kafin Felix dan duniya ya wayance da fadin yarinya yau kin taro much akanki tunda kika fara tsoma baki ga maganan manya haka.
Yana tsaye tsakiyan dakin ya harde hannayen shi oga Jimo ya rigani shiga shima haka ya sameshi tsaye a wurin.
Na shigo na bisu da kallo kafin yayi wani tako biyu zuwa uku ya juyo garemu yana fadin meke cikin drinks din da kika hanamu dauka a lokacin kuma meke faruwa a wurin?
Bai tsaya kallo na ko saurare ba ya juya yaci gaba da abinda yakeyi din a yadda muka sameshi da muka shigo dakin.
Shirune ya biyo baya ya kara takawa ya juyo yana fuskantana tare da fadin zanso jin mai farautan ran mu a wanan kasan.
Baku kadai bane don ba a kan mutum daya suke keson nufin su ya kaiba ga kowa dake wurin suke son mallaka wanda ya fada tarkon su,
Ba zasu so ku matasa ku sayi komai ba son a yanzu sun san akwai wa yanda suka fisu karfi a cikin ku shiyasa sukayi plan din da taron zai watse a hakan .
Nayi shiru shima ido ya daga yana kallon Jimoh din na dan lokaci kafin ya dawo da kallon a kaina yana fadin you can go now na juya na fita har nakai kofa naji yana fadin.
Take care of yourself nagode na fada na barsu tare da Jimoh din a dakin dakina na nufa inda na hadu da tawagan mu suna shigowa daga ciki.
Dakin na saka key din dake wurina na shiga saman kujera na zube tare da dafa kaina na dan lokaci mai tsawa komai na kasa yi don ko tunanen yaki zuwa min.
Hannuna na tura a cikin jakar dake gefena ina laluben abin da nake nema don a gaba umma ta saka min shi a jakkar dana bar komai ban dauko ba take tambayan na dauki maganina nace haba umma gobe fa muna gida war haka.
Shakawa nayi kamar yadda Alfa ya umurceni dayi kafin naji na fara dawowa normal a lokacin sai bayan wani lokaci mai tsawo na mike na nufi gadon dakin na dan zauna na fara cire takalman dake kafana.
Na jawo zanina nadaura na kwabe rigan dake jikina zuwa bandakin na dauro alwala na fito sallah nayi sosai na dade zaune a wurin kafin naji ana kwankwasa kofan.
Ban bude ba na tambaya daga ciki naji muryan mace na fadin room services na bude abincine ta kawo min na bata hanya ta shigo dashi na gaida ita.
Ta juya tafita na rufe kofan ina saye da hijjab din da nayi sallah a jikina na har lokacin ban cire ba na nufi cikin dakin lokacin wayana yayi kara alaman sako ya shigo min a wayana.
Daukan wayan nayi na duba ogan mune mamaki nayi ashe yana da lanbana shi tambayan a yake yi game da abincin da aka kawo muna normal kawai na bashi amsa dashi na aje wayan daga gefena.
Naci abincin sai dai ba sosai ba na gama abinda zanyi na kwanta zuciyana cike da tunanen abubuwa barkatai a lokacin.
Bazance nayi barcin dadi ba a ranan don dai koda na danyi saina falka don mugun mafalkin da nakeyi a lokacin.
Har gari ya waye nayi sallah tare da addakar din safe kafin na mike da wani itin barci a idona na nufi wurin tv dake dakin na kunna na rage damuwa a zuciyana.
Yau rabo da naga wanan labaran hausa sukeyi a tashan da ke kai na koma na zauna ina lumshe idanuwa don ko na kwanta ba barcin zanyi ba a lokacin.
Abinda ya farune a wurin taron jiyan da dare aka sanarwa anan tashan ashe har hakan yayi sanadiyar mutuwan wasu bayin Allah a wurin.
Hankalina ya dauku ina sauraren labaran ne naji an kwankwasa min kofa na mike ina tambaya waye ta amsa min da fadin Yemisi.
Na bude ta shigo tana bin dakin da kallo duk da komai nasu iri dayane da wanda take a ciki itama saida ta karewa dakin kallo ta juyo tana fadin A,a i tink say you de for oga room now, na dere you sleep with him ?
A cikin wani irin mamaki na kallota take fadin why you no sleep with him naw ?
i tink say, u de dare with him dat is why i no try my luck yesterday night ashe ke baki kwana dashi ba ni kuma banje na kwana a wurin shi ba duk mun tashi a zero.
Ta fada tana bata fuska ta dafa min kafadana tana cewa kinsan na dade ina kwadayin kasancewa da ogan nan namu tun ranan dana fara ganin shi ga dama ya samu jiyan kuma ya wuceni.
Me zance wa wanan mahaukaciyar ballagazan yar iskan inji sanyi a zuciyana sai kuma hankalinta ya karkata gun labaran take fadin caaye na d tin happen for dat place ?
Umm na fada tare da kallonta ina fadin i wan go bap now don dai kawai ta fice min a dakin don wani irin takaicin ta da nake ji a raina yanzu don gaba daya ta zube min ga gani.
Itako ko a jikin ta bata dauka ta fadi wani abu mai muni ba ga hakan sai kokarin jana da hira takeyi nayi shiru ban bata amsa take fadin wai kinsan irin tsadadun mazan nan kaza da kaza can abakin ta dai ita ta iya fadan maganan banzan ta.
Gabin ba zata fita ba yasa na mike ina kokarin shiga bandaki take fadin naje na fito zata zauna ta jirani nan kan duk da ta girmeni da komai.
Na rufe idona na nuna mata hakan ba zai yuyu ba ta fice dai kawai don ni bana yarda da irin hakan itama mamakine ya kamata take tambayana don ban yarda da ita bane ko me yasa na fadi hakan.
Nace no sirinane haka kuma addinina bai yarda da hakan ba gaskiya don haka ta fice kawai zai fi na shiga wankana.
Fushi tayi ta mike ta fice fuuu na mayar da kofana na rufe ina jin takaicin ta har kasan raina.
Wankan na shiga nayi bayan nafito na shirya a cikin wani dinki half atamfa gaban kuma material ne sai duwatsun da akai kwaliya yana daukan ido ina jiran inji sunce mu fito mu tafi sai ga sako wai ba jirgi a ranan da zai tafi lagos sai gobe.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login