Showing 141001 words to 144000 words out of 382072 words

Chapter 48 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28397

tana fadin good evening jere .
Kallon hannun nata nayi na dan sake murmushi kafin na amsa mata da evening missFunke ina fadin hakan na girgiza kai na wuce zuwa sama inda office din mu yake yanzu.
Da gudu ta kara biyo ni a dole sai tayi abinda tayi niyar yimin na taba jikina a lokacin saidai na fahinci hakan danaji muryan ta a bayana yasa ban dakata na haye zuwa office din da sauri na murda na shiga.
Yeh tace tana bin kofan da kallo don yadda nayi mata din ban tsaya ba tana fadin i don dead wooo if i no touch dis gurl twoday.
Ina shiga na gaida manyana dakr zaune office din kafin na hari wurin zamana ina addua a bakina lokacin nakai zaune takardun list din da aka tara min na shiga duba ina rubutawa .
Kafin can naji rikici ya kaure a tsakanin manyan nawa na kudi akan lissafi har suna kokarin daga hammata a lokacin.
Stop it na fada da karfi ina fadin ba haka aka bashi ba gaskiya yake fada an turo maida kudi kazane a ranan kaza da karfe goma na safe ya kuma tura a ranan banki har replay ya dawo gare ku a nan aka samu matsala kudin sun shiga cikin inda ba ayi niyar turawa bane mistakene.
Tsaye sukayi kowa na kallona nace babban accounter din ya duba sakon wayan shi ai baka goge ba ko yana nan ciki ?
Da sauri ya tura hannu cikin aljihun shi ya ciro waya ya shiga duba sakon daya shigo mai saiga bayanin a wayan shi ya dago kai da sauri ya kallo inda nake kafin ya sauke wani irin ajiyan zuciya ya dago kai ya kalli shugaban wurin ya mika mashi bayanan wayan shi.
Lokaci daya suka dago kai suka kalloni inda nake tsaye nima na kura mashi ido ina sauraren abinda zai fada a lokacin.
Fuskan su karara baiyane da mamaki a fuskokin su daidai lokacin na juya na koma na zauna tare da kifar da kaina saman taburina.
Smart girl we have to be carefull with u in dis place Sahiba u are very talent girl .
Ban dago kaina ba duk abinda yake fadi ina dai dan jin shi sama sama a lokacin na bude jakana na dauko maganin da Alfa ya ban in shaka idan naji alaman ciwon kai zai taso min cikin ikon Allah a hankali naji ya lafa min ba kaman yadda ya saba min ba.
Sai office din yayi tsit bayan kowa ya natsu ya zauna manager ya shigo kan maganan a yadda ya samemu a office din kowa na aikin gaban shi yasa mamaki ya kamashi na ganin ba wanda ya damu haka ana fadin kudi sun shige.
A kofa ya tsaya yana kare muna kallo a wurin kafin yace meke faruwa ya samu ba wani bincike da akeyi ?
Ogan mune ya dago yana fada mashi cewa an gane komai anyi solving da taimakon Sahiba tayi muna lissafi har yadda kudin ya shiga.
As how ya tambaya da mamaki akai mai bayani komai ya girgiza kai ya fita ba tare da yayi magana ba sai da muka dawo gida Abdulhamid ke fada min yana ganin fa zan bar aiki dasu abinda kawai ya fada min ke nan ba tare da bayanin komai ba.
Nayi mamakin jin hakan amma kuma ban tambayeshi dalilin korana wurin su da za ayi ba kawai na fara tunanen abinda zanyi nan gaba a rayuwana.
Jirgi Emerate ya sauke passenger daya dauko a Abuja daga cikin su harda Nazifa da yaran ta biyu daya yar shekara biyu sai karaman jaririyar yar wata biyu data haifa a lokacin.
Yan gidan su ne da sukazo daga Kaduna don taronta suka tarbesu a gidan wani abokin baban su suka sauka saida suka huta washegari suka kama hanyar Kaduna.
Bata sauka a gidan su ba gidan iyayyen ta ta sauka inda akai dafifi ana murna da zuwan ta don gabaki daya ta sauya ta kara zama wata babban mace yar gayu sai wani izza da isa takewa mutane.
Yaran basa jin hausa basu ma yarda da mutane bata samu ganawa da mahaifin su ba sai washe gari da safe ta sakeshi a falon shi zaune.
Yana saye da babban riga babu yar ciki a cikin rigan ya zauna ya baje saman kafet yana shan ferfesun kifi a gaban shi ta shigo da fara,an ta ga yaranta dauke a hannun ta.
Fuska ya daure ganin yaran sai dai hakan bai hanashi ya tareta ba don an dade ba,a haduba a tsakanin su saida takai kasa take gashe shi ya amsa tare da tambayan ya hanya ta amsa da lafiya.
Yake tambayan ta karatu tace ta hada a can bai tambayeta mijin ta ba kuma baiyi magana a kan haihuwan data samu a can kasan ba don bai iya tambayan ko daya don bakin hali irin nasa yana bakin ciki a zuciyar shi na hada iri da zuri,an daddy dayayi.
Har zata daga take fafin baba gafa matan ka nan suna gaida kai ya kalli yaran a lalace yana fadin nagan su ai saidai kinsan bana maraba da zurian Aliyu gidana.
Keda gwaggon ki kunja mun hada iri dasu don nacin uwarki badon ta nuna ra,ayinta kan son ki auri wanan dan iskan yaron ba ba abinda zaisa na hada zuria dasu a gida.
Jikin Nazifa ne yai sanyi saboda maganan mahaifin nata ga yayan nata da take so kamar ta mutu a rayuwan ta hakama mahaifin su ya Abubakar yake kaunan yayan nasa sosai.
Ganin yadda yanayin ta ya canza ya sake fadin nifa ban kaiki gidan nan aure don ki share kafa ki zauna har kina zuba masu yaya haka ba.
Na fada maki tun farko cewa ina da manufa ga auren nakune shiyasa har na yarda da hakan idan bashi ba ba abinda zaisa in daukeki in mika wanan gidan da raina a duniya.
Mijin ki da mahaifin shi sune ke son su ja dani a cikin dangi nayi alkawari kuma duk wanda yace zaija dani sai naga bayan shi a doron kasan nan.
Shi Ali idan ba rigima ba har me yake takama dashi a duniyan nan me yake dashi meya tara da yake ganin wuyan shi ya isa yanka har zaice zaija dani akan dansa ya saba maki nayi magana shima yayi ?
Wanan lokacin ta kasa rike kukan ta don Allah ya gani tana son mijin ta ita don ko huduban da yayi mata kancewa da wata manufa da yasa zata dan zauna a gidan nan ta dauka yanzu data hada zuria dasu komai zai wuya a zuciyan mahaifin nata ashe tunanen ta bai bata daidai ba.
Yanzu ta fara shedawa gaskiyan mutane da suke fadin shi din maison kansa ne kuma mugune a cikin dangi dolene kowa ya bishi a yadda yake so.
Yanzu kuma tasan ta kara sheda kowama ya shiga tarkon baban nasu sunan shi sorry ke nan do ko ita ya zama dole tayi taka tsantsan da yaran nan tunda har ya iya furta hakan a gaban ta yanzu.
Muryan shine ya dawo da ita ga tunanen ta da yake fadin ina son ki sani komai dadewa sai na rabaki da gidan yaron nan nan gaba kadan idan na gama aiwatar da shirina a kan su.
Wayan tane dake hannun ta ya shiga ruri shine kuma ya dakatar da mahaifin nata ga fadin abinda yake fadi a lokacin.
Mijin tane yake kiranta a lokacin yaji saukan su don bai samu layin nasu ba sai wanan lokacin amma har wayan ya katse bata iya dagawa ba.
Jin mahaifin nasu yayi shiru yasa ta mike zuwa don barin falon ranta a bace dakin mahaifiyar ta ta koma dake zaune ta hakince tana waya tana ba kawarta labarin dawowan yar nata.
Kawar na fadin ai gara da kika nace aikai wanan hadin irin matasan da ko wace uwa ke burin taga yarta ta aura ke nan a duniyan nan ai yanzu.
Saiga Nazifan ta shigo mata da kuka abinda ya dakatar da ita ke nan daga wayan da takeyi din lokacin tana tambayan yar nata hankali tashe abinda ke faruwa.
Dakin ta shiga bata iya ba uwar nata amsa ba don kukan da yaci karfinta a lokacin ba zata iya furta komai a lokacin.
Tashi tayi tabi bayan yar nata tana fadin ke lafiya ko mijin nakine wani abu ya sameshi baki fadi zaki dagawa mutane hankali haka ?
Mama bashi bane fa ta fada a cikin kuka Abba ne yace baya son diyan nan don baya kaunan zuri,an uban su kuma in rubuta in aje zai rabani da mahaifin su nan bada dadewa ba.
Zaune uwar takai tana salati tare da fadin abin na Alh har yakai can don wani bukata nasa ya mayar dake bazawara ko ya mayar maki da diya marayu don shi daukan ran wani a wajen shi ba a bakin komai yake ba.
Nazifa din ta dago tana fadin mama zan tafi tunda har Abba ya iya fadin haka kada ya zo halaka min yaran nan don Abba zai iya ga yadda na fahinta yanzu.
Dako na tona masa asiri a garin nan idan har ya taba min jikokina da Allah ya fara ban idan ma zasuyi abinsu shida mahaifin Abubakar ya tsaya iya su amma karya kawo gareku gaskiya ta mike da sauri yar tace mama dawo.
Zuwan ki yanzu zai iya haifan wani matsala da zai kawo fitina don shima Abba din ya hau yanzu don Allah mamakiyi hakkuri kada ki masa magana yanzu kan hakan.
Naji amma yasa duk abinda yake takama dashi nima din nasani don tafiyan duk gudane dani dashi idan yace zai taba min yaran nan yanzu sai inda karfina ya kare dashi wallahi.
Abubakar kuma yayi kita bai shiga ba yasa ya bugowa hjy Addah waya yaji ko lafiya matar nasa bata daga waya ba.
Don bai taba zaton wai gidan su zata tafi direct ba haka tunda yasa a gyara gidan su kuma tasani komai an saka masu sabo a gidan an kara gyara ko ina na gidan.
Wani dalili ya hanashi zuwa tare da iyalin nasa shi sai karshen wata zai shigo ya don aikin daya taso mashi bayan sun gama shirin tafiyan su tare dole ya bari su fara zuwa kafin shi ya biyosu daga baya.
Dauka tayi da sallama suka gaisa take tambayan shi aiki da iyalin shi sai mamakin jin hakan ya kamashi har yake fadin.
Mommy ai suna Nageria kwana biyu ke nan basu zo bane nan ko baku da labatin zuwan sune ya tambaya cikin mamaki .
Suna Nigeria fa kace yace kwarai kuwa mommy tun shekaran jiya suka taso kuma na tabbatar da tana kaduna yanzu haka.
Lafiya har ta shigo garin bamu da labarin hakan yace shine abinda ke ban mamaki yanzu ke nan ai mummy don tasan na gyara gida don zuwan ta din ai.
Kashe waya yanzu in kira mahaifiyarta muji idan tana gurin su yace tana can ma tunda bata zo nan gurin ku ba ai ya kashe wayan itama ta kalli nata wayan.
Ta kira layin baije ba not reachable ake fadi lokacin ne kuma Faiza ta fito daga dakin kwanan su ta zauna tayi shiru tana jin abinda suke magana a kai.
Ba wanan ne ke damun ta ba sai mafalkin da tayi shine ya tsaya mata a rai tayi shiru tana nazarin mafalkin a ranta .
Hauwace ta kira sunanta ta dago tana fadin na,am Sahiba me kike fadi duk suka zubo mata ido suna kallon ta kafin suce wata Sahiba kuma kike kira yau ?
Yau kuma kin tuno Sahibace a zuciyar ki ko me Sahiba kan ai sun manta damu yanzu sunci moriya sun manta kowa yanzu suna can suna bariki Nabila ta fada.
Bariki kuma Fa,iza ta tambaya a cikin mamaki idan ba bariki ba me sukeyi a can lagos din dama ?
Hjy dake jin su tana kokarin sake kiran mahaifiyar Nazifa ta katsesu da fadin uban wa yace daku haka wai ?
Tayi sa,a a lokacin kiran nata ya shiga ta kara a kunnen su har aka dauka da hello ta amsa sai dan gaisuwa sama sama tace na bugo in tambayene idan su Nazifa sun iso gida ?
Tace sun iso jiya da yammn nan gata kwance tana barci sai Addah djn tace Alhamdullahi dama mijin tane ya bugo yana tambayan isowar su din .
Ashe ta taso ita bamu da labari Allah ya hutar da gajiya yaushe zata iso gida ke nan ta tambaya a karshe.
Tace sai ta huta a nan an kwana biyu ko idan mijin ta yazo saita dawo hjy Addah tace amma ko in kunyi hakan bakuyi muna adalci ba gaskiya amma ba matsala zan turo yara su daukan min yaran nan ingansu ta kashe wayan ta.
Zage zage hjy ta fara da fadin zancen banza zancdinnmmwofo ni Addah zata kira ta raina min wayau kan danta idan zatayi mulki ta tsaya iya danta kawai don ko yaran nan ba zan yarda su shige mata ba cewa da diyan Nazifa din.
Me tace mama Nazifa dake kwance tana waye da kawayen ta ta tambaya ta dan dago tana kallon mahaifiyan nata sai ta fada mata yadda sukayi da Addah.
No ba inda zasu tafi ta bari idan ubansu ya dawo mun koma zata gansu kowa ban yarda dashi ba ai yanzu ta fada tana komawa kwancen da take din da farko.
Itama din dai Addah fada ta kamayi a nata bangaren tana fadin laiai ma yarinyar nan me take nufi da hakan wai da yin haka ?
Amma zata dawo ai zata fada muna dalilinta na komawa gida ta zauna ga dakinta ta bari a nan sai kuma taja tsuki tana fadin shima dai daya turota zuwa gida ita daya haka don su basu raina dalili ai.
Mommy yaran ba zamu gansu ba ashe yanzu don nasa ko anje daukan su ba zasu bayar dasu azo gidan nan dasu ba saidai idan yaya ya dawo kasan nan ke nan kuma.
Zanje zanje duk abinda zamuyi muyi ta akan yaran nan kafin Alh ya dawo gidan na kuma ya aza min nasa jidalin ina zaune kalau.
Wani irun nisawa Nabila tayi kafin tace solution dayane mommy kawai yaya ya kara aure zasu shiga hankalin su idan yayi hakan.
Amma wallahu nasan idan kin dogara da wa yan nan jikokin ba zaki taba nunasu a matsayin jikokin na fanin yaya ba tunda kinga sun fara haka.
Sun fasan yaran nan gidan nan ba wanda yasan su da ido saidai a photo kawai amma ta iya shigowa kasan nan dasu ta share kowa idan ba don shi din da ya kira yana fadin zuwan ta ba.
Kinji ki da wani zancen shirme Abubakar din ne zai kara aure ko wanan din da yaya na samu yayi har aka kai haka din.
Iskancin ta yayi yawa mommy haka ya dace ayi masu kawai don idan sun gashi da wata matar ai dole su kama kansu su daina kawowa mutane rainin wayau haka.


ZAINAB IDRIS MAKAWA


ANA DARA GA , , , , , , , ,

4️⃣3️⃣ BY, , , , , , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL LATIF, , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL DON ALLAH YAR UWA KI BIYA KAFIN KI KARANTA DON NA KUDINE ALLAH, , , ,

Kwace nake ban da niyar zuwa aiki duk da yau ya kamata in fita full day nayi aiki dasu amma na gyara kwanciya naja bargona na kara rufa.
Umma ce jin shiru ban fito ba yasa ta fito daga dakinta zuwa nawa tayi sallama ta shigo dakin ta sameni ina barcina hankali kwance ba niyar tashi a lokacin balle nayi shirin fita wirin aiki.
Kwana biyu ke nan ban zuwa aikin ina gida idan na dawo tare dasu tunda Abdulhamid ya fada min hakan naga kafin su dakatar dani gara na dakatar da kaina aiki dasu din.
Sahiba umma ta kira sunana tare da dan tabani kada na dan firgita ina falkawa na bude idona umma tace sahiba yau ba zaki fita aikin bane ga lokaci na tafiya ?
Idona na dan lumshe ina fadin umma na daina aiki dasune don Abdulhamid ya tsegunta min kamar zasu koremu a ma,aikatan nan bada dadewa ba.
Shiya fada maki haka na kada kai ta sake fadin koda zasu koreku ai zasu baku hakkin ku ko dkn haka ki tashi ki shirya ki fita bana son wani abu ya fito a bangaren ki gaskiya ki bari sai idan sun dakatar dake din tukun.
Wani iri nayi da fuska saidai ba yadda na iya dole na dan yunkura ina fadin zan shirya na tafi umma tace Allah maki albarka na amsa da amin.
Ban bata lokaci ba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login