Showing 318001 words to 321000 words out of 382072 words
wanan maganan ko waya mun daina yi dasu yanzu nikan ai yafi min ma don kada azo ace dama don gadon nasu nakeyiwa wanan rawan kan a kansu .
Sun dai jima suna magana inda a karshe ya fahinci a kan wa suke zance bayan sun kashe wayan ne ya kalli mahaifiyar nasa ya jefo mata tambaya da fadin.
Mami suwa Sahiba ta daukane kuma ina suka jene da mutanen da kuke magana a kai saita juyo tana fadin kaidai bari the boy.
Kaga abinda dama nake gudu ke nan tun wuri ku kuma baku fahinceni ba mutane su fara fadin don naga kudine nake kokarin cinna maka ita ka aura.
Kasan ko zasu fada irin wanan facakan arzikin da suka fara haka wai ace sahiba ta dauki mutum goma zuwa umurah lokaci guda haka kai tsaye ai wanan abin akwai ayan tambaya a cikin shi.
Shima jin tayi shiru ya jefo mata tambaya da har an mika masu dukiyan nasu ne ko haka ya tambaya yana kallon fuskanta ?
Wanan kuma ban sani ba har in an basu gaskiya banda labari kuma da an basu din aida naji kuma koba gaskiya ba wanan abin nasu aiba a boye yake ba kowa yasani.
Haba mami kin gani gashi kin ba kanki ansa yanzu cewa ba a basu ba amma kuma kuke masu wanan zargin haka why don Allah mami kika canza hakane yanzu ?
Ya kamata ku tausayawa mutanen nan da ace kunsan irin kaskancin rayuwan da mutanen nan suka gani a rayuwan ba zakuyi masu wanan abin ba yanzu.
Kudai maza haka kuke ga gaskiya mutum na gani amma sai ko rufe kuce mutum baiyi daidai idan bashi ba ba za a tsaya aji inda kudi ya fito ba sai a hau murna cewa wai tayi kokari.
Na fahinci yanzu don na furta ina son yarinyar nan kika taane su hakan ga amma idan ba haka ba ai da can naga kina tausayin su sosai ba kamar yanzu ba.
Duk abinda zaka fada ni ina nan bisa kan zance na ba zakasa mutane su zage a banza ba ko ka dauko min magana a cikin zuria ta.
KLlin mamaki yake jifan ta dashi don ya kasa gane mai take nufi har yanzu don kawai yace yana son sahiba din ne wanan abin ko kuma wani zance ne a kasa daban ?
Shiru yayi ya mayar da hankalinshi wurin tv dake aiki saidai zuciyar shi fam yake da tunanen me hakan ke nufi har zan dauki mutum goma zuwa umarah.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA , , , , , , , ,
9️⃣6️⃣BY, , , , , , , , , , , ,
ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MUNTAQIM, , , , , , , , , , ,
ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257
ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋
Sallah asubah a haram mukayi don tun karfe uku da rabi baffah ya tayar damu don zuwa masalaci.
Duk sakkon mu mun samu har masalacin ya fara cika mun daiyi sa,a mun samu shiga ciki mun zauna.
Bayan nafila da muke tayi bini bini zamu mike mu gabatar da nafila kuma gaba dayan mu saidai Fatima da take dan kwantawa tayi barci ta dago kuma ta bi sahun muba wanda ya matsa mata don mun san cewa ita din yarinyace a cikin mu.
Har karfe goman safe kafin mu dawo masaukin mu a gajiye kowan mu yake a lokacin wanka mukayi kowa yabi lafiyan gado ya kwanta don karfe sha biyu kawu yace zamu koma masalacin.
Muna da kwana biyu ba abinda mukeyi banda ibada tukuru babu kakautawa kowa na fadawa Allah zuciyan shi.
A rana ta ukune munje masalacin an idar da sallah sai ga baffah yazo inda muke zaune da abincin daya sawo muna saboda yace mu daina zuwa gida mu wuni a nan sai bayan sallah mu tafi masauki.
Bayan sun karba ne don ni ina addua a lokacin kai na samu daga mashi kawai a lokacin don banson katse azzakar ddin a lokacin.
Karfe tara muka iso masauki ba zancen tsayawa hira a yanzu gare mu don kowa a gajiye yake lokacin cikin mu.
Daga umma har sauran tsofin uku da suke tare basu shigowa dakin da muke a cikinsa dan gara mu din mukan shiga mu gaisa dasu ko mu dubasu wani lokaci idan muna a masaukin.
Wanka na fito lokacin don nice na shiga farko suna zaune suna dan ciye ciye kasa saman kafet ga sanyi AC ta ko ina a cikin dakin.
Umma ta turo kofa ta shigo daga inda nake tsaye ina kokarin saka riga a jikina jin suna gaida ita yasa na juyo da mamaki ina kallon ta.
Yarbanci muke yi don haka ba lalai bane suji me muke fadi a lokacin wanda kuma umma zuwa tayi tana fada min tsohuwa guda bata da lafiya tun a masalaci bata fadi ba murane ya kamata ya haifar mata da ciwon kai da zazzabi jikita yayi zafi.
Cikin nuna damuwa nace subbahanallahi duk suka kalloni suna son jin me ya faru da hausa naso yi masu bayanin cewa bata da lafiya sai kuma na kasa dole na juya da turanci ina fada masu abinda ke faruwa tunda hausan ya kiya lokacin .
A gurguje na saka riga a jikina muka fita zuwa nasu dakin dake kusa damu a kwance na sameta ta nade a cikin katon bargon su .
Yadda na gantane ya tayar min da hankali na karasa ina dadin mama meyene ya sameka zamu asibiti ko a dan yanayin tashin hankali nake magana.
Don Allah ya gani na tsorata da hakan a wurin yarbawa zasu camfa suce dama da wani manufa na kaisu saudiya don nayi kudi dasu ko wani abu.
Fita nayi a gigice daga dakin na fita zuwa waje don in samo magani a wanan lokacin Allah ya taimaka muka hadu da wani dan Nigeria ina masa bayani yace gaskiya ba wani phamacy a nan kusa amma barin taimaka ga wanan ku bata gobe sai ku kaita asibitin.
Dan jakkar dake bayab shi ya bude ya fito da wasu magani ya bani tare da bayanin yadda zata sha din nayi mai godiya na juya da sauri zuwa lifter.
Ina kokarin rufewa ne aka dagatar dani wasu mutane zasu shigo mazane ni kadaine mace a cikin su har suka karaso suka shiga tare dani duk hankalina bai a kansu ina can ina tunanen halin da mama take ciki kwance.
Mai tsiwa meke faruwane haka dake naga hankalinki a tashe yake is anything wrong somewhere ?
Duk wanan maganan da yakeyi a cikin harshen hausa yayi shi sai na karshen daya fada da turancine na fahinci dani yake magana lokacin.
Yasa na sauke fuskana a saman nasa ina dan kallon shi tabbas shine shine wanda yai sanadin zuwan mu saudiya da har muka fara zargin ko ba zai cika alkawarin da yayi muna bane yazo shima kamar yadda yace din.
Sai kuma na kara kai idona kan kayan su duk da ba wani kaya bane dan jakane irin na maza matafiya sai sauran jama, an dake ciki wanda na fahinci wani ban girma da suke mashi na musanman.
Manyan idanuna na dan kada don mayar da kallon gareshi saina sama nidin yake kallo har lokacin cikin daurewa nace you're welcome.
Lumshe ido yayi a daidai lokacin da kofan elevetor din ya bude aka fara fita nima yunkurin fitan nayi na bar wanan din daya taimaka min da magani yana masa bayani abinda na fada mai.
Wait sahiba ya fada daga bayana kafin suka karaso zuwa inda nake yana fadin na bari wanan zai dubata doctor din shine da yazo dashi dama don irin hakan .
A tare muka isa dakin su umma din na fara shiga nayi masu bayanin zuwan shi amma a cikin harshen yarbanci na fadawa umma din.
Nan umma ta shiga washe baki tare da daga hannu sama tana godewa Allah da zuwan shi kafin nace ta daina hakan mana kada su dauka wani abune hakan.
Na dan juya na fada masu da akwai wa yanda zasu shigo yanzu su dubata na fadawa faiza ta fada masu saida suka nasu na fita na sheda masu su shigo.
Da sallama yana rataye da cout din shi daya saba a hannun shi ga alaman gajiya a tare dashi gaisuwa na mutunci sukai masu kafin shi likitan ya nufi aurin da mama Amina take kwance din.
Nima takowa nayi nazo bakin gadon ta gefen shi ina dan kiran sunan ta ta dan yaye abin rufan ta amsa za a dubaki na fada a cikin hausana da ke dan sarkewa.
Har dai ya dubata ya gano cewa murane ya jawo mata matsala ya haifar mata da zazzabi haka mai zafi nan take ya bude dan jakkarshi ya fito da allura yai mata sukai mata sannu suka fita dakin zuwa masaukin su.
Mun dan jima a dakin har saida barci mai nauyi ya dauke ta kafin mu fito zuwa dakin mu mu kwanta da asuba kuma muka tashi zuwa masalaci yin sallah.
Sai bayan mun dawo ne su baffah suka shigo suna gaida mana da bata samu zuwa yin sallah ba lokacin.
Nan baffah yaso ya fada muna zuwan mukhatar da tawagan shi har da mahaifiyar shi a cewan baffa din ya shigo nan jiya har yasa anwa mama Amina allura umma ta fada.
Au kai wanan mutumin ai akwai mutunci a daidai lokacin na fita daga dakin zuwa dakin mu inda muke .
Ban tsaya ko wanka ba na fada saman gado don gajiya sai barci nayi barci sosai har da mafalkin naga ana wani taro wanda bansan kona meye ba lokacin.
A daidai lokacin da ban kaiga sanin ko taron me nagani ba na falka daga barcin kuma taron ya tsaya min a zuciyana.
Wanka nayi a gurguje don kada mu makara ga fita don sukan basu kwanta ba tun dawowan mu kuma harsun shiya ko .
Gaba dayan mu har su umma da mama Amina da yanzu taji sauki sosai don treatment din data samu muka fito don fita zuwa haram din.
A wajen haraban hotel din muka hade dasu sai a lokacin na tabbatar da maganan baffah din lalai da mahaifiyat shi sukazo umurah din ashe.
Don ya rike mata hannu suna tafiya tare a hankali tawagan shi suna biye a bayan su suma a hankali naso mu share amma zuciyana ta haneni da hakan.
Dole naje su umma zuwa wurin da suke don basu farga damu ba a lokacin sai jin muryana sukayi ina fadin salamu alaikum.
Haka yasa shi ya dan juyo da sauri ganin mu gaba dayan mu yasa yaja hannun mahaifiyar nasa suka tsaya.
Nan muka fara gaida mahaifiyar nasa a cikin girmamawa ba wata tsohuwa bace sosai saidai ta dan manyanta gaskiya amma da sauranta a rayuwa.
Ohh hjy yace kafin ya shiga yi mata bayani a cikin yare yana fada mata mune iyalin mariganyin ke nan da yan uwanshi.
Da sauri a wani irin yanayin tausayawa take fadi cikin hausanta itama da bai zauna mata a baki ba kamar mu a yanzu.
Tambaya takeyi tare da nunani tana fadin kai wanan kan ai tayi kama dashi sosai shima dai daga inda yaken ido ya kura min kamar yana son gano kamar data gani a jikina din.
Su kawune suka iso a daidai lokacin data rugume ni a jikinta tana dan buga bayana tare da jefawa Abban mu adduan samun rahama.
Sun gaisa dasu baffah suma tayi masu gaisuwan rashin Abba din tare da adduan albarka ga iyalan shi gefe na koma don wayana da yai kara na dan ja gefe ina amsa kira saidai hankalina yana wurin su duk da bana jin abinda suke fadi a lokacin don wayan daya dauke min hankali.
Ba a dade ba sai ga wani dogon motan kwasan mutane yazo nan baffah ke fadin wai muzo mu shiga motan a, a ba zamu shiga ba baffah Faiza ta fada zamu taka da kafa mukan tunda yafi lada ku tafi kawai zamu karso.
A nan dai din bayan bafdah yai masu bayani suka tafi suka barmu da kafa muka karasa zuwa ba wani abu da akeyi sai ibada tukuru.
Duk da muna tare mun hade da tasa tawagan a yanzu don dama signing din tafiyan duk tawaga guda muke dasu .
Haka yasa tun a ranan muka dan fara sabawa tundai wasu yan matasan mata da mukazo muka hade dasu su uku inda na dauka dai sudin kannesa ne na jini.
Shakuwa sosai ya shiga tsakanin mu dasu don kunsan mata da saurin sabo lokaci guda saidai na fahinci biyu daga cikin su matan aure ne su dayace bata da aure.
Haduwa dasu yasa muka fara dan sayayya a madina din don cewan su wai kayan madina sunfi na makka zama quality jin hakan yasa su faiza suka biye masu suna jibgan kayan tsaraba duk da su bafdah sun hanamu sayan kaya a madina din.
Ni dai iyakata in rakasu ban faye sayen kayan ba har suna min sherin hakan gashi munyi sa,a zamu kai kwana goma shabiyu a birnin madina don rashin zuwan shi da wuri ya jawo hakan.
Ina yawan ganin su tare dasu baffah sosai a ko ina zamu hadu suna tare dasu banda gaisuwa ba wani abinda ke hadamu dashi don yawan kallon da yake min idan mun hadu har na fara tsarguwan shi.
Ban faye zuwa inda yake ba idan suna tare dasu baffah zan tsaya daga nisa dasu ranan dai har nakai ga jan tsuki don na manta tare da yan uwanshi muke ina fadin kai nina tsani kallo wallahi.
Waye ke kallon ki faiza ta tambayeni wancan mutumin mana har bana son mu hadu yanzu wallahi sai ya dinga bin mutum da kallo haka kamar , , , ,
Faiza ce tayi min nuni da su cewa dan uwansune fa naja tsuki ina kawar da kaina gefe daya hankalina ya koma kan wasu yan kasan chaina na bisu da kallo.
Banyi aune ba sai jin muryan shi nayi a bayana kusa sosai yana fadin sun baki sha,awane kike kallon su haka ?
Firgigit na juyo inda muryan nasa yake yana kusa dani din kamar yadda nake zargin gaida shi nayi cikin basarwa kamar banji abinda ya fada ba da farko.
Ya gyara tsayuwa yana fadin kuna kokari sosai dake da yan uwanki uncle ya fada min irin kokarin da kukeyi ai saidai ku dan rika ba kanku hutu umurah ba aikin hajji bane dake da dokoki da yawa nayin sa.
Nagode kawai na fada ina kokarin wucewa muryan shi ya dakatar dani da yake fadin zanso ki samu lokaci mu dan tattauna dake kafin mu bar kasan nan don akwai abinda nake son muyi magana a kai daga ke sai ni a nan din.
Kallon ido da ido nayi masa wannan karon a cikin mamaki nake fadin a kan me ke nan zaka so zama dani fa ?.
Saida ya dan murmusa yace wani abune daya shafi rayuwan mu a yanzu duk da mun fara magana dasu malam hamza amma zanso naji ra,ayin ki kema kan hakan.
Idan ya shafi rayuwana ai ko a waya zamu iya maganan don ban faye son tsayi haka da mutane ba in public gashi kuma kace su baffah sun san zance ai is OK tunda shi baffah hamza yana da wayewan kai sosai ina fadin haka na juya na tafi.
Na barshi yana bina da kallo tare da mamakin baudaden halina nan kan sam ban biyo mahaifina ba ga hali ya fada cikin zuciyar shi.
Washe gari da darene bayan mun dawo masauki kwana biyu ya rage mu wuce zuwa makka sai ga kiran ya Abubakar ya shigo min.
Na dauka muka gaisa ya tambayeni yan uwa nace duk suna lafiya yai muna ya ibada har na bashi kowa su faiza suka gaisa dasu.
Kafin ta sake miko min wayan yace akwai wani abinda ke gudana ne dama tsakanina da mukhatar usman ashe don dazun uncle hamza ke fada mashi.
Da sauri na tare shi da meke nan fa no ni ba wani abu jiya madaine yake fadin yana son yin magana dani ai dadai ya fahinci ban san komai sai cewa yayi is OK zai kira gobe sai muyi magana don ya fahinci yanzu darene a wajen mu.
Bayan muyi sallama na kashe wayan zuciyana yana cike da tunanen wani magane wai gashi su baffah basuyi min wani bayani ba.
Muna kuma tare dasu dazun da zamu dawo masaukin mu ai kawai saina share zancen ni naci gaba da tsabgogina na