Showing 270001 words to 273000 words out of 382072 words

Chapter 91 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28427

Hamza nasani ba yauba kake son ganin bayan mu wanan zance nata ina shedun ta idan haukan ta ya bata haka tana shara karya har kuna yarda muma ba kyalesu zamuyi na bana muna suna da suke son yi tunda bata da sheda kan hakan .
Ya yun kura tare da daukan sandan shi ya mike tsaye ya kallo inda muke yana fadin zaku gane ba a taba mu a wayen lafiya gaba daya sai nayi karan ku kotu kan kokarin bata muna suna da akeson yi har kai hamza da nake ganin kana kokarin mara masu baya su bata muna suna.
Au haka kace to jeka kayi karan don Allah Allah ya kaika kaje karan su ke kuma zaki san kin tamu a garin nan karshen iskanci kikeyi yanzu.
Idan uwarki ta shiga bariki dake kin tashi a gaban yan jagali kin kwaso hauka kinzo muna kina barazana nan kaniyar ki zakici wallahi yana kainan ya fita fuuu kowa ya bishi da kallo.
Lalai zance na kasa don hauka na damun wa yan nan jahilan da suka dauki hukuma wasa baffah Abdullahi ya fada a cikin mamaki kafin ya juya kan Alh buhari yana fadin .
Yanzu kaima binsu zakayi kuyi kara ke nan kome ya nisa yana gyara zama yace gashi nan ku tambaye saunawa ina zuwa wurin shi kan wanan maganan.
Don haka wallahi ni yanzu a shirye nake da duk irin hukuncin da za ayi min muddin shine zai zama yafiya a gareni kan kuskuren da muka aikata duk da nasan bani cikin kashe shin da sukayi.
Amma kuma nasan sune ban fada ba don tsoron su da nake ji a lokacin kuma sun bani rabo na karba daga ciki ina amfani dashi.
Nuhu ne da shi gyade sai abokan shi mutum biyu Alh Shafi,u da Alh bello su suka aikata hakan ina waje ina jiran su a lokacin .
Don na dauka abinda suka kace zasuje yi wurin shine ya kaisu sai washe gari labarin mara dadi ya zo muna na mutuwan Sambo din.
Hankalina ya tashi sosai a lokacin don wanan abinda suka aikata ga dan uwan mu tun lokacin naso in fadi gaskiya amma sai suka kulleni a dakin bello sukai min barazanan kasheni nima idan na fadi gaskiya har kawo wa yau din nan kulun a cikin barazana suke min duk lokacin dana yunkuro masu da zancen.
Ko lokacin da yarinyar nan ke fadi daya tura a kashe mai Alh Ali nayi iya kokarina don inga na haja faruwan hakan amma basu saurareni ba.
Daddy hular shi ya cire ya goge zufan dake tsiyayo mashi daga cikin kanshi don tashi hankalin abinda kunuwan shi keji mai a lokaci.
Zuwa wanan lokacin duk wani wanda ke falon kuka yakeyi wiwi hankali tashe tsohon yace tir tir da hali irin na Nuhu da gyade.
Alh wanan maganan dole sai anje ga hukuma don ita kadai zata warware wanan manakisa nasu kai tsaye idan ba hakaba ko yanzu tsugunne bata kare muna ba a nan.
Ganin suna kan tataunwa akan zancen na mike zuwa ciki don ba zan iya zama ina sauraren wanan abinda ke kara daga min hankali ba haka.
Ya mustaphane zaune saman dining ya dafe kanshi da hannuwan shi bibiyu shima a cikin tashin hankali don duk abinda ake fadi daga inda yake yana jin su.
Yana jin motsi ba tare da yasan ko waye ba ya dago nice ya gani naji ya kira sunana a wani yanayi hakan yasa na tsaya a inda nake ba tare dana juyo na fuskance shi ba.
Mikewa yayi ya tako zuwa inda nake tsaye din ya yazo ya tsaya har muna iya jin hucin numfashin juna a lokacin don irin kusantar juna da mukayi .
Hannuwan shi ya fara hardewa fuskan shi ya nuna alaman damuwa a cikin sa sosa yasoma fadin nasan an cuta maku sosai a rayuwan ku.
Ban san ma da wani ido zamu kalleku ba a yanzu a matsayin mu na yan uwanku alhalin muna dashi muka bar rayuewan ku a cikin wahala haka.
Saidai ina son ki sani duk wani abinda za ayi a kotu don muga an hukunta mutanen nan ki sanar dani wanan zaluncin nasu ba zai tafi a banza ba insha Allahu.
Kaina dago na kalleshi tare da dan sake murmushi ina fadin mungode saidai duk wani shiri da zanyi kan hakan na riga na shirya a yanzu ba sai an taimaka min ba.
Oright hakan yayi kyau ya fada har na fara tafiya naji yace saidai ki sani dis is arewa not lagos ko yayane sai kin nemi taimako a wani wajen.
Ba damuwa na fada ina shigewa tare da fadi a raina da kasan dalilina kin kowa ya jefa kanshi cikin wanan fitinan da kowa yanzu ya fahinceni.


ZAINAB IDRIS MAKAWA



ANA DARA GA , , , , , , , ,

8️⃣0️⃣ BY, , , , , , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL WAHID , , , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257

ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋


Da yamman ranan muka koma gidan mu duk da aiken da daddy yayowa yaya Abubakar wurin mu cewa yana son ya gana damu a ranan hakan baisa mun je gunshi ba.
Don umma ta hana muje a cewan ta me zai fada muna kuma yanzu bayan baiso haka ya kasance da muba ya boyewa yan uwa baiyanan mu don rufuwar asirinshi shi.
Gashi tun faruwan hakan gaba daya ya Abubakar ya sauya kallo daya zakai mai ga duk wanda ya sanshi ka gane cewa yana cikin wani halin damuwa a zuciyar shi .
Don ya fada hasken nan nasa na gado ya dan dushe yayi baki ga gashi daya bari kadan a fuskan shi ko kana magana dashi sai ya tafi tunane ya barka nan.
Rashin zuwa dani aiki ranan yasa oga yaji halin da nake ciki inda sukai mai dan bayani briefly yasa yaji tausayin mu a zuciyar shi.
A can ma dai gidan Alh nuhu da suka kwaso shi daga asibiti cewan shi ciwonshi ai bana asibiti bane yasa suka dawo gida kowa na zuwa wurin malamai da bokaye ana karbowa ana dura mashi ko a shafeshi ko a turara mai yaki yayi ta tari.
Yau ko da uwargidan shi ta shiga dakin don duba halin da yake ciki don sunje sallah sai samun shi tayi ya falka yana bin ko ina da kallo na dakin.
Yana ganin ta yaso ya yun kura ya tashi a cikin mamaki sai kuma ya kasa don jikin da sauran nauyi a lokacin sai binta ya kamayi da kallo.
Juyawa tayi a guje ta fita a kofan falon ta tsaya tana fadi cikin daga murya tana fadi ku fito Alh ya tashi Alh ya bude idon shi.
Ai a guje kowa ke fitowa daga dakin shi zuwa wajen su har yaran dake wajen suka cika dakin lokaci guda ana faman mashi sannu da jikin kowa da mamaki a zuciyar shi.
Waya aka fara bugawa yan uwa da abokan arziki cewa Alh ya falka nan aka shiga shati fadi cewa maganin da akayi mai na karshe ne ya karbeshi.
Sai zuwan Alh gyade ne zancen ya canza don yana shigowa dakin dan uwan nasa dake makil da mutane ya tsaya a kofa yana fadin .
Ehh lalai kuwa ya tabbata yarinyar nan manyace ta gaske ashe don gashi ya tabbata a zahiri mun sheda .
Haka yasa kowa na dakin yake binshi da kallon mamaki karara a fuskan shi yaci gaba da fadin cewan da tayi muje ai ya tashi ko zancen gashi ya tabbata.
Haka baffa buhari daya iso shima cewa yayi tabbas babu sarki sai Allah Annabin mu Annabi mohammadu manzon shine .
Lalai Allah da Annabin shi suyi gaskiya koce babu Aljani a duniyan nan yai karya wallahi yanzu zancen yarinyar nan ya tabbata gaskiya ashe ko gaba da gaban ta a cikin wani aikin ke nan.
Nan kuma zance ya fara tashi kus kus a cikin yan uwa da abokan arziki an dai samu ya tashi har yai wanka yaci abinci sosai saidai jikin nasa da ba karfi har lokacin.
Sai lokacin ya samu zama da yan uwan shi har aminan shi biyu da matan shi yana tambayan su abinda ke faruwa suka fara fada mai abinda suka sani ya faru.
Har zuwa irin rikicin gida da nazo akayi dani da kuma zancen zaman su dani a safiyan jiya din da komai dana fada masu a falin mijin gwaggo hari har cewan nice sabbabin rike masa kafafun shi gyaden.
Shiru Allah Nuhu yayi yana sauraron abinda kowan su ke fadi a lokacin har suka gama yace akwai aiki a gaban mu sosai ke nan saidai nan na sheda yarinyar nan bata tunkaromu ba saida ta shirya muna tsab kafin tazo garemu.
Sai kuma ya murmusa kafin yace waini ce karamar yarinya a yanzu take shirin challanges dina don tana takama da guntun sihirin ta ko ?
Alh nidai tunda kaga haka wallahi abi abin nan a sannu uwargidan ta fada ya hararo ta don sai lokacin suka kulla da cewa ai suna kusa irin wanan zancen ba ayin shi a gaban mata.
Juyowa yayi cikin su a fusace yana fadin ku me kukeyi a nan da zakuzo ku wani zauna muna muna magana kan abinda mu ya shafa.
Biyun kan mikewa sukayi sai uwargidan ne da hjy salma a zaune da take binshi da wani irin kallon tsana da Allah waddan halin ka.
Can ta mike tana fadin lalaikan kai ya shafa Alh don ka shafa muna kashin kaji a jiki duk inda muka bi da yaran mu sai an nuna mu a matsayin naka yanzu.
Tana fadin haka ta juya ta fara tafiya yace ehh salma kikai kuwa yanzu tunda har zaki iya mayar min da martani haka kuwa amma zanyi maganin ki ita dai bata juyi ba ta fice.
Sai bayan fitan sune suka fara bashi labarin abinda ya daga mai hankali wanda bai dauka wani ya taba sani ko zaiji ba sai gashi a bakina yanzu yaji.
Kai ya girgiza yana lumshe idanuwan shi cikin takaici kafin ya bude idanun karo na biyu da a yanzu sun rikede zuwa ja ya furzo da iska daga bakin mai dan sauti yana fadin.
Yanzu na gama fahintar yarinyar nan kaf saidai ance wanda ya rigaka barci dole yake rigaka tashi ita yanzu ta soma muko min dade muna wanan.
Dadai mun barta mu bata dukkan abinda take nema kawai a rabu lafiya zaifi ina amfanin wanan tonun silar da mukeyi a tsakanin mu dasu.
Wani kallon zargi yake jifan dan uwan nasa dashi kafin yace ashe kai sakaran banzane yarinyar nan fa tazo da zuman kota halin kaka saita kaimu kasa a cikin garin nan.
Don muna sakarkkaru sai muyi zaune muko mu zuba mata ido ke nan tayi galaba a kan mu muna kallo kome kake son fada yanzu ?
Gaba dayan ku kubani kunnuwan ku kuje me zan fada maku nan ya kitsa masu duk yadda komai zai kasance idan anje kotu ga jibi banda goben sukace sun gane komai don dole haka zasu bishi din sai abinda yace dasu dole zasu bi.
Wanka na fito ina zaune gaban mirrow ina shafa mai a jiki wayana dake saman gadon ya dauki kira mikewa nayi na dauko wayan a inda yake aje saman gadon.
Duban layin nayi Abdul ne makwabcin mu kuma abokin aikina a lokacin mun gaisa yake tambaya su umm da ammar nace lafiya suke yake fadin gasu sun sauka kaduna a wanan gidan namu dai muke zaune ko nace eh.
Kaya mukazo saka hannu zamu kwana a nan nayi masu sannu da hanya don nasan aikin sane hakan saina dauka shi kadaine ko su biyu a lokacin saidai ban tambaya ba.
Bayan na fito ne nake fadawa umma zuwan shi take fadin gashi kuma ba zasu samemu a gida ba don yau fitan mu kotu na farko don haka dole muje cikin lokaci.
Karyawa mukayi tare da duk daukan wani abinda zamu bukata muka fito zuwa kotun a karo na farko da zamu shiga ke nan.
Har nakai bakin mota na juyo nacewa umma mu taka zuwa titi ba zamu shiga wanan motar ba sam a yanzu kallona umma tayi ina tafiya ina waya muka fita get din mu bamu dade da tsayuwa ba saiga mota an turo muna muka shiga.
Tun daga nisa na hango yadda wanan wurin ya cika da motoci wanda nasan na yan uwan mune mafi yawan motocin dake wanan waje duban lokaci nayi saura minti uku a fara yasa nace muyi zaman mu a motan kada mu fita.
Gashi ba mai ganemu don motar mai duhun glassce har wasu samari sukazo suka wuce wa yanda ba zan iya shedasu ba suna fadin wai ance ai kamar yarinyar nan taji tsoro ba zata zo ba kuma.
A to kai baba Alh na wasa ne ya gama ta da allon karfensa ya saka mata razana ta gudu kila itama ai rashin sani ne ya cuce ta.
Allah ya taimaka driver ya bude kofan shi yana shan iska muke tsinkayo zancen su daga inda suke tsaye a kusa damu .
Lokacin yana cika nace mu fita muka fito daga cikin motan muka nufi hanyar shiga wurin a lokacin har alkalin ya fara magana kan shari,an namu ko muka shigo don wani shari a akeyi kafin namu zaman.
Muna neman Sahiba sambo namadi da tai karan Alh Nuhu Allah gyade da buhari namadi duk yan uwan mahaifin ta.
Ko Sahiba na kusa ta gabata gaban mai shari,a na amsa da na,am gani sai lokacin kowa yasa muna wurin suka juyo a cikin mamaki karara a fuskokin su suna kallona.
Alh Nuhu da wanan ne karon shi na farko daya fara ganina shi ido ya kura min har nazo inda ake tsayi na tsaya ina kallon kowa idanu bushe.
Jikina dogon rigace a lokacin na yan kasan Mexico kinsan irin rigunan su ga kyau amma kuma dole akwai nakasu a dinki da bai dace da yar bahaushe ba.
Hakana saka don nasan zasuyi magana don kawai in nuna masu nifa ni dince da akwai bariki da komai a tare dani.
Mai gabatar da kara ya fara fadin abinda karan ya kunsa aka nemi su Alh nuhu da sufito sai gasu da babban riga ruuuuu sun fito suna fuskantar mai shari,a din sai wani cicika suke suna batsewa in ka debe mutum daya da fuskan shi ya nuna damuwa karara.
Tambayan su aka fara suka gabatar da sunayen su sai mai magana yake fadin ko sun san da wanan kalubalin da ake tuhuman su dashi ?
Alh nuhu yace su basu sanda hakan ba asalima basu san nidin ko wacece ba don haka basu san zancen da nake magana a kanshi ba yanzu.
Aka juyo wurina ana tambaya a daidai lokacin da yan tawagan mu suka karaso cikin kotun hakan ya mayar da hankalin mutane wurun kallon su din kowa sai yake zaton lauyoyine ko wasu bakin yan sa ido.
Mai maganan ya dan je wurin alkalin sukai kus,kus dashi kafin a juyo da zance a wurina suna fadin naji ko ina da lauya da zai kareni ?
Kafin nayi magana can ya dago hannu yana fadin gashi tare da gabatar da kanshi shine lauyan da zai kareni .
Aka juya wurin su Alh suma nasu lauyan ya mike yace shine mai kare bangaresu nan kotu ya fara aka bawa mai kareni dama mutumin da bansan inda ya fito ba sai a wanan ganin da nayi mai don har yaya Abubakar yazo da lauya wani abokin shine da ya kware shima wurin sharia.
Jin babban lauya da kasa ta sani a bayana yada har Alkalin ya fara kama kanshi a lokacin tambayan su yayi da cewa ko sun san dan uwan su daya mutu shekara goma sha biyar daya wuce ?
Mai karesu yace wanan tambayan ai batayi daidai ba gaskiya Alkali yace a barshi yayi ya kara maimaita tambayan sukacw sun sanshi dan uwan sune mahaifin su daya saidai uwa kowa da nasa uwar.
Yace da kyau shin ko kunsan yana da mata da ya a lokacin suka kalli juna kafin da sauri Alh gyade dake dan dogara sandan shi yace munsan da hakan.
Au to kuma kukace da farko baku san wanan zancen ba mai karesu ya daga don nema masu kariya a wurin shi yace an bashi a bar wanan tambayan shima aka bashi dama ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login