Showing 273001 words to 276000 words out of 382072 words
juyo gareni.
Ke kin taba ganin su kin san su a matsayin su na yan uwa gun mahaifin ki kema kuma ya a garesu nace na sansu mana amma da yake su basu nemeni ba kamar yadda mahaifina ya bar masu amanan mu nima kuma din ban nemesu ba kamar yadda suka sheremu a cikin duniya.
Au to baki nemesu ba tsawon wanan lokacin yanzu kuma da zaki nemesu sai kika nemesu a kotu ke nan ko ?
Hannu mai kareni ya daga kai an fafata sosai wanan yace wanan wanan yace wancan a karshe aka ce meye hujjana na tuhuman su da kissan mahaifina da kuma neman dukiyana da ban tunkaresu ba sai kotu ?
Nan suka tsaya ja inja har Alkali ya dan doki gudumar shari,a yayi gyara yana fadin kotu ta dage wanan karan sai nan da sati biyu mai zuwa tare da bani daman zuwa da hujjana na fadan hakan.
Nan aka fara fita daya bayan daya ga text din Adnan cewa kada in nuna ai tare muke haka yasa na fito muka koma wanan motan su kafin ma in fito har sun riga da sun shiga motocin su sun bar haraban kotu din lokacin.
Mun tsaya mun gaisa da yan uwan da basu da tsoro wasu kan tuni suka karawa talkaman su mai suk bace a wurin don sanin halin Alh nuhu din wurin iya baraza da rayukansu din.
Zagi kan nasha shi a motan da suka shiga sai can suka samu lauyan su da fada wai su ai sunso ya gama komai daga ranan nan alkali ya sallami karan namu ne.
Waiko kai Alh bello ka tabbatar da kaga Alkalin nan kuwa ya juyo yana kallon shi don son jin amsan da zai bashi a lokacin .
Yace komai kamar yadda ka tsara haka na shimfida mashi saidai kila wani hikimace nasu haka yasa ya daga karan a yau din.
Wayan shi ce tayi kara kamar kada ya dauka amma kuma ya daure ya dauka don sanin halin da suke ciki din ko wani zancen ne zaiji a kaina.
Muryan da yajine ana gargadin shi kan gobe ya tabbatar yana Abuja don case din dake can yana jiran shi.
Wani irin tsuki yaja tare da fadin anya yarinyar nan zan iya mata hakkurin wani abu a rayuwan ta kuwa din na tabbatar idan nayi wasa zata shige min hanci da kudundune a garin nan.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA , , , , , , , ,
8️⃣1️⃣ BY, , , , , , , , , , , ,
ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL AHAD, , , , , , , , ,
ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257
ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋
Mun nufi gidan na samu su Abdul gaba suna jiran mu dole mukaja muka tsaya muji abinda zasu fada muna.
Zasu tafi company suyi aiki idan sun dawo zasu shigo don lauyana zai so ya ganmu akwai maganan da yake son yi damu.
Bani cikin yanayin dadin rai don haka amsa masu dai kawai nakeyi don suma sun kula da hakan a lokacin yasa suka barni balle umma dake kukan bakin ciki tun fitowan mu kotu din.
Gida muka dawo kowan mu ya shigo ranshi bace bamu dade da shigowa ba Abubakar ya iso gidan namu shima yanashi har lokacin bai a cikin walwala.
Ya zauna andan tattauna ya kawo shawaran cewa mu juya mu koma lagos don zaman mu a kaduna yanzu akwai hatsari sosai saboda ya kula mutanen nan basu son gaskiya ga al, amarim su sam.
Nace nima nayi muna tunanen hakan ko banza kuma ga Amar dake karatu kada hakan yazo ya jawo mashi matsala saidai yanzu tunda Abdul yazo gobe zai koma zasu tafi da Ammar din ya zauna a wurin su .
Ni zanso muje da umma wurin danginta su ganta su san tana raye kamar yadda suke ji yace shima yayi tunanen hakan sai dai a yanzu dole mubar arewan nan mu koma can inda basu da ikon shiga suyi wani abu.
Don shi jikin shi ya bashi cewa da akwai matsala da wani shiri da yanzu sukeyi na kawar damu su hutu don ba wani abu bane mai wuya hakan a wurin anyi hakan yafi dubu ba a dauki wani mataki ba.
Jin hakan yasa na dan shiga dogon nazari kafin na yanke shawara a raina kawai dai mu tafi din yau ga baki dayan mu mu koma lagos din zaifi don nima na zargi hakan.
Dole da yamma muka bi jirgi zuwa lagos muka sauka goma na dare sai gida ba zancen barcin gajiya don dagani har umma tunane ya addabi zuciyar mu a lokacin.
Idan na zauna shiru zanyi ina tunane haka ko aiki na fara yanzune tunane zai shigo cikin haka nayi rana dana fita aikin saida irin hakan ya faru dani a nan suka gane ina cikin matala har saida nayi masu bayanin halin da nake fuskanta a yanzu din.
Shine Felix yayiwa ogan mu bayani da cewa na tafi kaduna a kan case din mahaifina shine ya tambaya na nemi lauya ne sukace zasu bincika.
Bayan sun bincika dinne kuma suka gane cewa banda wani lauya mai karfi shine shi ya dauki wanan lauyan da yazo daga Abuja don yana kokari sosai akace.
Kwana uku da dawowan mu lagos lauyan yazo har gida muka gana dashi bayan ya gama jin komai na labarin daga bakin umma.
Sai ya kara tambayan mu ko muna da wani sheda har munce a a sai na tuna da wanan dan littafin siri na Abban mu na dauko mashi bayan ya gama dubawane naga ya saki dan murmushi a fuskan shi.
Yana fadin wanan ma kawai zai isa sheda har in zamu samu wanda ya sheda rubutunsa a kotun akalla a samu mutum uku ko biyu da zasu sheda muna rubutun na marigayin ne.
Dan tunane nayi mai zurfi a lokacin kafin na amsa mashi a raunane da eh za a samu insha Allah yace good ki sa a ranki kamar munyi nasarane akansu da yardan Allah.
Kai kawai na iya gyada mai a lokacin don yadda nake jin zuciyana yana tafasa akansu babu tsoron Allah ko nadama a cikin zukatan su yadda suka iya kallon mu suka musanta maganan da sun san gaskiya anyi shi.
Haka ranaku ke zuwa suna shudewa har dai yakai saura kwana uku da zamu koma kaduna din shiryawa nayi tunda safe na fita zuwa makarantar su Ammar na sake daukan permition akan shi.
Don washegari ko safiyan tafiyan zamu bar lagos a yadda ya Abubakar ya tsara muna tafiyan namu na wanan karon da zamuyi zuwa shiga kotun.
Ina barci umma take tayar dani wai Falix ne a kofan gidan mu nayi mamakin hakan na dai shirya na fito na sameshi muka gaisa ya miko min envelope yace ogane yace ya kawo min zamu sauka a gidan shi don yafi wanan da muke ciki security sosai naso nayi gardama amma kuma Felix din ya ban shawara sai na yarda na karba.
Mun isa kaduna a ranan motocin shi sukazo suka dauke mu guda biyu sai kotun da ake sharian damu yau ma zance yafi wancan karon na farko cika.
Sharian muce ta farko a ranan don haka muna shiga aka fara kiran mu gabata a gaban kantan alkali suka fito a cikin shaddodin su sai maiko yakeyi suga alhazai masu fada aji a gari kowan su sai cicika yake yana mazurai a wurin.
Mai magana da yawun Alkali ya bukaci lauyana da ya taso ya fara gabatar da shedan shi na masu wanan zargin.
Ya mike yayi gaisuwa irin nasu kafin ya fara magana yana fadin Alh Nuhu kusan kaine shugan wanan tawagan naku a yanzu dama lokavcin aikin ku.
Shin ko za ka iya tuna kiran da kayiwa marigayin a waya landline na gidan shi ranan akan zancen alherin daya sameshi yaje a matsayin ka na dan uwan shi yana fada bayan dawowan shi gida kai kuma ka kirashi a waya .
Objection my lord mai karesu ya fada kotu kuma ya dauki kananan maganganu lokaci daya saida mai sharia ya buga gudumar shi wurin yayi tsit lokaci guda.
Ya kalli barister din yace yaci gaba da abinda yakeyi yanayi yana gyara glass din idon shi yana kallon bakin fuskokin da suke zaune wurin wanda yanayin su kawai ya nuna su din bakine daga wata nahiyar sukazo don wanan shari,an suma.
Sake maimaita masu tambayan farko dayayi masu yayi yace ko zai tuna da yadda sukayi a wanan ranan yace shi sam basuyi wani zance da marigayin ba.
Murmushi mai tambayan yayi kafin yace ko cikin ku akwai wanda zai iya tunawa a nan don kila Alh shiya mantane don an dade wanda kuma wanam zancen kasani Alh shine mafarin komai daya faru yanzu.
Kai Alh ya girgiza cikin dakewa da daure fuskan shi tamau a lokacin suma sauran aka tambaye su suka nuna basu sani ba basu ma san wanan zancen ba ai.
Hannu baffa hamza ya daga aka nunoshi don ya taso yazo ya tsaya ya gabatar da kanshi koshi waye da alakan shi da wanda ake sharia din dasu.
Yace a ranan attani goma ga watan biyu na alif dari tara da tamanin da biyar yayan nawa mai suna Yusuf wanda akafi sani da Sambo danmadi.
Ya dawo kasan nan da kwana biyu ya nememu mu yan uwan shi kaf akan nasara da Alherin daya samu a kasan turai na taron da yaje.
Inda ya malam hamza ko zaka gaya muna koku dasu waye a wurin lokacin da yake maku wanan bayanin?
Yace nida yan uwan haihuwan mu da mahaifin mu ya haifa kaf din mu maza mu tara a lokacin ina makaranta nazo hutu akai wanan abin.
Sunayen ku nan ya fara zano sunayen su kaf sai barister din yayi murmushi yace muna sauraron ka yace bayan ya gama muna bayani yace yana son wanan kudin filin shi na kusa da filin sukuwa na da yana son ya gina katon kafanin yin sugar dana filawa indan Allah ya yarda.
Saidai ya taramune don mu bashi shawara mukuma fahintar dashi saboda shi ba sanin mutane sosai yayi a nan ba ya bukaci yayan mu Nuhu da ya jagoranci komai da za ayi lokacin.
Amma budan bakin yayan namu sai cewa yayi a gaban kowa don ka mayar dani fakiri mabukaci zaka zo min da wanan zancen banzan.
Halan bamu san silar arzikin naka bane wai da dukiyan mahaifin mu ka samoshi don haka ba zamu yafe maka duk hakkin mu dake kan kaba ka sani yana fadin hakan ya mike ya fita yana kiran yan uwan shi.
Nan kotun ya dauki kace nace aka shiga mayar da zance kuma saida aka tsawata wa hakan kotun yayi shiru mai tambayan a lokacin yace bayan nan fa me zaka iya tunawa kuma ?
Yace eh bayan fitan su sai ya rage iya mu hudu a lokacin yayan mu mudi shima ya rasu a yanzu shine yace dashi yayi hakkuri yasan halin yaya Nuhu din da saurin fushi da zuciya.
Yace ai inda sabo ya saba don ma yau din bai furta mai Sambo sai naga bayan ka kaida kowa naka .
Barister din dake kare su Alh ya dago yana fadin bai yarda ba aka daga mashi hannu ya koma ya zauna .
Baffa hamza yaci gaba da fadin littafi wani brown yaciro yana rubutu kafin ya dago kai yana ce muna shi yana ganin duk abinda yaiwa yan dakin su ba zai taba yin haske a wurin su ba in ka debe buhari shine nakewa alheri ya dawo da baya yana min godiya.
Wanan ma ya isa mai tambayan ya fada yace angode idan bukatan sake neman shi yayi za a nemeshi kuma.
Ya dakata mai kare su Alh ya fada yana mikewa ya koma ya tsaya a inda yake yace malam hamza kace kake ko duk da yasan shi yasan komai nasa don har matar shi nada alaka dashi barister din dake mai wanan tambayan a lokacin.
Yace naji ka fadi wani zance yanzu cikin maganan ka dake nuna cewa shi mamacin yana hake da yan uwan nasa dama dake nuna cewa ashe shiyasa zargin iyalin mamacin a yanzu ya karkata a kansu su kadai ?
Dan murmushi baffa hamza ya sake kafin yace abune ai wanda bawai ahalin mu ba kadai kowa yasan da wanan zancen a gidan mu bako mamacin ba kowama idan ya taso zaifi su basu taba yarda wanan akidace ta wasu fulanin mu tun tele tele kun sani.
Mu bamu sani ba sai ka fada muna yanzu yace to koni nan dana sayi sabuwar moto waya ya bugo min kan cewa na bar ganin ya kyaleni ido ya saka min kada naga ina rike guntun ali na dauka nakai kowa ne yanzu idan nayi wasa zai batar dani a doron kasa yanzu haka ina da record din a cikin wayana kaf yadda mukayi dashi.
Yace basai kasa muna wayan ka ba tunda ba sharian ka mukeyi yanzu ba ai zaka iya tafiya ka zauna yace ya gode ya juya zai tafi sai mai karemu yace dakata ko zan iya samun record din inji don zai min amfani nan gaba kadan idan abinda nake nema yazo daidai.
Ya shiga laluban wayan shi yace gashi ka dan kuna muna nan kuma gardama ya kaure a tsakanin su lokaci guda har wasu daga can yan bayan fage na fadin ai aji irin furcin shi shiyafi.
Aka kawo wani na,uran kara sauti aka hada muryan shi tarara yanawa hamza din kashedi kafin barister din ya shiga tafa hanayen shi yana godiya ya mikawa baffa wayan shi.
Alkali ya bada lokacin hutu ya mike nan kowa ya samu daman mayar da zance ga nakusa dashi shima mai karesu din ya mike suka dan fita daga gefe a tare dasu.
A can kuma dakin hutu alkaline a zaune ya kwabe hular kanshi suna maganan siri da babban yaron shi kan wanan case din yaron yana fadawa alkali abinda ya gano a cikin case din.
Duk yadda akayi yarinyar tanada wani mai fada aji a kasan nan a yadda na fahinta gara kawai muyi abinda zai kara muna daraja da daukaka a indon mutane zaifi in yaso shi sai a mayar mashi da kudin shi.
Wayan alkalin ne yayi kara ya dauka yaji mai magana na fadin shin kasan sharian da kakeyi kuwa a yanzu ya fara yawo a kafafen labarai na kasan nan don haka ka gagauta yin abinda ya dace kada kasa son kai a cikin zancen nan.
Wani abokin aikin shine na wani jaha ya kirashi yana gargadin shi yace wai na tambaye ka man ita wanan yarinyar a karkashin wa take aiki a yanzu ?
Yace da gani dai yarinyar tana da daurin gindi sosai a wurin wani kusa a yanzu dai na kasa gano gaskiyan zancen ina dai kan binciken hakan.
Koda Alkali ya dawo lauyan su baffane yayi magana shima yana son ya samo hujjah don zargin da akewa wanda yake karewa din.
Aka daga karan sai karshen daya ga sabon wata mai zuwa za a kara zama lokacin sun gama fahintar inda zancen yake kafin nan su yanke hukunci.
Saida aka fito ne muka samu gaisawa da wa yanda sukazo wurin mu daga cikin yan uwa muka gaisa dasu suke muna fatan alheri akan Allah ya tona asirin maishi ko waye .
Mukayi sallama dasu a rana muka juyo zuwa lagos saidai ba kamar ranan ba don yanzu mun fara samun hujja mai karfi daga yan uwa.
Da daga farko suke tsoro da shayin bada sheda don kada a halakasu da tsafi ko wani abu nadaga cikin sherin Alh nuhun da suka shede shi dashi din.
Ni sai bayan mun dawone ma na tuna da envelop din da Felix ya kawo min washe gari ina kwance na mika hannu na dauka.
Katin fatan alheri ne maikyau dashi sai kalaman fatan samun nasara da akewa mutum a cikin katin da kallo shi kawai zaisa ka gane yana da tsada sosai.
Dan murmushi na sake a fuskana a karo na farko tun dawowan mu lagos din mikewa nayi na dauko wani takarda ina dubawa ni dai Allah ya gani a yanzu kaf yan uwan mu inka debe mutu hudu zuwa biyar har dana sanin fitowa a cikin su nakeyi.
Mutum biyar din kuwa sune ya Abubakar wanda Allah ya jefoshi a cikin rayuwan mu da alheri domin ya tallafa muna sai baffa hamza sai kuma gwaggo hari da danta sai baffa Abdulahi da shima yake nuna