Showing 78001 words to 81000 words out of 382072 words

Chapter 27 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28413

fuskan shi yana fadin Mairo kece ta hanyar nunata da yatsan shi har hamnun shi na rawa.
Umma tace nice yaya ina wuni mun sameku lafiya ya bayan rabo takai kasa tare da dukar da kanta kasa tana hawaye.
A cikin karfi hali na iya fadin good evening sir sai lokacin ya dan kalli inda muke ina saye da wando wanda ke hade da riga blue sai gyale fari da nayi rolling din kaina dashi.
Innalillahi wa inna alaihim raji,un ya fada yana mai kura muna ido dani da kanina da muke tsaye kimkyam muna kallon shi muna na rike hannun Amar din koda taka taso a hakan.
A hankali ya dago hannu yana fadin come to daddy kids da sauri kamar muna jiran jin hakan daga gareshi muka nufi inda yake tsaye din ya mika hannayen shi garemu muka fada mai sai kuka yazo min jin dumin jinina da nayi karo na farko da wayau na a jikina.
Kuka sosai nakeyi shima Amar ganin inna kuka yasa ya barke da kuka daddy ma da ya Abubakar duk kukan sukeyi ba mai bawa wani hakkuri a falon.
Jin kukan ne da iyalan shi daga ciki sukaji Nabila data fito zuwa kitchen taji ana koke koke a falon ta koma da sauri ta fadawa hjy yasa suka fito gaba dayan su.
Anyi daidai itama hjy karima taji tafito duk sukayo falon gaba dayan su lokaci guda kowa yaja yayi turus a cikin katfin hali hjy din ta karasa tana fadin.
Lafiya Alh suwaye suka zo haka ta fada don umma kanta yana duke tana rusan kuka don haka bata shedata ba a lokacin.
Har lokacin da hjy ke maganan muna jikin daddy din muna kuka sosai shima yana hawaye maidan sauti kafin ya dago yana fadin .
Addah kunga halin da rayuwan yan uwan mu diyan mu yau yake ciki saboda sakacin da son kai irin na wasu daga cikin dangin mu ko ?
Jin an ambaci sunan hjy Addah da umman mu tayi yasa ta dago kai a cikin sauri tana kallon inda hjy din take tsaye suna kallon mu cikin tuhuma don irin hjy karima kan ta dauka mu din diyan daddy ne na cikin sa daya haifa da wata mace a ganuwar aikin sa a lokacin da yake fita garuruwa yin aiki.
Hjy Adda ko ba wanan tunane tayi ba ita zuciyar ta yafi tafiya da cewa wasu ne dai can na daban da suke da alaka dashi daddy din.
Dago kan umma sai a idon hjy Adda din wani iri tayi ta danja baya tana dafe kirji da fadin Mairo kece a gabana ko mafalki nakeyi.
Sai ta kai zaune saman kujeran dake bayan ta tare da sake hawaye suna zuba mata lokaci guda.
Da kyat ta iya budan bakin ta tace Mairo ina kika shiga haka tsawon wanan lokaci haka kin tafi babu labarin ki bana diyan ki.
Hannu daddy ya dagawa hjy daga inda yake tsaye din hjy tayi shiru hannu daddy yasa ya dagoni daga jikin shi a hankali ya fara min magana kamar rada yana fadin.
Stop crying my daughter daddy is with you now yasa hannu yaci gaba da share min hawaye kafin ya koma wurin Amar ya kara jan shi a jikin shi shima.
Hjy karima dauke su ki kaisu part din can na ciki da babu kowa ku kuma ku dauki yar uwar ku kujata zuwa ciki .
Yana fadin haka ya juya inda Abubakar ya ke zaune yana fadin jeka gida ka huta harda safe yana fadin haka ya mike shima dan nasu ya mike ba tare da yayi magana da kowa ba ya fice gidan zuwa gidan shi.
Falon ya saura damu dasu hjy ana kalo kalo kafin hjy karima tayi karfin jalin fadin mujeku zuwa ciki ku huta.
Da kyat umma ta iya mikewa har lokacin tana rusa kuka mai tsuma zuciya tabi bayan hjy zuwa ciki muma muka bita.
Wani part din su dake can kuryan gidan aka kaimu kafin Asabe mai hirkin gidan ta kawo muna wani lafiyayyen abinci sai kamshin ke tashi na man shanu a cikin sa.
Duk muna zaune a cikin dar dar har lokacin kafin hjy Addah din ta shigo dakin Asabe da yaranta na biye da kayan mu da muka bari a cikin mota.
Hjy Addah din ce ta nuna inda za a aje muna suka aje suka fita yake fadin Asabe ki dauko abin shara ki gyara dakin nan don Allah.
Kafin ta juyo tana fadin au har yanzu zaune kuke gara ki saki jiki ko yaran nan zasu sake nasu jikin ki tashi Mairo kishiga bayi kiyi alwala kiyi sallah kuci abinci lokaci yana kurewa.
Tashi umma din tayi zuwa ban dakin data nuna mata kafin ta juyo inda nake zaune bakin gadon tana fadin .
What is your name na dan dago manyan idanuwa da suka rine nace Sahiba ma ta nuna Amar tana tambayan shi yace Amar ta dan kura mai ido sosai kafin ta numfasa tace feel free tana dan taba kafada na.
Dan murmushin yake nayi mata kawai na dukar da kaina kasa na dan lokaci saiga wanan mai aikin ta shigo take fadin yawa Asabe a canza masu zanin gadon nan a gyaro ko ina matar dan uwanane data bata da yaran da dadewa Allah ya baiyana muna ita.
Aikuwa ga kama nan da diyan na gani sosai ta fada tana kallon mu tare da fadin sannu sannun ku da zuwa.
Ai da alama wa yan nan basa jin hausa nake gani tare da dan kallon mu din kafin ta juya wurin Asabe din tana fadin don Allah fara da falon sai su koma can su jira har a gyara nan din.
Daga haka ta juya ta fice dakin yadda tace hakan akayi don mun koma falo aka gyara bedroom din.
Umma tayi muci abinvin mun kasa don wanan kamshin manshanun dake ciki bamu taba cinsa ba sai wanan ranan haka aka rufe abincin ko umma bata cisa ba.
Haka muka kwanta a takure a dakin da muke din saman gadon dake dakin zan iya cewa ranan umma batayi barci ba don na falko da dare na sameta tana sallah.
Na dawo na kara kwanciya sai barci don dadin barcin da nake ji a lokacin ban san a inda ma muke ba don ga gado ga sanyin AC duk a dakin.
Washe gari koda muka falka gari ya waye umma tana zaune saman salaya din da tayi sallah a wirin tana dan jan tasbi ta tare da maida gaba gasbas tana kallo.
Ban dakin na shiga na yo alwala nazo nayi sallah ina gamawa na gaida umma na shiga gyaran dakin da muke din har falo saidai ban yarda na leka wajen gidan ba don gidan ma tsit yake a lokacin kamar ba kowa a cikin sa.
Bayan na gama na shiga wanka na fito na shirya a cikin dan wani gown baki mai dan adon walkiya a gaban rigan.
Inda Allah ya taimakeni shine bai yarda ya dawo da mu gida ba saida muka zama mutanen arziki yadda ba za a gamu a raina ba idan anganmu a gida.
Don haka kaina yasha gyara ban damu da dan kwali ba hakana na koma na kwanta saman gado sai wani barcin ya daukeni kuma.
Muryan hjy Addahce ya tayar dani lokacin da take fadi mairo ya gajiyan hanya yaya yaran kuka kwana ta amsa da lafiya.
Mairo ina kika shege haka tsawon wanan shekarun da kuka kwasa baku gida wanab dan kuma gashi da ganin shi shima dan gidane shi don ya debo kamar mazan gidan mu sosai.
Banji me umma tace ba don ina mikewa na mike zaune ina fadin good morning ma ta juyo tana amsawa a cikin sakin fuska a garemu.
Dole ne ya kasance ba zamu iya sakewa dasu ba koda kuwa mun tashi a cikin su balle al,adun su yanzun da muke gani bakon lamari a idon mu zama da hausawan.
Naji tana tana tambayan umma din da cewa meyasa bamuci abincin da aka kawo muna ba da daren jiya din ko tabawa bamuyi ba.
Umma din ne ke fada mata cewa munce bama cin manshanu ta dan kallo inda nake da mamaki tana fadin a ikon Allah dan filo ne zaice baya cin man shanu kuma ?
Har saida ta fita nake tambayan umma da ita din wacece a wurin mu take fada min itace mahaifiyar Abubakar daya kawomu gida.
Akan hjy Addah din ta fara min bayanin yan uwa take fada min yadda muke da ita maimakon inji dadin hakan sai naji wani iri a raina na ba dadi.
Don su gasu a cikin wadata amma sun barmu ba tare da damuwa da muba a cikin duniya cikin wahala duk da nasan hakan akwai laifin umma a cikin hakan don itace ta tafi damu ai.
Na koma tambayan kaina me zaisa umma ta bar yan uwanta irun haka har ta shiga duniya damu ta kyalesu na tsawo shekaru haka.
Wanan zancen kan gaskiya abin dubawane ga duk mai tunane dole fa akwai wata a kasa da ya jawo barin umma din gida damu.
Abincin da ladi ta shigo muna dashi nake bi da kallo tare da gaida ita da gurbatacen hausa na da sannu kawai ba tare da karawa ba.
Son umma ta fada min kada in nunawa kowa cewa ina dan jin hausa dagani har Amar din mu boye dan hausan da muke ji a gaban dangin namu.
Sai gashi ko farawa da iyawa Asaben ta fita tana fadin ikon Allah yara sun koma kamar wasu kabila haka dasu nikan idan kin kwana yi mun shegeb yaren ku ainba zan gane me kike fada na yarinya.
Kallon umma din nayi tayi murmushi kawai mai nuna kin fara gane me nake nufi yanzu ke nan dai daukan abincin naga umma din tayi ta duba.
Ta dade tana kallon cikin kulan abincin kamar tana nazarin wani abu kafin ta juyo wurina tana fadin in taso munci abincin da aka kawo muna din na dan bi abincin da kallo kafin in tashi zuwa inda abincin yake.
Wanan kan munci sosai don shayi ne da bread sai dankalin turawa da kwai da kosai da koko aka kawo muna abin kari din.
Mun gama misalin karfe gomana safe daddy ya shigo har dakin da muke din suka kara gaisawa da umma muma muka gaida shi ya amsa yake tambayan sunan mu muka fada mai sunayen mu.
Hjy Addah ce ta shigo falon ganin haka a cikin yaren yarbancin umma tace damu mushiga daga ciki muka mu barsu a falon.
Koda muka shiga din hankalina bai kwanta ba don haka na dawo kofa na make ina sauraron su duk abinda ake fada a kunnuwa ina jinsu naji daddy na fadin.
Daddy sai a lokacin yake tambayan ta ya bayan rabo mairo ashe kina lagos duk wanan neman da ake maku ?.
Kin shige cikin duniya da yara haka kinyi shiru kamar baki da gata haka mairo ai mutum bai yanke irin wanan hukuncin ya tafi shiru haka har wanan dan ma da kika haifa a can gasu yaran gaba daya basu san mu.
Gara dai ka tambayeta tun kan zance yakai wirin yan uwa idan wanan yaron dan Sambo nd duk dai ya kwaso zubin gidan mu gaba daya shima don har ince kaf din jikokin baba babu wanda ya kwaso shi da komai kamar yaran nan wallahi.
Gara dai da kika ba kanki amsa karshe don ko makaho ya laluba yasan yaran nan jinin gidan mine su don babu ida suka rage gida wirin kama.
Da kuma kike zancen wani yace wani abu yanzu wa kike tunanen zan dagawa kafa cikin su a sake wullakanci ga zuri,an sambo kuma ?
Wanda dai da akayi mai dashi da iyalan nasa ya isa haka sai dai yanzu a nemin hanyan tuba da gyara gaba kuma amma a yanzu ba mai kara hada kai dani ayi irin shirmen da aka tafka a baya.
Ko wancan karon bani nan ne har haka ya faru suka bar kasan bada sani ba aida ina nan duk abinda za ayi saidai ayita amma ba inda zasu tafi a lokacin.
Amma Alh ka san yaya Nuhu fa ka kuma san halin sa da kudirin shi akan duk wani wanda ma yai magana game dasu tunda ya dauki abinda zafi sosai haka.
Da wani irin kallo ya juyo yana kallon ta a cikin takaci kafin yace shi din Allah ne waliyin Allah da zai saka wani dokan shi na banza yana amfani da mutane kamar wasu jahilai yana kaiku ga halaka.
Yanzu din abar min su din a nan gidan zasu zauna tare damu babu inda zasu har sai mai rabuwa ta rabamu ina dai dukiyan daya rike a hannin shi ya zama nasa a yanzu duk yake wa wanan fadan haka ?
Yaje yaci ko ince suje suci shida masu binshi a yanzu din Allah ya basu wani wanda yafi wanan din daya rike ina shike nan dai duk dai wanan abu akan abu daya akeyiwa fadan nan kuma sun karba basai a barsu su zauna lafiya ba.
Ni dama ai ba wai ina cikin zancen nasu bane kasani amma su yaya din nakejiwa a yanzu don yadda suka dauki zancen nasu na gani.
Kuma hakan zai iya jawo su kulla da kai kan hakan don ba kyau kega halinsu ba ka sani don, , , , ke dakata don Allah ya isa haka ya fada a kausashe.
Alokacin kuma Abubakar dake tsaye a kofa ya karasa shigowa falon namu fuska a daure jikin shi yayi la,asar don jin abinda mahaifanshi ke fadi.
Daddy bai dakata da abinda yake fadi ba a lokacin don ganin Abubakar din yaci gaba da fadin shi Nuhun Allah ne ?
Ko yayi kaman Allah a garemu da Allah zai fadi abu saboda wani akidan banza nasa ya sauyawa mutane zancen su don jahilci ko a da can ke kifi kowa sanin bana cikin wanan shirmen ni.
Abinda kikewa tsoro dai shine Nuhu ba Allah ba shi Nuhun kanshi ai ya sanni yasan koni waye don haka ne ma zasu zauna anan gidan tare damu babu ida zasu tafi koda ita mairo tace zata bar nan din ba zata zauna da muba yaran nan babu inda zasu tafi sun dawo gida ke nan har abada koda bana raye kai Abubakar karike min su ammana kamar yadda mahaifin su ya bar muna amanan su a baya.
Allah ne ya karbi addu,ana har yai sanadin ta tsatsona zasu dawo a garemu da zancen nake kwana dashi nake tashi don nasan Allah zai tambayen mu kan sakacin da mukayi akan yaran nan.
Nasan kuma zasu so ja da hakan don su a nan Allah ya ajesu akanyin hassada nima kaina aiba barina sukayi ba na sani duk da kuwa bana shiga zancen kowan su a yanzu.
Wanda yace yasan ni inyi dashi wanda baisan ni ba kuma ya zauna lafiya nima in zauna sai zancen dukiyan yaran nan ya zama dole duk wanda yaci dukiyan su a yanzu ya fito masu dashi abasu abinsu.
Wanan wani zance kakeson daukowa yaya don kasan yadda ko wurin raba dukiyan man aka samu matsala balle yanzu ace za a bawa masu hakki hakkin su.
Allah ya fisu akan hakan mommy hakki kan dole su dawowa yara da hakkin su don sule da alhakin abinsu ba wani ba.
Don Allah ku barsu da shi yaya matukar zasu ban min yarana a raye don sun fada sun kara fada a gabana ina jinsu sun fadawa mahaifin yaran cewa zasu kashe shi ko su batar dashi kuma suci arzikin shi.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

A NA DARA GA, , , , , , , , , ,

2️⃣4️⃣

BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM, AL KHALIQ, , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KAFIN KI KARANTA A CIKIN SALAMA NA FADA NA FITAR DA HAKKI RASHIN SANI A KANKI ALLAH YASA MU CIKA DA IMANI AMIN, , , , , , ,
A satin da zan rasashine ya fara danyi min wasu bayanen da ban san ma,anan su ba yana fadin.
Kin jaf takardun komai nawa suna a cikin ginan nan na boye su ya nuna min wani bari na kofan dakin shi yace a nan suke nan nake aje komai a cikin ginan nan.
Kuma ina son kiibi yan uwana kaf a sannu koda bayanane mairo don har gobe ba kaunata sukeyi ba na sani suna da mumunan akida a kaina tun tasowana a cikin su Allah ne kadai ke kaunana yai min wanan daukakan akansu.
Ban dauki maganan shi da wani muhinmanci ba raina don na saba jin hakan a wuri shi ko yaushe yana fada min hakan.
Sai ranan da zasu halakashi ne da safe nake tayar dashi yake fadin idon shi biyu ai tunda


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login