Showing 144001 words to 147000 words out of 382072 words

Chapter 49 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28391

don ko banza naji umma tayi min abinda nake so a rayuwana don babu abinda yakai dadi ga yaron daya san kansa koda kuwa karamine yaji uwa ta saka mai albarka kamar yadda umma tayi min.
Don yana karawa yaro karfin gwiwa da kuzari ya dinga aiki mai kyau a rayuwa koda kuwa babbane yana son jin kalman Allah yayi albarka daga bakin mahaifa.
Wanka nayi na shirya a gurguje kafin in fito har Abdulhamid ya kira umma yana fadin ya ban fito ba kowa na wurin aiki don yau akwai baki da zasu zo muna ma,aikatan.
Sai ga umma ina gaban mirrow ina shafa mai take fada min bata fita ba saida ta tsaya har na shirya na fito na samu ta hada min tea dole na zauna nasha na nufi wurin mota na tayar na dan bata wuta kafin inja in bar gida zuwa aiki.
Tun daga nisa na gane gaskiya Abdulhamid don akwai alaman baki don motacin da naga iri daya a wurin an jera su har guda biyar manya manyan jeep sai walkiya sukeyi suna daukan ido.
Haka na rabasu na shiga da sauri saidai na tsargu lokacin dana samu kowa a haraban wurin tsaye ga wanan matashin na kwanakin baya da akace shine wai mai wurin tsaye yana jawabi kowa yayi shiru.
Baka jin komai sai sautin takalmana dake kara a lokacin na ratso wurin daga can baya naja na samu wurina tsaya ina sauraren abinda yake fadi.
Turancin shima ko a cikin turawan abin kallone farine sol har yafi ya mustapha fari da kyau da komai saidai tsawone bakai mustapha din ban din shi mustapha har ya dan duka kadan don tsayin shi .
Wanan din kam sune tashin falo tutube da remote na gaskiya don baima san wani abu zafin rana ba ko talauci kila a rayuwa.
Ba wani abu yake fadi ba sai irin yadda ake sakaci da aiki a wurin ana samun matsala yake nuna baci ranshi da hakan sai a karshe da yace zai dauke wasu daga nan ma,aikatan ya kaisu sabon wurin da aka bude su koma can.
Sai kuma ya kara da godiya kan yadda wasu ke aiyukan su tukuru musanman kananan ma,aikatan wurin su yafi yabawa ya kara da cewa su kara karfi ga aikin su yayi hakan ne don a rage zaman banza a gari tafe suka fara yi mai Allah bai ban ikon taba mashi ba ni a lokacin .
Don na kagu da tsayin saidai ina dago kai yayi daidai yana kallon inda nake tsaye a takure din cikin shiga na na islama kamar kullun don zuwa kaduna a yanzu ya kara haska min hasken musulunci sosai a zuciyana ba kaman da danake sakaci da ibada ba don talla duk da alokavin ma ina sallah gaskiya.
Don umma tana iya kokarin ta wurin haska muna ibada ko lokacin shiyasa bamu sha wani wuya ba a can da mukaje don mun koya a wurin ta.
Sallaman mu yayi kowa ya fara tafiya ana kuskus da zantukan da yayi a wurin musaman na kara albashi da yayi alkawari gako wani ma,aikacin wurin har masu gadi don ya yaba masu sosai lokacin jawabin nasa.
Nima gyara dan jakar dake kafadana nayi a lokacin naji muryan manager yana tsayar dani ta hanya kiran sunana naja na tsaya yake fadin in sameshi office din shi suna tsaye tare da bakin nasu lokacin.
Yes sir na fada na juya zuwa office din mu na aje kayana da yar jakana na fito na zuwa office din su zuciyana cike da zargin dalilin kiran da yake min da safen nan.
Har zuciya ta fara raya min cewa shike nan zancen korana din ya baiyana ke nan a yanzu tunda manager ya kirani har office din shi.
Na isa na dan tsaya daga waje duk da nasan zasu iya ganina daga ciki tunda glass ne wurin ko wani office din dake cikin wurin.
Shigo mana yace min daga ciki na dan tako na bude na shiga da sallama sabo da yin hakan ko ina zan shiga babu kowa a office din sai shi daya yana hada takardu a tsaye na karaso ciki.
Kara gaidashi nayi ya amsa yana nuna min kujera in zauna nakai zaune din cikin mamaki kafin ya dago yace dani congrat miss Sahiba.
Na dago kai da mamaki ina kallon shi don ban san abinda yake min murna akanshi ba a lokacin sai naga ya miko min wani farin takarda yana fadin.
Nayi maki murna sahiba zaki bar wanan aikin damu na dan lokaci duk da dai ana tare din saidai zaman ki ba zai kasance nan na sidin din da kikeyi a yanzu ba.
Don idan oga yana gari zaku kasance dashi keda Adnan na dan lokaci don, kun san shi ba mai zama kasan nan bane sai udan yazo bai kuma yin fiye da sati daya ya koma sai dai idan wani abu ya tsayar dashi.
Saidai ba wani aiki mai yawa bane ke zaki koma a matsayin sakatariyan shi adnan kuma PA din shi zaku fara aikin ku a goben nan ko ince yau da company n an namu zaku fara zaiyi aiki damu idan kin duba takardan gobe kuma haka har jibi.
Shiru nayi ina jin wanan bayanin nasa kamar a mafalki yake min wanan bayane din don gaba daya ban san me zance ba a lokacin.
No kada ki shiga damuwa Allah ne ya zaboki ya baki wanan daman don kin cancanci hakan gaskiya mun yaba kwarai da irin kokarin da kike muna wajen warware muna matsalolin da sukaso taso muna har sau biyu muka samu saukin komai daga bangaren ki.
Wanan shine ya bamu daman karfin zaboki daga cikin ku don ki taimakawa masana,antun shi da yake dasu a kasan nan .
So congrat onces more again da wanan daman da kika samu da kowa yake fatan samun shi a rayuwa son zakiyi aiki da babban mutum a kasan nan kuma matashi.
Innalillahi na fada don ga baki daya kaina ya daure ga abinda duk yake son fahintar dani a lokacin.
Yanzu suna office don Adnan har ya tafi sun soma aiki a office din shi ko tun dazun a hankali na dago kaina na dan kalleshi zanyi magana ya sake fadin .
Idan kina da wani bayani saiki bari daga baya zamu zauna muyi maganan daya dace amma yanzu akwai aiki sosai a gaban ki.
Mikewa nayi a hankalin jiki ba kwari kamar kazan da kwai ya fashewa a ciki na fara takawa sai kuma naja na tsaya wuri daya tare da dan juyowa na kalle shi na bude baki da zuman tambayan shi.
Ya dago yana fadin you can go now nasan yanzu sun fara aiki ko tundazun bai kai ga rufe baki ba sai ga wani ya shigo yana fadin wai ance ina new sectrery din take tazo ta fara shigar da komai.
Muka kalli juna ni da manager kafin naji yace gata tafe yanzu ta tsaya ina mata bayani ne dole nabi bayan shi zuwa inda suke.
Daddy ya jijiga kai bayan hjy Addah ta gama mashi bayanin komai yana sauke nunfashi kafan shi ya mike daga yadda yake zaune a kasan.
Tsawon dan lokaci bai iya furta komai ba sai can yace yanzu me kike son nayi akan zancen nan ko kin manta da zancen mu na baya ne da mukayi lokacin da kika zo min da zabin yar Nuhu a matsayin matar da moddibo zai aura nace ki dai sake dubawa kikace ai itama din yar gidace ko ban son zumuncin ku da dan uwan ki ya kara kulluwane daga haka na goya maki baya ban kara furta komai ba.
Don haka yazu ma runda a gidan kawun modibbo take zaune ai nan da can duka gidane sai ta zauna mana menen ?
Wani irin kallo hjy din tayi mai na mamaki don jin abinda ya fada tasan zancen yana da ma,anoni masu yawa ke nan a zuciyan shi.
Can yace dama shi modibbo ya kirani ya fada min komai na bashi hakkuri don haka kuma ina nason ku fita zancen ku kyale su a zuba masu ido aga me suke nufi da hakan.
Sai lokacin hjy ta dan sauke ajiyan zuciya don jin abinda daddy din ya fada ta koma cewa saidai yaran da ba wanda ya sansu a nan bangaren fa Alh ?
Murmushi daddy ya sake yana fadin yara ai dole komai dadin dadewa a kawosu gidan nan idan kunyi hakkuri da hakan.
Don ta kan yaran ake son bi a aiwatar da nufin da ake kokarun aiwatarwa a kan mu yanzu nasan waye Nuhu nasan duk wani shirin shi na shirme da jahilci
Kai innalillahi hjy ta fada na dauka wanan hadin zai kawo zaman lafiya a tsakanin ku idan anyi sai gashi kuma hakan yana son kawo wani babban matsala kuma.
Daddy bai tanka ba yayi shiru kamar mai nazarin wani abu itama dai shirun tayi na dan lokaci kafin ta mike tsaye ganin baida niyar kara fadin wani abu kan zancen.
Fitan mommy falon daddy din yayi daidai da shigowan hjy karima falon itama tare da yarta na goye ta zauna tana gaidashi.
Ya amsa yake tambayan Amira ya jikin ta tace da sauki dama ai itace tajawa kanta ciwo idan ta tashi fitinar tsayan ta wai wani sabon iskanci Sahiba take kira tun wayewan garin nan data tashi sunan Sahibane a bakin ta.
Sahiba kuma ita har yanzu bata manta da zancen su sahiba a rayuwan ta ke nan daddy din ya tambaya.
Ai gaba dayan su basu manta da itaba a rayuwa kullun zancen su dai shine yaushe Sahiba zata dawone mami sai na masu tsiya suke barin zancen ta a gidan nan.
Shiru daddy yayi wani abune ya fado mai a rai game da su sahiba dai wanda ya kasa saita zuciyar shi a kan hakan.
Ban taba sani ko zaton akwai office a wurin ba haka kuma ban taba sanin cewa wanan wurin haka yake da girma ba sai wanan ranan.
Ashe duk wunin da mukeyi a cikin sa iyakar mu inda aka ajemu ne don baka zawa wani part don kanka sai idan an mayar dakai wurin yasa bamu san kan wirin ba ko dai nice da ban damu da komai ba sai abinda ya kawoni ban sani ba.
Wanda yazo kirana ya fara shiga ina biye a bayan shi muka shiga office din suna zaune kowan su ya kurawa computer dake gaban shi ido a lokacin.
Na shigo na gaida su da aiki ba tare da sun dago ba suke amsa min gaisuwan mutumin yayi min nuni da wurin zama nakai zaune daga barin shina dama inda suke zaune.
U are wellcome dayan ya fada min yana miko min takardan dake saman taburin shi na karba a sanyaye yake fadin nabi bayanan dake ciki na turawa chief sakon baiyanan dana gani a cikin takardan.
Hankalina na kwantar na fahinci me ake nufi duk bayan kawai zan tura a dayan suein shi shine abinda zanyi nan take na fara turawa kafin dan lokaci na gama na dan dago da zumar fadin na gama idanun shine akan yadda nake aikin kamar wace ke tsoron laptop din ko kyama haka nake dannawa na hada komai har na tura mai.
Kaina na dukar kasa yace cikin dan saurin maganan shi kin gama turawa na kada mashi kai alaman eh ya kara turo min wani takardan kuma aikin dai da muka wuni munayi ke nan har akai sallah azahar na dubi lokaci a wayana dake aje saman table din koshi wayan umma ne da nake amfani dashi duk ya tsufa yaji jiki sosai.
Tsab na mike tsaye daga zaunen da nake suka dago kai lokaci daya suna kallon inda nake tsaye din asalat kawai nace dasu ina kokarin fita daga wajen kujeran.
Sai lokacin ya dago kai ya kalleni jin abinda na fada kafin kuma ya kalli agogon dake daure a tsintsiyar hannun shi fari da gashin jiki yaiwa addo dasu ko ina.
Dan magana yayi a cikin muryan ruwa naji wanan yace dani daga can na wuce restuaran din wurin akwai abinci an hada naje naci kafin in dawo.
Ban iya furta komai ba na fice daga office din direct dakin da aka warewa mata don hutawa na tafi ban dakin na nufa nayi sallah kafin na fito na tayar da sallah har lokacin komai da nakeyi kamar a mafalki nakeyin sa nake gani don ban iya gaskanta hakan ba.
Na dade zaune ina tunane barkatai ga umma ba waya a hannun ta balle na kirata in fara sheda mata halin da ake ciki kan na dawo haka dai na daga na koma office din ban samu kowa a ciki ba lokacin duk sun fita basa ciki.
Hakan ya bani daman karewa ko ina kallo na dan lokaci kafin na mayar da kaina a waya na dauko earpiece dina na makala na fara shan free kira,a dana kan sha.
Na daga kaina sama na mayar da kai bayan kujera na mike ina bin karatun a hankali ko zanji sasauci a zuciyana lokacin ga sanyin AC da aka sake yana ratsa ko ina na jikina sai kamshi ke tashi a lokacin.
Har suka shigo banji motsin su ba saboda bakon yanayin dana tsunci kaina mai kama da mafalki a wurin har saida wanan din mai mun magana ya dan daki table din dake gabana na dago da sauri ina bude idanuwana da suke a lumshe kamar barci na son daukana a lokacin.
Da sauri na kai hannu na cire wayan a kunnena na mika kuma ina kashe kiran da nake saurare din ina gaida su da dawowa.
Wayan ya kara kallo karo na barkatai yana kaiwa zaune a mazaunin shi har lokacin bai magana da kowa a cikin su bamu muka bar wanan wajen ba sai gab da magariba.
A gajiye na isa gida daga shiga na wanka na fada nayi na fito na tayar da sallah ban daga wajen ba saida nayi isha,i na fito daga dakin.
Umma na sama falon tana sallah na samu wuri na kai kwance ina jiran ta idar ina gaida ita ta amsa min tare da tambayana ya aiki ?
Saida na lumshe ido na dago daga kwance ina fadin umma idan na fada maki abinda nake ciki yau ban san ya zaki dauki zancen nan ba.
Cikin damuwa take cewa dani Allah yasa lafiya ba wani abin bane ya faru kuma ba Sahiba ina jin tsoro da fargaba akan ki ako wani lokaci.
Eh to umma abin kan da fargaba kuma da mamaki ace duk manyan matan da muke aiki tare sai nice kadai a yau na samu karin girman da ko mazan wurin basu samu ba shine abin mamaki a wurina kuma yake damuna.
Nan dai na labarta mata komai daya faru ban raga komai ba na fada mata duk yadda abin yake har aikina.
Shiru umma tayi na dan lokaci kafin tace dani Abdulhamid ya kamata yanzu mu nema akan wanan maganan idan ba wani makarkashiya aka kulla maki ga hakan ba.
Amar ta kwalawa kira ya firo ta turashi wajen Abdulhamid din anyi sa,a yana gida bai fita ba ranan zuwa asalatu wurin daukan karatun da yake zuwa da yaran shi.
Mikewa nayi zuwa kitchen na dan zubo abinci kadan na fito na fara ci ke nan yayi sallama part din umma ta bashi izzini ya shigo.
Bayan sun gaisane take fada mai duk abindana fada mata yana jijiga kanshi har tagama fada mai komai yana sauranta kafin yace.
Hakane umma komai data fada maki tabbasa haka ya faru ba kuma komai yasa haka ba sai cancantan Sahiba.
Akwai masu takarda a hannu da suka karanci wanan fanin amma kuma sai Allah ya zabo sahiba a cikin duk dako ilimin nasu saboda gaskiyan ta da warware matsala irin nata tabbas nasan wanan shine kawai dalilin ba wani abu ba.
Aikin nan alheri ne ga yar ki dake dama mu baki daya haka kuma sai kinyi hakkuri sosai kin sa yarda da Amincewa ga tarbiyan da kika ba yar ki a rayuwa.
Don aikin ta yanzu zai iya kaita ko ina da Sha,aban yake a vikin kasan nan don gyin aiki tare dasu idan har bukatan haka ya taso.
Jin abinda ya fada yasa na dago kaina daga cin abincin danake dan cakula da cibi na kasa cin abin kirki ina sauraren su lokacin.
Barin gari akan aiki ita daya Abdulhamid yace kwarai kuwa don zasu iya tashi daga garin nan zuwa arewa ko kudu duk aikin zai iya kaisu wanan wuraren .
Ina sam hakan ba zai yuyu ba gaskiya aiki idan ya wuce fadin lagos din nan gaskiya saidai a bari yaushe zan bar yar marainiyar Allah tana wanan gararin don kawai rashin gata.
No no no anty ba haka bane ina sam na tabatar kuma na yarda wanan ba zasu cuta mata ba a nan Allah ma ba zai yarda wani


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login