Showing 219001 words to 222000 words out of 382072 words
uwar tasake kukan takaici haka yayi daidai da shigowan yayanta maza suke tambaya.
Lafiya mama wani abune ya faru kuma tace ba komai sai kanwar tasuce ke fada masu abinda yayan nasu tazo tace a wurin.
Saida ya falkane yaga goran ruwan data aje masa a wurin duk yadda yaso tashi ya dauko jikin sa yayi masa nauyi ya kasa tashi a lokacin haka ya mayar da barcin a wahalce sai cikin dare ya tashi daya dan lafamai ya samu rama sallolin dake kanshi dabai samu yiba.
Anan kuma ya zauna yasha tunane akan abinda ke addaban shi a lokacin ya dade yana rokon Allah da neman yafiya daga Allah kafin ya samu ya rarafa ya hau saman gadon ya koma kwance ringingine yana faman sakawa da kwancewa.
A haka gari ya waye masa baikai ga mafita ba da kyat ya iya samu yayi sallah ya koma ya kwanta yana jin zazzabin na neman ya dawo mai a lokacin.
Washe gari yakama asarbar ne don haka babu zancen fita aiki a wurina hakan ya ban daman samun gyaran gidan mu duk daba wani dattin dake cikin sa amma na daure na gyara don jikina ya kara sake min.
Ammar ne yake labarta min abubuwan da suka faru dani da yadda na kasance ba magana wani iri naji a zuciyana take hawaye ya fara silalowa daga idanuwana.
Sai tunane nake menayi suka zaune akaina duk yawan mu sai nice nake da wanan laluran mai matsala da batarwa a cikin yan uwa.
Muryan ummace data fito daga bandaki take fadi to mai surutun tsiya watau dana hana ka fada saidai ka faki idona ka fada mata komai tana kokarin kai mashi rankwashe a kai nace umma don Allah ki barshi.
Idan bai fada min ba waye zai fada min umma shi kadai nake dashi a yanzu shinake gani yake ganina a matsayin dan uwa na shikiki a gareni umma.
Dole duk abinda ya shafeni ya shafeshi shima umma kada ki hukantashi kan abinda ya dace yayi yayi din kuma zaki hukuntashi kan hakan.
Zama umma ta koma tayi tana ajiyan zuciya tare da fadin ban hana ya fada maki ba amma zai bari ai sai kin karasa murmurewa nan gaba sai ya fada maki haka akeyi.
Yaushe ne bukin baby umma na tambaya don in kawar da zancen ta dan sake ajiyan zuciya tace inaga wani satine ko shine bukin ko baifi dai kwana goma ba yanzu abinda ya rage.
Ok nace na gyara zamana da kyau zamu tafine amar ya tambayeni daga inda yake zaune nace ina ganin hakan zamu tafi insha Allah.
Naga ya dan sake murmushi a fuskan shi don jin dadi abinda na fada kafin na juyo ina fadin amma akai sai ranan daurin aure zaka tafi da yaya Abubakar ko ?
Wayan dana kirane aka dauka na fara magana kan ina son a turo min da kayan da nake bukata na dauki lokaci muna wayan kafin na kashe wayan .
Shiru babu ya Abubakar gidan mu har weekend din ya kare muka koma aiki ummace ma dai naji tayi maganan shi har sau biyu na rashin zuwan shi din saida dare muna cin abinci ranan monday ya kira waya yana shedawa umma rasgin lafiyan shi.
A nan muka karbi wayan duk muka jajanta mai tare da fatan Allah ya bashi lafiya ya amsa da amin.
A wurin aiki kuma an fadawa mutane tafiya nayi yasa basu ganni ba sai suke zaton na dawone a lokacin suke min sannu da zuwa ina karbawa.
Muna tsaka da aiki kwatsam ba zato ba tsamani ranan tuesday saiga Ogan mu gaba daya ya ziyarce mu shidasu oga jimo.
Ba wanda keda masaniyar zuwanshi a ranan sai ganin su mukayi sunzo kwatsan mun dan zauna dasu anyi bayanin da korafe korafe kafin su fito don gaba zasu tafi zai tafi kasan Niger republic shine ya tsaya yaga jikina don an masa bayanin komai daya faru dani a takaice.
Bayan mun fito ne muka dan kebe dashi ya kalleni yana kara yi min godiya tare da tambayana karfin jiki nace jikin da sauki.
Yace yazone ya duba idan aikin zai jawo min matsala mubar aikin a barsu da Allah abinda yasani sakin dan murmushi ke nan wanda ke nisa damu sai yayi zaton wani zancen soyayya mukeyi a lokacin duba ga yadda muka tsaya a jikin motan muna fuskan sauran jama,an da sukaja baya suna jiran mu gama tataunawan dashi.
Wanan matsalan bai shafi aikin nan ba na fada ciwone kawai lokacin zuwan shi yazo min i am OK now na fada godiya ya kara min bayan min fatan alheri da zai tafine mun taka zuwa inda suke yake fadin a gaida umma yaso ace ya samu ganin umma sun gaisa da ita.
Bakomai zan fada mata na fada da dan guntun murmushi dauke a fuskana yayi sallama da mutane bayan ya bada alheri ga kananan ma,aikatan dake bakin aiki a lokacin
Wanan zuwan nasa ne ya jawo tsegumi ga mutane kowa da zancen da yake fada a wurin ranan bamu dade ba don zuwan shi da tafiyan shi yasa muka bar aikin dake gaban mu din a ranan.
Hello mommy na kirakine in fada maki baban su maryam baida lafiya kwanan sa biyu bai iya fita ba .
Mommy din ne ta kalli wayan a cikin mamaki da karfin hali tace Nazifa kina da hankali kuwa a rayuwan ki wanan wani irin maganane haka kike fada min kai tsaye haka.
A gidan ku ba a koua maki sallama bane ko gaisuwa balle girmama na gaba kada ki kawo min diban albarka a gabana dif taji ta kashe wayab tabi wayan da kallo.
Daga Nabila har hauwa dake gefen ta suka kalleta da mamaki jin yau yadda mommy ke fada da sarakuwan nata haka hauwace ta kasa hakkuri take fadin mommy meya faru ?
Barni da mara hankalin yarinyar nan duk yadda ka iya hakkuri da lamarin Nazifa sai ta kaika karshe watau.
Wai yayan kune baida lafiya ashe kwana biyun nan shine takirani haka kai tsaye take fada min ba sallama ba komai.
Yayan mu mommy suka hada baki shifa ni wanan kaddarareb auren da bason nayi sabo ba danace da ba, ayi shi ba wallahi.
Don yarinuar nan bata da ranan canzawa a rayuwan ta abin nata ma sai gaba yake yi a yanzu kamar mara hankali.
Mommy din ta shige dakin ta tana ci gaba da fada da sarakuwan nata dabata masan tanayi ba a lokacin don itama tana can tana mita akan wai mommy din tayi mata cin fuska a kan dan ta.
Sam ta manta da cewa a daidai kofan shi take tsaye take wanan maganan saida taji muryan shi yana fadin kedawa ke wanan maganan haka ?
Ta wani irin kallo kofan kawai ta wuce yana kwance yake mamakin wanan hali na matar nasa da bata data ido sam kowa ta samu yanzu take wanan sababin haka yaja tsuki yana gyara kwanciyar shi.
Don likitan data ganine yazo har gida ya dubsshi yai masa allura yasa ta dan nuna damuwanta akan rashin lafiyan nasa lokacin har taga tayi abin arziki ta kira mommy .
Gashi kuma mommy din ta watsa mata kasa a ido har tana kokarin zagin gidan su ita nata gidan daban ne ko yarabta sun fisu tarbiyane ?.
Ba,a kai awa daya ba mommy din ta dira gidan ita da yaran ta biyu don lokacin Faiza tana school bata dawo ba yasa basu je da ita ba gidan.
Sunyi sallama kusan sau biyu ba a amsa masi ba da alama kuma suna ciki don ga tv na aiki ssidai babu kowa a falon lokacin.
Basu ankara ba hauwa ta kirashi a waya sai ji sukayi tana fadin yaya kana cikine gamu a falon ku da mommy duk suka kallo inda hauwan take.
Ba a dauki tsawon lokaci ba sai gashi ya fito yana saye da jallabiya a jikin shi kallo daya zakai mai ka gane ya rame sosai a lokacin da alaman yaji jiki sosai ke nan.
Gaidashi suka fara a lokaci guda a vikin kulawa da nuna damuwan su a kanshi ya zauna da kyat yana amsawa don alluran da akaimai a lokacin.
Bayan sun gama gaisawane mommy ke tambayan shi abinda ke samun shi yace zazzabine kawai mommy ya wuce kawai ai wanan uban raman da layi lokaci guda haka tun yaushe ne ka fara ciwon , ?
Ya dan shafo fuskan shi yana fadin tun ranan da naje gaida ku last nadawo da wanan zazzabin kana cin abinci kuwa yadanyi murmushi yana mayar da kanshi a makarin kujera yake fadin bakin nawane ba dadi mommy.
Nan dai ta danyi mai fada akan yaci wani abu ya kalli inda Nabila ke zaune yace dan dafa min wani abu naci mai ruwa ruwa .
Wanan maganan da yayi sai yaba uwar tausayi take fadin matarka fa tana inane ita yace ban sani ba ko tana gidan nan don banji duriyan ta ba dai.
Sallati hjy ta fara ta kalli hauwa tace ke kira min Nazifa a part din ta yanzun nan da sauri hauwa ta mike ta nufi part din Nazifa din.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA , , , , , , , ,
6️⃣5️⃣ BY, , , , , , , , , , , ,
ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL HAQQ, , , , , , , , , ,
ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257
ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋
Allah sarki duniya duk yadda ka raina kanka dole kana da makiyi a cikin dubu.
Ni zainab nasan ban taba novel in zagi wani akida na islama ba rayuwana ba don rayuwana bai taba kaiwa can ba ban kuma taba nasa inyi hakan a zuciyana ba harga Allah.
Ban tana nuna akidana ba a duniya darika, shi,a,tijjaniya ko izzala kadariya duk addinine masu mutunci a idona don sun sheda Allah dayane Annabi mohammad kuma manzon sane masoyin mune.
Shine mutum mafi daraja a cikin mutane why zaki nemi ki bata min suna kan abinda harga Allah ban taba nasa hakan ko a fili ga wani .
A wurina duk wanda ya sheda babu sarki sai Allah Annabi mohammad manzonsane mai shi ya zama dan uwa a gareni.
Akan me zaki hada da mutumin da ake fadin yana cikin duhun kai baida ko sani akan addini gidahumin jahili kawai, shi dai muna musuluncine shi wanda ake nuni da halin jahilci a kanshi da dogaro da wanin Allah ko baki fahinci me labarin yake nufi ba.
Don haka ki fahinceni ba wani akida dana ambata akan wanan mutumin labarine na gaskiya ko me labarin bata fada min akidan ta ba balle na wani.
Ba jahila nake ba da zan tsaya ina sukan dan uwana musulmi mai sallah biyar a rana da ambato Allah.
Ke yar uwa ki tubaga Allah da wanan sherin da kike son yiwa kanki kina ganin kamar ni kika kulawa hakan.
Babu inda na ambaci hakan ki koma ki duba ki karanta da kya ki fara istigifar ga Allah.
Haba yar uwa me nayi maki haka zaki min wanan abinda ko a fili da zaki tambaya ko ni wace akan addinina zaki gane hakan don Allah don son da kukewa Annabi ku barni in zauna lafiya da kowa da wanan sherin da kike kokarin kullawa kanki waini.
Ni dai na sheda babu sarki sai Allah Annabi mohammad manzonsane ki koma ki karanta da kyau idan na fadi hakan da kukace.
Ku dinga yiwa mutane uzuri don Allah ban taba samun wanan matsalan da yan group dina da yanzu mun zama yan uwa dasu tun akan tarko balle ke da aka dauko maki na Allah ya isa aka kai group din ku kuke kokarin min sheri shi fitina idan kayi sanadin kuna shi baka san a inda zai tsaya ba.
Kuyi hakkuri idan na bata maku nikan wallahi ban fada hakan ba har ga Allah cewa wai kai abin ma ba dadin fada can ga bakin wanda ya nasa hakan .
Ikon Allah mommy ta fada tana ajiyan zuciya takai kallon ta ga hauwa data aika tana zaune har lokacin ki kira min ita nace dake da sauri hauwa ta mike don zuwa kiran Nazifa din a kofan ta suka hadu hakan yasa hauwa ta juyo.
Kusan tare suka iso falon da Nazifan don batayi mata magana ba itama haka ta iso tana fadin sannu da zuwa ashe harkun karso ta samu wuri ta zauna saman kujeran dake fuskantar na mommy din.
Idon shi ya lumshe cikin jin kuna da zafin rai bayan na ciwon dake damun shi a zuciyan shi yace bai ci komai ba tun safe mommy ta fada tana kallonta wai abu mai dan ru, , , ,
Ke baki iya gaida babba bane ko bako ya fada yana kallonta ido jajir a lokacin saida ta wani kalleshi kamar tana mamaki da maganan shi kafin tace.
Nima ai naga ba a gaidani ba kuma ni akazo aka sama a gidana ai nagani wani irin zabura yayi daga saman kujeran zakace bashi bane mara lafiya dake takawa da kyat ya fito a lokacin.
Wa kike fadawa hakan mommy dince zata gaidake ko wa a cikin su ke kin gaida mahaifiyar sune balle kiyi mutumcin da za a gaidake ?
Har kina fadin ke aka sama a gidan ki inane gidan naki ki fada min yau idan na hada kudi da wani naki nagina wanan gidan ?
Modibbo mommy ta fada da dan karfi cikin bacin rai ya kallo mommy tace koma ka zauna tana da gaskiya don gidan ta muka zo ba karya ta fada ba ta mike tsaye tare da duban yaran tana fadin ku taso mu tafi Allah ya baka lafiya.
Mommy ina kuma zaku akan wanan da ko dabba yafita sanin darajan dan adam a wurinta yaja wani irun tsukin takaici da bakin ciki wanda shi kadai yasan zafin da yake ji a zuciyar shi lokacin.
Eh ai gara mu tafi irin hakan ke hana ko yaran nan in turo gidan nan wallahi bana son diban albarka ke kuma ki sani wuri daya na fito da mahaifin ki don haka na wuce raini a wurin ki ko wanin ki.
Ni yanzu me nayi kawai sai mutum na zaune kalau za a samu sherin da aka lakaka mai nima ai hakan yasa bana zuwa gidan naku.
Kada kije mana dama wake son ganin ki ko zuwan yanzuma don dan uwan mu mukazo gidan nan idan bashi ba wa zaki gani a gidan nan Nabila ta fada.
An daiyi hasara a koma gida a koyi ladabi wurin gyatuma hauwa ta bada a daidai inda zata wuceta cikin kashe murya ba tare da kowa ya jita ba.
Bani nayi hasara ba sai ku da kuke zaune a gida ko kare bai taya ba kece kika buda muna hanya indai kwantai ne saida aka roki yaya ya daure ya dan jona ki jaka.
Fau taji ta gwauce dukan bai sameta sosai ba mommy ce data dawo da baya bayan jin fada ya kaure a tsakanin su takaiwa hauwa din duka ta noke ta samu bayan kanta har dan kwalin kanta yana batun faduwa kasa.
Ke kuma Nazifa zaki biye mata ku zubarwa kanku mutunci idan ita bata da hankali aike kina da hankali ko ?
Saidai ta zubarwa kanta da mutunci don ni tasan nafi karfin ta ga komai takoma can tayiwa wa yanda ta saba yiwa bani ba nan don ba zan kyale yarinya ba.
Mommy ta gane metake nufi hakan yasa ta juya rai bace tana fadin Allah ya sauwaka kai kuma Allah ya baka lafiya tafita daga gidan sai bayan sun shiga motane suka hango shi ya dab tako yafito daga kofan falon ya rike da hannun sa daya .
Saida yaga tashin sune ya koma zuwa cikin gidan har lokacin Nazifa tana tsaye tana yankan kauna bata da niyar bari daga kofan ya dagata yana fadin ke ma yanzun nan basai anjima ba ki fice min daga gida.
Akan wanan maganan zakace na fice ma daga gida ba inda zan tafi dama abinda ya kawo su ke nan yanzu don suja min matsala tsakanina dakai kuma sunja din don haka babu inda zan tafi.
Haka kikace yau idan kika bari na fito na sameki a cikin gidan nan sai rayuwan ki yayi bala,in baci fiye da tsamanin ki yana fadin hakan ya sakai zuwa dakin nasa .
Ba zai iya kwanciya ba a lokacin din haka kai tsaye ya bude wardrobe din shi ya ciro kaya daga ciki yana sakawa a jikin shi.