Showing 378001 words to 381000 words out of 382072 words

Chapter 127 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28364

dana mallaka a rayuwana don haka zan iya sabawa kowaye yake son sheganta min jinina zufana da nayi wahala a wurin samun su.
Kaina yana duke duk yake wanan maganan ina nazarin abinda yake fadi watau dai ko ya kuke dashi zai iya sabama idan ka taba mashi diyanshi.
Jin yayi shiru yasa na dan dago kai na kalleshi yana zaune ya hada hannayen shi biyu saman kanshi ya dafe sai naji tausayin shi ya kamani lokaci guda haushin matar nasa zanji kome a yanzu ?
Don na fahinci ashe ba karamin zance bane ta fada sai a lokacin nake nazarin zancen na gane me hakan yake nufi mikewa nayi daga inda nake zaune a hankali.
Na taka zuwa inda yake zaune din cikin yanayin damuwa hannuna nakai a hankali saman kanshi ina fadin uncle kayi hakkuri mu bita da addua a yanzu.
Da sauri ya dago kanshi ya dubeni idanuwanshi nagani sun kade a lokaci guda sunyi jawur dasu alaman bacin rai karara a idanun nasa.
Da kyar ya bude bakin shi yace Falmata ba iri mata nan bane masu saukin kai hakana tana da matukar wuyan sha,ani sosai sam bata da fahinta abinda tasa a gaba shi take gani daidai a gareta.
Ina mata ragowa da farko don mahaifiyatace amma daga baya saina fahinci su basu san hakan ba don a yanzu suna ganin kamar sunfi karfinane bata san ina raga mata bane a yanzu don hjy din da kuma yayan mu a yanzu.
Bana son yarana su shiga cikin damuwa idan na sabawa mahaifiyarsu dolene abin ya damesu amma sam ita bata duban hakan tana ganin kamar duk abinda tskeyi fin karfina tayi yanzu din.
Ta manta da cewa nine sillar mayar da rayuwanta haka cikin inganci ta manta cewa a innuwana take shan iskan rayuwan da take taka kowa dashi yanzu.
Idan kayi hakkuri ka lalabata zata daina wanan tanayin shine yanzun a cikin zafin karin auren da kayi mata don haka ka lalaba ta ku fahincin juna ku zauna lafiya.
Shiru yayi yana saurarena kafin ya nisa yana fadin fatima you are wonderful and best among the best mm agode da baki kasance irin matan nan masu hali irin nasu falmata da ace wanan halin kike dashi yau nasan sunana zai baci a idon jamma,a.
Babu macen da za a zo har gida a batawa diyanta suna haka kuma har ta shanye hakan ba tare da ta dauki wani mataki ba haka .
Idan ma na dauki matakin ba zaikai wanda Allah zai daukar min ba idan na kyaleta da halin ta idan kuma tana da rabon shiryuwa Allah ya shiryamu baki dayan mu amin muka fada.
Nayi hakan ne a gaban shi don kada yasan kalar kishina don ba karamin tausan zuciyana nayi ba a lokacin har na nuna ba komai a zuciyana game da wanan haukan nata da tazo tayi muna a gida.
Saidai nasha alwashin cewa zanyi kokari nayi ta daurewa ina nuna sanyi a zuciyana kamar yadda matan yarbawa suke taushe zukakatan su akan kishin mijinsu wanda kai bare ba zaka taba gane hakan ba garesu.
Saidai zan manna mata karamin hauka a kaina ta yadda zan sace zuciyar mijin na rike a hannuna na juyashi yadda bata son ganin shi da ko wace mace a duniyar nan.
Tayaya zanyi hakan ba wani abu bane me wuya tunda kowa yasanshi zanyi kokari na yaki zuciyana bazan yarda na taba zancen abinda ya shafi hjy falmata ba a gaban shi.
Haka koda wasa ba zan taba nuna gazawa da yan uwanshi ba ko wani mutum da wata halaka ya hadashi dashi har na sanshi koda kuwa masu aikinmune irin maigadi da mai waki ko cookers da sauran su zuwa abokan hurda da yake girma da arziki dasu.
Fanin gyaran jikina koda yaushe na koma kamar yarinya wanan ya zama wajibi a gareni ko yaushe jikina gidana ya kasance min a gyare.
Haka kyautatawa a tsakanin mu ba gazawa ko kissa balle cutarwa tunda ni bai cutar dani ba ya zama dole nafishi son diyanshi da duk wani nasa a yanzu idan na dan kwatanta haka ina ganin na wadatar da yadda nake so.
Sun gwaggo satin su biyu a can suka dawo gida inda suka barni tare da ummana da dan uwana Ammar wanan shine sillar dawowan ummana a tare dani.
Hakan ya batawa yan uwan mu na kaduna rai sosai da suka fahinci cewa umma ba zata dawo Nigeria ba kuma ta zauna a nan din.
Don wai da har ana shirin cikin baffah Abdullahi ko baffah hamza daya ya nemi umma ya aureta sai gashi na dauke uwata na tafi da abata can inda mukai masu nisa.
Haka bai hanani yo masu aike ba lokaci lokaci sanan kuma zan bisu daga daga na aiko masu da sako mai ingaci a garesu wanda hakan ya jawo min farin jini da kauna garesu.
Zuwan mu na farko Nigeria mun zone lokacin da Fatima da Ammar suka samu hutu a makarantarsu a lokacin har yarana sun iya tafiya don suna da shekara uku da haihuwa a duniya.
Don haka ba wanda yasan yanayin su koda mukazo din dasu lokacin sallahne don haka a Maiduguri muka fara sauka .
Mun samu an gyara muna gidan mu sosai ba kamar yadda muka barshi ba a baya can yanzun an kara gyarashi yayi kyau sosai ga ganin mutum.
Hjy Falmata tazo a wanan shekaran don bukin sallah din duk da ita tana zuwa duk shekara nima don kawai ga irin yadda muke da yan uwanane yasa bandamu da zuwa ba na share kowa na zauna can tunda ga mahaifiyata a kusa dani yanzu.
Hjyn su mukhutar ta kara dan tsufa amma da yake akwai kulawa ba zaka gane hakan ba gareta sosai tare sukazo da uwargida falmata daga Paris don haka sun rigamu shigowa Nigeria su don mu sai washegari muka iso .
Amma bai zo gidan namu ba sai safiyan sallah ya kama ranan jumma,a za,a hau idi a Nigeria, ba wani aiki a gidana don sister tace kada muyi komai zasu kawo muna daga gidan hjyn su idan an girka a can.
Da safe ina daki kwance ya shigo kafin aje mosque yana cikin shirin shi na babban kayan day saka a jikin shi wanda ya fito mai da shekarunshi a fili kana ganin shi zaka hango kamalla da kasaita a tare dashi ga kwarjinin shi a fili.
Daga inda nake zaune nayi mai ina kwana duk da banji dadin rashin nuna kulawanshi da bai nuna muna ba lokacin da mukazo, duk da na kirshi bayan mun sauka din.
Sai baizo ba bai kira ba don haka na danji zafin hakan a raina, kisan halin namiji mijin mace biyu baibar kowa ba don haka yanzunma shima a tsarge ya shigo din yana dan kame kame amma haka na daure na nuna ba komai a zuciyana kamar yadda na saba yi mai duk daya fahinci hakan gareni a fuskana.
Bayan na gaidashi yana min ya hanya na basar tare da fadin har zaku tafi mosque ke nan yanzu ina duban lokacin a wayana.
Time ya kusa ya fada a kasalance yana gyara tsayuwan shi lokaci guda ba tare dana kalleshi ba nace sai a tafi dasu babami suma suje su hau sallah idi yace OK idan zasu yarda ai saimu tafi nima zanso hakan ya fada har lokacin yana kallon fuskata.
Mikewa nayi daga inda nake da sauri na fita na barshi dakin tsaye ya bini da kallo tare da mamakin hali irin nawa yana girgiza kai.
Na samu umma ta saka masu kayan da wani kanin mukhatar din ya dinka masu don hawan sallah idi don tun muna can ya turo min photo kayan a waya.
Dan Allah ya dorawa yaran farin jini sosai ga wanda ya gansu sai yaji yana son su a tare dashi kaunarsu yana shiga zuciya farat daya ga wasu .
Ida mai karatu baki manta ba farko labarin mukhutar din na fada maki wanan guy din sunzo wurin shi tare da mahaifiyan shi kan a taimaka mashi da sana,anyi a lokacin.
Mahaifan shine wanda suke mahaifan su daya dana mukhutar din kanin mahaifin mukhutar dine da har yayi sanadiyan daukan mukhatar zuwa kasan waje dashi sai suka samu matsala dasu a lokacin kuma ya hadu da mahaifina.
Yanzu muna zaune tare dashi a can shima yana zuwa yana dawowane don international business sukeyi dashi ta haka nake samun daman turo kayana zuwa Nigeria wa anty Amarya da mommy dasu gwaggona Amina da kudidi suna sayar min.
Ina kuma turawa sisters dinshi suma sai gashi Allah yasa muna albarka sosai ga harkan suna samu ina samu sosai ayanzu ga aikin company da nakeyi a can tare dasu.
Wanda koshi saida akasha fama sosai da jidalin hjy Falmata don tace itama sai tayi aikin irin nawa karshe ma dai yace to tafito itama ta fara aiki irin nawa din tace kuma bata yarda da hakan ba tunda bata iya ya sani.
Sai dai ya dinga biyanta albashi da kudi daidai wanda company ke biyana a bata itama hakana .
Don yace bai yarda ba shine sukai jidali kanshi sosai dole tazo ta hakkura ta barni ina aikina da nake jin dadin yinshi sosai araina.
Wanda hakan yana kara dauke min hankali ga komai ina kula da yarana da mahaifiyata da yan uwana dake tare dani sosai da kuma aikina
shi maigidan idan yana kasan mijine idan kuma ya tafi sai Allah ya dawo dashi lafiya kuma aikina dai inayin abina yadda ya dace ban dorawa kaina wahalan duniya akan namiji ba.
Yaran na riko daga dakin umma muka fito zuwa part dina sai muka hade dashi a falon tun daga nisa yake sakar muna murmushi har lokacin dana karaso dasu inda yake tsaye.
Mamaki ya fada har yaushe akai masu wanan dinkin haka ya fada yana mamaki nace Abba ne ya dinka masu kafin muzo kai ya jinjina ya mika hannu sai yaran sukaki zuwa gunshi.
Murmushi nayi a cikin harshen yarbanci nayi magana dasu suka dan kalleshi lokaci guda da kyar suka bishivdon basu saba dashi ba sosai saboda zaman da bayayi damu sosai.
A sauko lafiya daga masalaci ya wuce da yaran gidan sarki daga gidan sarki suka nufi gidan shi a can ne suka kwasa da hjy falmata wai don me zaizo mata da yaran gidan ta.
Sun danyi sa,insa dashi inda ya kwashe duka har da yaran ita falmata din suka wuce zuwa gidan mahaifiyar shi ancen yake fadawa hjy abinda falmata din tayi kan yaran yake fadi wana zai kawo masu babban matsala a tsakaninsu.
Sai gasu gidana lokacin duk muna falo a zaune har Ammar taro na mutunci suka samu a wurin mu ina jin yaran na tambayan shi who is she Dad ?
Your stepmother ya basu amsa sai dayan tace but mum told us that she is wicked and,and also a witch she is too dangerous i mean mun said.
But she is nice dayan ta fada to nima shinagani ai amma mum tace muyi hankali da ita ta fada tana dan satan kallona inda nake tsaye ina cirewa yarana kayan jikinsu da yai masu nauyi ajiki.
Wani tsawa ya dakawa yarinyar lokaci guda har ta dan kadu yake fadin she is my wife yaranta kuma sune blood brothers din kune nan ya shiga yi masu bayani suna kada kai.
Dakina na koma don yayi baki a lokacin saidai raina yayi matukar baci jin yadda matar shi ta batani a wurin diyanta duk saboda kishi .
Kinshin da ba a gida daya muke zaune tare da ita ba a lokacin amma saboda tsananin kishinmuna mata ta batani haka a wurin yaranta da haka suma zasu taso kishin su ya girma a zukatansu.
Na gama fadawa umma komai ta nisa tare da fadin ai yadda ya nuna shine daidai tunda yatsawata masu atake kuma yayi masu nuni da suso yan uwansu na jini a zuciyar su.
Da dare ya dawo gidan mu a nan zai kwana saida na gama hada mai komai da yake bukata kafin ya kwanta na juya zan fito.
Naji muryanshi yana fadi ina zaki naso muyi dan magana dake yanzu ya fada hankalinshi akan laptop din dake gaban shi tun shigowana dakin yana aiki a cikinsa.
Zan ba babami magani naji kamar mura nason kamashi OK baida matsala ya fada tare da dan dago kanshi a lokacin na juya na fita har lokacin bawai na sake bane hakana.
Nasamu yaran suna barci a jikin umma na shiga dakin take fadin kiba yaron nan magani kafin barcin shi yayi nisa na amsa da shina dawo in bashi a yanzu.
Da taimakon umma na bawa yaron magani kafin naji ta ambaci suna na juyo take fadin kada wanan zancen yasa ki sauyawa mijinki a yanzu sahiba.
Idan kinyi duba ga irin halin abokiyar zaman ki meye laifin shi a cikin zancen nan tunda bashi ya haliccetava haka ba.
Yana iya kokarin shi wajen gani hankalin ku ya hadu wuri daya musanman yaran nan nasa kinsan bada son ranta bane ai ya kwasosu zuwa gidan nan yau .
Don data sani bazata taba yarda da hakan ba tunda tana da mugun akida a zuciyanta na rashin fahinta.
Don haka kada ki dauki wanan zancen wani abu har ta hanaki jin dadin rayuwa keda mijinki dama abinda takeso ke nan tsakanin ku ko yaushe ya faru.
Umma naga ban damu da zancen taba ban kuma sa kaina cikin sha,anin yaranta ba don me ba zata barni ba na zauna lafiya a inda nake ?
Sahiba kishin matan arewa daban yake dana sauran mata idan kinyi tunane wanan ne ya jawo matsala maigirma a tsakanin mahaifinku da yan uwanshi duk a saboda dalilin kishine hakan ya faru.
A yanzu zakifi maida hankali wajen ganin cewa yaranki sun san yan uwansu kikuma koya masu kaunar suso su a zuciyar su kamar yadda mahaifinsu ke kokarin yi a yanzu.
Nasiha sosai umma tayi min kafin muyi sallah na tafi na shirya a dakina zuwa turakan maigidan duk da na samu ya hada har ya kwanta a lokacin.
A hankali naje na kwanta daga gefen shi a zato barci yakeyi a lokacin don haka nayi adduan kwaciya na kwanta a hankali don kada na tayar dashi.
Minti kamar uku tsakani naji muryan shi yana kiran sunana a hankali na bude idona dana fara lumshewa zan fara barci.
Iam sorry idan zancen yarinyar nan na dazun ya bata maki rai kinsan halin Falmata bansan ko yaushe zata fahince mu ba nasan kina kokari wurin yin hakkuri da halinta don haka ina rokonki da kici gaba da hakurin da kikeyi ko dan sabodani.
Bazan iya canzata ba saidai ina addua a ko yaushe gareta damu duka baki daya koda bata gane gaskiya a yanzu ba dole watarana zata gane hakan insha Allahu.
Nisawa nayi a hankali na gyara kwanciyana kamshin jikina yakai ahancin shi lokacin ya lumshe idon shi cikin wani yanayi zanyi hakkuri da duk abinda hjy zatayi min amma ban iya wani hakkuri da wullakancin da kai zakai min saboda wata.
I don't now why da zamu shigo garin nan na buga maka waya mun iso tun wajajen two na rana amma kika zuwa gidan nan a jiyan na dauka yanzu ko bakazo bacdon ni da yan uwana zakazo kaga saukan mu don diyan ka yanzu.
Na sani mu muna iya hakkuri da duk wani halin da zaku nuna muna tunda mun shiga rayuwan ku da rana tsaka tana ganin munzo a lokacin da bai dace ba cikin ku.
Duk da bawai so ko kauna yasa ka aureni ba don in zauna tare da kai sai tausayi zalla namu da kakeji yajaka kwadayin aurena a lokacin da sam aure baya cikin rayuwana a lokacin.
Ka tursasani akan dole kaida iyayyena kuka tilastamin adole nashiga rayuwan ku da ayanzu nake ganin kamar mun zama dolene.
Innalillahi haba Fatima keda bakinki kike fadan haka yau don kawai andan samu akasi a wurina jinyan nan koda kuka iso ina tare da emirate muna ganawa dasu.
Ban samu kaina ba wallahi sai goma da rabi na dare har lokacin wallahi kuna a raina saidai nasan a lokacin kunyi barci don kun gaji amma kiyi hakkuri insha Allahu hakan ba zai sake faruwa ba damu.
No ka daina bani hakkuri don mu da yan uwanmu suka gujemu ka tallafe babu nuna kyama a garemu ai kai ya kamata mubawa hakkuri idan mun saba mane ?
Murmushi naji ya sauke kafin ya mirgino zuwa inda nake ya rugumeni a jikinshi yana sauke numfashi tare da fadin kada ki taba tunanen irin hakan gareni.
Don in ban rikeku ba haka ina raye Allah bai hana mun ba sai Allah ya tuhumeni gobe kiyama kuma ki sani matsayi biyu kike dashi awurina .
Ke mamatace a yanzu kuma amana a gareni


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login