Showing 114001 words to 117000 words out of 382072 words

Chapter 39 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28327

falo saman kujera two setter Ammar yayi filo da cinyar umma din yana buga game.
Gaida ita nayi take fadin kin tashi ke nan ga abinci can ki dauka na bata rai tare da fadin umma banjin yunwa na kai zaune.
Naji tana fadin Fa,iza ta shigo sau biyu kina kwance har na zauna sai kuma na mike zuwa wurin faiza din in duba me take nemana dashi lokacin.
Ba kowa a falon nasu na bude dakin su na samu duk suna ciki anty Nabila zaune wurin mirrow tayi tagumi sai Fa,iza da hauwa dake saman gado fa,iza na kwance hauwa ta zauna ta mike kafa tana kadawa a cikin tunane nayi sallama na shigo ina kallon yanahin su da mamaki har lokacin.
Saida nakai zaune na dan sake kallon su kafin ince lafiya anty Nabila a cikin turancin nageria ta dan muskuta tana fadin wallahi ke dai Sahiba ba lafiya.
Mommy aka bugo waya cewa yayanta yayi hatsari dazun yana asibiti rai a hannun Allah shine kika ganmu haka.
Ikon Allah sai gashi sam banji komai ba ga hakan sai cewa danayi Allah bashi lafiya na juya inajawa kawata kafa Sahiba.
Ta dan dago kai ta kalleni kafin tace dani kin tashi ke nan sau biyu ina zuwa part din ku kina kwance nace shine umma ta fada min yanzu ai nazo.
Muryan mommy ne ta shigo duk suka mike zuwa falon wurinta nima na bisu a baya muna gaida ita da dawowa .
Ta dai amsa takai zaune zuciya ba dadi don yadda ta bar dan uwanta din a cikin wani hali mara dadi Nabila ce takai zaune kusa da uwar nasu take fadin mommy ya jikin nasa ?
Tace bari Nabila saidai ace da dama don har yanzu bai farfado ba baima san wanda yaje kansa ba har wanan lokacin.
Ikon Allah kawai wanan abin nan ne fama cikin gari daga badarawa zuwa unguwarsu ya fito gidan yaya Nuhu abin ya samesa motar tayi kaca kaca ba kyace mutum ya fita a cikin motar nan ba wallahi.
Daddy ya dawone ta dan bata rai kafin tace yadawa tare muka dawo ai shikuma wai yake fada min in barwa karima girki yau tayi.
Naga yaran sun kalleta da sauri Hauwa tace amma daddy din nan mommy me kikace masa ke tace umhumm hauwa ke nan mezan ce dashi tunda baya bukatan ni inyi.
Gaskiya gaskiya abinda daddy ke maki baida kyau mommy kullun sai aita tauye maki hakkin ki don kawai ita taji dadi tanawa mutane iskan ci a cikin gida.
Kyaleshi yana da daman fadin hakan tunda Allah yace in kayi tafiya ka dade ka dawo kana da right di kwana wurin wace kakeso a cikin iyalin ka ai.
Amma mommy wanan abin fa gaskiya yayi yawa don da ba haka daddy yake ba ai koma me tayi din kanta kanta take daukarwa alhakin haka bata sani ba .
Ni yanzu matsalan dan uwana yafi damuna don inda sabo ai yanzu na saba da wanan halin da suke min ba sabon abu bane kuma a wurina.
Sun danyi maganganu ina jin su duk da bana fahintar wani abin amma kuma ina fahintar wani inda na gane akan abinda suke magana a kai.
Na dago kai na dan kalli sama kamar mai tunane kafin ince itama din ai zasu samu matsala dashi ne ai .
Da sauri Fa,iza ta kalloni tana fadin da Anty din nace eh mana kilama a yau din nan ai na mike na shiga dakin su na dauko takardan Fa,iza saman gado na fito ina fadin zanje nayi karatu don mun fara jerabawa a lokacin.
Wait for me tace na tsaya tare muka nufi part din mu da ita muna can har dare bayan munyi sallah ta fito ta koma part din su.
Mukan muka rufe dakin mu ashe bamu dade da rufewa ba fada tsakanin Anty da daddy ya rikice akan yarta Suraiya dake makaranta zancen ya taso masu.
Har abin ya kaisu ga zage zage a tsakanin su ta fito rai bace har waje tana zage zage kowa najin ta a gidan mukan muyi barci a jikin umman mu a lokacin kamar yadda muka sabayi.
Tun safe sai ga mommy a dakin mu tashiga tana saye da hijjab din sallanta da gani daga wurin sallah take sallamta yasa umma bude kofan mu ta shigo.
Tambaya tayi ina sahiba gata nan ta koma kwanciya umma ta nuna mata ni tana fadin lafiya dai ko hjy ?
Wallahi lafiya kalau yar nan daine da abin al,ajabi jiya fa muke magana a gabanta ashe wai tace da Fa,iza itama ai ba zatayi girkin ba sai gashi kuwa sunyi fada sosai da Alh har da tonon asiri a jiya din shine Fa,iza ke fada min abinda tace din.
Umma ta nisa tana fadin ni lamarin Sahiba ya fara daure min kai sai kiga yarinya tayi magana kamar a cikin wasa sai kuma hakan ya zamo gaske ni wanan abin ya fara damuna gaskiya.
Nata baiwan ke nan ita kuma mommy ta fada tana kallona sai sukai shiru can umma take fadin ai naga kamar kece da girki din mana idan ya dawo.
Sai mommy ta nisa tana fadin hakane ni din ya kamata nayi amma jiya mun dawo daga dinan ya gyade yake fadin wai na barwa karima girki kai tsaye .
Ya jikin Alh din umma ta tambaya to da sauki yanzu na buga masu waya kafin in fito sunce har yanzu dai bai farfado ba sai dai likita yace ba komai bane wai zai farfado da yardan Allah Allah ya sauwaka umma ta fada.
Ina jin su na lafe banyi magana da kowan su ba don kada su gane idona biyu a lokacin naji umma tace kai ita kuma wanan kishiyar taki da takalan magana take wallahi.
Don me zatace itace zatayi gitki bayan tasan kece da girki kuma nifa kinga abinda ke ban tsoro da kishiyoyin zamanin nan ke nan hjy.
Kana zaune kalau da iyalin ka sai su shigo su bata zama a karshe su kuma din ba zaman zasuyi ba koda sun zauna din a cikin fita kowa na kusa dasu zai zauna.
Bari ke dai Mairo wallahi da farko Alh baya biyewa iskancin ta amma a yan shekarun nan yanzu kan ya biye mata wallahi.
Zama dai kawai nake a cikinsu ina hakkuri amma komai ban ganewa yanzu wurin Alh duk abinda nayi shi dai banyi daidai bane a wurin shi.
Kiyi hakkuri hjy duba ma ga yadda yaran nan a yanzu duk sun girma hakkuri kawai yanzu ya rage kuma ai don mazan yanzu sun fison haka suma.
Shine ai tunda dai ina zaune cikin iyalina ai ita ta rage da daukan nauyi a wuyan ta yanzu kumabarin je ina son a hada abin kari a aika masu asibiti ta fada tana mikewa tsaye.
Na dade a wurin idona biyu bayan fitan mommy din daga part din ban kuma daga ba balle umma tasan idona biyu lokacin.

Zaune suke falon yayi tsit sai Jibrin Arrow ke bayani kan abinda ya faru yake bayani aikai sauran suna sauraron shi shi kuma mustapha sai goshin shi yake murzawa kawai a lokacin.
Don yadda yake jin zuciyar shi kamar ya buga saboda bacin rai ya yarda dasu sun cuce shi da yawa zai nuna masu shi din kifine ne mai ganin mai jar koma ya fisu sanin kan duniya a yanzu.
Don shi da ilimi da siyasa yake tafiya da harkokin shi ba tare da duhun kai irin nasu ba da sukeyi yanzu a jahilce.
Har Arrow din ya gama bayanin shi bai dago kai ya kallesu ba shuru yayi ya tsurawa ogan nasu ido duk da sun girme masa a shekaru haka suke bashi girman shi da Allah ya bashi a kansu.
Yaro da kudi abokin manya ke nan mustapha boy din hjy hari don ita ke kiran shi da boy kasancewan shi dana farko a wurin mahaifiyar nashi bata kiran sunan shi na asali mustapha din.
Jin Jibrin din yayi shiru yasa ya dago yana binsu da kallo da idon shi da sukai ja jajir a lokacin murmushin dole ya kakaro masu .
Don ji yake falon na juya mashi da kyar ya iya budan bakin shi yadan lashi lebon shi da yaji ya bushe masa yana fadin yaushe ne kayan zasu iso ?
Jibrin ya gyara zama yana fadin zuwa karshen wata insha Allahu kayan na Nigeria yadda suka tsara kayi kokarin da namu kayan zasu dakata a can ba,a zo dasu ba ya fada ya mike tsaye tafiyan shi kawai yasa suka gane abin ba na wasa bane wanan karon.
Juyowa sukayi bayan sun rakashi da kallo ya shige suka hada idanun su cike da zargin junan su a lokacin.
Koda ya shiga dakin kwanciya yayi yana runtse idanuwan shi ba abunda ke fado mashi a rai sai dan uwan shi abokin gaban shi tuna kurciya da har yanzu sun kasa sake jiki da junan su a matsayin su na diyan yan uwa da suke.
Ya sani sarai dan uwan nasa yana farautan su a yanzu don so yake ya kamasu dumu dumu da laifin kan abinda ya shafi dokan kasa .
Ke nan da hakan na nufin Abubakar midibbo din yayi wining akanshi ke nan da komai don indan har ya kaishi ya kulle yasan ya gama gamawa dashi ke nan a duniyan nan.
Mikewa yayi daga inda yake kwance da sauri ya dauko Laptop dinshi duk bayanan da yake so suna ciki kamar yadda ya adana su a baya dan guntun murmushi ya sake a lokacin.
Asibiti zamu wai zamu kai abinci daga nan mu gaida maijiki duk da ban san waye ba lafiya ba a lokacin .
Saidai haka kawai nake jin ban damu da wanda akace din yayi hatsarin duk da ance maishi din dan uwan mommy ne kuma dan uwan daddy kuma.
Saidai hakan bai dameni ba kamar yadda naga sauran sun damu suna jin hatsarin mutumin a jikin su.
Bujene da riga na atamfa na saka mai kalar pink da adon filawa farare masu girma daga nisa zaka iya dauka lace ne sai idan nazo kusa zaka gane atamfane na saka.
Bayan mommy ta muna fada kamar yadda take muna duk lokacin da zamu fita daga gidan akan mu kama kan mu mu kula da mutuncin mu muyi tarbiya da da,a ga wa yanda zamu sama asibitin.
Na dauki basket din abincin nabi bayan su ina dan gyara gyalena da yake sabulo min a kafada don rashin sabo da yafa gyale haka .
Gaskiya ba yabo ba kyau kam Allah ya zuba min tundai yanzu da nake samun gyara daya dace dani don na murje nayi wani irin haske da dan jiki.
Ga kiran hallitana da yanzu ya fito a fili don na kai budurwa sosai kuma na iya gyara saidai har wanan lokacin shigana da nasu akwai bambamci sosai don kayan da nake sakawa su basu iya sakashi haka su fita.
Niko ko a jikina don gani ma nake ai na fisu shiga na fita a lokacin akai sa, a kuma ba wani mai kyani don daddy baida tsanani ga iyalin shi shi.
Nabila ce ta jamu mun isa ba wani wahala don gane wurin don dukkan su sun san asibitin tunda muka tun karo wurin na hango wani mutum mai karfi tsaye yana fada.
Sai faman gyaran babban rigan jikin shi yakeyi a lokacin ga yan uwa da abokan arziki anyi shiru ana sauraren shi har wasu ma,aikatan asibiti din suna wajen.
Ido suka sako muna duk da fadan da yake kwasa har muka karaso wurin muna gaida su shikan saboda masifa baiko amsa gaisuwan namu ba muka shige ciki asibitin don ganin wace mommy tace muba abincin bata wajen.
Mun shiga mun gaida na ciki mun masu ya mai jikin bamu tsaya ba muka fito daga ciki saidai wanan karon baya wajen da muka barshi sai sauran mutane ke wajen.
Suma mun masu sallama muka nufi inda motar take zamu shiga har mun fara shiga aka kiramu dole muka koma sai dai mun samu wata mata mai dan kiba tana bashi hakkuri kada yayi magana.
Jikin shi na bari yana fadin a fito da basket din da muka shiga ciki dashi sauran yan uwa na fadin son Allah yaya kada ai haka mana abin zai zama abin magana ai.
Muna zuwa yace kai ku dubeni da kyau ku koma ku fadawa munafukin uban ku cewa ni Nuhu nace baiyi abincin da zai kawo nan asibitin ba hakama uwar ku din.
Ku fada mata ni Nuhu nace kada akara kawo abinci nan sallon yaudara ko mayar da mutane fakirai ?
Wurin yayi tsit ana sauraren shi yasake fadin nan ma an biyo shine a kasara ko tunda anga bai mutu ba .
Sai wani zare idanuwa yake a kanmu yana kare muna kallo kafin ya sake fadi cikin tsawa maza ku dauki munafki kayan ku ku bace min da gani.
Waitin he talk na tambaya amma don tsoro Fa,iza ta kasa ban amsa gashisu sun duka har kasa suna saurareb shi cikin ladabi ni na kasa kaiwa kasa sai dan bending din da nayi ta bayan su kowa na kallon mu a wurin.
Ashe gaba da gababta shima Alh yana da wani dan iskan yaro wanda bai tsoron shi , shine yace muna kai ku tafi abin ku haba daddy wanan bai dace ba wallahi.
Yanzu idan mu, iyayyen su sukaiwa haka ai ba zakuji dadi ba wallahi su ina ruwan su cikin harkan maganan ku kuma fa gashi sunce gwaggo Addah ce ta bayar a kawo abincin nan.
Kasan kuma sauran yan uwa duk suna kawowa do me ita zakayi wanan batacin a garesu haka yanzu kuma wani magana ya fara bullowa ke nan kuma.
Nikan a lokacin na mikema tsaye ina kallon shi cikin tsana don saura kiris in bayana kaina a gareshi Allah dai ya gyara zancen a wurin.
Kai ku tashi ku tafi kuce an gode ana gaida ita guy din ya fada nikan na juya na fara tafiya shima ya kalli dan nasa kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru ya fara tafiya.
Yana huci har yakai kofa ya juyo yana fadin
Wanan dayan yarinyar da suke tare wacece ita sai matarshi dake gefen shi tace ban san ko yar waye ba a gidan dai take zama saidai naga kamar zuwa takeyi ta koma ko kuma diyan makwabta sune nake gani.
Yace amma fuskanta sai naga kamar nasan shi a wani wuri koda yake dai kamane kawai dai saidai yarinyar da gani bata da kunya naga.
Baba ko hausa bata ji fa wanan yar ance kabilace ita a unguwar suke zama ta shaku da yaran gidan shikan ya fada ya shige dakin da dan uwan nasa yake.
Motar yayi shiru sai Nabila dake shara gudu kafin hauwa tace kungani ko saida nacewa mommy bana son zuwa wurin nan yanzu ga abinda ya biyo baya.
Kikace ko nace nabila ta fada tare da fadin ni wallahi na tsure wanan da akace ko hararanka yayi sai kayi ciwo balle gashi kamar ya cinyemu da ran mu kan fada.
Ina bayan motan tare da Fa,iza kowan mu baiyi magana sai tunanen zuci da mukeyi kai ni wallahi tun farko ban son ko ganin kawu Nuhu a raina tun ina karama hauwa ta sake fada.
Daga bayan motan Fa,iza tayi magana tace wai da yake kiran daddyn mu da mugu shi din meye shiba ace masa mugu ba sai shi zai kira daddy da mugunta.
Kai ku bar zancen shi don Allah wallahi ance ko zancen shi akayi ya sani ko manyan mu suna tsoron shi balle mu.
Me zaiyi babu abinda zaiyi muna riga damun gama dashi ko saidai yaiwa wasu mugunta bamu ba insha Allahu.
Sai suka saka dariya muna shiga gida part din mommy din muka nufa gaba dayan mu ban suka fara mata bayani ta fara salati sai kuka.
Tana fadin wullakacin na yaya har yakai can aini badon shi na bayar da abuncin akaiba don jama,an dake wurin suna jinya ne na bayar.
Ganin da nayi tsayin bai mun yasa na mike nabar part din don yadda nake jin kaina a lokacin.



ANA DARA GA, , , , , , ,

3️⃣5️⃣ BY, , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL KHAFID, , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI GUJE ABINDA ZAI IYA HALAKAKI KAN HAKKI NOVEL DON KUDINE WANAN, , , , , ,


Umma yau na ganshi ido da ido wallahi wanan mutumin lalai mugune mugune na karshe umma yau na fara ganin a yau din kuma ya nuna min koshi waye.
Wa kika gani kika shigo min haka a razane umma wanan Alh daya kashe min mahaifina shina gani asibitin.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login