Showing 117001 words to 120000 words out of 382072 words

Chapter 40 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28325

Farine ba sosai ba dogo mai karfi da da dan gemu ga jajayen idanu maicin mutunci da zarafin mutane ko a gaban kowa.
Yaci muna mutunci ya tozarta mu yau a gaban kowa umma akan abincin da mommy ta aike mu mukai yace mu dawo dashi mu fadawa daddy shi Nuhu yace daddy baiyi abincin da zai aika masa ba.
Fa,izace ta shigo take fadin ana kirana a falon Daddy kallon umma nayi inda take zaune ta kura min ido kafin in mike umma ke fadin.
Ina fatan ba rashin mutunci kikaiwa yayyun mahaifin ki a fitan ku ba da yarbanci babaren data fada shine yasa Faiza dan kallon mu kaina kada nabi bayan Fa,iza din muka fita.
Suna zaune a falon har mommy din muka shigo wuri Fa,iza ta samu ta zauna na duka a gefen ta tare da dukar da kaina a kasa shima daddy din kanshi na kasa yana dan bubuga kafan shi a kasa.
Kafin ya dago yana fadin ungo Sahiba waitin dat man talk at d hospital ?
Nan na fara korawa daddy komai tun shigowan mu asibitin har fitowan mu nakare da fadin that,s all i know daddy.
Ya nisa tare da fadin fine kinyi kokarin fada min komai saidai ku meya sa zaku boye min koda yake ba laifin ku bane laifin uwarkune gata zaune.
Amma ina son ki sani duk da sudin yan uwanki ne na jini saidai a bangaren su yanzun ba haka suka daukeki ba su a wurin su don yanzu Nuhu da yan uwansa sun bata komai a yanzu.
Saidai ina son don Allah ki nisanta yaran nan da shiga harkan wanan mutumin da baida tauhidi a zuciyar shi kada ya taba min yayana don wanan kam bazan kyaleshi ba idan nayi hakkuri akan komai.
Allah sarki mai uwa da uba raye a duniya ya godewa Allah na fada a zuciyana ga Daddy duk abinda Alh yake masa bai ji bacin rai ba, sai yau da yakai ga yayan shi ranshi ya baci haka dasu.
Saidai dama idan yana da wata manufa a kaina don kai abinci yau aka saba kaiwa harshi abinci asibiti idan ya kwanta.
Eh mommy haushin bai samu kashe daddy da sukai niyar yi ranan ba ya komawa dan uwan shi shine yake jiwa haushi a yanzu.
What daddy ya fada karfi.
Nace a rude yes dad they atterm to murder you on that day.
How do you know all dis ?
Ya tambaya yana tsure ni da idanu hannu na ware tare da fadin i dont know .
Amma dai haka din ne daddy i know haka din ne sunyi plain su kashe ka a ranan sai ya juya masu akan kanin shi yayi arziki bai mutu ba.
Ke kinji hjy kinji wanan maganan kuma da yarinyar nan ke fada yanzu na sake fadin yes dad abinda suka shirya ma ke nan.
Innalillahi suke maimaitawa a lokaci daya mommy na fadin dama akan ka Alh aikai wanan aiken kai ku bar saurin yarda da orin zancen nan balle a bakin yarinya karama irin Sahiba.
Ya dago kai ya dan kura min ido na dan lokaci na wani huro iska a bakina tare da hade yatsun hannuna a wuri daya kamar ina wasa dasu suna dan bada sauti kas kas.
Tashi kije Sahiba daddy ya fada ban jira komai ba na mike na fita daga dakin daddy ya kallo sauran yaran dake wuein yana sauke numfashi tare da fadin.
Ku saurari abinda zan fada maku yanzu kuji kada inji wanan zancen ko a cikin gidan nan balle wani waje da fatan kunji abinda na fada suka amsa da eh daddy.
Suka mike suka fice daga dakin suna jin wani iri a zuciyoyin su , don haka ba wanda ya iya magana a lokacin ga baki dayan su.
Shiru dakin yayi na dan lokaci kafin hauwa tace waiko yarinyar nan dai yar securo ce ko me dai don nifa abin Sahiba ya fara ban tsoro.
Meye na tsoro a nan kawai dai wani bauwane na daban Allah yai mata kila ba,a sani ba amma ai zamu gane hakan udan zancen cikin anty ya fito gaskiya lalai Sahiba watace na daban a cikin mu.
Tsoro nake ji idan ba yar wani cult bane fa don kusan wanan haline na diyan kabilun nan su ba su daukeshi a komai ba kamar ma ado yake a garesu.
Don Allah hauwa ki bar wanan zancen don ni kin fara ban tsoro akan yarinyar nan wallahi wanan maganan da kikeyi ya fara firgitani da ita yanzu.
Kai don Allah ku bari da muguwace ai a kaina zata fara nunawa ni dake tare da ita akoda yaushe kuma ai da yar cult ce da ba zatayi ibada haka ba don sahiba badai a tuna mata lokacin sallah ba dai.
Shine kuma fa gaskya ba cult takeyi ba kawai dai wata kila iskokai ne a kanta suke mata hakan .

Bamu san ya daddy ya kwashe da mutanen sa ba saidai abubuwa da suke tafiya a boye don zancen manya bai shafemu ba.
Karshe dai saida aka fitar da Alh gyade kasan wajen suka kwashe watani kusan biyu suka dawo dashi hakana don ha samu kariya sosai a jikin shi an kuma kasa shawo matsalan jikin nasa.
Alokacin kumanecikin jikin Anty data shagala da bata da ciki yafito fili a jikin ta wanda da farko ta dauka girman tubine hakan sai ranan Asabe ke fadin hjy anyi nauyi haka ashe ?
Saidai wanan karon abin yazo maki da sauki bakya amai ko wani laulauyi mai bada wahala har tayi murmushi zata tafi sai kuma taja ta tsaya a wurin.
Ta juyo ta tsaya a ya tsune tana fadin wai me kike fadine haka Asabe yaushe har na fara wanan wasan dake ko wani ya aikoki ki zolayeni da wanan zancen.
Zolaya kuma hjy ?
Haba ni na isa nayi wanan wasan haka dake ko kuma wani ya aikoni in muzanta maki akan me ?
Sam ban san bakya son asan da zancen cikin nan bane a cikin gidan nan aida ban fada ba wallahi amma kiyi hakkuri hakan ba zai sake faruwa ba insha Allahu.
Ta wuce fuuu zuwa part din ta kwanciya tayi saman kujera ta shiga tunane kafin a wani irin shureta saida ta dan sake ihu kadan tana mikewa zaune a cikin mamaki.
Kara jin wani motsi irin wanda masu ciki keji a cikin cikin su lokacin da yaro yake a ciki kwance taji.
What ta fada tana mikewa tsaye kafin kuma ya koma wani gefen ya lai mata shuri again saida ta cije baki takai zaune kuma tana kiran sunan Allah.
Yau me take shirin ji kodai wai mutanen nan mayu ne Asabe da wanan yarinyar Sahiba data fara kira mata ciki a yanzu da take kokarin maintening din kanta.
Kai ina mikewa tayi ta fara kai hannu a saman cikin ta tana jin abin cikin cikin nata yana motsawa a hankali alaman yana canza gurbi sakamakon dan taba cikin da tayi a lokacin.
How come ciki har ya girma haka a jikin ta har da na iya motsawa haka amma bata farga da cewa cikine a tare da ita ba a jikin ta .
Ita duk da tana malam asibiti bata yarda dacewa mace zata iya nomal al,adanta ba kuma tare da ciki mai rai a jikin ta haka gaskiya.
Kai ina ta fada tayi waje zuwa kofan daddy ta samu dakin a rufe bata yarda baya ciki ba saida ta murda kofan tajishi a rufe.
Bata samu natsuwa ba harsai lokacin da daddy ya dawo suna falon da mommy yana cin abinci ta shigo da sallama kasa kasa .
Da mamaki suka amsa mata ba bata lokaci ta fara fadi gaskiya Alh ka dauko muna masifa a gidan nan ka hadamu dashi.
Subbahanallahi ya fada yana dago kai eh masifa mana don Sahiba tana kokarin zama muna kashin bakin tukiya a cikin gidan nan.
Tun ranan datake fadin wai ciki ne a jikina ban dauki zancen ta gaskiya ba sai yau din nan da Asabe ta kara furta min hakan kuma na tabbatar abin nason ya zama min gaskiya a yanzu.
Akan me zatayi min wanan furcin ita ta fini sanin cikine ko bayana take nema ta gani don ka auri uwar ta zauna makwafina.
Acikon kunan rai ya dakawa anty tsawa yana fadin wai karima kinyi haukana ko kuwa ki san abinda kike fadi kan mutanen nan a gidan nan.
Kamar yadda kuke zamana a cikin gidan nan haka Sahiba da uwarsu suke zamana a cikin wanan gidan .
Meyasa ke baki da fahinta ne akan abu ko yadda nakewa yarinyar nan idan ke mai kulane zaki fahinci suna da muhunmanci a wajena sosai.
Ga yadda na fahinta a yanzu har kinfi Addah cin moriyan yarinyar nan a gidan nan don da bakin ki ke fada min yadda yaran ki ke jin dadun ta dake kanki a zaman su gidan nan tare damu.
Amma da dan abu ya hadaki dasu yadda kike nuna rashin hakkuri kan diyan cikina haka kike kokarin nunawa gun sahiba a yanzu.
Zancen ciki a jikin ki har wani zance ne da zai kawo tashin hankali koda baki da aure balle kina dashi.
A nawa ganin ai kamar taimakon ki tayi ta fargar dake hakan tundake likitace kin kasa fahintar hakan idan kuma baki yarda ba sai kije asibiti ki bincika kiji gaakiyan maganan.
Idan suna da muhinmanci a gareka ke nan mu a yanzu bamu dashi ke nan a wajem ka su sunfimu kima da daraja ke nan ta fada.
Haba hjy karima ki fahinci me Alh ke nufi mana kada bacin rai ya sa idon ki ya makance ga hakan don Allah.
Zaki iya fadan haka ai tunda da hadin bakin ki ake komai ikon Allah komai kamar yaya mommy ta tambaye ta cikin mamaki.
Ai tare da yaran ki take ko wani lokaci waya sani ko wani abin kikasa tayi min yanzu ta fada tana wani cicikaka da kada jiki.
Au tanan kuma kika bullowa yarinyar nan amma kuma ai naga kinfi kusa da su don kema kina aiketa kina sakata aiki da sauran abubuwa sai ni ince me yanzu a kanta kuma ?
Ya isa haka Alh ya fada a cikin tsawa yana fadin duk wace ba zata tsaya ta tayani rokanwa yarinyar nan Allah saukin wanan laluran ba don Allah ta rabu dani da zancen banza a gidan nan.
Yarinya tana fama da lalura haka mai karfi har zaku zauna kuna sa,insa aikanta don ba wace ta haifeta a cikin ku ko ?
Da yau zaku tona cikin uwarta kuji yadda take ji da halin da yarta ke ciki na wanan laluran da baku iya daukan hakan a zuciyar ku.
Wanan ba karamin abu bane keson ya bullowa yarinyar nan don ko dubanta kayi ka kalli idunun sahiba kai kasan Allah yayi ajiyan shi a wurin.
Wallahi Allah hakane Alh uwar kan na cikin wani hali a yanzu da abin ke son yayiwa yarinyar nan yawa sosai aiko kan wanan furcin da tayi maki nakai karanta take mata fada wallahi a gabana sai cewa ita ita yaushe ta furta maki hakan ?
Yaushe ta furta min hakan ta tambayi mommy data fadin hakan tace wallahi Allah haka ta fada tace me kikai mata da zatayi maki rashin kunya har ta furta hakan a kanki.
Kin gani wanan wani bakon lamari ne kila ya shigeta bamu sani ba kuma don haka sai an kai zuciya nesa a yanzu don ina ga abubuwan zagayota sukeyi ba zaune suke a cikin jikin ta ba ai
Inma ance zaune suke ba a mussu da hakan mommy ta fada daga gefen shi jikin anty yayi sanyi takai zaune karshe sukai ta zancen dai har ana dan dariya a kanta.
Sun fito ne Anty dakin mu tayo direct ta samu muna cin abinci har da fatiman ta da Amira sai Fa,iza dake kallo a gefe kwance.
Gaisawa suke da umma na dago ina fadin Anty barka da yamma tace ban karba tunda kin min baki ya bini na dan dago kai a cikin mamaki ina kallon ta.
Tace eh bakin ne ya kamani Sahiba har nayi ciki a lokacin da ban shirya zuwan shi ba gareni yanzu.
Umma tayi saurin fadin haba aiba aiwa Allah wayau yar uwa ubangiji ya rabaku lafiya niko cewa nayi da ita ni anty ?
Ta kawar da zancen tana fadin yaushe wa yan nan suka shigo tana nuna yaran ta dake kallonta suna dariya nan a kwance na barsu suna kallo fa na fita.
Ai kuwa suna nan tun dazun umma ta bata amsa muna nan tare dasu yanzu yarsu ta matsa suci abinci suka zauna ci.
Ban san meke damun yaran nan da basa son cin abinci ba na gedigedi de wory dem na fada a cikin rashin kulawa ina fadin give dem local medicine for gedi gedi.
Tace me i no wan dat local medicine at all, but i will take dem to hospital nayi dan murmushi ba tare da nayi magana ba.
Daddy ya kara tambayan mommy abinda ya faru mommy din ta fada mai komai shiru daddy yayi na dan lokaci.
Kafin yace watau dai zancen yarinyar nan da gaske ne dai idan ta fadi magana ke nan kuma hakan na nufin da gaske ke nan nisu Alh Nuhu sukai niyar halakawa ke nan ashe ?
Allah kaga nufin wa yan nan yan uwan nawa ya Allah na rokeka kada ka taba basu daman da zasuci galaba a kaina har abada.
Hjy dake gefen shine ta amsa da amin tana ajiyan zuciya tare da fadin na dade da sanin yaya Nuhu yana da wani kudiri akan ka koma me suke nufi insha Allahu Allah bai basu sa,a a kaina.
Rayuwa ke nan yau da dadi gobe babu amma haka muke zaune a gidan babu ne bamu rasa ba a gidan don komai muka nema akwaishi gaskiya.
Haka yasa rayuwa ya canza muna a cikin dan lokaci ba zaka ce nice sahiban geto ba wace tasha gwagwalmayan duniyan lagos.
Zama da yan matan mommy da karatun da nake shiga yan Arewa a yanzu ya kawo min ci gaba sosai a rayuwa don yanzu idona ya bude kitsuwa yazo min wanda kowa na mamakin hakan ga dan zaman mu a arewa din nan kuma gidan daddy din.
Haka ya kawo min farin jini saidai tsiwana da izzana wanda tun farko idan baki manta ba na fada maki ina dasu talauci dai ya rufe hakan gareni.
Wanan matsalan tsiwan shine ya dan rage min farin jini a gurin mutanen don suna daukan hakan da don ina da kyau nake daukan kai a garesy haka nake wullakanci don azaton su wullakancine hakan basu san halin nawa bane haka bana shiga harkan kowa yasa sai mutane su dinga shareni.
Wanda niko sai hakan yayi min dadi don ban faye son yawan magana ba saidai idan na tashi ko waye kai kai tsaye zan fada ma gaskiya.
Haka zalika na mayar da hankalina ga karatu sosai don ban son a wuce ni ga ko wani famni na karatun boko dana mahammadiya ina mayar da hankali a garesu.
Gidan ya Abubakar tun farkon zuwan mu da muka tafi tayi min wullakanci har aka samu rikici tsakanin su ban kara taka gidan ba kamar yadda na fada a baya.
Saidai abinda na lura shine su kansu yan uwanshi ba son zuwa gidan sukeyi ba saidai saboda shi da mommy suke daurewa su tafi.
Sai gashi yau da kansa ya shigo gidan dama yasha tambayan wai ina nan kuwa indan yazo baya ganina a gida.
Sai ace ina school ko ina barci wanan yasa bamu haduwa dashi don haka bai san cewa Sahiban da yasani a da ba ita bace yanzu.
Yau a part din mommy ya rutsa dani jin muryan shi yasa muka fito muna gaida shi kusan nida Fa,izace karshen fitowa falon daga dakin.
Wando bakine a jikina sai wata riga pink dana hada da rigar mai dan hannu dabai karasa sauka ba sai gyale baki dana rufe kaina dashi.
Daga can bayan su na dan tsaya na dafa kujera ina fadin brother u are wellcome ya hanya har ya kawar da kanshi sai kuma ya juyo da sauri yana amsawa tare da jin wani irin faduwan gaba yadda na koma masa ga gani lokaci guda haka yake fadin har lokacin kallon mamaki yake min.
Sahiba kece wai ?
Long time no see u , nace ina nan broda ina dan dariya tare da noke kai zan juya ya sake fadin daddy ya fada min yasama maki addimition state university ko ?
Nace eh na fara zuwa wancan satin any whare zanga mommy don zaku koma lagos da zama na dan lokaci jin hakan yasa na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login