Showing 156001 words to 159000 words out of 382072 words
Da sauri na dauki waya na kira umma muka kara gaisawa take tambayan ko zamu tasone nan dai na bata labarin abinda ya faru garin ta dafe kirji tana fadin mun godewa Allah bai shafemu ba ashe.
A karshe sai cewa tayi dani sai ki shirya kije gida ke nan ki gaidasu don kada inja zancen nace to umma idan naje zan kiraki ai.
Barci na kwanta nayi a dakin na kuma samu nayi sosai don sai bayan karfe biyu na tashi nayi sallah jin fita daga wajen wurin nayi na dan yafa gyalena na fita.
Wurin shuke shuke na hango da farararen kujeru na nufi wajen hankalinane ya dauke a wayana dana zauna ina karanta sokonni.
Naji ance dani a bayana hello na dan dago da sauri don ganin waye Adnan ne a tsaye ya saka hannayen shi duk biyu cikin aljihun wandon shi.
Ashe kema kina nan ke nan ya fada na fito yanzu ne ina kallon garin garin yana da dadin yanayi sosai zanso na dan shiga garin na zagaya sai dai ban san inda zan tafi bane.
Muje mu taka kaga garin na bashi amsa muka fito daga cikin hotel din muna takawa kawai sai na tare taxis yaji na fadi sunan unguwa nace a kaimu as a drop ina hausa da mai Napep din.
Yace sai dubu biyu nace zuwa da dawowa 1500 idan zaka kaimu Adanan ya kura min ido har muka gama magana da mai a daidaita din muka shiga naji yace so you can speak that language abi nayi murmushi.
Wani shago na hango daga nisa nace my adaidaita din ya kaimu can muka fito na shiga na sayowa Fa,iza fatima da Amira kaya kala bibiyu da kayan kamshi.
Muna barin wurin na ciro memo na rubuta sunan kowa don haka kawai naji hankalina bai kwanta da in shiga gidan daddy din ba don ban san manufar su akan mu ba.
Da kwatance har muka kai gidan daddy din gidan nan da kyaushi yarda na barshi a baya daga dan nisa kadan muka tsaya na sauka na nufi get din gidan na kwankwasa maigadin ya leko ba malam Adamun dana sani bane a baya wanan din.
Mun gaisa nake tambayan shi don Allah ko Faiza tana gida Amira yace suna ciki nace ka karbi wanan sakon ka basu ina gaidasu ina saurine ba zan samu shiga ba.
Na bashi dubu biyu sabbi nace ka karbi wanan ka rike ina gaidasu na juya yace boyar Allah ince waye idan an tambayeni nace kace Sahibace daga lagos.
Muka juya muka wuce nace mubi ta gidan ya Abubakar gidan yaso bace min don sauyin da akai masa amma muma duk da haka na sheda gida.
Kofan get din gidan a bude yake na ja gyalen kaina na rufe fuskana dashi ganin wata mota zata fito a gidan shima bin mu yayi da kallo ganin muna kallon gidan nasa ya fito ya nufi gidan su su gaisa da mommy da daddy.
Nake cewa Adnan gidan blood brother dinane wanan gashi nan ma zai fito na fada shine kallon daya kamamu muna masa din.
A can gida kuma daya isa ya samu duk ilahirin gidan a waje har iyayyen su mata suna mayar da fadi ya shigo da motan shi yai parking ya fito.
Sin kasa hakkuri Fa,iza da hauwa da Fatima suka tako har inda yake suna fadin wallahi yaya Sahibace tazo gidan nan taba da sakon nan akawo cikin gida ba zata samu shiga ba ita.
Kai nifa na fada maku kila fatalwane ko aljannun ta sukayi shige da ita suke son su rudemu kawai.
Aljannun kuma mommy Sahiba dince dai tazo koni na ganta jiya da dare wurin comferences din nan da akayi har aka dasa bom a wurin.
Saidai kawai a yanzu dahiba ba Sahiban da muka sani bane a baya gaskiya koni ta bace min kama dai nayi amfani dashi na gano cewa itace sai yanzu kuma da naji wanan din na kara tabbatar da hakan ita dai din nagani jiya ashe.
Cabdijam Nabila ta fada daga inda take tsaye ta rike kugunta da hanayebta biyu tace hala yaya ta zama rikakkan bariki ne yanzu ko yasa har ka kasa gane ta.
Dama na fada ai wallahi yar barikice sosai bata da kunya ko tsoro ko kadan wallahi daganin Sahiba irin yan iskan lagos din nan ne dama.
Ke ja can da maganan banza kina zargin yar uwan ki ga banza to bari kiji indai sahibace a yanzu duk ta fiku aji da sanin duniya don banga wani abin asha a wurin ta.
Mamaki na daya yanzu shine yadda akayi sahiba ta samu wanan matsayin haka babba na sakatariyar wanan mutumin da suke aiki dashi dana gamsu jiya don ba karamin matashi bane a cikin kasan nan shi .
Ita Sahiba din mommy ta tambayeshi a cikin mamaki yace kwarai mommy wallahi sahiba a wani matsayi take yanzu dako mu maza sai anyi da kyar zamu kai hakan .
Aikuwa dai don ga alama nan ya nuna hakan cikin wanan sakon jifa wanan uban kayan masu tsada data aikowa yaran nan yanzu dashi.
Kada kayi mamakin hakan tunda mace ne ita kuma ko banza dama sahiba mace ce sosai idan ta samu wuri wahalane dama ya boye siffanta na kwarai.
Kai haba haba mommy bai kamata aji irin wanan kalamin a bakin ki ba yanzu don Allah a kan yaran nan don kusan daya take damu ai a wurin ki.
Yana fadin haka yasa kai ya shige cikin gidan ya barsu nan tsaye wajen kafin Nabila tace dashi mu kara ganin kayan Fa,iza tana karban ledan a hannun ta.
Mommu kan ta juya ta shiga ciki ta samu danta da take nema ruwa a jallo akan maganan shi da matar shi da aka sake samun matsala akan fitinan su.
A waje muka samesu tsaye suna neman mu don an duba dakunan mu bamu ciki sai gamu mai adaidaita ya sauke mu Adnan ne ya biyashi kudi yana godiya ya wuce.
Mr Jimone ya tare da fadin ina muka fito ba tare da sanar da mutane zamu fita ba hankalin mutane ya tashi ga rashin ganin mu.
Kai tsaye nace dashi sorry sir na tafi wurin yan uwana ne da mr Adnan dayace bai san gari ba lokacin kuma ba kowa a wajen da zamu fadawa zamu fita.
Cikin mamaki yake kallona kafin yace yan uwa ke kina da yan uwane a nan kaduna din ya sake tambayana a cikkn mamaki yana kallona.
Kafin inyi magana Felix ne yace ai ita din yar nan garin ce mahaifiyartace ta fada min haka jiya da naje daukata gidan su har tana fadin sai ta kwana a gidan su idan ba matsala.
Shiru yayi ya juya cikin bacin rai yana fadin don't repeat dis mess again kun tayarwa mutane da hankalin kun kuma san garin ba lafiya ana ta fada a kafafen labarai tun daren jiya.
Lokacin da muka juya muka hango ogan mu tafe wurin da muke yemisi tana bayan shi tana mashi surutu ya iso mr Jimo ke fadin sir wai ashe ita din yar wanan garin ce dama.
Really kawai ya fada ya nufi wurin motar shi kai tsaye yana fadin zai fita ba zai dade ba zai dawo budan bakin yemisi sai cewa tayi sir can i follow you ?
Bai ko kallota ba ya shiga mota ya fita mu kuma muka shiga cikin hotel din kowa ya nufi dakin shi don yin laluran shi.
Sallah nayi na fito sai ga Felix ya turo sako akan mu shirya zamu wuce zuwa jos mu kwana a can daga jos zamu wuce lagos gobe da safe akwai jirgin lagos a can.
Haka muka shirya a gurguje muka dauki hanyar jos da yamman nan wai ashe mahaifiyar ogan namu yar jos ce ita dama saidai tana waje a lokacin.
Sai mahaifanta kawai ke zaune jos a yanzu wanan tafiya kan gaskiya an dai yishine ba a cikin dadin rai bakan don tafiyan yazo muna da akasi kuma bamu ba duk wanda yai tafiyan alokacin ya samu matsala arewa ke nan abinda suka sabayi a kaaashen yare ayi lafiya a watse lafiya an kawo arewa an watse baram baram kowa yana neman mafita a lokaci ya tsere.
Mun isa jos ana sallah magariba kai tsaye wani gida naga mun nufa mun samu taro sosai a gidan wajen masu gidan da alokacin bamu iya tantance su.
Mu mata cikin gida aka kaimu direct mazan bamu san isalin su ba a waje na daiji ana kwalawa wata kira da mallam gasu sha,aban din sun iso a cikin hausa.
Daga cikin dakin akace au har sun karaso sannun ku da zuwa wace ta fito din tsohuwace sosai ta tsufa amma gata ya hana ta duka irin na tsufi.
Ganin mu, mu kadai yasa taja ta tsaya tana fadin ja,irin shi yana ina shi kuka barshi wa yan nan kan yare ne aida gani dangi shine na oduduwa basa jin hausa.
To shiga dai dasu ciki kafin ya shigo tsohuwan ta fada sai akace mu shigo ciki da harshen turanci muka shiga jikan na tsaya na kowane takalma daga kofa ban yarda na zauna ba saidai na gaida ita a cikin ladabi tana amsa min da yarbanci.
Mallam kodai sha,aban ya kawo maki kishiyane ki gani dama ai daya kyauta irin wanan yar haka mai zubi irin nasa ai sai su dinga haifo maku zabaya.
Duk suna dauka bama jin hausa ne ganin da nayi lokacin sallah na shigewa yasa nace dasu mama don Allah zanyi alwala nayi sallah.
Lah ashe yarnan tana jin hausa ke nan kika barmu muna zuba haka a gaban ku zo muje na kaiki ta fada tana mikewa duk suka bimu da kallo.
Na kwabe gyalena na nufi inda tabi ta nuna min ban dakin nayi alwala na fito daidai lokacin ya shigo falon ya kaure da hayaniya dashi jakkana na bude na fito da hijab dina har kasa na koma can gefe zan tayar da sallah.
Da sauri suke salati suna cewa don Allah zo ga daki nan ku shiga kiyi sallah mana kyayi sallah a nan kuma yar nan na bita zuwa ciki dakin ban kara fitowa ba shida kanshi ya turo yemisi ciki ta sameni na idar ina nuke kayan sallah.
Dakine mai kyau da komai na jin dadin rayuwan dan adam a cikin sa ga shimfida na alfarma anyiwa gadon dakin sai kamshi ke tashi tako ina a cikin dakin har falon nasu.
Babban falone da zai iya cin baki ko mutum nawane kwa yaji saitin kujeru na alfarma irin na kasan waje din nan da kashi katon photunan sune iyalan gidan tsaye an aje a jikin bango kamar wa yanda ke ciki zasu fito suyi magana.
Dan zaman da nayi a falon ne na kurawa photon wata mace ido da mijin ta dake cikin kaya saki irin na masu kudin yarbawa din nan nada can shekarun da suka wuce baya har wanan lokacin ma wasu na sakashi .
Babu tamtama sune iyayyen ogan mu da Felix ya ban labarin su ranan ban kai karshen tunane na ba naji sallaman matar ta shigo ga wata biye a bayan ta da katon tire dauke da abinci cikin sa tana fadin yata ga abinci ku tashi kuci kinji kada barci ya dauke ku.
Mun gode mama na fada ina mikewa zaune abincine mai rai da lafiya aka shirya muna munci mun sha kafin mu kwanta barci .
Duk da banda sabo amma na dan sake da matar da naji kowa na gidan na kira da hjy Laraba na dan sake jiki da ita muka dan taba hiran abinda ya faru a kaduna din damu.
Yemisi na kwance tayi waya tayi charting don na kula fushi take dani tun abinda ya faru tsakanin mu da safe nima na shareta.
Bayan hjy ta fitane na shiga ban daki na watsa ruwa dana fito nayi duk wani shirin barcina tare da addua na haye gado na kunna kira,a na barta zaune ta mike kafa saman gado tana zuba yare.
Washegari koda akazo tayar dani sun samu har na idar da sallah ina zaune ina addua ta juya tana fadi au ashe kin tashi ma.
Bayan na idar wanka nayi na shirya don nasan tafiyan safe zamuyi don haka ina idar sallah nayi wanka na shirya na koma bakin gado na zauna.
Ina turawa Ammar sako a waya a lokacin yemisi ta falka daga barci ta dan kalleni taja tsuki tana gyara kwanciya.
Shidda da tabi nayi sai ga kira a wayana cewa mu shirya gasu nan zuwa su dauke mu zamu wuce airport ke nan a lokacin tana jin haka ta wani zabura ta sauko daga gadon ni kan jakkana na dauka na nufi falin gidan a nan na samu hjy din tsohuwar gidan zaune tana ba yan aiki umurni don su samu suyi muna abin karyawa kafin mu tafi.
Gaba dayan su sukai sallama suka shigo gidan ana karbawa suka zube a gabab tsohuwan suna kwasan gaisuwa a wurin ta yana shigowa ya dubeni a inda nake zaune yana fadin ina yemisi din mu tafi mana.
Mikewa bayi aiko ya dinga fada sosai kan ba zasu kara tafiya da ita ba daga ranan don baiga amfanin zuwa da ita bama.
Badai tafiyan ke nan ba ya kalli agogo yana fadin hjy zamu makara a cikin hausa jirgi bakwai daidai zai tashi kinga in mun tsaya zamu makara mikewa tayi tana fadin haka ba zai yuyu ba ka kawo min kawata har gida kace ta tafi haka bata karya ba kuma.
Kitchen din ta nufa can sai gasu tare da mama Laraba da ledojin take away a hannun su suka mika ma kowa nasa nawa kan ko ba a ce ba yafi na kowa yawa a ciki muka karba muna godiya tana fadin kwa karya a jirgin ai.
Ta miko min wani warmer sabo yana kyali tana fafin karbi wanan ki rikawa ogan nasa kinji wanan in kunbi nasa baya cin abinci.
Mukai masu sallama muka fito a gurguje yana can dan nesa kadan da tsohuwar suna magana mama Laraba kamar yadda ya kira ta tasamesu a wurin har mun shiga mota mun zauna ta dangwara min wani leda a jikina na dago kai a cikin damuwa na kara mata godiya.
Mun samu jirgi da kyat da fudun tsiya da sukayi ba ai wani tsayawa ba jirgin namu ya tashi zuwa lagos .
Allah ya taimakeni a can baya na samu seat na zauna na sake saidai har lokacin ban wani sake jiki ko in duba abinda ke cikin leda ba.
Allah ya sauke mu lafiya mun sauka mu mata suka fara saukewa gidajen mu nice ta farko yaran Abdulhamid da Amar dake kwallo a waje suka sheko suka tareni.
Naji mamakin ganin ana sauke buhun dankalin turawa da doya wani na kulan dana bari nasa a mota da nake kaya sai ga yara nagani dashi sin shigo sun bayar akawo min.
Bayan yaran sun fitane muka zube a falo da umma da Amar ina basu labarin tafiya da abinda ya faru har hira da yemisi duk saida naba umma labarin komai.
Amar ne ya jawo kulan yana tambayana meke cikin sa nake fada masu yadda akayi har kulan yazo gareni lokacin kuma muka bude babu komai a cikin sa sai sayayyen kaji da dan irish da manyan suyan kwai a cikin sa kajin daine masu yawa sosai saida kulan yacika duk girmansa kuwa.
Mikewa nayi zuwa dakina daga nan ban fito ba na kwanta sai barci barci sosai nayi a ranan ban tashi ba sai bayan karfe uku da kwata na falka ma dubi lokaci.
Aida sauri na mike zuwa bandaki na dauro alwala na fito sallah nayi kafin in fara jin wani irin yunwa na ziyarana lokacin.
Falon na fito wanan abinci na sama din da alama basu girka komai naciba da rana don haka shina dauka nayi warming din shi naci nima.
Bayan ya gama sauraren mahaifiyar shine yaji tayi shiru ya kwantar da murya yana fadin naji hjy zan tafi amma ki sani wallahi idan naje suka zageki ko daddy aurena da Nazifa ya mutu ke nan har abada.
Da sauri hjy ta dago kai ta kalleshi yace kwarai mommy don haka tunda dai ba fada mukayi ba indai har tana sona har yanzu ku bari ta dawo dakinta da kanta yafi.
Mommy tasan kwanan wasan don dai sai sun nemi suja masa rai zasu iya zagan masa mahaifan sa a gaban shi tundai yayan nata dayafi kowa hawa a lokacin.
Budan bakin mommy din sai cewa tayi idan dai hakane kada kaje a bata goma daya bai gyaru ba abinda kawai zakace dasu ke nan.
Ta dawo dakin ta tunda ba fada kukayi ba shike nan don dai nasan sai yaya yayi masifan hakan don kai yake son gani yacima mutunci son ransa.
Da