Showing 222001 words to 225000 words out of 382072 words

Chapter 75 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28432

A can ko yar aikin tane take fadin hjy tunda kinji abinda ya fada gara ki sameshi ki bashi hakkuri son ba,a hakan da kikayi din .
Kamar kinci masa fuskane fa ga mahaifiyar shi a tsaye kike jefawa yan uwan shi wanan kalamin haka kiyi hakkuru ki bisa daki ki bashi hakkuri zai fi.
Wani irin kallo ta watsa mata kafin ta kawar da kanta takai zaune bata hakkura ba dai ta sake fadin hjy yi hakkuri ki sameshi a dakin shi don Allah.
Idan namiji ya fadi hakan yana nufin haka har cikin ranshi ne mikewa tayi zubur ba tare data kalli matar ba ta nufi dakin shi.
Agajiye na dawo gida bayan wucewan ogan mu na zauna ina cin abinci ina ba umma labarin zuwan shi da abinda ya fada game dani.
Yaushe zai koma ai ya tafi ko ba kasan nan dama yazo ba kawai ya ratso yaga aikin mune dukan kofan da akeyi ne a lokacin ya dakatar damu duka.
Ammar ne ya mike don hankalin shi na kallon ball da yakeyi ga kuma littafi a gaban shi nasan ko nayi mai magana hankalinshi zai kasu biyune a lokacin yasa na kyale don nasan da an gama ball din zaiyi abinda ke gaban shi.
Yana bude kofan ya Abubakar ne tare da yaran shi a kofan da sauri ya kara ja baya daga kofa yana basu hanyan shigowa ciki.
Nima dai da mamaki nake kallon shi daga inda nake zaune umma ne ta samu bakin fadin a, a yau da baki kake muna tafe ashe ?
Yayi murmushi yana kaiwa zaune tare da dora yaran saman jikin shi ya fara gaida umma tana tambayan shi ko lafiya ?
Ya dan dago yana murmushin dole tare da fadin bana jin dadin jikina wallahu mama shine kuma kafito hakan yace wallahi umma.
Inda nake ya kalla yana fadin Sahiba ko zan samu abu mara nauyi in ci yanzu ?
Umma ke fadin tashi maza ki duba a samu abinda akai masa yaci na mike zuwa kitchen din na dan tsaya ina duban kayan dake kitchen din kafin na dora ruwa saman gas.
Abincin mai sauki nayu mai hade da kunun gyada na kawo mai a dinning da kyar ya dago zuwa dinning din tare da yaran da nake satan kallo yan mata su duka biyun .
Ba laifi gaskiya yaran kama da yan uwa sukeyi suma sai dai na kasa tuna fuskan Nazifa balle na tantance fuskokin nasu kowa suka biyo ga kama.
Muryan shi naji yana fadib kizi ki dauke su a nan zan barsu in zan tafi da sauri na juyo ina kallon shi da mamaki umma sai cewa tayi lafiya ko modibbo ?
Dan murmushi ya sauke kafin yace lafiya mama nakawo su nan ne kawai dai ya fada sai ya mayar da hankalin shi wurin cin abincin dake gaban shi faten wake yaji kayan hadi a cikin sa dama mun jika wake kamar yadda mukan jika shi yayi awani idan zamu dafa saboda saukin dahuwa a saukake.
Da alama yaji dadin dahuwab sosai don idan kin jiki yafi dadi a wurin ci da daukan kayan hadi bai kara magana ba saida ya gama.
Ya dawo saman kujera ya zauna yana fadin mama a nan zan bar yaran nan su kwana biyu tare daku don nasan babu wanda zaisan suna gidan nan.
Meke faruwa umma ta sake tambayan shi nan ya fara jero mata irin cin mutuncin nazifa dabai tsaya a gareshi ta hada har mommy da yan uwan shi.
Nima dai sam banji dadin hakan ba gaskiya don nariga da nasan ko waye Nazifa akan kujeran ta taci min mutunci a baya don haka ba zan manta da ita ba a rayuwana gaskiya.
Sai kuma yaran suka ban tausayi don laifin uwarsune yanzu yake kokarin shafan su ke nan saidai naji umma na bashi baki yana fadin yana son ya horata ne umma tayi hakkuri don Allah.
Zai tafine yabada kudi wai a saya masu abin bukatan su sai idan ya dawo da sauri nace no ka barshi kawai yaya zan saya masu komai insha Allahu.
Har yakai bakin kofa nace kira sunan shi yaja ya tsaya wuri daya ba tare daya juyo ba nace ya Abubakar kana ganin kawo yaran nan gidan nan yin hakan ba zai jawo wani matsala daga baya ba ?
Saida yaji nayi shiru ya juyo yana fadin Sahiba shin akwai wanda yasan kuna garin nan ne bayan ni ?
Kai na girgiza mashi yace OKey ta yaya kike zaton wani zaiyi tsamanin a nan suke ga gobe zanyi tafiya nima don haka kada kiji komai a ranki saidai idan zasu damekune a nan din in canza masu wani wuri.
Kafin inyi magana umma tace haba dai koba diyan ka bane modibbo ai zamu rike ma balle diyan cikin kane wa yan nan kada kaji komai a kan zaman su a nan din.
Yace yagode yasa kai ya fita muryan yarinyar ne yayi sanadiyar juyowan mu ga barin kallo mamakin da muke mashi na ya tafi ya barmu da yaran a gidan take fadin.
Ina daddy mu ta fada kamar bata magana da farko irin haka idan kaganta don karantan su ita dai karaman har lokacin tana jikin umma a lafe da alama bata da rikici.
Fuska kumshe da murmushi nace daddy yaje ya sayo maku alawa yanzun nan zai dawo na fada ina mika mata hannu tazo wurina.
Kin zuwa tayi ta makale a jikin kujeran daya tashi a kai tana wasa da hannayen ta mikewa nayi daga inda nake na shiga dakin umma na dauko masu biscuit da sweet din amar masu dadi na kawo masu.
Abin mamaki sai naga ta fisga daga hannuna kamar mai fushi ko fada na mikawa dayan kafin in juyo gareta ina fadin ba zaki ce min thank you ba na karbe abina yanzu.
Kamar ba zatace ba ganin na mika mata hannu zan karba sai naji ta fada ciki ciki nace good girl ina shafan kanta a hankali.
Na koma na zauna a inda ya tashi din ina lumshe idanuna a hankali nasan yaran ba a koya masu komai daya shafi tarbiya a addinan ce.
Don shi kanshi godiya wata kallamace da yakamata a fara koyawa yaroshi a don yanada ma,anan da ke nuna yaro yana da tarbiya don yana mutunta wanda yayi maka hidiman ka gode mai.
Bayan ta gama shan alawan taso ta tayar muna da rikici na mata wanka na goyata a lokacin maniya ta shigo wurin umma.
Ganin yaran take fadin a anan babasu ya barsu ashe don naga zuwan su ina ciki kuma naji fitan shi kai yaran masha Allah kudai zurian ku suna da kyau.
Ina kyau a nan na fada ina juyo mata yar dake goye a bayana don yarinyar uwarta ta biyo yanzu na gane hakan danayi nazarin su da kyau.
Ta zauna tana mikawa yar dake jikin umma hannu ta lafe jikin umma taki zuwa mukai dariya ina fadin umma kin samu ya ke nan ashe ?
Jikokina ne kin sani don dai zumuncin ya koma hakane ina yar yaya Nuhu da dan hjy Addah ai duk nawane ko indaga zumunci don dukkansu a matsayin tobasai na suke ai don ni na kasance yar mace ce a cikin su.
Shiru nayi na fada tunane don fadin hakan da umma tayi a sanadin su baffa Nuhu umma ta rabu da yan uwanta hayatan hayatan.
Hankalin umma naga muniya bata kula da halin da nake ciki ba lokacin don na zurfafa ga tunane a lokaci fitan muniya nake fadin umma.
Ta juyo gaskiya ya kamata ace mun ziyarci yan uwan ki kafin mu bar kadunan nan da mukazo gaskiya saboda wani Alh Nuhu can har ki jefa kanki a cikin halakan alhakin zumunci.
Dukiyan nan suje suci ba shine a gaban mu tunda har ubangiji ya rayamu muka kai wanan lokacin ba tare da arzikin mu ba.
Umma tayi shiru tana saurarena kafin tanisa tace naso hakan don duk kwanakin nan hankalina yana wurin su gaba daya.
Ko barci na kwanta mafalkin gida da yan uwana nakeyi abin yana damuna sosai a rai nima zamu sa lokaci mu tafi na fada ina mikewa don yarinyar da tayi barci a bayana tayi min nauyi sosai a lokacin.
Yaushe rabona da goyo tun zaman mu kaduna ina goyo Amira sai kuma yau dana goya yar yaya Abubakar din badon uwarta ba sai don ubanta kawai.
A ranan kan bamuyi barci ba don yaran dukkan su suyi rikici tundai babban ina da maganin mura shi muka dinkirawa yan banza barci mai nauyi ya dauke su har safe na fita wurin aiki basu falka ba a lokacin.
Ina wurin aikin amma bini bini nakan kira umma inji halin da yaran suke ciki tace suna wurin muniya da suka fara tikici ta daukesu ta fita dasu zuwa wurin ta.
Sai lokacin hankalina ya kwanta na sauke ajiyan zuciya ina fada a zuciyana cewa haka kawai a dorawa mutane wahala don wani dalili.
Can kuma ashe abinda ya faru bayan barin mommy din da rikicin ya barke a tsakanin su bayan yar aikin ta matsa mata taje ta bashi hakkuri taje.
Tana shiga dakin ne ta zauna yana ci gaba da shiri tace wurin kafa nazo ganin baiko juyo ya kalleta ba a lokacin don yadda yake jin takaicinta a lokacin.
Kikazo yi me a nan na fada maki wallahi yau ba zaki kwana min a gida ba son haka ki fice tun muna sheda juna dani dake kan ranki ya baci kamar yadda kika batawa mahaifiyata rai kema.
Dama ai haka akeso idan kuma mutum bai fada ba ace baya da kirki sai lokacin ya juyo da kyau yana fuskantar ta yace dama kina dashine ashe rashin mutuncin naki yakai haka ban sani ba ?
Get out of my side ya fada da karfi ta fito yana fadin na baki minti biyu kacal wallahi idan baki fita a gidan nan ba komai zai iya faruwa ki kuka da kanki wallahi duk abinda ya faru kuwa.
Jin hakan yasa tayi fushin zuciya gyalen ta kawai sai jakka ta dauka da makullin motanta ta fice gidan da niyar ai tasan hakan ba zai yuyu ba dole za a dawo da ita.
Saidai tana fita ya fito ganin mai aiki tare da yara a cikin damuwa yasa ya tambaya a kausashe da ina take ne ?
Tace ta fita yanzun nan har ya dan taka ya juyo yana fadin OK kefa tace in bari ta dawo na tsare yaran yace OKey kina iya tafiya yanzu kema ya fada cikin daure fuska don zan kulle gidanane in fita.
Dakin shi ya koma ya fito saiga mai aikin ta fito tana kokarin daukan yaran yace barsu a nan dasu zan fita.
Tare suka fito daga gidan yasa yaran a motashi ya ya koma ya kulle gidan yashiga yana magana da maigadi itama ta tafi tana mamakin hakan.
Gidan mommy yaso kai yaran kafin kuma ya canza tunanen shi ya juya zuwa unguwar mu a yakai muna yaran ya kuma ci abinci a can yana fita hotel ya nufa ya kama daki a can ya kashe wayan shi kuma.
Nazifa ko gidan su ta nufa ta samu mahaifiyar da jiya suka dawo daga asibiti ta sanar mata da komai wani kallo uwar ke mata kafin takai karshe tayi shiru.
Nazifa kasheni kuke son yine a gidan nan kome ?
Don ku nake zaune gidan nan ina hakkuri ina bin umurmin shi duk da irin takuran da muke fuskanta a aurin shi.
Farko dana gane halin shi naso fita gidan nan saidai kaddara ta riga fata don na samu cikin ki dole na zauna na haihu bayan haihuwan ki kuma komai bai canza ba lokacin amma mahaifiyata tace na zauna nayi hakkuri in sama maki abokan shawara a gidan nan.
Har yau da kuke ku biyar hakkuri nakeyi kin sani don kunfini sanin mahaifin ku baudaden rayuwa ke gareshi.
Balle ke da dadi yayi maki yawa don iskanci da rashin sanin ciwon kai kin kasa zama ki natsu a dakin ki ko zamu samu salaman rayuwa a wurin ki.
Yau har iskancin naki yakai kiciwa uwarshi mutunci a gaban shi haka bako bayan idon ta ba kin dauka kowa irin kine da zai zauna don kina zinariyan mata kiciwa uwarshi mutunci yana kallon ki ?
Wallahi kiyi maza ki koma tun wani baiji wanan badalan da kika aikata ba a gidan nan yanzun nan gasu Tasi,u nan su rakaki ki koma su bashi hakkuri dacewa kannen ta dake zaune sai tsuki suke ja a gefen su.
Shigowan yar aikin ne ya hana uwar magana nan ta gaisa dasu ta fara rabtabo masu bayanin komai a karshe dai kowa zabura yayi jin ya rufe gidan ya kuma tafi da yaran.
Ina yakai min yara ta fada a zafafe wurin mommy mana kaninta ya bata amsa taji ranta ya baci sosai lokaci guda.
Uwar tace kin gani ko kinga abinda kike kokarin ki jawowa mutane yanzu kuma in ba ai hankali ba sai zancen nan ya fita kowa yaji.
Wallahi kiranta zanyi ta aiko min da yarana yanzun nan ba zan bar yarana a can suko kwana tare dasu ba akan me zai daukan min yara yakai min su can ?
Ta fara kiran layin mommy din uwar tace miko min wayan wawiya yanzu zaki bata komai don baki da wayau ko kadan ke .
Kiran har ya tsuke mommy bata daga ba don a zaton ta cin mutunci zata kara masu saiga nabiyune ta dauka sai taji muryan mahaifiyar Nazifa din tana sallama.
Nan dai suka gaisa take fadin haka kuma wanan mara hankalin ashe tayi maku ni bansan meke damun rayuwan Nazifa ba wallahi.
Ba komai ai taci albarkacin haihuwa saidai ta bari don gaba in ta dauki hakan zata sha wuya harni Nazifa zata kalla ta zaga a gabana meye laifina a cikin dubu dana zabota tazo mu zauna tare ashe yin hakan kuma laifine hjy salma ?
Gaskiyane hjy Addah don Allah kiyi hakkuri idan na samu lokaci zanzo har gida in kara baki hakkuri kan hakan baki da laifi wallahi.
Don yar banzan bata san yadda na samu akayi wanan hadin bane kwarai da ba hakan ba don da ta zama muna ya kuwa taba mara da kunya.
Ba komai ai ya wuce nikan a wurina hjy Addah ta fada tona gode inji hjy salma din ta fada kafin tace yaran dai basu yi maki fitina ba dai ko ?
A cikin mamaki hjy Addah ke tambaya yara kuma wasu yaran ke nan su mimi wai tace ai basa nan ba a can na barsu ba gidan.
Kallon juna sukayi a cikin mamaki suka hada ido basi wurin ki fa tace wallahi ba a zo dasu nan ba ai ko an fada maki suna gidan nan ne.
Ga Nazifa nan yace ta fice masa gida tafito tabar yaran karshe kuma bayan tazo yanzu saiga yar aikinta tazo tana fadin ya dauki yaran ya rufe gidan shi ya tafi dasu.
Ina yakaisu hjy Addah ta kara tambaya aine nima nake mamakin hakan don inba nan ba ina zai kaisu ke nan ?


ZAINAB IDRIS MAKAWA


ANA DARA GA , , , , , , , ,

6️⃣6️⃣ BY, , , , , , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL WAKIL , , , , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257

ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋

Ina bara adduan ku da bakunan ku masu albarka ga wanda Allah yaba ikon tunawa yayi min nagode.
Muniya naba kudi ta sayowa yaran abin bukata daga tufafi permppers da alawa da biscuit har magani don yaro baka rabashi da ciwo.
Kwana biyu kawai nasan mun samu matsala da yaran bayan shi mun zauna lafiya dasu babu wani matsala gaskiya ganin haka sai na daina damuwa akan yaran
Don muma yayi muna shine silar mayar damu cikkakun mutane a yanzu har na tsaya nayi karatu da taimakon Allah ga har Amar shima yana karatun don da karatun lagos natsaya nayi sai yanzune zan shiga jami,a a lokacin.
Amma gani a mataayin dako makiyina baiyi tunanen hakan ba gareni koda a mafalkine cikin kuduran ubangiji .
Wanan yasa nakeji da diyan ya Abubakar din na kawar da tsanan uwarsu a zuciyana tunda basu sukai min laifi ba uwarsune da kakan su.
Ina jin yaran har cikin zuciyana sosai dan zaman mu dasu dama kuma in baki manta ba haka nake da yarani har yaran


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login