Showing 372001 words to 375000 words out of 382072 words

Chapter 125 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28446

gabanki akai komai yanzu na gamsu indai hakane abin ba zaizo da wani matsala ba sosai insha Allahu.
Shirun da yajine ba amsana yasashi kallon wayan shi muryan fatima yaji tana kwallamin kira kamar a cikin tashin hankali bai kashe wayan tasaba yanajin duk abindake faruwa alokacin wurin.
Innalillahi ya ambata hankali tashe kafin yayi dabaran kiran layin fatima din yayi mata bayanin abinda zatayi min a lokacin.
Wanan karon ban wani sha wahala sosai ba na mike don yanzu abin nawa akwai sauki sosai ba kamar dacan da mm nake wahala sosai ba idan ya tashi min.
Barcin nan dai da nakan yi shinayi alaman sun sauka min a kai kenan lokacin kodana falka magariba tayi a lokacin.
Duk yadda yadda yan uwa sukai tsamanin zancen ya wuce hakana yanzu a garesu don labari yazo masu cewa ai har an kashesu ko don an kamasu da babban laifi maigirma a kasan don haka aka halbesu.
Ranan wayan gwaggo hari ya tayar damu barci karfe hudu da rabi na safe da kukanta take fadamuna cewa sun samu labarin cewa an halbe su boy don Allah na bincika masu gaskiyan zancen suji.
Nima salati na saka a rude kafin na jawowa kaina natsuwa ina bata hakkuri tare da fadin gwaggo ki natsu wanan maganan ba gaskiya bane don ko jiyan nan munyi waya da uncle ya fada min ya samu ganin shi.
A cikin wani irin karagi tace ya ganshi fa nace kwarai kuwa gwaggo don insha Allahu da alaman nasara sosai a case din.
Sai naji ta sake wani irin shesheka kuka lokaci guda wanda nima yasani sake hawayen da suka taru min a fuskana lokacin.
Wanan labarin ya dan karfafa mata gwiwa har yan uwa sun fara cika mata gida da sunan makoki da tayata jimame kan matsalan sai gashi ta fito tana fadin insha Allahu boy yana nan dawowa don ko jiya mijin sahiba ya ganshi har sunyi magana dashi.
Nan take aka dauka zancen ya tabi zuciyar tane harta fara sakin magana haka taci gaba da fadin insha Allahu sahiba tace zai dawo gida da yardan ubangiji.
Nan yan gulma suka samu nayi don basu yarda da abinda take fadi ba sun dauka zancen ya fara taba mata kwakwalwanta ne haka.
Sai sam basu yarda da abinda take fadin ba wasu nacewa ina wani mijin sahiba can zai iya fitar dashi a wanan hatsarin daya fada ?
Ya Abubakar duk da yadda suke da mustapha din yaji zafin kamashin da akace anyi munyi waya dashi yake fada muna sai dai ta Allah amma yana da wuya a fito dashi sai ban gaya mai zancen kokarin da uncle keyi ba a can din.
An dai sha wuya hankali ya tashi sosai Allah da ikon shi watan su hudu a can sai gashi anyi nasaran fito dashi din ta hanyar kamo masu laifin aka wankeshi.
Uncle da kanshi ya dawo dasu Nigeria bai fadawa kowa zuwan su ba sai ganin su gwaggo tayi tare baikai awa biyu ba ya juya zuwa Maiduguri.
Ganin mustapha din ya fito ta hanyar uncle mukhatar ya kara daga darajan shi dani a idanun su tunda sunga yayi abinda basu taba tunanen zai yuyuba ga mustapha din.
A sai zuwa barka da arziki akewa gwaggo hari kowa yana fadin albarkacin bakinshi a lokacin irin yadda a yanzu nayi masu rana a cikin su bayan sun wofintar damu a baya.
Don ba,a dade ba da nayo masu aiken abubuwan azumi dana aikowa dangin mu ga baki daya har wa yanda ke yola dana nan garin kaduna daga ciki kuwa har da na Family din Alh Nuhu da Alh gyade da suke tsare har lokacin a gidan wakafi amma haka na aiko masu da kayan shiga azumi.
Suma lokacin da baffah hamza ya kai masu kayan abincin dana tea din saida suka so su nuna bore wai ba zasu karba ba inji yaranshi.
Amma iyayyensu mata da wahala ya gama kamasu zuwa lokacin sukace ai ba a haka tunda har na nuna kulawa a garesu kada suga laifina su dubi laifin iyayyensu maza kawai.
Shima baffah hamza ya dora masu da nasiha kan tunda har ban nuna komai ba duk da irin laifin da akai muna amma ina nuna su yan uwanane na jini ya kamata suma su sauke makaman su hakana a kan mu.
Su kwatanta idan sune mahaifinmu ya raba mahaifinsu da duniya yaya zasuji a ransu a kan mu sai jikin su yayi sanyi inda akai masu mm asiha sosai har wasun su suka nuna nadaman su sosai.
A Wanan zuwan munje har lagos wurin su umma mun gaidasu mun kai masu dan abin azumi inda umma tayi ta murnan ganina a lokacin.
Sai bayan mun samu kebewa da itane ta kallani tana fadin sahiba naji dadin yadda kika kwantar da hankalin ki haka sahiba don da farko hannuna a gaba yake yadda akai auren nan.
Amma yanzu ganin ki haka hankalina ya kwanta sosai wallahi gashi ina ganin har da rabo a jikin ki idan ba karya idona ke min ba kila ?
Dan murmshi na sake kawai Allah ya taimakeni fatima uwar baki bata jin yarbanci data kaini inda banso don ni cikin jikina bai hana min yin komai kamar yadda na saba ba haka kuma ina cin komai da nake ci a baya .
Nafi da son sai cikin ya fito da kansa a gani bawai na dinga fadawa mutane ba don wanan camfin yarbawane haka don baka san bakin wani ba.
Haka mukai kwana biyu tare dasu ummu a lagos muka dawo Maiduguri a wanan lokacin ne tawagan yan uwan mu maza da mata sun kai su ashirin sukazo mashi godiya kan tsimakon da yaiwa ya mustapha tare da abin alheri iya karfin su da sunan sun kawowa yarsu garan taron azumine.
Yace ai ba sai sun taso ba don sunci albarkacin yai masu hakan a wurare da dama don haka ba sai sin wahalal da kansu ba illa iyaka dai ya kara kula sosai tunda ana binshi da sheri irin haka dole yana da makiya a wani wajen da bai sani ba.
Gwaggo hari kasa ne kawai bata kaiba wajen mashi godiya a lokacin na dauka zasu kwana sai gashi sunce a ranan zasu dawo kaduna.
Nagode Allah ba wanda ya farga da cikin dake jikina wanda zaikai wata biyar ko shidda a lokacin a jikina amma ya shafe ba a ganin shi sam.
Har shi maigidan baisan da cikin ba Inda uwargida falmata duk da abinda ya faru haka baisa ta saduda ba don kullun a cikin barazanan fadi take ba aiwa diyanta yan uba ita.
Yadda nazo haka zan koma don kullun a cikin sabon shiri take a kaina duk da bata samun nasara hakan baisa ta daina ba ita.
Gashi a yanzu duk wani kafa da zata samu labarina a toshe yake tunda bana hurda da kowa in kin debe yan uwan mijina na kusa su kuma ba zataji komai a wurinsu ba don ba yarda a tsakanin su.
Gashi dole zamu bishi zuwa Hong Kong saboda azumi da za a fara haka muka bar Nigeria zuwa kasan amma mun tafi da fatima da har yanzu itace zaune tare dani.
Mun isa lafiya an kuma tashi da azumi saidai saboda wahalan tafiya kuma ga laluran ciki da zan iya cewa wanan ne wahalan farko dana farayi kan cikin jikina gaskiya.
Wanan yakai saida mukaje asibiti dole aka bani gado na huta don ina bukatan hutu a lokacin barci sosai nakeyi yayin da yabar komai nasa ya dawo jinya ta asibitin.
Ina bude Ido shine naga a zaune yana karatun kur,ani ya saka glass a idanunshi hankalinshi ya dauku ga karatun da yakeyi a lokacin .
Haka yasa na samu daman kare masa kallo sosai a lokacin don banyi motsi ba shima bai dago kanshi ba a lokacin yana duke yana karatu.
A hankali na mayar da idanuwana na rufe lokaci guda ina sauke ajiyan zuciya a hankan na tsukayo muryanshi yana sadakallahullazi.
Jin hakan yasa na bude idona muka hada ido dashi yace kin tashi na dan gyada kai ya samu wuri mai kyau ya aje littafin ya mike tare da zare glass din daya manna a idon shi na karatu.
Ya karaso zuwa inda nake kwance yana fadin sannu ya jinkin naki yanzu Alhamdullahi na fada ina lumshe idanuna lokaci guda.
Yanzu ina ke damun ki yana kai hannunshi a saman wuyana a lokacin ba ko ina na fada a hankali ga abinci nan ki tashi kici .
Fuska na bata lokaci don sam yanzu ban son cin komai a cikina duk kwanakin nan ga baki daya duk da ina kokarin wurin ganin ban zauna da yunwa ba.
Baki isa ba ya fada yana kokarin jawo basket din abincin tare da fadin kina son ki wahalar da kanki ne da abinda ke cikin ki ku wahala ?
Da dan mamaki a fuskana na dan kalleshi sai kuma na dan turo baki lokaci guda ina kawar da kaina gefe abincin ya fara zubamin har lokacin ban kalli inda yake ba.
Aje min yayi a gabana sai na kalli abincin wanan dahuwan nasan na fatimane don yadda akayishi ya hadu ba irin da yan aikin gidan da muka sama suke muna ba.
Mikewa nayi ina kokarin sauka saman gadon da nake kwance sa sauri ya kalloni yana tambaya ina zaki bandaki na bashi amsa.
Bayan na dawone na zauna bakin gadon ya miko min abincin na karba cibi biyu kawai nayi na aje spoon din cikin plate ina kokarin komawa na kwanta ya sake fadin.
Likita yace idan baki cin abinci akai,akai zaku samu matsala dake da abinda ke cikin, cikin ya fada yana kallon fuskan nikan dukar da kaina nayi.
Banda abinda zance dashi tunda ya riga da yasan abinda nake boyewa a yanzu shi yasa nayi shiru a lokacin cikin jin nauyin hakan da kunyanshi.
Kaina na kawar gefe daya na sake jin muryan shi a kusa dani yana fadin akan wani dalili kika boye min alheri da ubangiji ya azurtani dashi tsawom wanan lokacin.?
Nasan dole kina da dalili naso ba kaina hakkuri in biki a yadda kike so amma zuciyana ya kasa daure hakan a yanzu don farin cikin da nake ciki duk da kin rage min hakan .
Ciki a jikin ki fatima har tsawon wata shidda ban sani ba sai wanan lokacin daya rage saura kiris ki haihu ?
Amma banyi mamakin hakan ba don koshi likitan da kyar ya iya gano hakan don da farko ya nuna babu komai a jikin ki.
Forget about that yanzun me kike son kici ya sake tambayana yana kallon fuskana dake daure tamau a lokacin kamar banson zancen.



ZAINAB IDRIS MAKAWA


ANA DARA, , , , , , , , ,

BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , ,

1️⃣1️⃣3️⃣

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM, , , , AL,WARITH, , ,

YAR UWA KIJI TSORON ALLAH KI DAINA FITAR MIN DA NOVEL DON KIN BIYA KI BARI WANI YA BIYA SABODA ALLAH👋

Kwana biyar nayi asibiti ina hutawa kafin na dawo gida nan ma sun bani doka kada inyi wani dogon motsi don yanzu cikin yana barazanan zubewa ne daga jikina.
Wanan yasa yake kara nuna min wani irin kulawa da kauna yana kuma kafa kafa da zancen cikin kamar yadda na gargadeshi tun a asibiti da kada ya sake yayi wanan maganan ko a gaban fatimane sai idan bukatan haka ya taso ayi din ..
Wanan kuma ya samo asaline kan sanin halin hjy Falmata da nayi don kasancewar ta shu,uman mace mai karfin hali da shige shige akan duk abinda tasa a gabanta.
Tunda har ta iya tura min asirin da yayi tasiri a jikina ya zama dole in kiyayye duk wani siri a yanzu duk a kanta kuma don babu abinda bata iyawa a rayuwa.
Anyi azumi lafiya inda nagodewa Allah har Allah ya ban ikon samu nayi fiye da rabin azumin shine baya zama wuri daya ko yaushe a cikin tafiye tafiye yake wanan ya ban dama idan bai gari sai na dauki azumina in kuma kaishi lafiya.
Kamar yadda na rabawa dangi kayan azumi wanda daga wurin shi komai ya fito don dama haka dabian shi yake zai bawa hjy falmata abinda zata rabawa dagjn da mabukata a wanan lokacin amma sai ta soke kudinta taki rabawa kowa.
Yadda ya bata haka ya bani nima hakan kuma na aikawa baffah hamza ya rabawa yan uwa zanuwa da shadda masu kyau da kudin abin sallah kowa yana samin albarka.
Har cikin Maiduguri na aika da alheri wa yan unguwan mu ta hanyar wata malama da muke dan hurda da ita nan ma sun saka min albarka sosai tare da addua dama shi nake nema a wajen mutane addua a wanan lokacin.
Babban sallah a duk inda yake gida yake komawa yayi sallah shine kuma watan haihuwana ga Fatima ta fara karatu dole sai su kadai sukazo Nigeria sallah duk da yaransu.
Saidai kafin su dawone Allah ya saukeni lafiya a daren ranan sallah din na haifi yarana duk maza tagwaye sai lokacin na gane hikimar sayen abu bibiyu da yakeyi idan zai sayo kaya a duk kasan da yaje aiki.
Watau ashe tun kwaciyana asibiti likita ya fada mai cewa yan biyune a cikina yake yin hakan labari ya riskesu na cewa na haihu a bazata banda shi da yasan da zancen cikin a lokacin.
Duk wanda aka fadawa haihuwan nawa saiya musa hakan yace sahiba fa ta haihu cikine da ita dama wai har labari ya samu hjy falmata a lokacin suna tare da kawayen ta gidan nasu yana cike kamar ana buki wata yar uwanta tazo.
Bayan sun gaisa take fadin barka fa ashe amaryanki ta sauka kuma yanzu nake ji nima na biya gidan su mariya take fada min.
Wacece hakan take tambaya a yatsine tana wani bata fuska lokaci daya don daukan mara hankali tayiwa matar duk da tasan tana da hankali amma kuma baya bayada kadan ai.
Da sauri matar data fahinci katobaran da tasoyi ta dan wayance da fadin au jini bafa abinda naso fadaba ke nan dama ?
Sai kuma ga wani kanin ta ya shigo shima bayan sun gaisa yayi mata murnan sallah yake fadin ashe maigida ya samu karuwane haka amarya ta haifi tagwaye maza ?
Zaune take saida ta mike tsaye ta fara fadin wai a ina kuka samo wanan zancen banzan haka dazun nan wacan tazo min da wanan zancen karyan yanzu kuma kai kazo dashi mutane sai ku dinga kirkiran labaran karya kawai kuna yaddawa.
Shigowan kaunanta da waya a hannu falon a kuma gigice yasa ta dakata da zancenta a cikin yare take fadin dubi abun mamaki nan anty.
Ta karbi wayan ina zaune a gadon asibitin dana haihu saye da rigan asibitin a jikina sai hularsu a kaina ga yaran biyu sun sha kayan sanyi masu tsada likitoci farare biyu sun da duko mukayi photon dasu.
Aikin fatima ne data turo wanan photon a lokacin dama abinda nake gudu ke nan tun farko yasa na boye zancen cikin yanzu kuma ba zancen boyo ga kowa.
Duk da sanyin Ac biyu dake falon bai hana goshinta tartso da zufa ba a lokacin yayinda ta kafawa yaran dake hannuna ido wa yanda kamar ubansu yayi kankisune don kama.
Photocopy ke nan wata kawarsu ta fada daga gefe sai lokacin ta nisa kafin ta fara ganin duhu duhu ta lumshe idanunta a hankali tare da fadin mukhutar.
Bata gudun abin kunya don haka nuna react dinta bai dameta ba lokacin ta fara fadin ni zakayiwa haka ka boye min zancen cikin matar ka ?
Ku rage a falon nan yarta ta fada kafin su fara fita daya baya daya sai aminanta mutum uku suka rage ta kalleta tana fadin zaki fara haukan ki ?
Zaki hanashi abinda Allah ya halasta mashine falmata ki natsu ki dinga daukan girman ki duba yadda yaranki suka fara girma yanzu fa.
Wani malolon bakin ciki ta hade lokaci guda da taji ya rufe mata kan zuciya har bata iya ganin kowa a lokacin don bakin ciki wai ita falmata guda a gidan mukhatar yau akaiwa yaranta yan uba ?
Bama kishiya da takewa fathting din ta fita ta bata wuri ba har da karin wasu yara maza biyu da yanzu suka shigo cikin file dinta.
Amma mukhutar ya shammaceta ya gama da rayuwanta da har yaiwa diyanta yan uba a yanzu dama shi take gudu kuma ya faru.
Wanan abin kunyar da zubar da mutuncin dayaja mata ina zata kaishi a cikin kawayenta dake mata kallon ita ogace ta tare gaba ta tare baya a gidan mijinta bayan cika bakin da tasha yi masu a baya ?
No warnder ya fita da yaranta yau tunda safe da sunan zasu ziyara ashe yasan abinda ya shuka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login