Showing 105001 words to 108000 words out of 382072 words
nan daga gida gwaggo Asiya ake shigo da abinci don yan aiki dake girkawa.
Don haka na koma nakai kwance a inda na tashi din umma zama tayi tare da kuna tv tana sauraren azkar din safiya da sukeyi a tv kullun .
Barcine ya kara daukana a wurin na danyu nisa kuma na sake yin maka mancin wanan mafalkin da daddy din sai dai wanan karon wani mutum na gani yana kwasan dariya irin na kyata muryan shi babu dadin ji.
Wani irin falkawa barci nayi tare wani irin zabura da har umma saida ta dan razana dani yadda na falka din fita nayi irin na dazun din .
Saidai wanan lokacin motar an gama wanke ta sai sheki takeyi hasken ranan daya fara fitowa yana haskata .
Juyawa nayi na koma cikin gidan da shigana part din mu nace umma suna son su kashe daddy a yau din nan.
Sahiba kanki daya kuwa nace wallahi umma na gani har sau biyu a cikin mafalki sai akace maki mafalki kuma gaskiyane ko ?
Wanan gaskiyane idan har daddy ya shiga motar shi baka a yau zai iya halaka subbahanallahi ta fada tare da mayar da hankalinta a wurina.
Kada ki yarda kiyi wanan zancen da kowa ta fada min a cikin daure fuska idan banyi ba duk abinda ya samu daddy din kece da laifin hakan umma .
Na fada ina komawa na kwanta tare da runtse idanuwana mafalkin yana dawo min kamar a lokacin nayi sa.
Mikewa naga umma tayi ta fita daga part din namu na mayar da idona na rufe sai can naji muryan mommy a kusa dani take fadin.
Sahiba meke faruwane wai dake idanu na bude a hankali nace mommy ban sani ba nima amma dai wani abu mara kyau zai samu daddy a motar shi yau idan ya shigeta.
Kallon umma tayi jikin ta ya fara rawa umma ke fadin yanzu ya za,ayi hjy dole in fadawa Alh mommy ta fada kada ya dauki zancen da wani manufa amma ?
Bari dai inje mommy ta fada ta mike da sauri ta fita zuwa part din daddy din ankai kamar awa daya sai gasu tare da mommy din har part din mu.
Ina zaune a cikin damuwa nayi shiru na kurawa kasa ido ina tunaje yayin da duk kafana na dora saman kujeran na dunkule a cikin light pink din hijjab dina da yaya ya saya mun.
Ummace da take zaune ta kurawa tv da ake bayani akan sallah ido tana kallon yadda malamin ke bayani ta amsa masu sallama.
Tun daga kofa daddy ke fadin yau meke faruwane diyana ance kinyi mugun mafalki dani hankalin ki ya tashi ko ?
No ba mafalki bane daddy gaskiya ne na fada mai ina dagowa a cikin damuwa zama yayi a kusa dani yana fadin meya faru fada min inji.
Sai hawaye na kasa magana a lokacin umma tace tunda asuba fa ta fita ta dawo ina tambayan ta tace min ba komai.
Ta kwanta kuma sai gashi ta tashi a tsorace tana firgita take fada min wai zasu kashe ka yau din nan idan har ka shiga motar nan taka Baka ta waje.
Ba abinda zai samu daddy ki da yardan Allah kinji Sahiba yana dafa min kafada na na girgiza kai nace don Allah kada ka shiga daddy.
Yayi murmushi irin na manya jin haka da sauri na mike tsaye na nufi dakin kwanan mu don bamu raba daki da uwata ba har yanzu a gado daya muke kwana tare.
Wani ruwa na dauko na fito dashi hannun shi na kama na shafa mai ruwan yana dai kallona bai ce min komai ba suma duk ido suka zuba min suna kallona.
Alh yarinyar nan fa akwai abubuwa a kanta gaskiya baiyana daine basuyi ba har a gane hakan don wallahi ranan itace hana muci naman nan dana kai ma ya canza kala .
Sahiba din daddy ya tambaya mommy tace kwarai kuwa Alh tace kabar yar nan wurin nan kawai inda ka ganta abubuwa da dama wallahi in sahiba ta fada duk sun zama gaskiya zuwanta garin nan.
Kin san maza da karfin hali don daddy din murmushi yayi yana mikewa yace ashe tarihi zai maimaita kansa ke nan don haka mahaifiyar Attu take ai itama sai bayan mutuwan ta aka samu galaba a kan zuri,an ta.
Ba komai kada ku yarda da wanan abin kinji idan kana yarda da irin hakan imanin ka ne ke samun rauni ya fada a karshe ya fita mommy ta bishi da fadin kada dai ka shiga motar nan yau Alh gaskiya tunda har an fadi hakan.
Bayan fitan shine mommy da hankalinta bai kwanta ba ta daga waya ta kira yaya Abubakar din tace bayan sun gaisa kazo yanzu ina neman ka ta kashe wayan nata.
Sai gashi ya kira hankali tashe da alama a barci yake lokacin yake fadin mommy lafiya meke faruwane i hope dai kowa na lafiya a gidan tace kadai zo nace maka yace gani tafe mommy.
Ba a dauki lokaci ba sai gashi su Nabila ke fada mai muna part din mu tare da mommy din ya nufo can.
Sun gaisa ne mommy tayi mashi bayani tiryan tiryan tundaga farko kallona yayi tare da fadin Na, ur mamiyota tell u dis torry in ur dream, or what, sai kuma yayi murmshi yana fadin yanzu me daddy yace akan hakan ?
Zaifa shigane idan ba an masa da gaske ba mommy ta fada a cikin damuwa ya mike yana fadin daddy ne baisan wanan yar tasa ba don har magani tayi talla a lagos,
Don haka ba abin mamaki bane idan tana fadin hakan a yanzu ni ba abun mamaki bane a wurina don nasan waye Sahiba.
Ya fita yana fita ya nufi wurin daddy suka gaisa yake tambayan shi matar shi yace tana lafiya bissimillah daddy yayi mai yace ban koyi brush ba na zo nan .
Daddy ina key din garejin nan ya kallo dan nasa yace yana nan yace a dauko wancan dayan motan dake ciki a wankrshi kafin daurin aure sai a kai wanan din ciki ajeshi.
Kaima ka yarda da zancen su ke nan ko yayi murmushi ya mike ya soma tafiya zuwa waje kana yace ba kasan yar nan taka bace daddy har yanzu .
Bai yarda yabar gidan ba saida aka fito da wata motan aka fara wankewa yace zai tafi gida ya shirya kada ya makara sukai sallama .
Mommy ne tazo take fada muna yadda akayi hankalin kowa ya kwanta saidai kuma mommy tace waye wanan mutumin da sahiba ta gani a cikin mafarki?
Hakana na shirya muka tafi don ranan ne bukin gashi kuma hankalin mu ya kasu gida biyu kan wanan zancen.
Muna gidan bukin aka bugowa su mommy waya motan daddy ta kama da wuta a cikin gareji sai da kyat aka samu aka kashe wutan .
Gaba dayan mu muka koma gida tare da wasu yan uwa nasu abin dai baiyi kyau ba gaskiya don haka kawai akaga motar ta kama da wuta.
Kusan motar muce ta karshen dawowa a gidan muna fitowa ido yayo kanmu caaa har saida muka tsargu da kallon da ake muna din ashe mommy ne ta fara fadin dama Sahiba ta fadi.
Ashe abinda zai faru ke nan ya tsaya ga motan shine mutane suka sako muna ido da muka shigo gidan a take sai akaso a juya zancen wasu suce kila ina sikiro ne naso na cinye daddy din.
Sai da daddy yake fadin ita kuma nata baiwan ke nan sanin abu a cikin mafalki abinda zai faru ke nan ta gani ta fada muna dazun ashe ?
Haka kowa ya tafi yana fadin albarkacin bakin shi su Anty kuwa cewa akeyi yaya za ayi haka kawai mota tana ajiye ta kama da wuta idan ba wani kullalan da akayi masa su dai kan basu taba ganin haka a gidan su.
Duk da naso komawa gidan bukin ban samu hakan ba don kaina dake min mugunciwon nan dai da yakan dameni idan haka ya faru dani.
Kwantawa nayi sai bayan magariba umma ta tayar dani daga barci tana fada dole haka na tashi naje nayi wanka sanan na danji dadin jikina.
Don maitan Fa,iza a kaina ina shirin kwanciya sai gata dakin mu wai ta dawone muje wurin dinner da za ayi mu tafi tare.
Naso naki zuwa amma sai umma tayi min magana akan nashirya mu tafi wata kila idan na dan fita jikin nawa ya kara walwale mun a can .
Dole haka na shirya muka fita zuwa wurin bukin inda ake dinner din wurin ya cika sosai da mutane har wajen wurin.
Haka muka samu muka kusa muka shiga bayan mun nuna pass din mu dukko da anko din dina din dake jikin mu a lokacin.
Alh Nuhu ya kasa ya tsare yana zaune falin shi bayan ya gama ganawa da babban yaron shi kuma aminin shi da yake turawa yin duk wani sheri nasa.
Wayoyinsa duka hudu suna gaban shi ya tsura ido yaji ta inda za a kirashi a lokacin don bashi labarin abinda yake da tabbacin faruwan shi a ranan sai murmushi yake faman sakewa shi daya a zaune falon duk ya kori kowa a lokacin yace a bashi wuri har iyalin shi.
Shiko babban yaron nasa yana barin gidan kai tsaye unguwar dasu daddy ke ciki ya nufa a daidai inda zaiga wucewan daddy din ya bisu a baya.
Saidai kuma sabanin hankali maimakon ya ga daddy a cikin wanan motan da aka asirce sai suka ganshi a cikin wani motan da basuyi zato ba.
Da farko ma bai dauka shi din bane ya wuce saida ya gaji da zaman jirane yake kiran Alh Nuhun shi kuma akayi sa, a yakirashi a fusace don har yazo wirin daurin auren sukayi musabu,a da daddy din yaji kamar wani abu ya sokeshi a lokacin .
Kafin ya kai gida hannu ya kumbura sumdum baiko iya daga hannuwan shi haka ya samu yakai gida hankali tashe dakin shi ya shige inda bai yarda kowa ya shiga mai ya dade a ciki ba wanda yasan halin da yake ciki .
Sai bayan wasu awanin ne ya fito yana jin kamar ya cire hannun ya huta don azaban ciwon da yakeji yana masa lokacin.
Shine karfe uku bayan daddy ya dawo gida suna falon shi da wasu bakin da sukazo masu daurin aure daga yola sukaji yan aikin gidan maza suna ihun wuta wuta a lokacin.
A wurin dinner din kuma muna shiga cikan wurin yayi yawa haka dole muka ratso taron jama,an muka nemi wuri muka zauna a can dan baya.
Bamu dade da zama ba aka aiko yaro wai yacewa Fa,iza mu zo ga wuri a nan gaba mu biyo shi hakan kuma muka fara ratsa wurun zuwa gaban inda akai muna nuni ashe duk yan family din suna wurin azaune muka bi sahun su.
Zaune kawai nake kowa na harkokin shi ko ruwa ban iya dauka a wurin na sha ba duk ina ji ba dadi gida kawai nake son komawa in kwanta a lokacin.
Wayan Fa,iza ta miko min shi ya dan dauke min hankali har na mayar da hankalina a wurin wayan ban damu da abinda akeyi a wurin ba.
Kamar ance in dago kaina sai mukai ido hudu da shi yana zaune ya kura min ido daga inda yake zaune da sauri na kawar da kaina zuwa kasa.
Tun wanan lokacin ban kara yin wani yunkurin dago kai ko dogon motsi ba a wurin sai naji hankalina ya kara tashi sosai da zama wurin.
Ana tashi na nemi motan yan gidan don su Nabila basu tashi ba na rigasu komawa gida ban yarda sun barni a wurin ba.
Ina shiga gida part din mu na nufa kaya kawai na cire na nemi wurin kwanciya sai barci ai kuwa dai yau ma na sake mafalkin katon mutumin nan sai dai duhu bai bari nagane fuskan mai shi.
Yana nunani dan yatsan shi yana mun kashedi a kanshi sai gani na fara addu,a aikin mafalkin ya fara ja da baya baya ya bace a cikin duhun dare.
Yana bacewa ina falkawa daga barcin tsorone ya kamani sosai na rarafa na shige cikin jikin umman mu na dunkule ga barci bai kara daukana ba kuma sai wajajan asuba.
Ban fadawa umma komai ba da gari ya waye haka nayi ta faman hadiyan damuwana ni kadai a zuciyana.
Da yamma ne mommy ta aiko wai inzo zata aike mu zo mu dauko kaya a gidan gwaggo hari dole na tashi hakana muka tafi mun samu an gyara gidan tsab kamar ba ai taron buki ba ciki a jiyan don wasu bakin su duk a gidan ta suka sauka.
Sai da muka dade a falon kasa kafin tace mu shigo suna sama mu samesu a nan muka shiga da sallaman mu katon photon sune ya taremu a falon ban samu tsayawa duban photo ba don gaisawa da ita da muka tsaya yi.
Don har mijin ta yana zaune tare da wani dake duban waya banga maishi ba a lokacin sai dai naji Fa,iza tace ina wuni ya mustapha.
Lokacin ya dago kai yana amsawa saida na mike zaune don gani shi a gidan ga kuma Fa,iza ta kirashi da yaya a gabana yanzu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA, , , , , , , ,
3️⃣2️⃣ BY
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL ALIM , , , , , , , ,
ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI SAN ALLAH YANA GANIN KI GA KOMAI UBANGIJI YA BADA IKON BIYA AMIN, , , ,
Kin sanshi ne Gwaggo ta tambayeni daga inda take a cikin rudewa nace eh nasan shi da sauri na sake fadin eh a wurin bukin nan na hadu dashi a nan na san shi.
Sai kuma nayi kasa da kaina ikon Allah don kin sanshi a wurin buki nan sai kuma ki kadu haka ko wani abu yayi maki daya baki tsoro dashi haka ?
Lafin inyi magana naji yace yar kauyece don kawai mun tashi kadeta da mota shine taso ta kawo muna rainin wayau a wurin na gyara mata saiti.
Kai ubbana indai ba dukan yar mutane kayi ba har yasa take kaduwa haka yanzu data ganka don nasan halin ka sosai da rashin son rainin wayau mahaifin sa ya fada .
Kai haba Alh ai ba zai duketa ba ba kasan su yarbawa da shegen tsoron tsiya yanzu haka dan tsoro ya bata shine ya zama wani abu a wurin ta inji gwaggo din.
Fa,iza shiga ki dauko wani leda blue a saman gado kizo ku tafi da wanan shirmen nata don Allah kar ta zo ta dami mutane a nan muna zaune kalau din mu.
Fa,iza na shiga dakin ya mike uwar ke fadin ina kuma zaka ana hira yaushe rabonka damune wai , ?
Yace No mama ba ko iba zani ba zan danyi wayane yanzu in dawo ai yau ba zan fita ko ina ba ina nan tare daku nayi alkawarin hakan.
Yana fadin haka yasa kai ya fice a falon zuwa kasa Fa,iza ta dauko ledan ina ganin ta na mike tsaye da sauri zamu tafi.
Sai gwaggon ke fadin kice idan na kara hutawa zan shigo muyi magana da ita zuwa jibi don boy na gari ba zan samu fita ko ina ba.
Kasa na kai ina fadin sai anjima na juya wurin mijin nata ina fadin bye uncle yace nazo na ji gabana ya fadi saida naga yana saka hannu a cikin babban rigan shi ya ciro bandar din yan Naira dari ya bamu mukai mai godiya har muna hada baki muka kara masu sallama muka fita daga falon gwaggo na fadin Fa,iza ki turo min yayan ku a waje don Allah ta amsa da to gwaggo.
Muna barin falon take fasin shiyasa nake son nazo gida na samu uncle a gida don akwaishi da alheri duk kazo yana gida sai ya baka kyauta.
Amma kinga dan nan nasu kamar baison yan uwa yake don shi ko gaida shi akeyi bai son amsawa kamar yana jin kyamar mutane yake sam baida saki wallahi wai kuma haka anty hauwa ke mutuwan s, , ,
Ganin shi zaune saman three setter ya hade hannayen shi a wuri daya tare da dan kura muna idanuwan shi.
Dan kaduwa tayi kafin ta fara wayancewa da fadin sai anjima yaya nikan ban juyo ba nayi gaba ya daka muna wani tsawa yana fadin kai ku tsaya nan inda kuke.
Ban tsaya din ba na soma tafiya kafin yace zan balla yarinya a wurin nan yanzu fa,iza ta gane me yake