Showing 237001 words to 240000 words out of 382072 words
su karasa zancen shima basu yarda ya shiga ciki ba don sunayen su bai fito a ciki ba.
Kafin wani lokaci kofan wurin ya koma kamar kasuwa da jama,a wasu su shiga wasu kuma a dakatar dasu daga aikin.
Manyan da abin ya shafa sunyi kiran layin duk wani wanda ya kamata ace sun kira a lokacin sai dai basu samu layukan su ba a lokacin.
Alh Nuhu yana zaune a falon shi suna waya da kanin sa gyade akan matsalan daya shafesu suna zagin daddy har gyade din na fadin da yau lafiyan kalau ba abinda zai hanashi zuwa gidan Ali dcp yaci masa mutunci sosai wallahi.
Yaron shine ya shigo yana fadin Abba wasu mutane suna maka sallama a waje harda yan sanda a tare dasu.
Yan sanda ya tambayi yaron yace kwarai don da matan yan sandan me zasu shigo gidan sai gani na iso suka turo ni.
Fada ya tashi yanayi akan me zasu zo min har gida idan ma wani abu aisai su kirani inzo in samesu ya fada a cikin gadara.
Yana fita a fusace hango taron da yayi ne ya bashi mamaki lokaci guda yana isa suke fada mai sunzo tafiya dashine don anyi karan shi a sha,anban company.
SHA,ABAN ya maimaita sunan a cikin mamaki sunan manager din na chairman ya kira yana fadin sune sukai karana kowa ?
Alh idan kaje can zakaji yanzu mu wanan ba case din mu bane case yana hannun Oganin mune can wanan ai wullakancine da rainin wayau zasuce sunyi karan mutun haka.
Alfarma daya sukai mai don kasamcewar shi babban mutum yasa suka kyaleshi ya shiga motarshi zuwa headquater din su inda ake neman shi a can.
Saidai yana zuwa yaga ashw bashi kadai bane mutane da dama ne a wurin case din ya shafa yaso ya nuna masu halin shi amma basu bashi daman hakan ba don sun fada mai umurni suka samu daga sama.
Muna zaune kiran ya Abubakar ya shigo yake tambaya muna nan gida na amsa mashi da eh ba a dauki wani lokaci ba mai tsawo sai gashi gidan namu.
Yaran nasa na ganin sa suka shiga murna saidai ya mika hannu karamar ta lafe a jikin umma tana mashi dariya babban ma tazo ta kwanta min a jiki tana boye fuskan ta.
Gaidashi mukayi kafin ya fara magana yana fadin umma nasan duk kinsan abinda ke faruwa a yanzu kan gabatar dasu da Sahiba tayi ta hanyar da kowa bai tsamanin ta haka zata fitowa kowa ba lokaci guda haka ta girgiza kowa na ahalin lokaci guda.
Da wanda ya dace ya sani wanda bai dace ba duk sun sani a lokaci guda abin kamar an fasa kwaine a gari don kowa zancen da yakeyi ke nan a yanzu.
Saidai a gaskiya umma ba zance hakan baiyi daidai ba ko yayi daidai duba ga sanin waye Uncle Nuhu a cikin garin nan dama kasa baki daya.
Uncle dai basai na fada maku ba shu,umine na gaske wallahi naso ace ta bari sai zuwa lokacin da muka shirya tunkaransa mu tunkareshi alokacin da muke da shirin mu.
Amma yanzu aikin gama ya gama ko don yasan kuna raye an fada mashi kuma hankalin su a yanzu duk a tashe yake don wanan abin ya jawo rabuwan hankali da baraka a tsakaninsu sun kashi gida biyu.
Nan dai yaiwa umma data sansu bayan duk abubuwan dake gudana a tsakanin yan,uwa na tashin hankali kan zancen cewa mu din diyan marigayi ne dan uwansu.
Ikon Allah wanan hakikancewar haka umma ta fada a cikin mamaki yace eh saboda sun san basu shuka gaskiya bane ya jawo hakan ba komai ba.
Idan ba wani abinku a hannun su ai duk wanan tayar da jijiyoyin wuyan ba za ayi shi ba ayanzu asalima ba zasu damu daku ba ai sam don kun baiyana din yanzu.
Dago yarinyar dake jikina a kwance nayi don gyara zama da nake son yi inyi magana a lokacin sai naga yarinyar ashe tayi barci ne a hakan data lafe a jikina wai.
Abinda ya jawo hankalin shi garemu ke nan yake fadawa umma mommy ta dameni kan indawo da yaran nan hakana don ma bukin nan ne ta daga min kafa da zancen nace dasu Abuja nakaisu gidan abokina.
Uwar tasu ta dawo ke nan umma ta tambaya yace ta dawo don mommy kawai na dawo da ita saboda naga mommy tana shakun mahaifinta sosai a rayuwan tane.
Dolene aji shakan wanan shu,imin mara imani don kawar da rayuwan kiyashi yafi girma dana mutum a wurin shi sam bashi da imani ko kadan.
Amma umma banda ya Abubakar na fada ina jawo yar ina gyara mata kwanciya a kujera wayan shi ya dauki kara ya ciro yana dubawa sunan Nazifa ya gani ya dauka cikin basarwa yana amsawa.
Hankali tashe take fada mai wai yan sanda sunzo har gida sun tafi da Abban su yace akan wani dalili tace yasir yace wai akan wani company ne na SHA,ABAN sukai karan su daddy din shine ake neman ka a yanzu gida.
Daga inda yake zaune ya dago kai ya tsureni da idanun shi shanyayu masu kamada yana jin barci ko wani shauki yace kunyi karan wasune yau din nan yana mai kura min idon nashi har lokacin ?
Kai kawai na iya gyada mai a lokacin don yadda yake kallona a cikin mamaki ba zan iya yunkurin fadan komai ba a lokacin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA , , , , , , , ,
7️⃣0️⃣ BY, , , , , , , , , , , ,
ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL HAMID, , , , , , , , , ,
ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257
ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋
Hankali ya daga sosai lokaci guda don zancen kama Alh Nuhu da abokan harkallan shi ya bazu ko ina iya abinda ya sani a lokacin shine cewa.
Wata yar kabilace take son ta shiga masu hanci a kundundune a lokacin take kokarin kawo masu cikasa ga harkokin su ta bata masu suna akan abinda aka riga aka saba dashi na kasuwanci da hadawa da bashi .
Da akarshe dole mai bin bashi yagaji ya kyalesu dashi da taimakon hadin kan manyan ma,aikatan wuri idan sun dosheshi sai sunyi raga raga da wurin kafin su canza alkibila zuwa wani sabon wuri.
Wanan yake kawo muna koma baya a cikin arewa duk wanda zaizo aiki bada sunan maishi ya karu dakai bane saidai kai ka debi rabonka kwana biyu harkan ya watse wuri ya zamo tarihi.
Don haka banda kawai mu makasu kotu a lokacin babu abinda zamu iya yi don barnan da sukaiwa oga Shaaban tayi yawa sosai da har muke mamakin hakan don dole mukakai karan su kotu saboda mun fuskanci ba zasu basa hasin kai ba a samu maslaha a tsakani mudasu ba a lokacin don hakane muka yanke shawaran yin hakan ba tare da sanar da kowa ba balle a tare mu da ban hakkuri da daure bakin mu da asiri wanda kowa yasan shiyafi yawa a wanan karnin sosai a ckin al,umma.
Don haka nasan zamu samu kalubali sosai kan wanan abin don haka sai naji dadin kwasan yaran da yaya yazo yi a gidan mu washe gari kawai muka bar garin kaduna zuwa lagos don karatuna da nake na masters a yanzu hutun da muke ya kare don aikin bai daukemu wani tsawon lokaci ba sosai yadda mukai tsamani zai dauke mu har tsawon wata ukun da mukai zato da farko.
Mun isa lagos lafiya bayan mun gama daidaita komai anan kaduna da kano munyi warning din sabbin ma aikatan muna yanzu inda bellone zai jagorance su a yanzu.
Kano kuma Adamu muka tura zai kula da can din don haka muka juya muka dawo kai tsaye lagos din bayan komai ya daidaita.
Gidan mu banda dan kura da yayi ba abinda ya sameshi duk akwai aiki a gidan su manira amma hakan bai hanata zuwa ta tayamu gyaran wurin mu ba da umma tayi magana sai cewa da tayi ai mijin ta da yarane ke gyara yasa tazo nan din.
Mun gyara ko ina kafin na watsa ruwa na kwanta don aikin da mukayu din na gaji sosai ke nan a yanzu watau jikina a yanzu har ya manta da wahalan daya saba dashi a baya ke nan kome ?
Ban tashi ba duk da umma itama tadan runtsa amma ana azahar ta tashi bata kara kwamciya ba girki muniya tayi ta kawo muna shi su umma sukaci har aka dan aje mun don kayan freezer din mu gaba daya na kwashe da muke aiki muniya ta tafi dashi wurin su can part din su.
Karfe hudu na kamala sallah na zauna na shafa mai tare da saka kaya a jikina dan simple makeup nayi a fuskana na fito abinci umma ta fara min tayi nace sai na dawo zan dan shiga lagos market in sayo muna wasu abin bukatan gida a lokacin.
Ya dade a tsaye kofan namu yana danna bell tare da dan waige waige ko zaiji motsi a gidan Abdul kamar yadda ya saba ji don yana da wuya yazo wurin mu baiga wani ya fito daga cikin gidan su ba ya gaidashi ko matar ko diyan ne.
Saidai ranan suma kofan su a rufe yake kamar yadda namu din yake kuma site din yayi wani irin shiru kamar ba mutane a wurin.
Ya danna door bell kusan sau uku yasa shi mamakin hakan wayan shi ya ciro daga aljihun shi ya fara neman layina wayan na kashe yasa ya kira na umma din saida ya kusa katsewa ta daga da sallama a bakin ta.
Tana fadin yi hakkuri ina kitchen waya na falo yasa banji ba a lokacin suka gaisa yake fadin yazo gida a rufe shine ya kira ta dan sake murmushi tana fadin .
Wai a wanan gidan na kaduna ko nan lagos shima mamaki yayi sosai kafin yace lagos kuma mama kun koma lagos din ne ko ?
Muna nan lagos tun jiya da safe ai muka dawo kayi hakkuri bamu samu sanar da kaiba hankali baya kwance a lokacin.
Lagos umma kun koma amma bamu da labarin hakan mama naga ina gidan naku two days ago tace kayi hakkuri tafiyan ne ya taso masu haka a uzurce muka dawo nan din .
Mama gaskiya banji dafin hakan ba gashi baku samu ganin juna dasu mommy ba kun bar garin koda yake da yuyuwan zaku dawo ai nake gani ko ?
Banda masniya ga hakan koda zasu dawo wanan karon badani zasu dawo ba don aikin ba zai kai wanan da sukayi ba a yanzu nake gani.
Shiru ya danyi kafin yace to mama Allah bamu alheri sai na sake kira ke nan ta amsa da Allah ya nufa ya kashe wayan yana bin wayan da kallon mamaki tare da furta me hakan ke nufi ke nan kuma ?
Ya juya zuwa wurin motar shi ya shiga yabar site din yana jin wani iri a zuciyar shi ba dade a lokacin don sam ba haka yaso ya rabu da mutanen ba amma don me zasuyi mai hakane.
Iska ya furzo tare da fasin Sahiba a fili don yasan a yanzu sai yadda nayi da umma kuma don nice ke tsarawa rayuwan mu komai a yadda ya fahinta a yanzu din.
Wanan zuwan yazo wurin mune da niyar ya zauna damu ayu magana kan zancen zuwan mu gidan baffa su daddy da suka rage don su baffa hamza ne suka turoshi zuwa garemu suna son ganin mu su gana damu din.
Saidai gashi yazo ya iske sabanin hakan a wurin mu wai mun bar garin muna lagos umma ke fada mashi yasan ba zanyi hakan ga banza ba dole akwai wani abinda na shirya a yin hakan ya shafo fuskan shi a karo na barkatai yana furzo iska yanzu me zai fadawa su Uncle din ke nan sun bar garin ko me ya fada a fili.
Yaje ya samu su uncle din ya fada masu cewa mun tafi hakan yabawa kowa mamaki don me ana cikin wanan rikicin haka zamu bar gari kuma ba tare da kowa ya sheda zuwan mu yadda suke a kage da sugan mu din.
Abubuwa da dama na sayo muna gidan ya koma kamar bamuyi tafiya ba a cikin kwana biyun da muka dawo cikin sa din.
Sakon da Felix ya turo min nake zaune a falo ina faman juya tare da tunanen hanyar da zanbi in sullubewa wanan tafiyan a yanzu kuma.
Tafiyace dai kika sani mai karatu dana fada maki a baya cewa muna cikin wa yanda zasu tafi labeno daga can zamu wuce bukin yaye sister shi a can england.
Yar t-shirt farace ta zaman gida sai wando baki tied dake jikina na shan iska kaina ba dan kwali gashina yana daure da ribon baki mai kyau shima a kaina sai kamshin turare da nakeyi a lokacin don yanzu na saba ko bazan fita ba zan saka kamshi jikin rigan da zan saka lokacin.
Tsuki naja daga inda nake zaune din ina aje wayan a gefena bayan na gama karanta sakon karshe da Felix din ya turomin a lokacin saboda list din dana karanta a yanzu.
Don nasan banda wata mafita da zanyi a yanzu kuma don tabbas tafiya dani dolene ke nan duba ga yadda aka tsara sunayen mu a list din nice ta ukku a cikin list din tafiyan .
Ma,ana dai dukkan mun ya committe din mu ke nan zamuyi wanan tafiyan ke nan hakan na nufin zamu fita yin wani abin ke nan a can kuma.
Umma ce ta dago daga lissafin da takeyi tana fadin meye kuma nace zancen tafiyan mu daine wallahi.
Tafiya akan kare karatun kanwar tashi ke nan ko me inaga dai a yanzu zancen ya sake ganin gaba dayan mune wanan tafiya din.
Waya dana jefa a gefena ne ya dauki kara ina magana da umma nake kai hannu na dauko wayan ina dubawa cikin mamaki na dago kai ina fadin ya Abubakar umma cikin mamaki.
Kiran ya katse nace ba kunyi magana dashi ba umma kin fada mai mun bar kaduna tace na fada mai saidau ya nuna baiji dadin hakan ba a yadda ya nuna min.
Wayan ya kara daukan kara karo na biyu nayi mamakin hakan doshi baya kira sau biyu idan ya kira daya ko an dauka ko ba a dauka ba bazai sake kira ba kuma sai gashi yau ya sake kira a karo na biyu .
Dauka mana kiji me yake son fadi umma ta fada daga inda take zaune na mika hannu na danna kiran tare da kaiwa a kunnena naji yana sallama na amamsa.
A harshen turanci na fara gaidashi ya amsa tare da fdin uncle Hamza nason yin magana dani sunan na maimaita yadda ya fada yace eh gashi.
Wani business nake dashi koma meye ya fada ma ba zanyi magana da kowan su a yanzu don basu san damu bayn kashe muna mahaifi da sukayi na kashe wayan dip.
Kallon sauran yayi don wayan na a handfree a lokacin kowa dake wurin yana iya jin abindana fada mai lokacin.
Eh ba mamaki idan tayi hakan tunda ba tarbiya ta samu ba dama jin wanan kalamin na baffa sani yasa Abubakar dan kallo inda yake zaune.
Kai ya girgiza kafin yace duk ilahirin dan wanan zurian tamu banga wanda yakaisu samun tarbiya ba amma sai ka zauna dasu ka natsune zaka fahinci hakan .
Yanzu akwai zafin mu a zukatan su don sun dauka gaba daya babu mai kaunan su amma a sannu idan an fahinci juna zaku gane cewa yaran sun samu tarbiya sosai a rayuwan su.
Basu bar wurin ba saida suka yanke shawara kancewa zasu tafi lagos a karshen mako bisa jagorancin ya Abubakar da zaikaisu har inda muke zaune din.
Saidai sunyi rashin sa,a a lokacin sunzo basu samemu ba ance munyi tafiya don har su umma sunje garin su muniya wurn buki don nasan bana gida yasa na yarda da tafiyan su din tare saboda hakan yafi kwantar min da hankali.
Wani mamakine ya kama kowan su lokacin da wanda suka sama yake fada masu cewa ayyah ai basa nan sun tafi America tun jiya nan gaba dayan su.
Kara maimaita sunan baffah Hamza yayi yana gyada kai yace America kuma yana kallon Abubakar dashi ma yake mamakin hakan .
Ikon Allah yaushe har mutanen nan suka bunkasa haka kowa bai sani ba lamarin daga Allah ne Abubakar daya shiga motan karshe yake fadi.
Baiwane kawai na ubangiji don Ita babban Allah yai mata wani baiwa