Showing 45001 words to 48000 words out of 382072 words

Chapter 16 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28444

Daga nisa Ladi data tun karo kofan tana fadin yar ta dawo ko umma data amsa mata daga ciki tana fadin gata nan ta dawo wai mota ne bata samu ba ashe sai yanzu.
Ta karaso dakin ta hankade labule tana fadin sannu yar nan ya kasuwan da hanya ai dai an godewa Allah tunda kin dawo lafiya.
Na amsa mata ina mikewa take fadin yar umma yau umman ki ta shiga wani hali na rashin jin inda kika shiga haka tun safe ?
Daga ita har umma dariya sukayi umma ke fadin uhm ina da gaskiyana Ladi kada yar mutane ta bata a hannu na gashi ba mutunci ne ga yan uwan mahaifinta ba.
Ladi tace lalai kan a raina nace komai rashin mutuncin su a haka nake son sanin su waye su na bude ledan dana dawo dashi na dauko mata take away daya na bata tare da dan sauran tsaraban dana sayo muna
Ta karba tana washe baki tare da saka min albarka buta na dauka na nufi dan wurin da muka kewaye don wanka da zagayawa na yo tsarki nafito na fara alwala har saida nayi rabi ne naji suna wani zance daga dakin don haka na tsaya ina sauraren su
Ina alwalan nake jin suna ci gaba da magana ladi na fadin amma dai kinsan yanzu ya kamata ace gida sunsan inda kika shiga da yaran nan don ko baki fada masu yanzu ba nan gaba dole su sani saboda yar nan taki.
Don kinsan dai ta fara girma gata da zati kwana biyu zaki fara ganin maza suna sallama a kofan nan din ko yanzu sun fara yi min magana a kanta.
Don haka gara ki san nayi tun lokaci bai kure maki ba abinda kike faman boyo a fassara maki shi a wani hanya na daban.
Sauu nayi na kasa ci gaba da anbin da nakeyi don ina son inji amsan da umma zata bata a lokacin saidai umman a sanyayye tayi magana don haka banji me ta fada wa ladin ba a lokacin.
Haka na shigo dakin jiki ba karfi suna ganina suka canza wani magana har na tayar da sallah nakai rabi ladi tayi mata saida safe ta fice a dakin.
Bayan na idar ne na juyo ina gaida umma da wuni ta amsa min tare da fadin ke kinci abincin ne nace yanzu zanci ina son in baki sakon da hjy ta bayar a baki ne.
Yanzu Sahiba gidan wannan matar kika je nace eh umma naje naji ya jikin danta don bamu samu komawa asibitin ba a lokacin.
Sai na samu dan nata ya rasu ashe a take naji umma na salati a wurin tana fadin yanzu dan nan ya kare ashe Allah ya rahama masa yasa iyakar wahalan sa ke nan na amsa da amin a lokacin naji karfin gwiwan dauko ledan da ta ban na bude ina nunawa umma din kayane na jikin ta da na wanan budurwan dana gani a gidan suka hado muna sai kayan yaron nan daya rasu masu kyau nasan na Amar ne sai da suka ciko min ledan ghana most go baka da kayayyaki a cikin sa.
Kayan umma ta shiga budewa tana dan haska dan tocin mu da baida haske sosai saidai haka muke amfani dashi wurin gani da dare koda asuba idan na tashin yin wani abu na sana,an mu rayuwa ke nan.
Tun bayan komawan shi masaukin shi yake faman tunane a zuciyar shi wanan yarinyar kamar ba mutum ba duk inda zaka ganta sai tayi ma walkiya ta bata.
Towai me ye hadin su da daddy ne ma dayake neman su haka ruwa a jallo ya juya ya gyara kwancinyan shi yana fadi a fili dole akwai wani abinda ban sani ba da su suka sanshi kuma suke boyewa a tsakanin su .
Don ga sanin sa ai inma har yan uwane dasu yadda daddy yake zato sun fi kusa da hjyn su ke nan don hjy ce yar gidan ga baki daya bisa ga daddy din dashi su ukune kawai mahaifin su ya haifa kafin ya rasu.
Kai abin dai ya daure mai kai a karshe ya yanke shima zai fara bincike alakan da wanan matar data bata da ya"yan ta wace daddy ke nema a yanzu ruwa a jallo.
Wayan shine yayi kara daga gefen shi ya dauka hjy ce ya dauka murya a dakushe kamar mara lafiya yana fadin Allah ya bar min hjy ta .
Ta lumshe ido tana jin dadin addu,an shi gareta tare da kiran sunan shi ya amsa ya fara gaida ita da wuni.
Bayan ta amsa a cikin kawaici da alkunya irin nasu na fulani don a gaban mutane bata sake jiki tayi hira dashi don idon jama,a.
Hjy tace mudibbo dama na kirakane akan zancen auren ka kamar yadda kace in duba in zabama wace ta dace dakai .
To na zaba na kuma fadawa Alh zabin nawa yakuma yi na,am da zabin shima yaba da goyon baya ga hakan.
Ya dakatar da mahaifiyar nasa da fasdin hjy ban fahinta ba don zancen ya daure min kai gaskiya.
Uwar tace ai kasan halin family mu dama basu bari a fita a auro matar farko a waje sai a cikin gida don haka a cikin gidan na zaba ma yar wurin Alh Nuhu yayan mu dake zaune a nan kaduna ina dai kasanshi ai.
Abubakar ya tsuke fuska kamar mahaifiyar nasa na kusa dashi yana fadin mommy na fada maku ni banson wanan auren hadin naku tun farko.
Kuma ko zanyi irin sa hjy sai a rasa gidan da za a nema min mata sai wanan gidan da basu da tarbiya da hankali.
Hjy Addah ta dakatar dashi tana fadin wanan ba hujja bane idan ma har bata da tarbiya idan ta shigo gidan ka sai ka koya mata mana.
Mommy dan Allah ku bar wanan zancen ku bari ni zan zabo da kaina don ba tsarina bane yan gidan nan.
Kai dakata hjy tace dashi don aikin gama yagama ko don Alh ya kira yaya din ya fada mai kuma ya amince da hakan .
Don haka yanzu babu wani zancen da zaka bullo muna dashi mu yarda dakai indai ba kasa zaka watsa muna a idon jama,a ba kuma.
Mommy ba zan taba hakan a gareku ba insha Allahu kawai dai kiyi tunane akai don yaran gidan nan sam basu dace dani ba.
Don sam basu san girman mutane ba basu da tarbiya ko kadan gashi basu da addini na tabbatar ko auren yar gidan nan nayi ba zamuyi zaman lafiya dasu ba.
Don abinda sukaga dama shi sukeyi a rayuwan su mommy kinga ashe ban isa in sata ko in hata ba ke nan wani riba ke nan zan samu a karshe ?
Don yayan mu ba zasu samu kyakyawan tarbiyan daya dace uwa taba diyanta ba don ko ita bashi ke gareta ba.
Mommy nifa ban damu da wayewa ko wani ilimi ba can nafi burin auren mai ladabi da biyayya da natsuwa tare da kamun kai.
Jikin hjy ne yayi sanyi tana sauraren dan nata don tasan duk abinda ya fada game da yaran gaskiya ya fada ba karya ko kare kai acikin zancen shi din.
Don yaran dan uwan nata sam basu da tarbiya ko kadan tunda tana zuwa gidan itama tana ganin irun rayuwan su da rashin girmama na gaba dasu.
Don ko sunje gidan idan ya kama sai iyayyen nasu sun ce dasu halan bakuga wance ba zasu dan gaida mutum a tsaye kamar wani sa,an su can.
Dama shi mahaifin nasu ne ya nuna yana son ayi wanan hadin a tsakanin su don itama sam bata da ra,ayin hakan a ranta itama.
Ta numfasa har yana jiyo hakan a cikin wayan tana fadin yanzu kai dama wacece wace kake so kuma a ina take ?
Duk da ya danji sanyi a zuciyar shi da alama zai iya shawo kan mahaifan nasa kada ayi wanan hadin da suke shirin masa a yanzu.
Yanzu kan likafa taci gaba kamar yadda na fada maku mun samu abokan hamaiya a wurin sana,an mu sanin halin yarbawa umma tace na rike addua sosai a bakina kafun na fita.
Haka din ne kuwa don dana tashi zan kwaba sai nayi addua idan kuma zan fitar da kayan sai na tsaya naja abinda umma ta koyar dani daga bakin ta na addua.
Amma duk da hakan suna biye damu yauma din na tashi a makare don mafalkin da nayi gabanin asubahin.
Sai mafalkin ya tsaya min a raina sosai haka na fita na fara share wurin kafin na fitar da kayan mu da dan tocina kamar ance na haska tsakiyan wurin da muke aje murhun da muke suya dashi.
Sai na hasko tsakiyan daya nuna alaman an gina wurin anyi wani abu da sauri naja baya ina fadin back to sender may evils eyes rich his sender oba my deat bodi notin will happen to me insha Allah.
Hakan ya jawo hankalin sauran abokan kasuwancina da suma sun fito a lokacin suna gyara wurin da zasuyi sana,an su din.
What happen omo wata yar matashiyar dattijuwa da itama ta kama wanan sana,an na suyan fanken safen da mukeyi don ma,aikata da sauran masu samakon fita suna saye su tafi dashi don muna a saman hanyane sosai mu.
Nace see di tin somebodi do for my place ta duba da sauri taja baya tana fadin eh wai holy ghost fire.
Who send dis for u ? somebodi wan see ur down fall at dis place ta fada tana kara ja da baya insha Allahu d evil tin may go back to his sender, notin will happen to me ,
Wata ta karba da insha Allah ban san ya akayi ba har yan cikin gidan mu sukaji sai gasu sun fito Ladi na fadin.
We will see notin insha Allah noti go rich our daughter we no put our eyes on person business, why somebodi will put his eyes on her ?
Tazo dauke da wani sabon kwarya a hannun ta da wani ruwa a cikin sa tana ta zage zage tana yayyafa ruwan a wurin kafin ta dakata tana fada.
Ranan dai sai da kyat na iya suya sai ummace ta ansa ta karasa min duk da ba lafiya hakan ke bata ba shiyasa ban yarda umma din tayi wani abu nike komai idan ina kusa dasu don yanayin jikin ta daba lafiya.
Daki na koma na kwanta ranan banyi sana,an rana ba sai hakan ya tayar wa umma da hankali sosai.
Addua ta fara min tana dafe da goshina cikin ikon Allah har na sami barci a lokacin .
Ladi kan hankalinta ne ya daga saboda zama a cikin yarbawa duk tasaba da al,adun su nacan bale wa yan nan dake da akidun al,adun su kala daban daban na kauye zama dasu duk yasa ta iya wanan al,adan da akidun su.
Ladi farace bakatsina da kalagun ta irin na katsinawa gata dai dattijuwace amma ko yaushe zaka samu tana busa karan sigari ko goro a bakin ta.
Yarbanci ko abakin ta kamar zuban ruwa zakace a iko din aka haife ta kana ganin ta kaga tsohuwar yar dandi data sha bariki a zamanin kuruciyan ta.
Saidai dadina da Ladi akwai ibada duk da wanan kallon da nakan mata in tsane ta wani lokacin sai wanan ya dan gusar min da abinda nakan ji na tsana game da ita.
Ni dai na bude idanu naga umma zaune kusa dani har lokacin tana min addua ga kuma muryan Ladi daga waje yana tashi tana fadin .
Turancisu na bariki any person who de try to inter my road i wil show dat person my juju pass am meke hi quick quick live my daughter to live in piece.
Da kyar dai ranan na samu nasha tun wanan lokacin umma tace indai sana,a ce a nan na daina ke nan ayi da wani kuma suje suyi tayi.
Ladi tace don su za aki neman kudi tun farko sakaci mukayi ai ba a barin irin yaran nan haka su fada gari kai tsaye ba a nema mata tsari ba.
Tunda su shegen tambaye tambaye ke gare su da zaran sunga bako yazo cikin su yana samu sai sunyi tambaya a kanshi.
Allah ya taimakemu yarki tana da wayau bata dora tunkunya a wurun ta fara suya ba ta farga da hakan wanda nasan karfin adduan kine a garesu Allah ya tsare da sai ta kwanta ciwon da sai Allah a yau din nan.
Hankalin umma ya kara tashi ta kara miko min ruwan maganin da ladin ta kawo aka bani sai zufa nake karyowa a jikina.
Wanan ne dalilin dana dakatar da duk wani sana,a a cikin semi boda ga baki daya don umma taki yarda in kara yin wani a garin kuma duk da na roke ta ko a cikin gida in dinga yi idan ladi ta yarda da hakan.
Amma umma tace sam idan dai wani zaiyi ba bakin ciki ba kyashi amma nikan nagama wanan sana,an kuma.
Ganin da umma tayi yau ciwo gobe lafiya yasa ta yanke shawara muje asibitin nan da Amar ya taba kwamciya .
Don likitan yace muna da sauran kudi da zamu dinga zuwa ana dubamu a cikkn kudinganin da umma tayi taji sauki yasa ta tattara ta aje zancen asibitin a gefe daya.
Gaba dayan mu muka shirya ranan wata alhamis da jikin nawa dai ya kiya muka tafi asibitin bayan likitan ya dubanine ya bamu magani har umma mun fito naji umma tace.
Tunda akwai sauran lokaci in kaita gidan hjy na tayi mata gaisuwa tare da godiya ga alherin data aiko muna ranan danaje gidan.
Mun sameta a gida tayi maraba da zuwan mu kallo daya tayi min ta fahinci banda lafiya take tambayan umma .
Umma ta labarta mata komai daya faru dani tun lokacin nan dai ta tausaya min ta bamu wani maganin gargajiya in shaka nakafa atishawa a nan sai can ya tsaya sai barci.
Ba yadda hjy batayi da umma ba kan mu kwana har washe gari mu tafi amma umma takiya haka muka fito bakin titi neman motan da zai kaimu semi boda bamu samu mota ba.
Na who be dis iya sahiba na u aka fada a bayan iya bisi ne tana tallan kayan maganin agumo na yarbawa akai.
Take fadin ah long time no see dat day one man come to our house e de look for u nd sayiba.
He say e bi sayiba father d man look rich he even say he go give amount for person when bring ur torry.
Where are liven naw ta tambaya kamar umma ta sani tace da ita we de obalade now we de sell food there.
Zama nayi don ban iya tsayawa a lokacin na kurawa titi ido daga can gefen da suke tafiya ya hango mu wani irin burki yaja don shi ke jan motan.
Saida na bayan shi yazo ya dakeshi abinda ya dauke mai hankali ke nan a wurin kafin ya juyo har mota tazo mun fada da gudu don kada mu rasa mun bar wurin.
Matar da yaga muna magana da ita din ya sama yana tambayan ta ko ta sanmu take fadin eh sai kuma ta nuna shi tana fadin na u come to our house dat day looking for dem ?
Yace eh nan dai ta fada mai kamar yadda umma ta fada mata ya ciro dubu goma ya bata ta wuce tana murna shi kuma ya koma masaukin shi saidai bai yadda ya kira daddy ya fada mai ba don so yake ya tabbatar da hakan kafin ya sanar da daddy din.
Saboda ya kula akwai wani abinda bai sani ba a cikkn maganan don haka sai yayi bincike kafin ya taimakawa daddy nasa akan mu.
Duk da sun kirashi da dare suna sanar mashi da irin haukan da Alh Nuhu yazo har gida yayi masu ya kuma ce ba za a fasa auren ba shi yayi kadan ya basu kunya a gari.
Da wanan bakin cikin ya kwana har ya mantar dashi zancen yarinyar daya fara nazari akai dole washe gari ya shirya zuwa gida don ayi ta ta kare a lokacin.


ZAINAB IDRIS MAKAWA



.ANA DARA GA, , , , , , , , , ,

1️⃣5️⃣

BY

ZAINAB IDRIS MAKAWA YAURI, , , , ,

PAID ONLINE NOVEL KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA YAR UWA, , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AR-RAHIM, , , , , ,

Mun isa gida hankalin umma a tashe ranan don na gane hakan ne ta yadda take amsawa mutanen dake cewa damu u are wellcome, ko u na don comeback ?
Mun shiga gidan dayake muna farkon a gidan sauran na daga ciki don ni sau daya na taba shiga cikin gidan naga ashe gidane babba dake dauke da mutane kala kala kuma wai duk irin ginan bamboo tree daine ko a cikin gidan.
Wasu zakaga nasu har AC akwai a ciki wasu ginan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login