Showing 249001 words to 252000 words out of 382072 words

Chapter 84 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28365

dawo da Alh ko ?
Abba ya dawo ta tambaya a cikin mamaki tare da fadin nidai yanzu naga ya shigo ya shige part din shi baicewa kowa komai ba.
Waiko Nazifa kin san abinda kikeyi kuwa kinsan me ake nufi da aure to mama ya fita bai fada min inda zai tafi ba ya dawo sai nace mai me ?
Tsuki uwar taja mai karfi tana fadin zaki shukawa kan ki tsiyane wata rana ji yadda su Alh gyade suke bada labarin yadda aka kai ruwa rana dashi sai da kyat da sanin koshi waye suka ba da bellin Alh yau.
Nikan bai fada min ba son haka ban san yayi ba yanzu ina Abba din yake ta tambaya yana nan gida mana tare suka dawo dashi ai.
Zan iya kiran shi yanzu ta tambayi uwar cikin nuna ta gaji da wayan lokaci ki kira din ko zai dauko yanzu dai ya shiga wanka don mutane sunyi yawa saida aka rufe gida ya samu ya huta.
Barin bari sai gobe na kirashi kada ki soma don nasan halin ki da sakaci ko goben sai lokacin da kikaga daman tashi da barci zaki zo don haka ki gwada kiran shi a yanzu ko zai dauka.
Tace zan gwada barin bada minti biyar nan gaba amma fa ina ganin tsiyan da mukayi da baban maryam ne a daren jiya yasa ya tafi yau din.
Shirmen banza shirin tafiyan da sukeyi yau kwana hudu ke nan zakice wai kunyi tsiya dashi kan haka yasa kila yaje indai zaki gyara ki gyara don iskacin ki ba inda zai kaiki .
Kallon wayan tayi bayan uwar ta kashe taja tsuki tana ajeshi a gefe daya kafin ta dan fada tunane na san lokaci tana nazari can ta kalli me aiki tana fadin haule ki kwashi yaran nan zuwa daki gani tafe yar aikin ta amsa da to hajiya.
Dakin ta shigo a dai lokacin data sameshi ya zuba ruwan tea din daya dafo a kicin tana waya bata ji fitan shi ba har ya gama ya dawo dakin shi kuma ya tsunci wani abinda take fadi a lokacin daga inda yake.
Yana tsaye daidai saitin window dakin dake bude iska na shigo mashi yana tsiyaya ruwan shayin tashigo da sallaman ciki ciki.
Dan juyowa yayi ya kallota kafin ya mayar da kanshi ga abinda yakeyi a lokacin ta karaso tana fadin ashe tafiya kayi yau din baka sanar muna ba.
Eh tafiya nayi lokacin dana fita baki tashi daga barci ba a lokacin OK ta fada tana kaiwa zaune can tace dashi kuma ashe anyi nasaran fito da Abba yau din ke nan.
Eh anyi don munyi magana da wace ta tsare shi tace a sakoshi ya nemi kudin idan babu su ya biya company abinsu .
Wai saima data saka baki ke nan ashe aka sako Abba din ta fada cikin mamaki yace eh dama ba abinsu ya taba ba.
Shiru tayi tana binshi da kallo ganin cewa duk maganan da sukeyi bai juyo ya kalli inda take ba yake bata amsa.
Mama ce ta bugo min take fada min cewa kaine kayi kokari har aka sakoshi din eh hakan ai rufin asirin kowane banyi don wani ko wata ba ni kaina nayiwa hakan ai.
Bata kara tanka mashi ba sai nazarin da takeyi a cikin zuciyar ta kafin can ta nisa tana mikewa tace dashi saida safe Allah bamu alheri ya fada shima.
Washe gari sai goma ta isa gidan nasu ta samu har mai aure abuja ta iso a lokacin duk suna falo tare da mahaifin su ta shigo falon kowa ya bita da kallo.
Gaban mahaifin nasu taje ta gaidashi ya amsa take gaida shi tare da mai Allah ya kara tsare gaba ya amsa cikin rashin walwalan data sameshi a ciki .
Wai Abba ita din waye dahar take da iko haka da zatace zata wullakantaka mu kyaleta haka kawai wata banza can tazo ta batawa mutane suna wani dan shi saurayi ke fadin haka.
Shiru mahaifin yayi kamar baiji shiba ya share zancen dan nasa don koda ya dawo jiya duk yana cikin tashin hankali sosai matarshi ta biyune ta shigo tana fadin wai Alh Inusa suna falon ka na baki suna jiran ka.
Sun iso ke nan ya fada yana kokarin mikewa da sauri nan ya fice yabar yaran nasa a cikin damuwa suka fara mikewa zuwa cikin gida inda uwayen su suke.
Mommy ne tashigo falon daddy din da sallama ya amsa mata tana binshi da kallo don taga yana shirin fita haka da sassafe kuma hakan ba dabian shi bane sai idan wani abu ya faru yake fitan safe haka a cikin garin.
Ina kwana tayi mai ya amsa don irin kallon mamakin daya kula tana mai yasa yace gida Nuhu zamu don ya dawo jiya cikin dare akace.
Wallahi nima hjy salma takirani tana fada min har na kirashi mun gaisa dashi tun jiya din yace OK yanzu ni zan tafi can din.
Ya kafa hula akanshi ya dauki waya yana mata sai ya dawo tayi mai Allah ya tsare a tare suka fito daga falon don bata ko zauna ba ya fita.
Tana komawa part din ta yaranta ne a zaune falon ta samu wuri ta zauna kallon su tayi don ta fahinci akwai maganan da sukeyi suka ganta suka shiru.
Daddy bai tashi bane Nabila ta fada ya tashi mana ya dai fitane zuwa gaida yaya Nuhu daya dawo jiya.
Au yadawo ashe ya dawo jiya ance yayan kune yaje ya fito dashi wai dama jiya yanzo nan da safe yana sallaman mu zasu tafi wurin shi.
Mommy wai kinji kuma hauwa ta fada sai sauran suka kalleta da sauri me akayi mommy din ta tambaye ta ?
Wai aahe Sufynu yana shaye shayene da gaske yaba baby kashi har ta dawo gida jiya saida wanan yar ta anty tazo ta mayar da ita.
Subbahanallahi mommy ta fada da sauri har da duka tace wallahi wai ya farfasa mata jiki ya korata kai Allah ya kyauta har yaushe akai aure da haka ya fara biyowa baya ?
A mommy dama ai sun sani suka yarda baki nawa ya fada masu cewa baida hali amma saboda kudin da yake basu ya rufe masu ido har da cewa anty tayi ana masu bakin ciki da hassadane da nakin ciki don anga yarta tayi saurin samun miji.
Indai yan gidan uncle ban hana wanan Isma,il din nan ba shine mai dama nidai ga yaran gidan nake gani jinan mommy ta fada duk suka dago suna kallon ta .
Bana son jin irin wanan maganan a bakin ku da baby din da shi Sufynu din duk yan uwan kune don haka kowa matsalan shi ya shafe ku ku kama bakin ko kuyi masu addua.
Shiru sukayi wanan yasa tun farko basu son mommy din taji zancen a bakin su hauwa kuma ta fada mata yanzu don haka basu so ta fada mata ba.
Yaushe ne hakan ya faru mommy ta sake tambaya hauwa ta kalli Faiza tace ga wace ke fada muna yanzu mu.
Faiza ta bata rai tace nima Fatimace ai ta fada min tace wai mommy ta kora su waje don baby tazo mijinta ya duketa sai take ban labari.
Shiru mommy tayi bata kara magana ba bayan Allah kyauta data fada ta dauki remote din tv tana canza chenal Faiza ta mike zuwa daki.
Falon cike yake da ire iren su ana hayaniya daddy yayi sallama ya shigo suka amsa banda Alh Nuhu daya kawar da kanshi gefe tun shigowan daddy din falon.
Gaisawa ya fara yi da mutanen daya sama a wurin suma suna amsawa a cikin girmamawa mutuntashi don girmanshi da irin darajan shi.
Har kasa ya duka a gaban shi yana bashi girman shi na matsayin shi babban yaya a garesu a family su.
Hakan ya kara fasa kan Alh nuhun dole ya juyo yana amsawa babban mutum kamar daddy ya bashi girma haka a gaban kowa aishi babu kamarshi ya sani.
Yaya ina can ina jin yadda abubuwa suka dinga gudana yace a cikin basarwa eh abune mai kama da an shirya shi dama saidai ai zai koma kan duk wanda ya shirya haka don baisan Nuhu ba dakyau yasa aka kulla hakan don kawai a tozartani a idon jama,a.
Shi abu idan yazo a daina sa zargi a cikin shi don duk nan mun sanda haka na iya faruwa da kowa a kan harkan shi ba komaine muke samu yazo muna daidai ba yadda muka tsara.
Kwarai kuwa wanan haka yake Alh Bello ya fada daga inda yake zaune yaci gaba da fadin kai kasan idan ba kaddara ba har yaushe wanan yarinyar me kama da yar tsana zata zo tayi nasara haka a kan mu lokaci daya.
Kada kai mamaki Alh bello ina fada ma wanan abin kamar wani shiri ne akai muna akan hakan don kawai aga mun tozarta a idon jama, a.
Ban dauka yadda kake tunane bane Alh hakan dai kamar wani al,amari ke shirin faruwa haka na dauki zancen idan kayi zurfin tunane .
Me kake nufi da hakan daga fada Alh Nuhu ya tambayi Alh Bellon abokin shi yana mai tsure shi da idanuwan shi.
Eh ko ka manta da kowa nan abinda kake tunane ya shafeshi sallaman wasu abokan sune ya dakatar da faaa kwan da Alh bello ya tashi yi a lokacin.
Mikewa daddy yayi yana masu sallama da niyar tafiya yana furta Allah ya tsare shi zai koma idan ba damuwa zamu iya ganin juna karfe hudu a gidan gonana Alh nuhu ya fada.
Ba damuwa Allah ya kaimu lokaci lafiya ya fada ba tare da damuwa da komai ba ko darrr yadda wasu keji idan ya furta hakan.
Daga inda muke tsaye muna hangosu kan shi a duke Ganiyat nayi mai magana kanshi yana a duke can ya dago ya tura wayan shi cikin aljihun shi.
Kai tsaye ya taka zuwa inda Alaja suke zaune da mutanen ta yai magana dasu na dan second ya juya yayiwa Jimoh alama da hannu jimoh ya taso da sauri ya sameshi.
Mun hango dai jimoh na kada kai kafin ya juya zuwa wurin yan uwan tafiyan mu yai masu magana shi kuma ya nufo inda muke tsaye din kai tsaye.
A nan ya same mu mu tafi yace damu kawai yai gaba muka bishi a baya zuwa wurin da aka tanadar muna motocin da muke amfani dasu kasan.
Kai tsaye wurareb tarihi muka nufa ranan munsha yawo shikan sai aiyu kan shi yake a cikin computer din shi dake lake dashi Jiddadun Alaina.
Mun dawo masaukin mu a gajiye sai shirin tafiya kamar yadda ya fada muna zamuyi gaba a ranan su alaja zasu biyo mu baya idan Aishat Ganiyat ta karbi kayan ta daga makaranta.
Karfe goman dare na ranan muka daga zuwa Dubai muka sauka da safe ana a can ma mun samu masu taron mu kamar yadda aka shirya.
Masauki maikyau ga nagarta da jin dadin rayuwa nikan tun bayan sallah dana kwanta barcina nayi sosai sai uku na rana na falka koshi don sallah dana tuna yana kaina banyi ba.
Na idar na zauna ina addua tare da jan lokaci don la,asar daya gabato a lokacin saidai kafin lokacin cikina ya fara kiran ciroma .
Gaskiya a wanan tafiyan mun sheda cewa Oga Sha,aaban ya nuna jin dadin shi ga aiki mu kamar yadda ya fada din don a gaskiya mun ga gari gari ya gan mu.
Shin shi mai hali Allah kan ga zuciyar shi yai mashi zarafi duk da ba duka masu halin Allah yaiwa halin kwarai haka ba akwai irin su baffana Nuhu da suka riki arziki abokin tafiya lahira a garesu.
Wani kuma mai kudin Allah kan bashi basira da zai gane cewa yiwa wasu shine abinda zai tsira ya samu daga cikin arzikin shi a gobe kiyama.
Samun irin su kalilan masu kafin basira da tunane a wanan zamanin zakaga wani a cikin daula kamar ba gobe gare shi wanan yasa ya shagala imanin shi baya kaishi tuna halin da rayuwan wasu suke aciki.
Amma saidai cikin dubu akan samu goma da zukatan su fal yake a wurin taimako taimakon da zai zama silar dagawa wani dagawan wani da shi kuma fiye da mutum dubu zasu karu a dalilin shi nan gaba duk ta dalilin mutum daya ubangiji Allah ya karawa mai arzikin taimakon tallaka arziki na duniya da kiyama Allahuma amin.
Nayi wanan bayanin ganin yadda ogan mu ya tallafawa rayuwa cikin rayuwa da yayi sanadin dagawan wasu da dama a dalilin shi bawa ya tuna idan har Allah ya bashi ikon aikata hakan wani irin lada zai tara a wurin Allah wanda ya samu a sanadin tallafawa rayuwan mutum daya rayuwa itama ta ceci rayuwan dubu nan gaba ?


ZAINAB IDRIS MAKAWA



ANA DARA GA , , , , , , , ,

7️⃣4️⃣ BY, , , , , , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MUH,YI , , , , , , , , ,



ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257

ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋

Kamar yadda suka aje din hakane ya kasance da daddy don da yamma ya shirya zuwa gidan gonan da Alh Nuhu ya gaiyace shi zuwa da sunan zasu gana.
Saidai yai masu bazata ga zuwan don ranan ya fito masu dsp din shi sak don mota biyu yazo dashi da wanda yake ciki driver yana jan shi sai dayan motan da security uku a cikin shi sun mara mai baya.
Tun tsayawan su wurin hankali ya dawo gareshi har yafito a motan yana bin motocin wurin da kallo don ya sheda ko motocin su waye a wurin.
Har ciki security din suka rakashi a kofa ya tsaya ya daga masu hannu su dakance shi wurin suka ja baya suna jiran shi.
Kallon juna na tsayen sukayi lokaci guda kafin su mayar da idon su akan daddy din da yashigo a gadarance yana binsu da kallo ya samu wuri ya zauna bayan ya basu hannu sun gaisa.
Alh Nuhu Sai wani cika yakeyi yana batsewa kafin ya bushi iska daga bakin shi yana sauke ajiyan zuciya yace Ali dpc kai muke jira duk nan daka ganmu kan zancen mu dakai na shekarun da suka shude a baya.
Don nasan ganin iyamu ne zaune a wurin nan mu da wanan abin ya shafa zai iya tunama da ko wani zance nake magana a yanzu.
Don haka ba sai na bude baki na fadama cewa ga dalilin gaiyatan ka nan da nayi ba a yanzu don kaida dan ka kunci amanan mu da kuka dawo da ahalin Sambo yanzu a cikin mu bayan tsawon lokacin da suka dauka da bace a cikin duniya .
Yana kaiwa nan ya ja yayi shiru a cikin hasala yana wani irin mazurai da ido kamar zai kama da wuta lokaci guda.
Jin yayi shiru daddy dake dan motsa hannayen shi daya harde a cikin yan uwa yana wasa da yantsun hannun nasa yana kuma sauraren abinda dan uwan nasa ke fadi a lokacin.
Ya dago kai yana gyara zama tare da gyaran murya kafin ya fara fadin Alh Nuhu wanan ne dalilun da yasa kuka gyatoni a nan yanzu ?
Don kuna ganin ko zaton na aikata wani abinda bai dace ba zuwa gareku sai kuma ya girgiza kan shi alaman takaici gami da sauke murmushi a fuskan shi yace.
Idan ma har abinda da kuke zargina dashi a yanzu gaskiyane haka din ne eh hakan ne don tun farko aina fada maku ni duk ranan da akaga mutanen nan a shirye nake da in rungumesu in kuma danka masu abinsu dake hannuna a lokacin.
Bai gama rufe baki ba Alh gyade daya kai iya hasala yace dashi billahillazi karya kakeyi Ali kayi kuma kadan a yanzu.
Kai kai kai Gyade aika bari mu gama jin shi tukuna ayanzu kafin wani ya furta wani kalami a gareshi don dama ai gaskiyan zancen muke son ji daga bakin shi tunda ance tun farkon maganan nan yaki ya furta komai a kai har yanzu.
Au da me kuke son in furta bayan nasan gaskiya cewa su din daine a yanzu ubangiji ya dawo muna dasu cikin mu ta sanadin dana daya gan su ya daukosu zuwa gidana har suka zauna tare damu na shekara kusan biyu kafin kuma nayi nadama da bakin ciki akan abinda ya faru a tsakanin mu dasu abaya.
Ban fada maku cewa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login