Showing 42001 words to 45000 words out of 382072 words
ba zaka kaini ba zan kira Haroon ya kaini tunda tare dashi kuka je gidan yasan wurin.
Shike nan daddy sai mu tafi taren ya fada idan kaji sauki sai mu je lagos din a tare in hakan zai fi ma sauki zaifi Alh ya fada.
Haka ya fita daga dakin cike da zargin mahaifin nasa don gaba daya abin ya kulle mai kai a yanzu ya kasa gane meye hadin shi da wayan nan mutanen da yake nemane wai har yake zatin yarinyar nan nada alaka dasu yanzu.
Dakin mahaifiyar su ya nufa ya samu ta fito wanka tana gyara jukin ta ya shigo kallo daya tayi mai ta fahinci damuwa a tare dashi take fadin.
Zaka sakawa zuciyar ka damuwa akan wa yan nan mutanen ni yanzu na bar sakawa kaina damuwa kan lamarin wayewar karima na shashanci.
Mommy anty kuma ina ruwana da lamarun ta a yanzu tunda ba zamana takeyi a gidan nan ba shi daddy da yaji ya gani shi suke ba kunya ai.
Ido uwar ta bishi dashi tana nazarin sa kafin tace ai dole muma mu damu da haukanta tunda ta sakamu gaba a gidan har ku.
Don tsaban samun wuri karima zatace wai idan wani abu ya samu Alh kaine silar hakan don dakai kukai waya ya shiga wanan halin don haka kaine silar.
Kai innalillahi haka ta fada yana kallon mahaifiyar nasu da wani irin kallo na mamaki kafin yace.
Zato zunubi don koni bansan dalilin da yasa daddy din shiga wanan halin ba daya shiga yanzu.
Har kuma da damuwa da har takaishi kwanciya asibiti kan wanan zancen da mukayi dashi kawai a waya din ban san hadin shi da wanan mutanen ba.
Wasu mutane ke nan kake magana a kai wai hjy ta tambaya a cikin mamaki tana kallon dan nata da shima ita yake kallo.
Wallahi hjy ban san ko suwaye ba su na dai san a lagos suke zaune daga kawai naba daddy din musalin su yace wai yana son ganin su.
Matane ko maza hjy ta tambaye shi ya dago kai ya kalleta kafin yace da ita a sanyayye wata yarinyace da mahaifiyan ta da sukai bala,in kama da yan gidan malam na tudun wada.
Wai malam mahaifin mu ko wa yace malam dai namadi naku hjy ya kara fada wani kallo tayi mai ta mike tsaye tana saka hijab din ta tare da fadin kana da photo sune a wurin ka.
Ban dauki photonta ba tunda nidai nasan ba wani hadin da ake dasu kamane kawai na yanayi sukayi da yan gidan.
Ikon Allah ashe har yanzu zancen iyalin Badaru na cikin zuciyar Alh don nasan su yake hasashen ko sune aka gani a can din.
Wani ne hakana kanin mu mana daya bata har yau ba a samu labarun shi ba ita kuma matar da yarta an nemesu ko kasa ko sama ba asan inda ta shiga ba ga ciki koda ta bar gida har ya fara tsufa a jikinta don cikin zaikai wata hudu da dan kai a lokacin.
Shiru yayi yana tunane kafin yace anya wa yan nan sune kuwa do naga uwar yarinyar kama wata yarece fa.
Ina fa za,a gansu tunda tunda yanzu kusan shekara goma sha wani abu ke nan da batan su ya dauki zancen tsawon shekaru yasa a zuciyat shi.
Shima dai Abubakar din yasa zancen a ransa yana faman tunane kala kala meyasa sai daddy ne zai damu haka bayan ga yan uwan su nan suna harkokin gaban su basu damu ba.
Washe gari tun cikin dare na tashi na kwaba filawan yadda nake so don na iya kwabin washegari da safe ina idar da sallah na shiga soyan da wani murhun tsoho dana tsinto na gyara a bayan dakin mu.
Take kamshi ya karade ko ina na gidan mutum zai gane ana suyan wani abin filawa a lokacin.
Sai ga yan gidan dake fitowa suna wucewa wurin sana,oin su suna tambaya na sayarwane nake cewa eh.
Sai gashi tun ban fita ba na sayar ga baki daya a wanan gidan har ma bai isa ba don ban samu aje muna ba don mu karya dashi.
Daga wana ranan sai na samu sana,an yi idan nayi na safe ya kare saina kwaba na ran da zan fita dashi waje in sayar.
Sai ya kasance ina suyan umma nabawa mutane masu saya ni kuma nakan mayar da hankalina akan suya .
Sai gashi har wasu wure an gane shigo a saya, muka kwasa muka koma wajen gidan ga badaya don abinka da dan Adam.
Sai gashi an fara nuna muna hasada ga sana,an tamu har mun samu wa yanda suka fara irin sa a unguwar duk da dama sunayi saidai ba a lokacin da muke namu ba din.
Yau ina son zuwa cikin garine don da shirin haka na kwana a raina ba kuma komai zai kaini ba can don saro kaya da sauki don yanzu kan mun wuce sayan mudu mudu da muke saye a da.
Sun shirya tafiyan kamaan yadda suka tsara bayan sati biyu a lokacin har Abubakar din yayi tafiya zuwa onicha ya dawo lokacin daddy ya murmure ga baki daya.
Duk yadda hjy karima taso jin dalilin tafiyan su a tare ta kasa gane komai sai ta dauki hakan da wani abu zai kaisu can din tare.
Tafiyan safe sukayi suka shigo cikin gari haroon ya dauko su daga airport din zuwa wani hotel inda zasu huta suci abinci.
Bayan sun gama ne suka shiga mota sai tsohon gidan mu da muka tashi haroon dinne ya fada masu mu suka zo nema da cewa wanan shine mahaifina.
Mamaki sukayi suke fada masu ai mun tashi daga unguwan yan makwanin da suka wuce mun koma wani wuri na daban suma bamu fada masu inda muka koma ba.
Ran Alh ya baci sosai da jin hakan sai ya dauki laifin ya dora gaba daya kan Abubakar da yaki yarda ya kawo shi tun lokacin da yaso zuwa din.
Basu gane komai ba legas kuma ba karamin gari bane da zasu saka cigiyan mu har a samemu a cikin sauki don haka suka bada lamban wayan haroon da yafi kusa idan an ganmu a kirashi akwai kyauta da zasu bayar.
Haka Alh ya dawo gida ranshi a bace duk da bai tabatar da cewa mu din bane ko wasune a lokacin amma haka yaji rayuwan shi ya baci da rashin ganin wa yan nan mutanen.
Kafin takwas na safe har na gama soyan bounce din na aje a cikin katon roba duk wanda yazo saya umma ke kidaya masa hamsin hamsin
Na fito a cikin shiri na samesu tare da ladi a tsaye gurin da muke suyan waje umma i wan go naw na fada tace seb joni take care of ur self nace yes ma na juya na fita bayan na dan taba kan Amar dake mikawa wasu fanke.
Mota a legas ba matsala bane don haka ina zuwa bus stop ji ana fadin my2 apapa ajagule agege ikeja da dai sauran wurare a cikin garin.
Wanan hjy ta fado min a rai da muka taba haduwa a asibiti sai kawai na fada motan ikeja condaster din motan yace min dari biyar na zaro na mika mashi ba tare da damuwa ba.
A inda suke saukewa na sauka na samu mai mashin nace ya kaini toyin road yace dari biyu ba haye tare da fada mai street din da zani.
Ban manta lambam gidan data ban ba sai gamu a kofan gidan nabiya shi kudin shi na fara tafiya zuwa kofan gidan.
Kwakwasa get din gidan nayi saubiyu kafin na mayar da hankali ina karewa unguwar kallo naji an bude get din gidan maigadine ya leko yana fadin.
Who de nock nace nice who u de look nace hjy halima kafin kuma ince maman Bilal yace i de come ya koma ciki sai kuma ya sake lekowa yana fadin.
Waitin be ur name nace tell her na Sahiba d girl she meet at hospital ya dab kalleni na dan lokaci ya juya ya shige ciki na gyara tsayuwana a wajen.
Can naji an bude kofan sai na hangota tafe bayan maigadi tana tafe cikin takon kasaita irin na manyan matan hausawa.
Fuskan ta dauke da murmushi tana fadin wai mafalki nake koko dai yau Sahiba kece a gidan namu yau kin tuno damu ke nannta fada a daidai lokavin data iso inda nake tsaye din ta riko min hannu tana fadin barka da hanya ya mamanki.
Gaskiya nayi farinciki da zuwan ki don har na debe tsamani da ganin ku kuma a garin nan nayi dan murmushi muka karasa shiga cikin gidan.
Falo muka fara samu ya tsaru iya tsaruwa da kayan alatun zamani nayi sallama tsohuwar gidan tana zaune tare da jikokin ta a falon saman dima diman kujerun daya zagaye falon.
Ta amsa min sallamana fuskanta itama cike da murmushi fa tasbaha a hannun ta tana ja a dayan hannun ta nuna min wurin zama tana fadin.
Ashe kun samu rabarin rasuwan mijin nawa ke nan kuma sai na kalli hjy da mamakin abinda tsihuwar ta fada naji hjyn tace ai bata sani ba mama ina zataji inba yanzu data zo ba.
Ke yesmin kice a kawowa bakuwata abin sha ta fada tana kallon wata matashiya dake zaune a falon tana karatu gwanin ban sha,wa.
Don dai taban sha,awa yadda naga ta zauna ta mayar da hankalinta ga karatu ba abinda ya dameta a rayuwan ta ita .
Itama mikewa tayi bayan tayi min wani irin kallo na yatsuna ta shiga ciki bata dadeba ta dawo ta zauna tana fadin na fada mata anty.
Ok hjy tace ta juyo gareni nace ina wanan dan naki da baida lafiya sai ta dan lumshe ido kafin ta jingina bayan ta da kujera tana fadin ai ya rasu sahiba.
Bayan barin ku asibiti mun dan kara kwana a asibitin har an sallamo mu ranan cikin dare ciwon ya tashi kuma maka kwashe shi zuwa asibiti kafin mukai yace ga garin ku.
Yeh na fada instead ince innalillahi nace u mean dat boy has pass away oh may his soul rest in piece tace amin aishi ya huta ya tafi ya barmu da duniyan nan mai wahalan zama.
Lokacin mai aikin ta kawo lemon fivealibe da ruwa ta aje a gabana tana gaidani na amsa a cikin ladabi.
Ta juya ta wuce a lokacin ne hjy ke fadin nasha don na kwaso ranan da zafi ga tafiya can kuma tace ai kuna Ajagule ne dazama ko ?
Na dan kurba lemon kadan na aje ina fadin mun bar ajagule tun bayan barin mu asibiti da kwana biyu muka sake unguwa.
Yanzu kuna inane ta tambaya tana kallona nave muna seme boada semi boda ta ambata a cikin mamaki tare da fadin yanzu daga can kika zo ke nan ?
A cikin ladabi nace da ita eh daga can nake nazo sayen filawa ne da muke bounce dashi a cikin gari don a company yafi sauki sosai.
Fuska ta bata tana fadin kai banji dadin jin hakan ba gaskiya har ina tunanen wata rana nakai maku ziyara ashe kun kara nisa damu din kuma yanzu.
Akan me kuka tashi a nan inda kuke ajagule din nayi dan raurau da ido kadin nace nima bansan dalili ba saidai ina hashen ko umma taga kamar an fara gane muna nan ne zaune a unguwar oho.
Gaskiya kin kyauta da kizo inda muke da ba haka ba ba zamu san inda kuke ba a yanzu.
Na dan kara kurban juice din kafin in mike ina fadin zan koma kada dare yayi banje na saya ba a rufe wurin tun yanzun zaki tafi ta fada nace eh nagode.
Daki bari agama abinci idan kinci sai ki tafi ai ke tafi da yunwa yaushe kika kasan layi zaizo kanki idan kin tafi.
Na danyi murmushi ina fadin ban tare da yunwa hjy ko hakan ma nagode na kara fada ina kokarun fita daga falon .
Tace dani tana zuwa mike zuwa cikin dakunan kwanan su tadan dade kafin ta kwala wa yarinyar nan data kirata da anty kira ta mike ta shiga dakin ta sameta.
Sai gashi sun fito yarinyar na dauke da leda a bayanta ta nufoni cikin murmushi tana fadin na barki a tsaye ko Sahiba ga wanan sai ki kara ki sai filawa din.
Wanan kuma kuyi amfani dashi dake da ummantaki daga yau dan Allah idan kin shigo ki dinga zuwa muna gaisawa don a sada zumucin.
Dafe baki nayi a cikin mamaki abin alherin da tayi min ina fadin haba idan tana min haka ai ba zan sake zuwa gidan ba.
Ko yanzu ma wallahi hankalina bai kwanta ga yadda muka bar yaron ta bane da jiki a lokacin shine naga dacewan shigowa in kara duba ahi ashema baya raye a duniya shi.
Nayi godiya na karbi kayan ta rakani har bakin get din su mukai sallama ta dawo ciki ni kuma na tare wani mai mashin daya kawo wasu mutum biyu na fada mai inda zai kaini na haye.
Na samu layi sai dai ba wani dadewa tunda a kwai kaya a kasa na saya lokacin biyar na yamma yayi kusa.
Mota ya fara wahala don haka na dade a titi kafin in samu abin hawa a can other side din titin kamar ance ya dago kai ha hango wata kamar yarinyar nan da sukazo nema shida daddy .
Da sausauri yayo turne zuwa in da nake tsaye saida irin nisan u turne din su na legas kafin yazo har na samu mai napwp munyi jinga zai kaini har semi din har na wuce na bar wurin.
Tun yana iya bin mu har muka bacewa ganin sa ya daki sitiyarin motan yana jan tsuki don haushin da taji a lokacin.
Kodana isa seme boda na iske hankalin umman mu a tashe suna waje da Amar duk da duhun daren dake akwai sunyi zugun suna jiran suga inda zan bulo sai ga my nape ya tsaya dani a kofan na fito.
Dubu biyu ya cajeni banji haushin bashi hakan ba don dare yayi sosai a lokacin umma ta mike ta nufo ni tun nan ta hauni da fada kamar zata mareni a lokacin nayi shiru sai me nape din ne ke bata hakkuri yana fadin koshi ya tausaya min ne ya kawoni don ba mota dare yayi lokacin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , ,
DANA DARA GA, , , , , , , , ,
1️⃣4️⃣
BY
ZAINAB IDRIS MAKAWA YAURI , , , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIN AR-RAHAMAN, , , , ,
PAID ONLINE NOVEL NE YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DON DARAJAN ANNABI DA KOYIN SA, , , , ,
Ganin irin kayan da driver ya jibge min a kofan dam gidan namu na ciro kudin shi na bashi yayi min godiya yana fadin daga yau na karbi lambam shi har in muna da sako a cikon gari sai mu baga ya sayo muna ya kawo mu bashi kudin shi tunda yaga mu mutanen kirkine shima bahaushe ne dan uwan mu mutumin jahar sakwato ne shi.
Umma tayi mai godiya ta karbi dan katin shedan daya bata mai dauke da layin shi a ciki yaja keken shi ya wuce.
Kayan na fara dauka naji umma tace dani Sahiba wanan uban kayan a ina kika samu kudin sayen shi don ba zan fara zargin ki akan wani hali da ban sanki dashi ba a baya har yan amin su amsa min.
Wallahi umma duk abinda kikaga na sayo da kudina na sayo shi na sana,an nan sai kuma wanan hjy ta asibiti data ban kudi na hada na karo dashi don kayan ya dauke mu wani dan lokaci.
Wani irin kallon mamaki tayi duk da duhun dake akwai saida na gane hakan muryan yan gidan ne da zasu shiga suke fadin ur daughter don come back ?
Ta amsa a sanyaye tana fadin ehn she don come back naw thank u for d care suka shige abin su ni kuma na fara kokarin jan kayan zuwa cikin gidan don mai keken ya taimaka ya kai min buhu ukun ta dan cikin gidan kadan ya aje ya tafi.
Haka nayi ta wahalan jan kayan zuwa cikin dakin mu har Allah ya taimakeni na kwashe su kaf nakai ciki na zauna ina haki.
Muryan Amar ne ke fadin u no buy some tin for me sister i no eat anytin since i de wait for u to come back.
Nasan da hakan don son junan da mukeyiwa juna guntun juice din da nasha gidan hjy tace in tafi dashi da naman data saka min a cikin ledan na ciro na bashi sai take away din da na hado muna idan na dawo muci duka na aje a gaban shi.