Showing 96001 words to 99000 words out of 382072 words
baya ba.
Daddy bai tsaya ba ya shigo motar shi ya bar gidan kanin mahaifin su din yana cike da bakin ciki tare da tunanen yadda Nuhu ya dauki kanshi da girma har yana ganun yana iya taka kowa a yanzu.
Dan guntun murmushi ya sake a fuskan shi don yin wani tunanen da yayi a zuciyar shi tare da dan dukan sitiyarin motan da yake tuki.
Tun jiya muke da labarin dawowan daddy din a bakin fa,iza saida bamu samun ganin shi ba sai da yamma suna zaune tare da ya Abubakar mun dawo daga islamiya muka ganshi.
Wurun su na nufa nakai har kasa ina gaida shi kafin na juya ina gaida ya Abubakar din dake zaune a cikin bacin rai yayi dukun dukun da ranshi.
Daddy ne yake tambaya muna karatu sosai ko nace muna dai tabawa don na kusa fita harufa zan iya hada kalma yanzu yace yayi kyau mu mayar da hankali nagode nace na mike zuwa cikin gidan.
Yabini da kallin tausayi kafin ya juya yana cewa dan nasa komai ya kusa zuwa karshe don ba zan bar yaran nan haka ba ana kokarin aibantasu a cikin yan uwa.
Gashima a cikin gida har karima tana zargina a kansu da uwarsu akwai abinda yakai wanan muni a rayuwan bawa a sheganta ka don wani dalili can na daban.
Yaba zaune yadda yake ya kurawa mahaifin nasa ido don baison tuna wanan zancen ko kadan kafin yace .
Daddy tun farko ban so ka boyewa kowa wanan zance ba tunda ba tsoron su akeji ba don baka san ko waye wanan yarinyar ba kake dauka ba zata iya kwato wa kansu yanci akan komai ba .
Tayi kankanta ga yadda kake nufi amma yanzu ai dole in fasa kowa ya sani don nasan ko waye Nuhu idan ya fadi magana da wasa kada ka dauka wasan ne yake maka kaima don zai iya aikata abinda ya fada.
Saidai kaima modibbo ya zama dole ka kara jajircewa a ko wani lokaci ka zamo kuma mai hankuri da matar ka don kasan irin da uwarka ta zaba ma.
Kamar yadda muka saba dakin mommy mukan fara shiga mu gaida ita kafin na hjy karima karshe wanda yaga dama a cikin su yakan leka umman mu a part din mu ya gaida ita.
Muna shiga a yadda muka samu mommy din yasa ban tsaya ba na fito zuwa dakin hjy karima na tsaya daga kofa ina gadai ita ta amsa min ba yabo ba fallasa lokaci daya muka shigo da diyanta.
Don har babban tana gida an samu hutun makaranta a lokacin bayan fitanane suke fada mata ai nice na goya Amira da zamu tafi kuma na dawo da ita a goye don ta taka wani abu da zamu fita tana kuka.
Da sauri take fadin taga kafan yarinyar sai babban take fadin wanan sahiba din cire mata shi kuma tayi mata addu,a a wurin.
Mai karatu idan baku manta ba nayi tallan magani a lagos kuma matar da mijinta sun yarda danu sun ban nasha sin kuma fada min wasu ina kuma gwadawa yana amfani sosai a tare dani a yanzu.
Bayan na shiga ban tsaya ba don na samu umma har part din ta gyara ko ina tayi abincin da zamuci.
Wanka na shuga na fito na saka wani dongon rigan silk a jikina sallah nayi don magariba ya gabato sai bayan mun idar din muna zaune a falo ne da littafi a hannu don haka kawai naji bana son cin abunci a ranan.
Sallaman hjy karima ne a kofan mu take shigowa dakin muka karba kallo daya nayi mata nikan na dukar da kaina naci gaba da karatun da nakeyi.
Sai bayan sun gaisa da umma ne naji ta abanci sunana tana fadin sahiba yau meya samu kafan kanwaki ne haka.
Na dago da sauri na dan kalli gurin da take tsaye din ina fadin ina ganin dutse ta taka ko wani abu kafan ya dan mata ciwo.
Amma na lalasheta tayi shiru mantawa nayi i fada a gasa mata da ruwan zafi da muka dawo kada wurin yayi mata ciwo da dare.
Amma ai da takalma a kafanta na gani ta sake fada nace kaddara idan zai sameka sai ya samu sanadi don ban san yadda akayi ba ta cire takalman ta tako da kafa shine har hakan ya sameta.
Shiru tayi ta juya ta fita bayan tace dani ta gode ta barni zaune ina binta da kallo ta fita umma ta juyo tana fadin.
Bana fada maki ki rabu da yaran matar nan ba son bata da mutunci a dan maraice nace umma suke biyoni ni kuma ban iya daina kulasu don daddy.
Sallaman da akayine yasa umma fasa fadin abinda zata fada a lokacin tabi kofan da kallo kaina na kasa ban dago naga mai shigowa part din ba a lokacin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA, , , , , , , ,
2️⃣9️⃣
BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL WAHHAB, , , , , ,
ONLINE PAID NOVEL DON ALLAH YAR UWA KI BIYA KAFIN KI KARANTA NA FITAR MAKI DA ALHAKKIN RASHIN SANI NA FADA MAKI NA KUDI NE, , , , , ,
Mommy ce ta shigo da fuska a dare muka fara gaida ita bayan ta amsa ta samu wuri ta zauna take fadawa umma duk yadda aka kwashe da Alh Nuhu da take kira da yaya Nuhu da mijin ta daddy da modibbo .
Ba karamin mamakin faruwan hakan umma tayi ba don ban fada mata komai ba a ranan da muka dawo din.
Tambayana umma tayi abinda ya kawo hakan sai ban boye komai ba na fada masu kamar yadda su fa,iza suka mayarwa mommy din da zancen.
Ta dai fahinci ba laifina bane don ban mata wani abin bacin rai ba ra,ayin yin hakan daine tayi taso ta muzantani kuma abin bai tsaya a kaina ba sai ya koma mata.
Amma duk da hakan sunyi min fada wanda nake mamakin meye laifina a cikin hakan da har akaga laifina kan wanan zancen.
Tun wanan wajen nasha alwashi a raina cewa ba zan sake zuwa gidan su ba ko idan na ganta in gaida ita na kula wanan a cikin zuciyana ni kadai na barwa cikina hakan.
A fannin daddy da Alh Nuhu kuma shi Alh Nuhu yasan ko waye daddy din don sun sha buga irin wanan wasa a tsakanin shi Nuhun nakaiwa daddy hari baiyi nasara ba.
Don daddy tsohon jami,in tsarone yasan kansa son bai zauna kamar mace ba don yasan halinsu fulani da bakin rai ga riko kan dan abu kadan sai a salwantar da mutum ba komai bane a wurin su.
Lokacin da yan uwa suka watse daga gidan kanin mahaifin su sai duk hankalin su ya tashi da kakaman da Alh Nuhu din yayiwa dan uwan nasu mai taimakon su don sanin halin Alh Nuhu din da kowa yayi.
Domin bai fadin zance da wasa shi idan ya fada har cikin ranshi yake nufin hakan don hakane hankalin su bai kwanta ba musan man yan uwan haihuwan shi dcp din da shine jigo a cikin su a yanzu wurin shi suke dan samun hasafin rayuwa.
Daddy dake zaune yana lazumi bayan idar da sallah asuba yaji wayan shi dake gefe ya dauki kara kirirrr kirirrr daddy bai motsa ba saida ya shafa addua ya kai hannu ya dauki wayan daya kara shigo da sabon wani kiran da sallama .
Ba suna sai nomba tun kan ya dauka ya gane kiran nada wani manufa gareshi a lokacin.
Hello ya sake fada bayan sallamannda yayi din a kamar kausashe don ya fahinci kowaye ke kiran nasa amma ya daure cikin muryan izza da isa yace wake magana bakin shi fam da addu,a .
Bai dace na fadama sunana ba domin fadin sunana a gareka kamar na kaskantar da kainane gareka aka fada a dayan bangaren.
Dan murmushi manya da kamar ya zamawa daddy dabi,an sa ya sake tare da fadin nasan dama kana kufule dani nima sin jiran ka nakeyi a ko wani lokaci.
Au ashe kasan da hakan dama koda yake ni ba bakon ka bane ka sani don haka kar kaga kamar kaci bulus a wurina kaida danka ka saurareni nan da yan shekaru ka gani muddin danka yace zai wullakanta min ya wallahi sai inda karfina ya tsaya a kansu.
Don a iya rayuwana bana son rainin wayau da wullakanci balle har kaida danka kunemi takani ta hanyar auren diyana ku nuna wai ku mazane a gareta.
Aiko daddy yace dashi ashe kai kasan gaibu ke nan har kasan da cewa rayuwan namu zata kai nan da yan shekaru ke nan kuma.
Yana fadan haka kawai ya kashe wayan don baida likacin wanan bakin jahilin da jahilci yayi mashi katutu a zuciyashi yake kuma rudin shi a duniya don baida arabi da boko.
Yayi recording din komai ya nade a wayan shi ya kuma turawa danshi komai daya dauka din ya Abubakar yana gama saurare ya mike yana fadin lalai wanan mutumin dole su dauki mataki a kanshi ke nan.
Ya kuma kira daddy din suka kara tatauna maganan har daddy na fadin shu,umine na gaske shiyasa na turo maka koda yaka fito muna ta hanyar baya.
Duk da nasan ba zai iya min komai ba da yardan ubangiji duk da nasan cewa kafin duk ya aiwatar da wani abu mun gama tara komai da muke son samu game dashi insha Allahu sai mu rigashi yin komai yadda ya dace.
Wanan sakon da mahaifin shi ya tura maine yasa ya kara kaimi wurin hada duk wasu bayanan da yake son tarawa akan surukin nasa.
Yayin da syrukin nasa shi kuma a nasan bangaren yake kokarin bin hanyar da zaibi yaga ya halaka Alh Ali dcp har lahira karshe ya dan san tilon dansane zai gaji komai nasa sai yayan shi mata.
Daga baya kuma ya dawo ya halaka kanawar shi hjy Addah gadon dan nasu yayi yawa a karshe sai ya juyo kan Abubakar din da yasan yarshi ce zataci gadon shi tunda uwarshi da ubanshi basu raye idan diyan mata ta kama a kawar dasu suma sai abatar dasu a huta da banza kamar yadda ya shafe Sambo da iyalin shi a doron kasa har abada.
Wani shu,umin murmushi ya sake don yaga plain din shi ya tafi daidai ga yadda ya tsara komai a zuciyan shi shida kanshi yayiwa kanshi kirari da Nuhu maciji baka ramin kan kan ka saidai ka kashe ka shige.
Sun dauka wahalan bokon da sukayi shine sunfimu ko mai daya bayan daya zanga bayan yan iska daga su har iyalan su don ba fin kowa sukayi ba da zamu zuba ido muna kallon su a cikin daula.
Daddy bai koma ba mun dawo daga school muka samu mutanen gidan tsaye a waje in ka debe umman mu dake faman boyo a cikin daki wai yuka ya yanke hjy karima zasuje asibiti .
Muma da dawowan mu ke nan muka tsaya muna mata sannu a wajen har suka tafi kafin mu shiga cikin gida muna masu tausaya mata.
Wanan yasa yan abokan hurdan ta ke zuwa gaida ita dama wasu daga cikin yan uwa mijin da suka samu labarin hakan.
Da dare bayan magariba fatima yar ta na tsakiya ta shigo dakin tana fadin wai maman su na kirana a cikin mamaki na dan kalli umman mu kafin tayi min alama da inje nabi yarinyar zuwa part din su.
Tana zaune saman dogon kujera ta tallabe hannun don zugin da yakw mata ga bande an daure hannun dashi da gani dai ciwo taji ba kadan ba a hannun nata.
Nan na kara yi mata sannu na kai kasa ina fadin gani ta kalleni tana fadin na shiga wurun yaran don Allah in gyara masu shimfida .
Allah ya gani ban son wuce falon su iyakana in tsaya a falo in gaidasu in fita har in shiga ya kama min dole a part din su ke nan .
Saida na danyi jim kafin in iya daga kafa zuwa dakin na gyara ko ina na dakin tsaba duk da darene na wanko har bayin yaran da bai samun gyara na fito.
Na samu Amira tayi barci a falon zan dauketa zuwa cikine daddy ya shigo ya samemu .
Gaida shi nayi ya amsa min a cikin fara,a yana fadin mutumiyan tayi barci ke nan ashe na danyi murmushi na tafi da yarinyar fatima tana bayana ta nuna min inda Amira din ke kwanciya.
Kafin in fito ita yarinyar ta rigani fitowa falon wurin iyayyen dake zaune take fadin yau mami baki ga yadda anty ta gyara muna dakin mu ba yayi kyau sosai sai gani.
Ban tsaya ba nayi mata Allah ya sauwaka da saida safe na fita zuwa dakin mu ina shiga kuma umma ta aikeni nakaiwa mommy abinci.
Na samesu zaune suna kallo Fa,iza ke fadin aita dauka nayi barci ne nace hjy karima ce ta kirani wai na gyarawa yaranta dakin su.
A cikin hausa naji mommy tace ita suraiyya bata iya gyaran daki har yanzu ko me da sai an kiraki Nabila tace bashi bama mommy su dafa mata sata a karshe aishine ba kyau.
Wanan kan idan sun dafa mata sata ashe zasuji tsiya ranan hauwa ta fadi tana gyara zama ni kuwa murmushi kawai na sake don jin abinda suke fada.
Washe gari kuma still ta kara nemana wai na gyaro mata part din gaba daya sai na kira suraiyya din muyi tare har fatima diyan ta.
Mun fara da falo muka gama muka koma ciki ban yarda nabawa yaran fuskan raini ba muna gab da karasa dakintane dake da uban gyara don ni ganin dakin yasa na raina da wayau anty din ashe iya tsabatan ta a waje ne kawai dan muhalinta bai kalluwa sau biyu don kazanta.
Muryoyin sune ya karade falon suna fadi ina mara lafiyan take ne ko tana gun Alh ne don matar bata da dama .
Anty ta mike ta fito tana fadin kudai kuka sani da safen nan haka, suka ina mukaga zama ance hannu saura kiris ya guntule ta dago masu hannun ta zauna ta fara basu labarin abinda ya faru.
Muna gamawa nikan nafito gaba dayan su suka sako min ido irin anga bakon fuska din nan a inda ba a zata ba don dagani sai yar wando dogo da riga irin na exacirses din a jikina na kaina kuma da hula sai sock dake kafana da muke yawon cikin gida dashi don sanyin ties din kasan.
Tsab suka kalleni ban damu da kallon su ba a yanzu don na saba da hakan tun shigowan mu arewa haka zasu zubo min ido suna kallona kamar sunga wani halitta can na daban.
We na don fisnish anty na fada kafin na juya ina cewa welcome ma u na good morning wooo na sakai zan fita naji anty tace dani.
Ibeg sahiba go and help dem to cook break fasat for us before u go na amsa da ok ma nabada baya naji daya na fadin wanan fa ita kuma kuka samota haka.
Dayan kuma tace ke badai abuwar yar aiki kuka daukaba haka wanan tsaleliyar haka kai haba wace yar aiki kika san zan dauka sirina waje aini sam ban yardada wata yar aiki ba can a yanzu.
Itace dai wace nake fada maku din nan sunzo au don Allah ki bari dai ke kice muna dai irin yayan ashawo din nan da turawa ko larabawa kewa ciki akazo maku da ita gida.
Wanan kinyi gangancin barin ta cikin ku wallahi fuska anty ta tabe tana fadin ke dai bari nayi magana da uban da matar gidan har dansu sunce ina nafito .
Wai yar aminin ogace daya rasu don haka suba zasu yarda in wullakanta suba lokacun fa Alh nunawa yayi kona bar gidan idan ban iya zama dasu.
Kinga ko ya zanyi ga yaran nan kaf din su sun dauki son duniya sun dora a kanta kona hana suna part din su lake a wurun su .
Idan kinga hakan sakin fuska suka samu aishi yaro haka yake kaman kare in yaga sakin fuska saidai gaskiya kiyi taka tsantsan da irin wa yan nan tsintattun mage din idan idon ta ya bude nan gaba ba zaku iyata gidan nan.
Sai ta ukun su tace kai haba menene ba gashi yanzu tana more mata ba albarkacin zama tare meye wani abin tayi hankali a nan don Allah ku bar wanan zancen haka tunda yarinyar na taimaka mata jifa yau yadda muka samu part din nan tsab.
Wani iri naji na wanan maganan da sykeyi naji kamar in saka masu magana saidai yin hakan zaisa a gane ina jin hausa.
Tunda a zaton su har daddy din