Showing 357001 words to 360000 words out of 382072 words
a nan shiko duk maganan da yakeyi a lokacin hankalinshi yana a kaina.
Ya karaso ciki yana fadin idan zaku shige ku dinga saka key daga ciki saboda tsaro duk da akwai masu gadi dags wajen gidan amma hakan is not safe gaskiya.
Da hausan shi yake maganan da fatima kafin daga inda nake zaune bakin gadon nake fadin nothing will happen koda masu gadin ma basu ai a cikin hausana dana iya.
Kallo Fatima yayi a inda ya barta sai yaga har ta fita dakin ko alokacin yaci gaba da fadi cikin mamaki so you are hering the languege abi ?
Not long na bashi amsa ya karaso har inda nake zaune yakai saman gadon kusa dani har jikin mu na iya guganna juna sosai a lokacin yake fadin.
How far my Lady kada kiyi fushi dani please aikine da wasu baki suka zo min dashi ya hanani zuwa nan in time kiyi hakkuri da hakan don Allah.
Haba haba don't say that to me again ko ba baki ai akwai iyali dole ka gana dasu and beside you are my elder you have the right to do whatever you like a rayuwanka bani da matsalan haka sam na fada a cikin ladabi da iyakar gaskiyana a fuskana.
Murmushi yayi tare da kai hannunshi sama hannuna yana fadin nagode da kika zamo mai fahintar hakan amma yana da kyau na tsare maki hakkin ki koba haka bane?
Ya tambaya yana kokarin son mu hada ido dashi sai dai sam ba zan iya hakan ba a lokacin don ni din jinin hausa fulanice ko yayane akwai wanan kunyat a jinina na addini dana al,ada.
Dukar da kai nayi don na gane me yake nufi sai naji yayi murmushi tare da fadin anyway anything to eat ko sai an fita an sayo aci ?
No mun riga mun yi girki for the first tima bayan hakan banda ra,ayin cin girki waje ga rayuwana nafi ganewa na girka muci.
Masha Allah Alhamdullahi sahiba akwaiki da abubuwan mamaki na rayuwa ga wanda bai sanda hakan ba zai dauka ba abindata sani game da rayuwan duniya don tashin da sukayi a cikin bariki.
Farko abindaya tuna shine yadda ya bar gidanshi a cikin tashin hankali da fitina kan zaizo gidan sahiba din ya kwana.
Gashi yadda ita sahiban ta nuna mashi ba komai zai iya kasancewa da iyalin shi ba damuwanta bane hakan, shin wanan maganan nata gaskiyane akwai matar da zata yarda da wanan a tsakanin ta da kishiyarta ko ?
Ko dai hakan na nuna cewa wanan yarinyar har cikin ranta har yanzu bata aminta da aurenshi da ita bane ga kuma zancen abinci da yanzu ta fada.
Haka ya nuna cewa kuma tana shirye da ladabi akan auren su ko zama dashi ke nan donga Falmata haka kawai zata kwashi iska afima shekara sai abincin fizza da sauran ire iren su zata dinga sa akawo suci duk da tasan baida bukatan hakan a rayuwan shi .
Shi mutum ne da yafi bukatan irin abincin mu na gida da al,ada ya koyar damu cin shi don hakane idan yana Nageria koda tare da iyalinshi yazo ya kwanmace da yaje gun mahaifiyarshi yaci abinci a can .
Kokarin mikewa nayi tsaye sai naji ya mayar dani na zauna muna fuskantar juna dashi da sauri na mayar da kaina a kasa don kallon da yake min yasa gabana faduwa lokaci guda.
Kin gaji da yawa ina zaki yanzu ya fada kamar me rada yana kokarin mayar da bayana saman katifa dan rutse idanuwana nayi kafin nayi karfin halin fadin zan tafi falone na hada abinci don naga kamar a bukace kake dashi yanzu.
Murmushi yayi irin na manya kafin yace ban fada maki hakan ba don ina son kasancewa dake ne kawai a yanzu naji dumin jikin ki na saurari muryan nan naki a kunnuwana.
Jin wanan yasa na dan saki murmushin iya baki na lumshe idanuna kawai don ni nauyin shi da kwarjinshi yanzu nake ji musanman ma ida yana agaban nawa haka ?
Balle yanzu da yazo min da wani abinda nake hangowa a tsakiyan kwayar idanun shi lokaci guda tun bayan shigowan shi daki.
Ji nayi yayi min rumfa da kirjinshi lokaci guda tare da kokarin kai bakinshi a cikin nawa da sauri na kawar da kaina gefe da sauri ?
Dan bina yayi da kallo kafin naji sautin ajiyan zuciyan shi yana mikewa zaune daga yadda yake din kada Fatima ta shigo ta samemu a haka ko ?
Tana da hankali sosai ba zata shigo nan ba yanzu tunda kana ciki na fada tare da mikewa tsaye ga baki daya bin jikina yayi da kallo don rigan yayi matukar matseni ya fitar min da duk suran jikina a baiyane.
Kusan duk haka dinkuna na suke don haka ni ban dauki wanan a komai ba a wurina shiko wani iri yaji lokaci guda yana dan lumshe idanun shi.
A tare muka fito zuwa falon yana rike da hannu na muka tako a cikin natsuwa fatima tana tsaye a gaban dinning din ta kara gyara ko ina ga candles ta kunna a tsakiya da akai decoretion dinshi a jikin wasu glass an kawata wurin sai gwanin ban sha,awa.
Tun daga nisa ya fara fadin a, a Fatima wanan aikin bai maki yaba ke kadai haja keyinsa tana dan dariya naji tace a, a wallahi bani nayi karasawa nayi kawai anty Sahibace tayi komai tunda da kanta.
Da sauri ya kallo inda nake wai yana mamaki kamar karamin yaro yace kune duk da wanan aikin haka gaskiya ku daina aiki haka yana kallon inda nake daga gefen shi.
Dan murmushin yake na sake haka yaja hannuna zuwa bakin table din muka kai zaune ya nunawa Fatima kujera ta zauna sai cewa tayi a, a zanci a daki alaman nauyi da kunya.
Shima murmushi yayi tare da fadin au na tuna fulanine ku ai kunya ko zaki daina idan kina gidan nan ki zauna muci matata ta ciyar dake irin abincin da baki taba ci ba.
Da alama dai shi mutum ne mai son barkwancin da raha sosai ashe kada ka yankewa mutum hukunci a lokacin daka fara ganin shi sai ka gama nazarin shi zaka gane hakan amma ganin farko na dauka ko magana aikine a gareshi.
Bayan mun zauna jin abinda ya fada yasa na mike na fara zuba masu abincin na zata irinane shi saina zuba kadan ina kokarin juyawa yake fadin.
Har kin zuba min ke nan kome na kalli abincin dana zuba din yake fadin kara min nikan aini da tuwo muna gaisuwan mutunci sosai dashi.
Dauko wani ledan nayi na bude na zuba a plate din na gyara cup din ruwan dake gefen shi da plate din miyan ina dan tusunawa nace bissimillah.
Nagode ya fada na juya na zubawa Fatima itama kafin na dauki plate na dauko leda daya na rabashi biyu saidai daya yafi daya yawa sosai na saka karamin a plate.
Sai duk suka bini da kallo lokaci daya kowa na kallon abinda na zuba meye wanan din ya tambaya yana kallon abincin da nake kokarin zama inci din gaz kuma cibi na dora a sama.
Samun wuri nayi nakai zaune wanan ma ai yayi mata yawa indai anty Sahibace sam bata cin abinci haka kamar kowa .
No ki dinga cin abinci zaifi yanzu ba daya bane da wancan lokacin ko kina son yan kaduna su Fatima su raina da kiwona ne ?
So ki daure ki koyi cin abinci please ya fada yana jawo plete dinshi zuwa gaban shi da kyau kafin ya fara da bissimillah.
Zance ruwan miya nasha da dan naman dana zuba abinci kan cibi biyu kawai nayi na ture sai wayana na jawo dake gabana na fara dubawa.
A hankali ya dago kai ya dubeni kafin ya juya ya kalli fatima data soke kai tana murmushi a kasa kasa don ganin draman da mukeyi dama tasan ba zanci komai ba ita.
Ankai kamar minti biyar sai tura loma yake yana kurba ruwa lokaci lokaci muryan shine ya dawo dani daga sakon faiza da nake karantawa a lokacin.
Badai kinci abincin ba ke nan ya fada kai na dago ina dan bata rai nace naci ya isheni haka tsam ta mike tare da fadin uncle saida safe.
Ya dan bita da kallo kafin ya juyo gareni yana fadin idan baki saba da wanan abincin bane aida saiki girka wanda zaki iya ci koma meye ni zan koyi cinsa.
Amma ba zan barki ki dinga zama da yunwa haka na kallon shi nayi cikin ladabi nake fadin wallahi i am OK with diis haka nake cin abinci ko a gidama.
A hakan shine ci ya sake tambayana yana kallon plate din dake gabana a lokacin sorry sir iam OK!
Lumshe ido yayi yaci gaba da cin abincin shi hankali kwance yana ci yana dan kurba ruwan dake gefen shi a hankali.
Sai mamakin yadda yake cin abinci haka nakeyi a zuciyana kafin ya kusa gamawa ya dago kai tare da fadin.
Zanyi kwana hudu tare dake a nan kafin na juya zuwa London yin wani aiki zan kwana biyu a can naso in tafi dake saidai hakan ba zai samu ba .
Don mahaifiyata ta riga ta shedawa kowa zaki dan zauna a nan kwana biyu kafin nazo mu wuce Hong Kong a can zaki zauna don can business dina ke tashi yanzu nafi zama a Hong ko Dubai.
Saiki zabi inda zaki zauna daga cikin biyun ya fada yana kallona tare da sakale loman daya diba a hannun shi.
Inda hankalinka yafi kwanciya dana zauna duk dayane a gareni koda a nan din ne ma banda matsala ga hakan na fada a hankali ina sada kaina kasa lokaci guda.
Hong din yafi don a can nafi zama sosai beside dubai din falmata da yara suna yawan zuwa hutu a can lokaci lokaci kuma gidan gudane.
Naso nace dubai din amma kada na nuna kalana a fili sai nace is OK ba matsala kawai na mayar da hankali ga wayana.
Hannu ya tsame a ruwan daya wankesu daidai lokacin naji muryan shi yana fadin will you be my guest at dis night ?
Maganan yazo min a bazata har yakai ga haifar min da wani ciwon kai lokaci guda amma haka na dake bandai bashi amsa ba sai dan yaken danayi kawai a fuskana.
Wayan shi yai kara ya dauka sai naga ya share kallon wayan da yaga na dan kalleshi sai ya dauki wayan tare da mikewa yana fadin hello ya dago min hannu alaman yana zuwa ya tafi .
Dan binshi nayi da kallo kafin na mike na fara hada kayan don babu mai aiki nima kuma ban dauki hakan aiki ba na tsaya na gyara wurin saida ziciyana yana tune da zancen daya furta min dan mintina da suka wuce.
Saidai duk abinda nake ina jin wani irin kullewan da marana yayi lokaci guda kamar dutse ya danne min maran abinda ban taba jiba a rayuwana.
Haka na daure na kawar da komai a dadafe nakai dakina ina jin kamaf abu zai fito min a gabana lokaci guda.
Haka na samu na isa bandakin don na kewaya ina tsugunnawa wani jini ya zubo min mai yawa kamar saren nono ya fado min da karfi saida na zabura dan tsoro.
Da kyat na samu na dawo dakin na fada samsn gado ina faman nishin wahala da haka na lalubo wayana na kira fatima saidai tana busy a lokacin .
Bandade da aje wayan ba sai gata a dakin daidai lokacin ins dunkule abin tausayi dani ina wani gurjin nishi mai nuna wahala ga mutum.
Da sauri take fadin innalillahi meya faru anty sahiba da kyat na iya daga kai na nuna mata kasan marana dake min ciwon bala,i a lokacin guda haka.
Shiga toilets kigani na iya fada da sauri ta fada toilet din dan ihunta naji lokaci guda ta fito tana fadin anty meye hakan tana tambayana.
Ban sani ba na fada da kyar harfa motsi yakeyi nake gani ta fada a dan tsorace tare da kallon kofan toilet din a firgice.
Uncle yasan da baki da lafiya ta tambayeni tare da tsureni da ido na kasa kai alaman a,a akirashi ke nan gaskiya wanan ba abin wasa bane.
Da sauri na daga mata hannu alaman a,a ta barshi kawai, can wani tunane yazo min da hannu na nuna mata ta dauko min jakkana a cikin wardobe da sauri ta juya ta dauko.
Na lalubi abinda nake nema na gani haka na daure ba mike zuwa toilet din har lokacin abin na nan yana motsi kamar abu mai rai.
Na dade tsaye ina kallon abin kafin na fidda kwalban turarena na shaka a hancina nasan matsala don haka na daure nayi duk abinda ya dace inyi a lokacin sai lokacin abin mai kamar tsokan nama ko anta ya fara narkewa a hankali ya koma jini duk ina tsaye ina kallo.
Ina jin muryan Fatima daga dakin tana kiran sunana anty ko in shigone nace gani fitowa yanzu haka na fito daga bayin bayan na wanke wurin na gyara jikina zakace kona haihune ina wani irin zufa na samu wuri na kwanta tun tana min sanni ina karbawa sai barci ya daukeni ban sani ba mai nauyi.
Har ya gama abinda yakeyi baiga na leko ba sai yaga rashin dacewan hakan don shi ya kamata ya biyoni for the first time ai haka yasa ya taso daga dakin zuwa nawa part din.
Yana sallama Fatima ta amsa mai idon shi a kaina yadda nake kwance din da sauri yake tambayan ta ko lafiya nan ta kwashe abindata sani ta fada mai.
Hankalin shine ya tashi sosai yake fadin shine baku kirani ba bari muje asibiti kawai fatima din tace ta hana in fadamane kuma sai ina ganin ba na zuwa asibiti bane .
Ana ciwon da bana asibiti ba fatima kada yazo ya zama mata matsala fa nan gaba bari kawai muje asibiti a tayar da ita lokacin nayi wani irin mika a cikin barcin har suna iya jin yadda kassan jikina ke wani kara lokaci guda .
Dole haka suka kwana dani ina wanan mikan sai zuwa asuba komai ya lafa na koma barcina norman kamar bani ba hankalinshi yayi matukar tashi sosai har fatima din.
Washe gari ban tashi da wuri ba sai wajajen takwas da rabi na safe na falka ina tashi ba wanan duduken a tafiya na koma normal dani kamar bani bace haka ya faru dani ba.
Shima barci yayi don barcin dabai samu ba suna tare dani a halinda nake ciki da daren sai karfe daya yaje gidan nasa.
Hira ya samu sunayi kamar ba ita ba ta sake sosai da kannenta da wata bakuwa kana kallonta kasan matar yar duniyace ta gaske.
Haka ya wucesu suna gaidashi da kwana ya amsa ya shige yana jin dariyar Falmata din kamaf da gayya tana fadin saike hjyta ina yinki sosai hjyn kare kukanki.
Dan ja yayi ya tsaya kafin ya daga kafa ya shige dakinshi duk zuciyar shi babu dadi a yadda yake ji suna jin rufo kofan shi.
Take fadin wasa kake da Falmata wallahi baka sanni bane a yanzu mukhatar mu zuba dani daku aga karshen wasan .
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA , , , , , , , ,
1️⃣0️⃣7️⃣BY, , , , , , , , , , , ,
ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AN NAFI,E , , , , , , , , , , ,
ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257
ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U 👋
Barci nayi sosai a ranan tun abin safe sai bayan karfe biyun rana dana tashi don saboda yin sallah a lokacin sauka nayi daga kan gadon zuwa bandaki na kewa da niyar na watsa dan ruwa a jikina kawai na fito.
Tunda nasan bana sallah don irin jin dana zubar a daren jiya din daga jikina wanda haka na kwana yana zuba min duk da nasan ba lokacin period dina bane a lokacin.
Saidai me gani nayi kamar da daids duniya bani bace nayi wanan jinin haka a daren na jiya din don babushi ba alaman shi sam.
Sanan kuma babu wanan ciwon mara din daya hanani shakat a daren don ji nake tankar marana zai ballene lokacin don ciwon da yakeyi din.
Amma yanzu sam babu shi babu alaman shi a gareni tankar a duniya banice a daren jiyan face face a cikin jini ba.
Dole haka na daure cike da mamaki nayi wanka a dadafe zuciyana cike da mamakin ganin hakan a gareni din.
Sallah fatima ta shigo ta samu ina yi taja