Showing 15001 words to 18000 words out of 382072 words

Chapter 6 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28416

Tamike tana fadin sai nayi maganin wanan tsohuwar banzan da bata san ta tsufa ba wallahi.
Part din maigidan ta nufa da dan fushinta saidai tana zuwa dakin ta nemi fushinta ta rasa don yadda ya hade rai data shigo dakin ko sallama ya zama mai dole ya amsa ne ya amsa mata.
Yana zaune saye dogon jalabiya mai laushi a jikin shi medan karmin hannu ya mike kafafun shi saman gadon dakin daya ya gyara.
Alh sannu da zuwa ta fada da dan fara,an kissa a fuskan tare da fadin ashe kana hanya bamu sani ba ?
Ke dakata fice ki ban wuri dan Allah banda lokacin wanan shirmen naki yanzu ya fada yana lumshe idanun shi don takaici yana maijin zafin wanan halin yan barikin na karima.
Yanzu yake daya sanin kara aure da yayi yana zaune kalau da yar uwanshi wace aka gina su da tarbiya irin na islama tun a gida yanzun kuma itama tana gina mashi zuri,a da wanan dabi,an da suka koya gun iyayye da kakanni.
Sai gashi kwatsam ita karima din ta shigo rayuwansu da rana tsaka tana batun tabarbare masa tarbiyan gidan shi da suka taru suka gina da yar uwarshi kuma matar shi a yanzu.
Tsaye tayi tana kallon shi da mamaki a fuskanta kafin tace me kuma nayi Alh har kake korata haka a dakin ka yau ?
Oh baki san kinyi komai ke nan da izinin wa kika fita daga gidan nan waya baki izinin fita a cikin gidan nan ya kara nanatawa gareta.
Bafa wani wuri naje ba Alh na leka gidane in dubusu don an kwana biyu ban lekasu ba.
Babu wayane da ba bazaki kirani ki tambayeni ba sai kiyi yadda kika ga dama ko to ki koma gidan naku har ki jini.
Alh a kan wanan maganan kake fadin wai in koma gida to kayi hakkuri idan ranka ya baci ta fada tana zama a kusa dashi.
A hasale ya juyo yana fadin watau fitan bada izinina ba shine dan magana ko lalai ya kara tabbatar da baki da hankali karima.
Shiru tayi kafin ta mike ta fita daga dakin ganin baida niyar yi mata magana a lokacin yasa ta fice ta bashi wuri.
Tana fitowa sukai kicibis da hjy Addah wace ta fito daga kitchen da sauri ganin hjy kariman ta ce a, a karima kin dawo ashe ina nan hankalina a tashe tun dazun.
Eh na dawo ta fada a gadarance tunda bukata ya biya ai a ce yanzu wai an damu don bana nan to sai me iyaka dai yace inje gidan mu din.
Kamar Alh ya sani tana fita daga dakin ya mike shima ya fito yana bayan ta tsaye yana jin abinda take fadawa hjy Addah din.
Karima kanki daya kuwa meye laifina a cikin maganan nan ko da zaki fita kin fada min ne amma haka na daure na kiraki ki dawo Alh ya dawo kada hakan ya zama matsala a tsakanin ku.
Ummhumm hjy ke nan sai ki samu yara gasu can ki masu wanan dadin bakin amma ai daya fada maki zai dawo baki fada min a lokaci ba sai daya dawo ya samu hakan.
Yau wani iskamci kike jine a gidan nan karima Alh ya fada daga bayan ta ta juyo munafucine banso Alh .
Ni baka kirani ba amma ita ka kirata ka fada mata dawan ka harta bari na fita bata fada min komai ba don munafuci sai a dinga nunawa mutum ana sin sa a fili.
Alhalin zuciya tab da bakin ciki da hassada yakewa mutum a hankali ya tako yana fadin fice daga gidan nan kafin ranki ya kai ga baci yanzu cikin dakewa da nuna shi din tsohon dan kakine shi yayi maganan.
Ya juya wurin hjy yana fadin ki hado min abin sha yanzu ya juya zuwa dakin shi din sai yaji tabe a bayan shi tana fadin aikin banza ta wuce.
Kamar yadda ya dace a ranan karima din ce da girki wanan matsalan dai ne daya faru ya kawo hakan a yanzu.
Ji abinda ya fada sai ta fada kicin a fusace tana hada mai abinda yake sha din daya umurci Addah ta hadomai din ta shiga hadawa da abinci ha baki daya nasa.
Hjy Addah tana ganin hakan ta juya abinta zuwa dakinta cike da tunane da takaicin irin wullakancin yarinyar data tsiro ranan.
Shima maigidan daki ya koma ya zauna yana bakin cikin abinda ya faru din bayan kamar rabin awa sai gata ta shigo dakin dauke da kayan abinci zata aje yace.
Ke dakata waya umurce ki kikawo wanan ko dake nayi dana bukaci hakan ki kwashe kayan nan ki bace min da gani kuma dole yau sai kinje gida ba zaki kwana min a gida ba.
To sai me ta fada a hasale tana mikewa tare da ci gabada fadin nasan makircin maza dama ka tayar muna da hankaline don a cuceni.
Tunda kasan yau nice da girki ai amma da yake ba ita bace zaka kawo wani fitina kuma .
Naji girkine idan ga da,a da biyayya amma tunda yanzu kin isa da kanki ba umurni na kike bi ba don haka yanzu ina da daman sauka a inda naga dama .
Ai don ka fadi haka a yanzu banyi mamaki ba don nasan duk abinda kakewa a yanzu kakw hakan don kawai musguna min.
Don ka dawo ta baka tsohon abu kayi yadda kake so a ciki zaka zalunceni yanzu ko don an mayar dani ban san abinda ke faruwa ba.
Dan murmushin takaici ya sake ba tare daya dago a yadda yake ba yace ke kike ganin shi tsoho don ni a wurina sabone .
Don ni tsohon nan yafi min na yar yarinya sharaf don ya wadatar dani komai karima sai ayau nake nadaman auren ki a ruyuwana walh.
Tun sunayi suyi kadan kadan har yakai ta fara daga murya hankalin wanda ke gidan a lokacin ya dawo garesu muyi hattara mata fadan mu ya tsaya iya daki da mazajen mu.

Yau kusan kwana biyu ke nan ina zama a wurin ko zanganshi in rokeshi ya karbi kudin shi sai dai ban gashi ba har wanan lokacin.
Dole na daina fitowa tunda ya fada min dama wani yazo nema a unguwan don haka ba lalai bane in kara ganin shi kuma.
Gashi yanzun ba wani ciniki sosai don ruwan dake hana mutane samun sukuni yin cinikaiya a garin.
Don haka nake faman yin dan buga buga don mu samu abinda zamuci nida umman mu da dan kanina Amar da shima dai bai faye lafiya ba sosai.
Ga wanan kudin da aka ban umman mu ta hana a taba ko abinci mu saye dashi mu danci irin na kowa ta hana sam nima dai da farko na tsorace da zancen kudin.
Amma yanzu da ban kara ganin shi ba sai tsoro hakan ya fita min zuciya na koma harkokina na neman kudi kadan kadan don mu samu abinci da zamu ci kada mu kwana da yunwa.
Yau na makara da fita don ban dawo daga makaranta da wuri ba don haka na yanke shawaran kawai na je sarin kati in hada da bara lokaci guda ko Allah zai bani sa,a
Sai dai tunda na tunkaro wurin Indibisi dake bani sarin kati na hango shagon shi a rufe hakan na nufin bai nan ke nan a lokacin.
Gabana ya fadi da tsoro da fargaban kada mu kwana da yunwa a ranan haka na karasa ina tambayan makwatan shi sai da kyar dayan ya kalleni lalace yace bai nan ya tafi garin su an masa rasuwa.
Haka na juya da sanyin gwiwa ina tunanen ina zan dosa a lokacin gashi yamma tayi sosai don biyar da wani abu na yamma a lokacin.
Come now indibisi customer maker give u for today naw ai indibisi yana bamu labari ki u are good customer now oya come meke u quic quic go and come back in time b4 eight.
Tsaye nayi ina kallonta kafin ta kara fadin oya come naw ko ruwa zaki dauka gashi mai sanyi sun fara kankara a hankali na gyada kai tace da sauri tana mikewa taga kasuwa .
Don ni da niyata in dauki kati sai in hada dayin bara ko zan samu abinda mukai sai abincin da zamuci ga Amar ba lafiya kwana biyu ke nan tunda ruwan sama ya dukeshi hanyan dawowa daga school.
Allah da ikon shi duk da sanyin da akeyi sai gashi na sayar da daukan farko da nayi na dawo da murna nace zani gida ta bani share dina tace I beg me u cary anoda one now try u go sellam all please help me sellam .
Matar ta ban tausayi na dauka nakoma titi na fara bin layin motocin dake dawowa daga wurin aiki wasu daga kasuwa ina fadin buy cool water,
Pure water oga buy cool water daidai wata mota green dana tsaya ina kallon motan aka zuge glass din motan akace pure water.
Da sauri na haro wurin motan kafin in karaso har masu ruwa irina sun kawo ko naji a na fadin No you how much is your money inji wanda ke jan motan yana nuna roban ruwan da nake dauke dashi.
Nace da sauri three hundred naira i carry daga gefen shi aka miko kudi ana fadin in karba sai driver ya miko min daga haka ya motan shi suka tafi ina fadin oga u no carry d water naw.
Tsayawa kowa yayi yana kallona ganin haka sai na soke kudin a cikin jikina don ba abu mai wuya bane yanzu wani ya kwace a hannu na.
Na karasa yawata saura ruwa Allah ya kara ban sa,a na sayar na koma da sauri na mayar da kayan na hada da dan gudu wurin sayen abinci kada ya kare.
Na biya chemist na sayo magani wa umman mu da Amir na doso gida da gudu duk da akwai mutane a wurin lokacin amma suma ba abin yarda bane


ZAINAB IDRIS MAKAWA



ANA DARA GA, , , , ,


6️⃣

BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILAHI RAHAMANIN RAHIM IYA KA NA, ABUDDU WA IYAKA NAS, TA, IN, , , , , , , ,


LITTAFIN KUDINE KI BIYA KI KARANTA YAR UWA A CIKIN SALAMA, , , , , , ,


Zan shiga gidan nayi kicibis da wani mutum wanda ba yafita ko yaushe a gidan mu sai jefi jefi zaka ganshi koda darene ya fito.
Hakama ba ruwan shi da kowa a gidan sai dai zaka ga manyan mutane suna sintirin zuwa wajen safiya da marance yana daki shi a can kuma zasu same shi dakin suyi duk abinda zasuyi a dakin wanda bamu sani ba mu.
Na shigo da sauri don tunanen irin fadan da umma zatayi min don daren da nakai yau har misalin takwas da rabi nasan a lokacin hankalin su yana tashe da rashin dawowa na gidan da banyi ba akan lokaci.
Don duk iya dadewana a waje shine bakwai na dare zan dawo ko ina nake da duk abinda nakeyi zan barshi in dawo gida a wanan lokacin.
Sai gashi yau tunanen halin da muke ciki a dakin mu yasa nakai wanan lokacin a waje wurin neman kudi ban sanda shi tsaye a wurin ba ina zuwa da sauri ina haki don gudun dana danyo mukaci karo dashi har dan abincin da na sawo ya bare a kasa don zafin da naji ban san lokacin dana sake abincin ba wurin.
Abi ware ni ?
u no de si road u de warker wit ur eyes closed daya daga cikin yaran mutumin ke fadin haka da suka taso kamar zasu cinyeni danya a lokacin.
Ina kasa ina bin abincin dake kasa zube da kallo da takaici sai hawaye ke zuba min daga idona a lokacin nace.
Na dan dago a hankali daga duken da nake na soma fadin god go ponish u ina nuna wanda ya tureni din da yatsan hannuna ina hawaye.
Na sake fadin god go ponish u wetin i go gibe my mama today na d food i buy for dem naw u push me with dis ur big bodi d food don fowl down all.
Wani dan gidan bisi da muke kira iya bisi da sunan shi yana fitowa ya same mu a wurin yace ehh ya sayiba na d food wen your mama de wetin for nayin u puur ?
Hungry go kill u nd ur mama today wani irin haushi na kara ji a raina na sake fadin na dis yeye push me down.
Dayan da suke tarene ya daga hannu zai kai min mari sai wanda mukai karon dashi cikin tsawa yace mashi.
Takwabe don't toch her give her dat money make she buy anoda one na kalleshi a fusace ina fadin .
Me i no wan money my mama go beat me if i kwalet de money u wan give me na food i want na fada a gadarance.
C dis yeye girl wen de talk rubush i beg mey u carry d money go don't west our time joo sai naji ogan ya kalleni yace carry d money first meke he bring food for u inside.
Nan yacewa dan uwan ya dauko wanan abincin na dakin su ya kawo min shi dayan ya tura min kudin da yace a ban da karfi a jikina har saida na dan ja baya ya taka zuwa dakin da suke zama wanda gidan hayane ba ruwan wani da wani a gidan.
Ina tsaye ina dan kakaban ledan maganin dana sayo wa su umma wanda duk mai ya bata yana tsaye yana kallona har dayan ya iso da irin ledan nan na abincin resturan mai sunan shagon a jikin ledan ya miko min a fusace na karba sai kuma na kalli kudin dake hannuna nace.
Carry ur money back dis one is ok for me i go nak ur darty mouth if u no live dis place wanda ya ban ledan ya fada a fusace.
Ganin zasu iya dukana na wuce ina fadin my mama d come now if i go inside na wuce da sauri na bar wurin.
Ina jin shi yana fadin cary ur wahala go yeye girl u na disturb people for nothing hungry girl omo jagu.
Ni dai na shige da sauri a kofa na hango umma tsaye tana diban ta hanyar da zan fito da daren nan .
Ina karasowa take fadin Sahiba irin tarbiyan dana baki ke nan ki tsaya kina fada da maza a bainar jama,a haka yanzu fa iya wale ta kwankwasa min take fadin gaki can kina fada da maza a bakin kofa.
Umma tureni yayi fa abinci ya zube shine nake magana a kai sai kika ce su biya ki ko ?
Ta fada a fusace tana kallona a dan maraice nace ni ban ce su biyani ba sune dai suka bada kudin nan gasu na miko mata kudin da abinci .
Ta kalla tace na meye shi kuma kudin bayan abincin da suka bayar sai mukaji muryan wanan daya dauko min abincin a daki yana fadi whare are u come carry you vein u be lucky girl today our oga have macy on u.
Ya jefo min dan gyalen dana barshi a can da nake yafawa inyi sallah dashi idan sallah ya riskeni a waje.

KADUNA
Tsayawa Alh yayi saida yaga fitan hjy karima gidan don bai iya jure cin mutuncin da ta daukowa kanta a gidab nasa yanzu.
Wurin motar ta ta nufa tana fadin Asmau kina ina wai kin san mutumin nan yau korata yayi a gidan sa kuwa ?
Gani nan zan fito wallahi ban san inda zan dosa ba tunda ba gida naje ba dazun din kuma yace lalai dole inje gida a yau.
To ki tafi mana wani wuri zaki ba gidan ku ba tace tana tayar da mota to idan naje gidan me zan fadawa iyayyena shi nake tunane a yanzu.
Ki je gani tafe gidan naku asamu ta fada kai tsaye kafin tace yaran fa yace kada in fita da kowa a cikin su suna can na barsu ciki dole.
Wanan mutumin fa sai munyi da gaske a kanshi wallahi inba haka ba wanan munafukan tsohuwar matar nasa zata fitar dake a gidan kina ji kina gani kibar mata yayan ki ta bautar dasu.
Wallahi basu kai min can ba dukkan su kuwa ta fada a hasale kafin taja tsuki ga maganan da Asmau ta fada a karshe tana kashe wayanta.
Taje gida sai ganin ta akayi kwatsam ta shigo da kukan muna funci hankalin mahaifiyar ta ya tashi sosai a wurin.
Tana tambayan ke lafiya kike kin shigo kinawa mutane kuka haka ai sai ki tsorata mu ga hakan.
Cikin kuka tace


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login