Showing 180001 words to 183000 words out of 382072 words

Chapter 61 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28439

suna amfani dashi wuri saka kaya ya shigo masu dashi a cikin rashin sani.
Sai dai amma yanzu din ai yasan komai don shi kanshi kyamar abokan harkallan nasa yakeyi sosai a yanzu suma din suna farautan shine kamar yadda suka san yana nasu.
Kallona ya tsaya yana yi a cikin mamaki na mike nace kwarai idan baka yarda ba ka bincika kaji zaka gane gaskiya insha Allah duk dani banda wani business dashi kamar yadda kake zato.
Abin harin ka yana cikin gidan yanzu haka hanya dayane duk asirin da ta dauko maka yana a cikin dakinta a kasan wardrobe din kayan ta cikin farin leda da zaka samu dama ka dauke zaku zauna lafiya duk da shirmen na mahaifiyar tane ba nata bane daga haka na wuce na barshi zaune da mamaki yana bina da kallo.
Kafin ya juyo wurin umma yana fadin har yanzu wanan abin nasu bar kanta bane ashe umma but how comes har tayi wanan tsowon lokacin dasu haka basu jirkitata ba ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA


ANA DARA GA , , , , , , , ,

5️⃣3️⃣ BY, , , , , , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL HASIB, , , , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257

Nikan tunda na shige daki ban fito ba barcine ma ya daukeni don akwai gajiya a jikina dama ban gama warwarewa daga gajiyan dana kwaso a gidan ogan mu ba lokacin.
Bana son shiga wurin aiki mu sai ranan monday don haka nayi zamana a gida ina hutawa kuma wayana a kashe don wanda ya kira yajishi kashe.
Barci na samu nayi sosai natashi nayi sallah na gyara jikina don zan dan fita zuwa lasuwan kusa damu in sai muna kayan miya don yayi low sosai idan na fara fita aiki ba lokaci gareni kuma.
Dogowar rigace dai har kasa a mutunce saidai zuwa kafadantace shakallo don idan zan sakata hakan sai dole dantsena sun fito a fili hakama gaban rigan irin mai nuna girman nonon mutum din nan ne a fili.
Amma ni da nasaka sai nakawo yar cikin nan da ake yayi mai makuraren wuya da dogon hannu na saka daga ciki sai hakan ya bada kala mai ma,ana .
Saidai ranan ban saka hijab ba son wata rana haka nakan fita sai hula a kaina hakan ba komai bane a wurin mu don dankwalin ne na daura kwai kamar daurin tura din ka yafashi kamar gyale a saman kan ki.
Shagon umma na nufa na sameta da custermers gaidasu nayi na samu wuri na kai zaune ina kallon abinda zan kira akawo muna a shagon don na kwana biyu ban leka ba.
Sallaman Felix mukaji a bakin shagon yana gaida umma da good day mah ta amsa mashi sai ya hangoni a cikin shagon zaune.
Why d u swich up your phone today ? We de call u sinces morning we nerver reach u why now ?
Oga don base with u today, true true ido kawai na zuba mai ina kallon shi kafin yace u no dey talk today ?
Na dan mere baki ina fadin waiting i dey talk now call my phone nd it swich den ?
U see na now now ogo live dis country travel to Dubai see d money he give us before he go ya fada yana taba aljihun shi don shi sarkin son barkwanci ne sosai idan ka saba dashi.
Nace kun gode ina mikewa tare da fadin na market i de go now to buy some fresh vegetables and other tins .
Ina kokarin fita daga cikin shagon umma din take fadin in sawo mata cheas idan na gani nace yes mah muka jera da Felix din zuwa wurin motan shi.
Motan dake saukowa saman titin ne yana nufo inda muke muka tsaya muna kallo har ya iso ya tsaya muna ta magana daganin yanayin tsayin mu zaka gane mun san juna sosai da Felix din saidai hankali yana surin motan duk da na ciki bai fito ba a lokacin.
Can ya sako kafa daya waje babu abinda nake gani sai bakin takalman maishi da bakin wando shi don sauran jikin shi na cikin mota a lokacin.
Felix yai min sallama zai shiga motan shi ya tafi nima a lokacin nabar wurin zuwa motana dake parke a gefe na kwarai ke nan naji an ambaci sunana a bayana saidai kodana waigo naga mai maganan .
Yar motana da bai taka kara ya karya ba shima yake kallo a cikin mamaki karara a fuskan shi nasan mamakin shi na dayan biyune bai wuce motar tawa bace ko na wani zan shiga dai ?
Ya mustaphane a cikin shiga na suit a jikin shi bakake he look classique sai dai kyakyawan fuska yau a daure yake irin sanin farko da nayi mashi a baya.
Na dan yi tsam wuri daya kafin na jingija jikina a motana don ganin yana takowa zuwa inda nake tsaye nakai hannu na zare dan glass din dake idona.
Ya karaso a lokacin nima dai na gama daure nawa fuskan a gareshi kamar yadda shima nasa yake daure lokacin.
Na dago kaina a hankali na dan kalleshi ina fadin ina wuni ya amsa yabi motan da kallo kafin ya juyo gareni yana fadin ina mama take na nuna mai shagon da hannu ba tare da nayi magana da bakina ba .
I would like to see you now ya fada ya juya zuwa inda na nuna mashi umma din a cikin shago nabi bayan shi da kallon mamakin yadda yanayin shi yake yau nasan akwai matsala.
Ban shiga ba sai kawao na shiga motana naja nabar wurin bakuma komai yasa nayi haka ba sai dan nasan idan daman ya wuce min ban shiga kasuwa ba zamu dan shiga cikin wani hali na yan kwanaki idan bamu da kayan girki da muke bukata.
Hankalina kwance na sayo duk abinda nake da buka ban kuma wani dadeba na dawo gidan saidai ga mamaki har lokacin motar shi na nan a haraban gidan .
Saidai wanan karon har umma bata shago suna ciki tare da ita yaran Abdulhamid ne suka tayani kwasan kayan zuwa ciki na shiga da sallamana a bakina.
Zaune yake saman kujera kamar yadda itama umma din ke fuskanta shi suna hira akan sana, an ta .
Amar ne ya mike da sauri ya karbi farin ledan dana shigo dashi a hannuna yana gaidani da dawo na amsa kitchen ya nufa da komai tare da yaran ciki suka barshi yana saka komai a inda ya dace a aje shi.
Na fito ina sauri zan shige daki umma take fadin tun dazun yayan ku yazo yace kun hadu kince zakije ki dawo yana da magana damune.
Kallo daya nayiwa inda yake ban iya maimaitawa saboda kwarjin da yai min don idon daya tsura min yaji me zance da umma din kan abinda ta fada.
Au bansan ni yake son gani ba ai gani na fada a karshe tare da zagayowa na samu wuri na zauna shirune ya dan biyo falon kafin ya gyara murya yace umma zaso na danyiwa sahiba yan tambayoyine kadan don Allah ya kare magana yana kallon umma.
Baida matsala yar uwakace ai zaka iya mata tambayan da kake son yi mata ba damuwa ga hakan don a zaton umma akan wani aiki zai tambayeni.
Don Allah ina son ki fada min yadda kukayi da Abubakar modibbo a jiya da na barshi gidan nan wurin ku don ya sameni da wani zancen da yaban mamaki sosai yau din nan.
Akan me zanyi zancen ka dashi tunda ban san komai a kanka ba na dai tare shi da fadi su daina zargin ka akan abinda bakai ka aikata ba suke zargin ka dashi.
Kamar meke nan Sahiba kike nufi rana wata lokaci duk ban raga mashi komai ba saida na zaiyana mashi komai daya faru dashi bai iya magana ba bayan idon daya tsura min kawai yana kallona da saurarena.
Sahiba waya fada maki wanan zancen ina rokon ki daki fada min gaskiya don na dade ina son sanin duk wani abinda kika lissafo min a yanzu.
Nasani ne kawai yace hakan kuma bai taba yuyuwa dole wani ya sanar dake hakan na mike kawai nabar falon don yadda nake ji har cikin raina.
Umma tace ka yada da hakan don baiwan da ubangiji yai mata ke nan a yanzu har idan kuma baka yarda da wanan ba zaka iya tambayanta wani abin na daban ka gani.
Shiru yayi na dan lokaci kafin yace zan gwada don in kawar da zargin hakan a raina Amar umma ta tura ya kirani wani kallo da nayi mashi saida yaron ya firgita ya koma yana fadawa umma din a furgice.
Me kake son tambayana a yanzu zancen kayan da kuka boye a cikin conteiner na Alh yayafi don kana ganin shine ke ma sherin haka.
What ya fada ya mike tsaye yana fadin lalai umma na yarda don ba wanda yasan da nayi haka sai babban yarona na kasan waje gashi kuma sahiba ta fada yanzu.
How come,s wanan ta koma haka yanzu yaushe wanan abin ya sameta haka mama ya sake tambaya yana fadin no warnder halinta keda wuyan sha,ani.
Stop it aka daka mai tsawa ranan dai a takaice yaji tonon asiri na yan kungiyar su har da abinda bai taba zato duk na fallasa mai shi jikin shi ya dauki rawa sosai a gaban shi nasha wuya sosai don sai da umma ta shaka min wanan abin na samu kaina da kyat har magariba muna abu guda hankalin umma ya tashi sosai tayi data sanin faruwan hakan saida kyat suka lafa min na shiga wani irin barci mai nauyi.
Sai washe gari na falka jikina a dake ko ina yana min ciwo muryan Abdulhamid naji a part din mu yana fadin idan mun shirya yana waje yana jiran mu.
Abin duniya ya damu Nazifa gashi majaifiyarta ta hanata fadawa mahaifinta zancen ya daukan mata mataki akanta.
Haka ta zauna tayi shiru bayan fitan shi tana tunane ita kaidai a katon falon nasu sai yayanta dake wasan su a gefen ta taji ana kwala sallama tun a waje.
Duk da ta sheda muryan mahaifiyar nata saidai hakan bai sa ta yunkura zuwa taron ta ba don irin yanayin da take ciki a lokacin.
Sallama ta kara daga murya tanayi da kyat ta iya amsa mata saidai ita hjy salma din muryan yaran da taji yasa ta nufi falon tana shiga ta hango yar nata zaune cikin wani hali na tashin hankali.
Me zan gani haka nazifa me kike son mayar da kankine wai ko so kike dani dake mu koma abin dariya idan an kashe auren naki ne ?
Hawaye ke zuba daga idanuwan ta tana fadin wallahi mama baki ga irin wullakancin da yayi min bane shiyasa kike ganin laifina.
Ban gani ba kuma ba zan gani ba ke da idon ki da girman mu kina dai ganin irun wullakacin da mahaifin ki ke muna a gidan ku ai mun fita kowa muka fadawa hakan da yake muna.
Ba hakkuri muke muna zama dashi ba wanda bai sani ba sai ya dauka wani dadin duniya muke kwasa a wurin shi.
Gaban ku zai zagemu har iyayyen mu tas a gaban kowa zai dukemu da girman nan namu kuma kin sani ba baki sani bane.
Mama baki dai son a fada ne kawai amma idan na zauna wanan dan iskan kasheni zaiyi don yaga ina son shi.
Uwarta kwashi salati tana taba hannayen ta wuri daya tace mjin nakine dan iska Nazifa yaushe kika zama haka wai ban sani ba .
Duk tantirancina da iya shege duk kuma irin cin fuskan da Alh zaimun kin taba jin na bude baki na zage shi ?
Lalai dole kijawa kanki duka ki zagi uwarshin ki zageshi har kannen shi dan banzane da bazai dukeki ba ?
To wai ma fada min meye yaron nan modibbo ya rageki dashi a duniyan ko kuwa cikin yan uwan ki kaf dake aure waya kaiki samun dakin aure haka ki fada min.
Mama kin sani fa uwarnan nashi ba zata taha barin mu zauna lafiya dashi ba cikin tsawa uwar tace da ita rufa min baki wace tayi gadon rashin hankali a wurin ubanta.
Ke da kina da hankali hjy Addah ba kanwar uban ki bane da zaki buga mata waya nacin mutunci irin haka.
Wallahi mama kar, , , rufa min baki na kira hjy Addah din ta fada min komai kuma ta rantse min bata san komai ba akan wanan zancen don baya ko zuwa gidan nasu.
Ke gaki sarkin marasa hankali da wayau kin kirata kin zageta ko kin manta ita ta haifi dan kuma ta aura maki shi da yardan ta .
Idan ba yana bin umurnin mahaifiyar shi ba ko kusa dashi ke nazifa kina zaton zaki iya zuwa kon nunawa duniya tayi masa zaben tumun dare ke nan a kan ki.
Gobe sai ki nemi wace zata gyara tsakanin ku dashi idan kun bata son ko tayi niyar taimakon ki diyan ta ba zasu bari ba.
Idan kina dauka maganata wallahi kiyi gagawan gyara tsakanin ki da mijin ki idan kuma kinki har suka gaji dake karshe ba zaki sha da dadi ba.
Dolene ki sauke girman kanki da wani fadin rai in kina son ku zauna lafiya da mijin ki dolene kuma ki masa biyayayya kamar yadda Allah yace ai masu.
Abincin shi shimfidan sa dama yan uwan shi su kasance kin kiyayye hakan sai ki kamo su daga kasa an fada maki haka ake kama gida a cikin karfi da yaji kome ?
Duk gatan ki da wani girma da kikaga yan uwan ki na baki a yanzu yau in akace auren ki ya mutu da yaron nan angama baki shi don mahaifin ki ba zai baki abinda mijin ki ke baki ba har ya hasakaki haka a cikin yan uwa ba.
Fada sosai mahaifiyar tayi mata tare da nuna damuwan ta kan kada auren yar nata ya mutu asirin su ya tono don samun da sukeyi a wurin shi.
Sam bata bata daman furta komai ba a gaban ta har ta gama tayi mata sallama ta fito zuwa gida ta bar yar nata na hadiyan rai.
Sai fadi take kaji mun mama da wani zance ai hakan kukayi har baba yake ganin yafi karfin ku yake maku abinda yaga dama irin nacin fuskan da yake masu.
Nikan babu da namijin da zan zauna yana min haka na kyaleshi don bai isa yace ya juyani yadda yaga dama ba har yan uwan shi su samu kafan rainani ina sam hakan bazai yuyu ba.
Gabantane ya fadi ras don tunawa da kalamin mahaifiyar ta na karshe me mamake nufi da hakan tana nufin saki ke nan ko me ?
Komawa tayi ta lankwashe a cikin kujeran da take zaune tana maida numfashinta a hankali tare da lumshe idanun ta.
Ba komai take tunane ba sai tunanen rabuwan ta dashi don tasan idan fitinan su yakai fitina mahaifinta kai tsaye zai bashi rashin gaskiya shi kuma din ya saketa.
Ta dade zaune ta nemawa kanta mafita saidai mafitan ne da kamar wuya a wurin ta don haka na nufin sai ta kwanta an hauta za a zauna daidai ke nan haka ke nufi.
Tun bayan sallah asuba dana iya tashi nayi na koma na kwanta wani irin zazzabi da ciwon kai suka rufeni lokaci guda maganin dana sha na shaka yasa har barci ya dan daukeni lokacin.
Yar uwa idan nace maki wanan abin baya damuna bata lokacine son in akwai abinda ke damuna a rayuwana lokacin danayi wayau din nan nasan duniya shine wanan laluran fadi ba a tambayeka ba din da yanzu yake son zama min babban lalura don har wasau nason amfani dani wurin cin ma bukatan su wanda hakan ya dan so kawo min matsala a rayuwana daga baya.
Don ba kowa zai yarda da hakan lalura bace da akan jarabi bawa dashi kai tsaye musaman nida nayi zama a cikin kabilu da za a iya ganin kamar harkan wani cultisim na shiga acan nake haka.
Shine dalilin daya sa na bakishi a cikin labarina don ki fahinci kan labarin cewa ina da wani lalura ko baiwa zan kirashi yadda bature ke kiran shi a turance da talents yan baiwa ke nan.
Gani ba kawa ta kut da kut ummace dai komai nawa don da ita na bude ido da ita na tashi kuma nake rayuwa da ita sai dan kanina Amar dake tare damu shi din namijine kuma tunda ya kai secondry ya fara barin mu gida haka kuma ya samo asaline don yaran Abdulhamid da suke fita tare wurin buga ball.
Ban san dadin kawa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login