Showing 243001 words to 246000 words out of 382072 words

Chapter 82 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28367

nashi ya sameshi.
Na fada maki gada kiyi wa yarinyar nan komai idan sunzo garin nan ummi saida kikai mata wani zance a yanzu ashe ya fada rai bace yana bin bayan felix din.
Sun kai su goma ko fiye da goma a police station din tun safe suke wurin a tsaye su shiga su fita sun kasa yin komai daya dace a wurin don suna neman bellin shine a ranan.
Bayan ya kwana har biyu a hannun hukuma nan garin Abuja wanda da kyat suka iya nemo inda yake lokacin kafin su fara wanan shige da ficen na neman bellin shi bisa jagorancin babban abokin shi wanda shi din dan majalisnane a lokacin wanda yaci zabe da taimakon Alh Nuhu din.
Sai fada yake da yan kakin wurin kan basu san matsayin shi bane ko basu shedashi bani suke mai yawo da hankali.
Dan sandan ya dubeshi cikin girmamawa yana fadin wanan case din Alh daga sama take don haka sai kun koma can kun gyaro don mu kamar ajiyan shi aka bamu nan ai.
Nan ya matsawa dan sandan yake fada mai ai case din daga office din sakataren gwaunati ya fito don haka su koma a gyaro komai.
Fitowan shi office din yasa sukayo ruuu a kanshi don suji halinda ake ciki, saboda shi kadai ya samu ganin IG din lokacin ko shi dun kuma don mukamin shi da yazo dashine aka barshi ya shiga.
A daidai lokacin kuma sauran yan uwanshi Alh Nuhu din da suka biyo mota daga kaduna zuwa abuja suka iso wirin a gajiye.
Basu samu labari mai dadi ba a wurin don haka hankalin su sai ya kara tashi fada sosai sukeyi suna fadin haka kawai za a kawo mutum a tsare shi kan kudi a ina zai samu kudin da zai biya yana daure ?
Kallon su baffa Hamza yayi a cikin takaici kafin yace nifa na dauka wanan abin anyishine da wata manufa don yarinyar da tayi aikin files din nan harta zakulo su yaya din ba wata bace yar mu ce yar dan uwan mu kuma na uba daya wanda ya rasu shekarun baya .
Wani kallo suka jefa mai kafin dayan Alhazawan yace yar kufa kace malam Hamza yana tambaya a cikin mamaki tare da kallon baffah hamza din da yai magana.
Kai ya gyada yace kwarai don kusanma ba tantama nakeyi ba don itace tazo daga lagos tayi wanan aikin har hakan ya faru.
Yar waye ke nan Alh gyade ya dan tako da sandan da yake dogarawa ya samu ya dan shiga mutane yace yar waye ke nan kake nufi wai ?
Baffa hamza din yace yarinyar nan dai yar wurin yaya sambo marigayi data baiyana wancan satin ai itace ashe tayi wanan aikin a company sha,aban din.
Wai kana nufin cewa wanan yar da gaske yar samboce ita toshi da namijin fa to ?
Shima kwarai danshine don ance kamar su daya da yaron sosai yaron ya kwaso mahaifin shi fiye da ita macen ya fada yana gyada kai.
Kai wanan abinda daure kai yake gaskiya a lokacin wani daga cikin abokan su yake fadin tazo da wani manufa ke nan yanzu dai ?
Kwarai ba kadan ba sanan tayi tafiya zuwa england sai nan da sati uku zasu dawo kasan nan a yadda mukaji.
Duk Alh yana tsare har wanan lokacin sai lokacin data dawo za a jirata ko me ?
Shi muke kokari yanzu mu sameta ai saidai wayan ta baya shiga don yaron nan Abubakar da dan wurin harira suna da layin ta su.
Kaji matsala babba ke nan yanzu bullowan wanan yarinyar da uwarta har kuma gada namiji ya fada a tsorace hankalin shi a tashe.
Meye matsala don sun bayana a yanzu din tunda dama dauka ake sun mutu ne kuma ashe suna raye ba shike nan yanzu abinda ya rage kawai mu jawosu zuwa cikin mu ai shike nan.
Shike nan fa kace hamza kai hamza nafa gano me kake nufi daka matsa mutanen nan yanzu su shigo cikin mu bayan wofinta kansu da sukayi a baya can.
Ba komai kake kokarin nunawa ba gare mu yanzu sai zalla bakin ciki da jin haushi irin na yan uba da kake kokarin nuna muna.
Haba Alh gyade wanan zancen haka a nan ai bai dace ba a tsakanin ku muyi abinda ya hadamu yanzu a nan shine mafita kan Alh a yanzu baffa buhari ya fada rai bace.
Daga can gefe daya kuma baffa hamza na fadin meye abinjin zafi a cikin nan yanzu don haba don Allah haka bai dace ba abinda kukeyi yanzu baffa Abdullahi ya fada a harzuke.
Tafiya nakeyi duk da sunana da Felix ke ihun kira haka baisa na tsaya ko in juyo in kalleshi ba don yadda nake jin idona ya rufe a lokacin sam na manta a wani kasan muke ma.
Kai tsaye masaukin mu nakai kaina saidai kowan su yayi mamakin hakan zakace na san garin ne na kuma taba zuwa kasan .
Bansha wahala ba wurin kai kaina dakunan da aka saukemu a cikin sa, ina elevator karshe da zai sadani da dakunan suka iya nasaran cin mun a cikin sa.
Do u want to kill your self Sahiba ki duba yadda kike ratsa motoci haka ba tare da damuwa ba a zuciyar ki .
Idan kin kashe kanki ko wani abu ya sameki me kike son in fadawa yan uwan ki ko mahaifiyar ki ?
Kallon shi na dingayi kawai lokacin da yake magana yaci gaba da fadin don ummi ta fadamaki magana zaisa kiyi wanan abin idan wani abu ya sameki fa ke baki tunanen hakan ne ?
Kaina na dukar kasa saiga hawaye takaici ya zobo min yana sauka a fuskana nake fadin a cikin karfin hali don kukan daya zo min din nace.
Kasa a mayar dani Nigeria don ba zan iya ci gaba da zama haka mahaifiyar ka tana min wani zargi ba na daban don kawai ni ba yar kowa bace ina aikine a karkashin ku.
Elevator din ne ya bude lokacin mun kawo inda zamu sauka ke nan zuwa wurin dakunan namu fita mukayi gaba dayan mu sai ya juya ya kalli Felix yana fadin ka koma can ka dauko min briefcase dina yanzun nan daga haka ya biyo bayana a daidai lokacin dana bude dakin da aka kama min na hotel din da muke a ciki.
Shima lokaci daya ya biyoni zuwa cikin dakin mamakin hakan ne yani sosai sai tunane nake me nayi na rashin gaskiya ko nuna wani halin da Alajan zatai min wanan mumunan zato a kan danta da bamu taba tsayuwa ko na minti talatin ba dani dashi.
Muryan shine a bayana yake fadin nasan wanan ba plan din ummi bane nasan daga inda zancen hakan ya fito.
Don ko jiya mun dade muna magana a kanku tare da ita bata nuna min akwai wani jin zafin ki a zuciyar ta ba saima kara yabawa da kwazon aikin ki da tayi min duk a jiya din nan da kukazo.
But why yanzu ummi zata fito min da wanan matsalan haka tana kokarin rushe min farin cuikin dana rasa na shekaru da dama kan wani bukata can nasu na daban.
Watau da gaske mrs kubura keyi bazata daina abinda ta shirya min ba irin wancan karon ita burin ta ke nan ta assasa kiyayya da bakin ciki ko yaushe tsakani da ummi ?
Look Sahiba duk da nasan ba zaki gane inda zancen nan ya dosa ba a yanzu ina rokon ki wani alfara kiyi min koda sau dayane kawai a rayuwan ki .
Sai lokacin na sake dago ido na kalloshi inda yake din tsaye a cikin bacin rai ganin na kalloshi yace yes ki taimaka min koda sau daya ki taimaki rayuwa na please .
Kada ki bari suyi nasara akan ummi dani sai kin daure da wanan taumakon da zaki min a yanzu ki nuna wanan zancen da ta turo ummi ta fada maki bai dameki ba haka kuma zaton su a kan mu din gaskiyane ki barni da sauran plan din zan karasa da kaina insha Allah.
Ganin irin kallon tuhumar da nake maine yasa ya kara fadin please kada zuciya ya hanaki irin taimakon da kike muna a baya nasan zaki iya hakan ya kara marairaicewa kamar zaiyi kuka a lokaci guda cikin tashin hankali.
Hakan yasa naji tausayin shi sosai naji wani irin ba dadi a lokacin don ko banza shine wani haske na rayuwana da ayanzu nake amfana dashi don haka shima dole in taimakeshi kamar yadda ya taimakawa rayuwa don nasan dai ko ya amfana dani shima ya taimake ni ai.
Yana batun zube min nayi saurin fadin please Sir i can help you yadda kake so zan daure in shanye duk wani bacin rai da zan gani a wurin mahaifiyar nasa da sauran yan uwan shi don bansan manufarshi ga niyar yin hakan da yake son in masa ba a yanzu.
Felix ne ya kwankwasa kofan ya shigo don a bude kofan yake har lokacin ya shigo dauke da briefcase din oga din a hannun shi.
Yana mika mai ya karba yana maigodiya don oga badai godiya ba kan gaskiya ko dan karamin yaro kake kayi mashi abin kyautatawa sai ya godema.
Wanan wani haline nasa na daban don gaskiya ni kan ba zan iya kiyasta maki halin salihanci da kirki irin nasa ba don shi mutum ne na daban zakaita magana yana shiru kamar baya jin ka.
Sai can idan yaji inda ya dace ya dan bada amsa zai dago ya fadi kalma daya zuwa biyu shike nan iya zancen shi.
Laptop din shi ya dauka ya danyi abu a ciki duk muna tsaye a cikin ladabi muna kallon shi kafin ya dago yana fadin zamu fitane ya aikawa jimo sako suna jiran mu a waje yanzu.
Felix ne ya fara fita daga dakin kafin ya juyo kamar rada yana fadin plan din mu zai fara aiki daga yanzu sai ki kula ki daure sosai ya fada a hankalin cikin kalman hausa da dukan mu kinsan hausa ba zama yayi sosai a bakin mu ba.
Wasu shaguna muka tafi an yace kowa ya dauki abinda ranshi ke so a wurin a gaban idon kowa da muke tare yaja hannuna muka nufi wani sashe na wurin .
Kaya ya fara jidan mai yawa irin na matan musulmai na kasan inda ina kallo yemisi sai cika take tana batsewa ta dauka wani sabon gani ba bazata tayiwa idon ta akan mu ba yemisi ba kawai duk wanda ke tare damu hakan ya dauka lokacin.
Sai dare sosai muka dawo masaukin mu da kaya niki niki shida kanshi kamar gaske ya taimaka kama min kayan zuwa dakina.
Ban tsaya jiran komai ba bayan fitan su bandaki na fada nayi wanka tare sa alwala na fito nayi sallolina sai barci don banjin cin komai a lokacin.
Washegari kamar yadda yace karfe takwas duk mun shirya zuwa airport mukai ban kwana da wanan kasan mai dadin zama da ni,ima dukda zaman kasan yazo min da akasi saidai hakan bai hanani jin wani iri ba lokacin.
A nan airport tun nufar mu wurin muka hagoshi suna magana da wasu mutanen kasan na Turkeya su biyu suna tsaye .
Yana saye a cikin suit dark blue clour daya kara haska farin shi ya fito mashi da kurciyarshi a fili ba zakace ya haura talinta da dan kai ba lokacin.
Mutum akullum shekarun shi gaba sukeyi yana kara canzawa amma shi sai ka rantse da Allah a kullun kara masa kuruciya akeyi idan ka kalleshi.
Ganin muna tun karo inda suke tsaye din ne yasa ya juyo yana kallon mu da alama cikin mutanen akwai wanda yayi magana a kan mu.
Wani iri naji lokaci guda faduwan gabane ya ziyarceni a lokacin ga tsikan jikina da yai wani yarrr har zuwa yatsan kafana ganin yadda yake sako min murmushi daga nisa.
Kafin mu karasa sai ganin Alaja da mutanen ta su shidda din nan a tsakanin mu dasu don haka sun tare muna hangoshi da mukeyi .
Haka yasa a hankali na sauke ajiyan zuciya tare da ja na tsaya a wuri daya don dan tako kadan ne ya saura dama tsakanin mu dasu.


ZAINAB IDRIS MAKAWA



ANA DARA GA , , , , , , , ,

7️⃣2️⃣ BY, , , , , , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MUB,DI , , , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257

ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋.

Yana ganina ya bar mutanen da suke tare lokacin tsaye haka ya wuto mahaifiyar nasa yana tafe yana murmushi dauke a fuskan shi har ya karaso inda muke tsaye gab dani yaja ya tsaya har muna dan hada kafada dashi.
Nayi saurin dan ja da baya kadan yayi murmushi yana fadi kamar rada kada ki yarda ki nunawa kowa dake wurin nan wani abu please.
Kamar gaba na ya tsage a lokacin don nauyi hakana daure na biyewa yadda yake so muje ko ya fada yana nuna min hanya da hannu tare da dan wani dukar da kanshi kasa.
Wani kallo suke bin mu dashi yayin da Alaja taji wani irin tukukin bakin ciki ya kara rufeta a lokaci guda as a mother to him ba zata taba barin dan ta ya rabi wanan yarinyar mai tattare da sihiri ba a fili haka ta fada a ranta.
Sam ba zai yuyu bama ace dan ta da daya tillo datake alfahari dashi a duniya ya auri yarinyar da bata da background ba yar kowa ba yarinyar da ko da nacikin cikin uwar shi ta kalla tasan me yake fadi.
Ba kyau baje abin duba nasaba da dacewa sam wanan yar bata cancanci zama surukarta ba ta kara dago kai ta kalle mu a daidai lokacin da muka karaso inda take tsaye tare da mutanenta gaba dayansu duk sun sha mur a fuskan su lokaci guda.
Da alama hakan bai dameshi ba shi ya nuna masu don muna isowa wurin su yaja ya tsaya yana gaisawa dasu sama sama tare da fadin ya suka kwana ?
Daga inda nake tsaye na gaida Alaja da ekkaro mah da yatsune a fuskan ta ta amsa da karo joo tana kawar da ido a kaina take fadin ya bai jirasu ba ya wuto zuwa airport.
Yake fasin yana sauri ne kada mu iso baya wurin Nabil ne ai ya dauko shi zuwa nan din bai dagakata ba ya juya ga fadin Sahiba meet my friend Nabil living in turkiya.
Muka gaisa da wanda ya kira da Nabil din ya kara fadin she is Sahiba by name a cikin dan murmushi Nabil din ke fadi nice name is she the lucky girl that charm your heart ?
Shima sin dariya kawai yayi mukayi gaba muna jere da juna gashi duk wani iri nake jin kaina a wurin don gaba daya sun zubo muna idanun su a kan mune felix ya yafuto yana fadin mu shiga kada a bata lokaci ka tabbatar da kowa ya gama kafin ka biyo mu.
Ya fada har munyi gaba kadan ya tsaya kuma yana fadin idan da wani matsala ina ciki sai ka sameni suka dan tsaya da abokan nasa suka dayi magana da larabci sanan muka nufi ciki.
Mazaunin mu daya da oga da tun zamana ban dago kai ba balle in juya inga na bayana da gefen mu shima kuma bai min magana ba sai zama dayayi ya harde kafafun shi.
Barcine ya daukeni wanda nasan rashin yin shi da darene da ban samuyi sosai ba a lokacin don tunanen zancen Alaja da na kwana fassarawa a lokacin ban gano manufar Alaja din ba gareni.
Tafiya ganin gari akace muna jin england da labarai a kanshi yau sai gamu a kasan cikin hukuncin ubangijin mu Allah.
Ba zan tsaya mamaki ba akan abubuwan da mukaga su Alaja da danta nayi don shi kudi babu abinda bai saka bawayi idan suna dashi.
Yammane muka isa masaukin da zamu zauna lafiyayyen daki irin na manyan mutane shi aka kama min don ashe wanda muke ciki iri dayane da nasa da Alaja sai sauran suna a cikin wanda baikai wanan din kudi ba.
Tun shigana ban fito ba ina cikin dakin bayan ramuwar sallah dake kaina sai kuma na haye gado da niyar barci a lokacin kararawan dakin naji yana kara na tashi naje na bude inga kowa waye.
Room service ce tsaye dauke da dan abin turo abinci tana min murmushi miss sahiba ko na gyada mata kai abincin ta shiga dashi bayan ta gaya min wanda yace a kawo


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login