Showing 294001 words to 297000 words out of 382072 words
To ba laifina ya kamata yanzu ki gani kiga laifin iyayyen mu da sukabi son zuciya suka aikatawa bayin Allah irin haka a baya yanzu lokacin namu fuskantar tashjn hankalin ne yayi.
Da ace basu bi son zuciyarsu da kuma hassada ga dan uwan sy ba da yanzu kowa na zaune kalau a cikin salama amma yanzu ba yadda muka iya don zakanya ta girma ko tsakiyan daji ni kaina abin a yanzu na kara gaskanta sakaiyane kawai ke bin iyayyen mu na abinda suka aikatawa dan uwan su a baya.
Yana kai nan ta dago kai da sauri tana mai wani irun kallo kamar zata cinyeshi danye ya gyada mata kai kawai ya figi suit din shi dake saman gadon daya gama feshewa ya fita nan ya barta zaune tana mai matsakancin kuka cikin tashin hankali.
Gidan su ya nufa don yana son ganin daddy a wanan lokacin kan binciken dayayi din saidai yayi rashin sa,a daddy din baya gida a wanan lokacin.
Yana tsaye yana mamakin inda mahaifin nasu yajene don yasan baya sakkon fita irin wanan lokacin haka sai idan wani abu mai muhinmaci sosai ya taso gareshi.
Bai kaiga karasa isa wurin motar nasa ba wasu mutane suka iso ya sheda su dan yasan wasu daga cikin su kusan irin aikin su daya saidai ba a ma,aikata daya suke aikiba don kowa da nasa bangaren wurin aikin ne.
Nan dai suka sameshi suka gaisa dashi suke fada mai sunzo neman maigidan nan ne don basu dauka daddy shine mahaifin shi ba a zaton su wani aikine ya kawoshi shima wurin daddy din .
Yake cewa dasu shima ai wurin shi yazo saidai baya gida OK babban nasu ya fada zamu dawo munzo ne mu tafi dashi dama don ya amsa muna wasu tambayoyi da muke so daga gareshi .
Basu tsaya mashi bayani ba suka juya nan suka barshi a tsaye cikin jimame a lokacin hjy karima ta fito zata fita unguwa zuwa gidan yarta don haka a gabanta aka fadi komai.
Itama dai hankalinta ne ya tashi sosai a lokacin jin abinda jami,an suka fada take fadin wanan tashin hankali haka dame yai kama ?
Haka jiya bamuyi barci da wuri ba a gidan nan don su hamza da yara su ya Nuhu sun dade a gidan nan tare dashi wanan abin gaskiya baidai yi dadi ba wallahi .
Mutum yanzu in kai masa rana sai yayima dare in ba shi ba wai yau Sahibace da kanta takewa Alh haka a garin nan.
Murmushi yayi yakai bakin motarshi ya jingina jikin shi da motan yace me Sahiban tayi kuma anty da ake mata wanan zargin haka yanzu.
Modibbo kai yanzu bakaga rashin kunyar yarinyar nan ba haka meye Alh bai mata ba zaman su garin nan don Allah ?
Anty idan yai mata ai yayiwa kanshine don wata kila da wani manufa yai haka din garesu mutanen da dukiyan su yana hannun daddy da Allah kadai yasan adadin abinda aka bar masu sai shi wanda keda dukiyar nashi kuma baya raye a yanzu.
Tsaye tayi cikin yanayin mamaki da rudewa yadda modibbo da bakin shi yake fadin ha tana kallon yadda yake fadin magana haka ranshi a bace.
Abinda bata taba ganin ya faru dashi ba yau ta gani a fuskan shi lokaci guda ya rikede ya koma wani kala dashi lokaci guda zaka fahinci tsananin tashin hankali ne yake ciki a lokacin.
Nan dai yayi mata bayanin komai yadda zata gane sai ga hjy na komawa bayan mota takai har tana kai ga jingina jikinta a motan .
Lailai muna cikin halin tsaka mai wuya a yanzu don nima wanan fita da zuwa zanyi can gidan mijin baby ance duk yan uwan nasa suna nan gidan a yanzu.
Zaki iya zuwa ki duba muna halin da take ciki in yaso sai a san abinda za ayi nan gaba don ba zasu zauna masu a gida haka gata gasu ba.
Har hjy ta fita daga gidan da motar ta yana tsaye yana waya da wani abokin shi daya bugo mashi wayan a lokacin.
Yana cire wayan an kunnen shi yana kokarin turawa aljihu motan daddy ya danno cikin get din gidan suna tafe tare dasu baffa Abdullahi da baffah hamza da wasu mutum biyu daga cikin yan uwan su.
Yana tsaye har suka gama fitowa daga motan ya karasa wurin su yana gaidasu a cikin ladabi suka amsa mai ganin shi baisa dakata da zance da sukeyi ba.
Daga can inda ya danja ya harde hannayen shi saman kirjin shi ya jefe masu tambaya daddy waye mukhatar usman Marwa ?
Mukhatar usman marwa baffa Abdullahi ya maimaita sunan cikin mamaki daga gefe baffa hamza yace wanan matashin ne da yai arzikin fice a harkan ma,adaina da sauran su.
Ai dan asalin kasan maidugurinr shi kuma yana taimakawa matasa sosai akace musan idan yasan sana,an ka kuma kana da sheda kan hakan zai iya tallafa maka ka daga kaima.
Wait amma kamar nasan mai wanan sunan a baya duk da ina tantaman cewa shine a yanzu don an dade ban kara jin duriyan shi bama ni.
Wanan dai dan maidugurine oh wanan kuma da nake fadi kamar a wurin sambo na sanshi a baya yazo dashi lokacin muna maiduguri har gidana wai ya hadu dashine yaje karatu ya samu matsala ana son aimai wullakanci a can shine ya taimaka mashi.
Shi din daine shine wanda a yanzu ya dauki wanan karan da karfi shine case a yanzu ya koma hannun shi kan wasu abu da yake tuhuma garemu sai ya gyara zancen.
Salati suka dauka lokaci guda baffa Abdullahine yake tambayan wa ya sanar mai da wanan maganan yanzu sai daddy ya dan yi murmushin manya yace mai yuyuwa su Sahiba dine ko?
Don idan basu ba wa kake ganin yasan dashi ko yana tare da marigayin a baya sai su sai ko ni da Allah yasa zan sani din a lokacin.
Sam basu bane don su na fara tuntuba koda sun san wani daya daukaka wanan maganan haka suka nuna min basu san komai su.
Zasu fada ma gaskiyane daddy ya fada kai modibbo ya girgiza mashi yace tun zamana da su ban taba jin sahiba ta fadi karya ba ko abinda ba daidai ita fa kai tsaye take abinta .
Daddy bayan wanan din jamin yansandan siri sun zo gidan nan neman ka na fada masu baka nan sunce zasu je su dawo dan anjima.
Ni ni suka zo nema akan wani dalili kuma zasu zo har gida suna nemana ko wanan zance kotu dinne kuma suka biyoni gida kanshi.
Ban tsamanin hakane gaskiya don su sai idan ana tuhuman mutum kan wani abu mai girma shine zasu baiyana ai.
Nasan da wanan amma kuma zuwan su din shine ya daure min kai a yanzu bai gama rufe baki ba motan su ya danno ya tsaya a wajen gidan basu shigo ba .
Ashe motocin har biyune ma bakake sabbi dal dasu suna sheki ga rubutun shi daga federal government suka zo Abuja can babban headquarters din su ke nan na Abuja.
Har suka karaso aka gaisa nan suke tambayan waye Alh Ali dcp a cikin su ya dan murmusa jin wai basu sanshi ya nuna masu kanshi.
Ok you're under are rest suka fito da takarda suka nuna mashi da sauri modibbo ya karaso yana fadin for what ?
Sorry sir ya fada da alaman sun san mukamin shi sukace umurnine daga headquater din mu kan supect da ake mashi.
Kafadan shi daddy ya dafa yana fadin kyalesu mu tafi amma ku dan ! da baya suma hankali a tashe a lokacin ne modibbo ya fito da wayan shi yana neman layin umma.
Daddy daya shiga ciki kuwa rudewa yayi ya kama kwalawa matan shi kira sai mommy ce ta fito take fadin hjy karima ai ina ga bata gidan nan don yara sunce tafita.
Ya manta data kirashi zata tafi gidan baby din ta duk da baiso ba dole saida ya barta ta tafi din ta cikin waya don ba yadda ya iya da fitinan ta alokacin.
Yace to zamu tafi don anzo tafiya dani Abuja a razane mommy tace Abuja lafiya Alh suwa zasu tafi dakai ?
Jami,an tsaro ya bata amsa da gani baya cikin hankalin shi a lokacin kuka ta sake tana fadin akan wanan case din ne kuma za a tafi dakai ko me baffah Abdullahi ne ya bata amsa da shine dai ya taso kuma yanzu saidai bamu san akan me bane kuma yanzu ake neman shi can.
Nan dai modibbo da ya shigo yana waya da basu san dawa yake ba a lokacin yake fadin wallahi fa yanzun nan gashima zasu wuce ai dashi yanzu haka ya tsaya yana sauraren wayan tare da fadin to shike nan hakan za ayi don umma tace ya bari na dawo na fita aiki dazun nan zata bincika yasa yace hakan.
Bai samu kanshi ba sai wajajan karfe dayan rana ya samu shigowa wurin mahaifiyar nasa dattijuwace baka amma ba sosai ba da zubin irin na kunuri.
Tana saye a cikin lafaya mai laushi kana gani kasan mai tsadane ga kamshin turaren su na asali dake tashi a falon tun har waje idan zaka shigo gida kamshine na asali zai tare ka.
Da murmushi a fuskan shi ya karaso falon sukai arba da mahaifiyan nasa yasa ya sake mata lalausan murmushin dake karawa fuskan shi annuri.
Saidai ya zube a kasa daidai saitin kafafuwan ta yana fadin ya salam tare da dora kanan shi saman kafafuwan ta ya sauke ajiyan zuciya kafin yace.
INDA, WATTU UMMI, ta sauke murmushi tare da shafo kanshi daya dora saman jikin ta tana fadin WATTU KILLEFIYA ya dan murmusa cikin jin dadi ya kara noke kanshi saman cinyan nata yana dan sauke ajiyan zuciya karo na barkatai.
Amma sun san da zaka zo yaudin ne ko wanan dandazon taron dana gani a waje haka nan ya dago yana fadin nima abinda ya ban mamaki ke nan dana tun karo gidan nan wai hakama a cikin siri na shigoma.
Tashi kaci wani abu kafin komai lokacin sallah ya gabato kada wani kuma yazo ya hanaka samun lokacin haka da dare ma zauna idan ka samu kanka.
Jin zata mike yasashi dagowa don yasan abinda take nufi shima tashi yayi suka nufi dinning inda abinci ke jiran shi aje alokacin da kanta ta zuba masu abincin ta dawo kusa dashi ta zauna.
Kin yin magana tayi a lokacin donshi kawai sai hakan ya bashi daman samun lokacin dayaci abincin sosai tana kallon shi.
Har saida ya kusa gamawa take fadin yanzun dai asirin su ya tono ke nan ya tabbata din zargin da kakeyi na shekaru su din ne suka kashe bawan Allah nan ashe ?
Sai lokacin ya dago kai ya dan kalleta yace wallahi ummi sune sune da kansu sukai mashi wanan aikin kuma suka tura iyalan shi nisa da gida don barazanan da sukai masu lokacin.
Salati dattijuwar ta sake tare da fadin kai duniya ina zaki damune haka wai yau har mun kai dan uwa ya kashe dan uwan shi don saboda dukiya.
Mutum mai kirki mai mutunci ga addini da sun barshi ya rayu dasu da Allah kadai yasan abinda zai zama yanzu a kasan nan yau ba gakuba kuma na kasa gareshi Allah ya tsayawa rayuwan ku tai albarka.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA , , , , , , , ,
8️⃣8️⃣BY, , , , , , , , , , , ,
ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL AWWAL, , , , , , , , , , ,
ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257
ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋
Sallaman hjy ghana da yaran ta mata a falon ya dakatar dasu daga hiran da suka dauko a cikin fara,a suka amsa masu sallaman tare da nuna jin dadin ganin su a lokacin.
Hjy ghana dake tafe tana fadin ashe ko shawaran autana yaci gashi ko mun sameshi a cikin gidan kamar yadda ya fada.
Nan dai suka karasa shigowa aka gaisa a cikin raha da nuna jin dadi daganin juna hjy din ke fadin dayaya muka samu shiga gidan nan ?
Mukhatar sai mu kara godewa Allah da wanan baiwan da yai maka a yanzu lumshe idamuwan shi yayi a lokacin zuciyan shi naso ta tuno mai da wasu abubuwa da suka wuce a baya amma yana tausan zuciyar nasa don kada ya tuna hakan a wanan lokacin.
Yare ya barke a tsakanin su wanda kowa ke ji a cikin su hjy ghana babban yayace ga mahaifin shi mukhatar din na uwa daya uba daya.
Suma suna da nasu rufin asirin tun can baya amma yanzu nasa ya taushe nasu har suke ganin suba komai bane a yanzu kinsan halin mu yan adam da hangen nisa.
Bamu waigen baya kullun idon mu a samane muna hango wa yanda suka zarce mu maimakon mu dinga kallon wa yanda muka fi don haka zaisa mi dinga godewa ubangijin mu kullun.
Zancen autan tane da suka fara dashi a baya ya kawota yanzu sai kuma yaran ta mata dake son su gana dashi kan wasu bukatu nasu.
Yaya kamar yadda suka saba kira a bakin su don yadda mahaifiyan su ke kiranta ke nan suma suka dauka ya tsaya masu a bakin su kuma.
Ban manta da zancen autan ki ba idan yadda nake so ya samu nan da dan lokaci autan ki zai bar kasan nan ga baki daya zamu zauna dashi acan inda nake zama a yanzu.
Wani irin dadi dattijuwar taji don wanan albishir din da yai mata duk da tasan a baya basu kyautawa yaron ba amma shi sam ba rikesu da komai ba asalima sai nuna yake kamar wani abu bai taba faruwa dasu na rashin mutunci ba can baya.
Abinda basu sani ba shine yana iya danne zuciyar shine baison ya tuna da wanan abin daya zama mai sanadin alheri a yanzu don su nashi sun kishi wani bare yazo ya daga rayuwan shi.
Nazone nagane ku a yau din nan kuma zan juya don na bar tarin aiyuka a gabana jin hakan yasa mahaifiyar shi ta dago kai da sauri tana kallon shi cikin mamaki.
Yace eh ummi yau din nan da yamma zan wuce lagos ina son a yau in gana da iyalan marigari na gansu su san ina nan ban manta dasu ba a raina inda taimakon da zan masu sai in masu kuma.
Taimako kan ai kayi masu shi yanzu tunda ka taimaka dukiyan su yana fitowa hannun azzuluman mutane a yanzu.
Ummi zan daiyi ni yanzu wancan din su sukayi kokarin koma da kansu har gaskiya ya baiya saidai zaluncin ya hana su fadi inda suka shiga da kudaden shi na baya wanda yafi komai yawa kuma don shi suka kashe din.
Wai wa kuke zance haka akanshi hjy ghana ta tambaya cikin rashin fahintan su a lokacin sai ummi din tace wanan bawan Allah daya tallafawa rayuwanshi da aka kashe shi a kaduna wancan lokacin .
Dan tunane hjyn ta tsayayi kafinta tunoshi tace duk tsawon wanan shekarun dama ana bincike a kai ?
Dama hjy ai baka kashe mutum ka zauna lafiya komai daren dadewa sai Allah ya tonama asirin kan Alhakin dake kan ka Allah dai ya tsare ya karemu daga miyagun kaddarori kawai babban yar nata daga cikin su ta fada.
Abin takaici ma wai ace yan uwan haihuwan kane sukai ma haka kuma suka wawashe dukiyan nasa iya tsakanin su basu tuna da iyalan shi va ummi ta fada
Yana jin su idanuwan shi a lumshe ba abinda yake tunowa sai ranan daya fara haduwa da Abba lokacin da suka amshe visa ga koran wullakaci.
Kan laifin data san cewa dasune ya aikatama uban laifi amma aka dora akanshi don yana matsayin dan cin galihu a wurin su.
Jin yayi shiru bai magana sai faman tunanen da yake yi yasa wace ake kira da anty shuwa take cewa dashi dan uwa nazone kan zancen muna baya dakai.
Sai lokacin ya bude idanuwan shi yana dan kallon ida suke zaune din cikin kokarin son ya tuna da alkawarin da take nufi sunyi dashi.
Nan dai suka dan tatauna abinda ya shafi rayuwan ko wanen su da irin taimakon da suke nema a wurin shi yace daya koma ummi ta tuna mashi .
Bayan tafiyan sune ya kara yiwa mahaifiyan shi bayanin abinda yake son zuwa yi lagos din da irin taimakon da yake sonyi din idan yaga halin da muke ciki a can.
Karfe biyar yabar maiduguri zuwa lagos bayan ya gama ganawa da duk wani