Showing 168001 words to 171000 words out of 382072 words
ka zauna a saman shi sai bayan gama bukin nan baki daya don manufan su su jefeka ka kafadi daga wanan bukin da zakuyi.
Fitowan felix ne dakin dauke da abinda ya aikeshi yakawo mai ya mika mai shine ya hanamu cigaba da maganan.
Rubutu yayi saman check din ya miko min tare da fadin gashi ki karba ayi yadda ya dace aikomai na taso daga inda nake zaune.
Na nufoshi don na karba a cikin ladabi ina fadin Allah ya karba yasa haske yakai gareshi dashi da sauran mamatan mu ga baki daya.
Ina isowa wani irin kamshine mai kashe jzuciya yaji ya daki hancin shi lokaci guda saida ya lumshe idon shi yana amsawa a cikin taushin murya da Amin ya Allah.
Don gaskiya yaji dadin wanan adduan nawa don shi yana son yaji wani nama mahaifin shi addua irin haka.
Har na juya naji yana fadin ki tabbatar da kunyi amfani da kudin sosai ga family din ki nina baki bakin hakan ki dauki iya bukatanki ki bada saura ga wanda kike so final.
Ina fita ya kalli felix da ke kokarin mikewa tsaye lokacin yake fadin a samo wasu kujeru yau din nan a saka a falon nan ka kwashe wanan a fita dasu.
Ya dago kai tare da fadin oga wanan fa basuyi ko wata uku ba da aka shigo dasu falon nan ko ka manta da hakan neya fada yana kallon kofan dana fita.
Yace dashi a cikin dan tsawa do as i said felix ko ka manta da mahaifiyana zata shigo gobe da yan uwan ta ne kasan nan wurin adduan .
Yace sorry sir ya dukar da kanshi kasa shi kuma ya shige zuwa ciki zuciyar shi cike da tunanen zancen da mukayi dashi a falon.
Tun safe take tsaye tana faman aiki duk da ba wani aiki bane takeyi umurni ne ga abinda zasuyi mata don girki da gyaran gida saboda wayan da tayi da mommy ta sheda mata dawowan mijin nata a ranan da ita mahaifiyar ta tursasa mashi sai ya dawo gida matansa ta dawo dakin ta itama.
Yayi mamakin jin haka don shi sam baiso haka baima cikin tsarin shi a lokacin don gaba daya yaso ya basu mamakine da sai sun girgiza dashi amma kuma aikin gama ya riga da ya gama mommy ta bata masa tsarin komai yanzu.
Tana zaune ta tsala kwaliya daga ita har yaran ga wani irin kiba data zauna tayi a yanzu tun bayan haihuwan yar su na biyu ta fara wanan kiban daya kara munanta ta a yanzu.
Tana zaune a falo tana jiran isowan shi koda taji tsayawan mota da hamzari ta mike ta kwashi yaran zuwa waje don su tareshi.
Sai ganin su yayi a gaban shi girshi ba kunya wai tana mashi sannu da zuwa a cikin daure fuskan shi gareta ya fito daga motan ta kara gaidashi ya amsa a daure ya wuce har yaran ba tare daya taba su ba zuwa falon shi.
Kamshine ya tare shi a falon zai shige yaji babban yar mai sunan mommy tana kiran shi da daddy yaja ya tsaya ya juyo yana kallon yarinyar tare da rage tsawon shi gareta yadda ya saba masu a can idan ya dawo.
Ya sunbanci yarinyar a goshi tare da tambayanta yaya take tana masa gwalanci duk da ta fara mantawa dashi don watan su hudu ke nan basu tare dashi.
Daga bayan shi inda Nazifa take tsaye ne yaji muryan ta tana fadin watau mu ba za ai muna wellcome ba da dawowa ba sai ita mai sunan hjy ku ko ?
Bai mata magana ba sai mikewa da yayi yana karban yarshi a hannunta ya daukesu duka biyu zywa dakin shi driver daya daukoshi ya shigo mai da kayan shi ciki a lokacin Nazifa ta dauka zuwa dakin shi abinda bata saba yi ba ke nan a baya.
Saida ya huta tare da yaran a dakin shi ya fito zuwa falon don kiranshi da Nazifa ta matsa dayi na ya fito yaci abincin da yasha gamin bokaye da malamai da mamanta tayi ta karbo mata shi don kawai a samun kanshi a dinga juya shi yadda ake so saboda kafiyan shi da taurin kai da yake dashi kuma yake nuna masu shidin shine fa.
Saidai sun makaro don nacin ta yasa ya ankara da hakan don haka koda yana zaune sai waya yakeyi harda na iska tana zaune a cikin damuwan rashin cin abincin shi duk ta kagu taga yakai cokali a bakin shi.
Can dai da taga ya gama wayan ta kirkiro murmushin kissa tana fadin wai ko fushi kake damune na abinda ya ffaru kaki cin abincin nan ?
Ya kallota a lalace yana fadin fushi fushi akan me mekikai min da zanyi fushi aiku zance kuna fushi keda kuka koma gida ba tare da nasan laifin da nayi maku ba bayan mun rabu lafiya dake.
Tace kayi hakkuri don Allah nagane kuskurena nayin hakan don ban dauka Abba zai canza abinda wani manufa ba haka.
Ban san wani irin kiyayya ke tsakanin gidan ku da Abban mu ba har yake ikirarin shafan diyan da muka haifa dakai suma abin ya shafesu don sam Abba ya gwada min baya kaunan jinin ku ko kadan wallahi.
Duk da mama ta dan fada min cewa matsala aka samu na rabon dukiyan wani dan uwansu maikudi da yarasu tun muna kanana wai kowa nason wani abu ya kasa barwa dan uwa a tsakanin su shine wai mafarin wanan fadan nasu har yanzu.
A yadda naji mamana cewa har zargin duk suna da hannu a cikin mutuwan dan uwan nasu a lokacin da yake daddy na sama aka rufe zancen wai har yanzu kuma ba, a san inda iyalin dan uwan nasu suke ba gashi su sun raba dukiyan nasa a tsakanin su suda su baffah gyade da sauran su.
Gaskiya abinda su Abba keyi baida kyau saidai kuma ai dukiyan dan uwan sune shine kawai amma aibai kamata ace har ya zama matsala a tsakanin su ba haka.
Tayi shiru tana dago kai ta kalloshi don dama tana duke tana sharewa yarta dake shan nono bakine saita dago kai jin yayi shiru yana sauraren ta.
Irin kallon da yake mata a lokacin shiyasa tasha jinin jikin ta ta fara zargin irin baran baraman da tayi ko katobara a gaban shi duk a wautanta nason su shirya dashi ya sake jiki da ita saboda kewan shi da sharenta da taga yanayi.
Amma cikin labarin abu biyu yafi tsaya mai a rai na farko shine cewan da tayi mahaifin shi na cikin harkalan da akayi na kashe namu mahaifin.
Sai kuma cewan da tayi mahaifinta har diyan da suka haifa baya kaunan su yana iya sabauta su don irin kiyayyen da yake nuna masu.
Mikewa yayi a zabure saida gabanta ya fadi ganin yadda lokaci daya ya juye mata kamar wani zaki dashi yakai hannu ya karbi yar dake hannun ta ta rike tana kallon yanayin shi.
Ina zaka da ita ya mika hannu ya fisgeta da karfin tsiya yana fadin bani yata in kaisu inda za a kulamin dasu don bazan barsu inda zasu tashi da rashin imani ba.
Ganin da gaske yakeyi yana shirin fita mata da yaran yasa ta yunkura ta rigashi isa kofa ta kulle ta saka makulin a cikin jikin ta.
Hakkuri ta fara bashi yana kokatin gyara yaran baida niyar bata su dabara ya fado mata ta dauki waya a cikin kuka ta kira mommy a cikin kuka take fada mata komai mommy din tace bashi wayan ta mika mai yaki karba tasaka handsfree tana fadin koma meye na fada ma kajirani gani nan zuwa yanzu gidan.
Koda mommy ta iso ta samesu a cikin tashin hankali sosai don Nazifa tasha kuka har ta godewa Allah a lokacin don tashin hankali data gani a fili lokacin.
Da umurnu ta fara bashi ya mika mata yar data fara kuka sosai a lokacin baiso ba ya mika mata yar ta zauna tana fadin meya kawo haka yau yau da dawowan ka ?
Ina na fadama cewa komai ya wuce kada inji wani magana wani irin huci yayi da baki kafin yakai zaune yafara fadawa mahaifiyar nasa abinda ya faru tiryan tiryan.
Hjy sai kada kai takeyi tana fadin Nazifa mai ya kaiki wanan katobaran haka a gaban mijin ki baki tunanen in mahaifin ki yaji wanan zancen dake da uwarki duk kun shiga cikin matsala ke nan.
Nan dai mommy ta samu ta kwatar da fitinan har ya sauko kan dan bakin data bashi yace yaji amma yaran sa ba zasu taba zuwa wanan gidan ba a yanzu.
Hakana ya kwana ranan yana faman tunanen wanan zancen biyu a zuciyar shi abunda ya hanashi barci ke nan a ranan.
Saida na isa gida na duba abinda ya ban tunda na saka a jakka kafin in fito ban dauko na dubaba saidana gama cin abinci na dauko jakkana ina dubawa.
Ba karamin kaduwa nayi ba lokacin da naga yawan kudin da yai signing a karbo gashi har ga Allah yace na zari kusan rabi muyi amfani dashi a gidan mu muma din ai marayune.
Umma na kira ina fada mata abinda ya faru tayi shiru tare da mamaki cikin rike habanta can tace dani duk da hakan ki masa sadaka yadda ya kamata sai ki kwantata ki rage saura din Allah ya jikan musulmai ya gafarta masu.
Na amsa da Amin zuwa la,asar na samu Abdulhamid a office na fada mai duk halin da ake ciki game da yadda mukayi da ogan mu din dashi muka fito tun a ranan muka fara bin masalataiya muna ganin limamai muna basu sadaka da abubuwan amfani a masalcin.
Washe gari muka dora a inda muka tsaya don muyi yadda ya dace gaskiya mungama da masalataiya muka koma ba mabukata musulmai abinci sosai har labari yakai kunnen ogan namu.
Ranan dayace din ranan mahaifiyan shi ta shigo suna falo sai ga wasu mata sunzo gaida ita da zuwa nan suke fada mata cewa sunga an saka hoton mijin nata babba ana mashi addua taji dadin hakan sosai kallon dan nata tayi don tasan aikin shine bana kowa ba.
Murmushi ya sake mata taka tsantsan yakeyi da mahaifiyar nasa sosai da kanwarshi da sukazo don bai yarda wani mai aiki dan lagos ya dafa masu wani abinci ba da abinsu sukazo daga can don tsaro.
Ranan da za ai taron bamu zauna ba tun safe muke faman shiye shirye da zirga zirgan komai ya kammala daidai yadda aka saba yi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA, , , , , , , ,
5️⃣0️⃣ BY, , , , , , , , , ,
ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL KABIR, , , , , , , ,
ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KARFIN IMANI KE SAKA TSORON HADUWAN BAWA DA UBANGIJIN SA ALLAH YA KARA MUNA IMANI A ZUCIYAR MU AMIN, , , , , , ,
Tsatsaye muke duk kan mu a falon nasa daya ban mamakin sabon gyaran da naga anwa falo din a cikin kwana biyu haka har center kafet din nan daya dauke min hankali a ranan babu shi yau dana shigo.
Dukkan mu farin tufafine a jikin don wanan sha, anin na dinka farin less da akai min dinkin buje da riga kuma dinkin ya karbeni don zamanin buje darigane abin yayi sosai sai kuma dogon riga wanda ni nafi saka dogon riga redmade ba wanda aka dinka ba.
Takon ogane ya fito ya samemu inda muke tsaye muka shiga gaidashi ya nuna muna kujera mu zauna shima don ya kai zaune yana fuskantar mu.
Jimoh ya fara kira ya dago kai yace kasan wanan abu yashafe ku dukkan ku tunda ya shafeni don haka zaka kula da komai dake gudana a wurin taron nan har abincin da za,aci ka kula da lafiyan shi you know you people are special from d other and kuma ba kowane yasan alakata daku haka ba a cikin family dina so take care.
Oga Jimo din yace yes sir ya juyo kan Felix yace make sure u felix kana hankalce da duk wani motsi na kowa a wurin ka kula da abinci da abin sha wanda bakin mu zasu ci baida illa ko kadan yace yagane.
Sai ke yemisi bakin mu mata su samu kulawa sosai ta hanyar directing din masu kula da bangare su yaza kina kulawa da wanan banda rawan kai ya kara mata hakan aka kwashe da dariya sabanin nida ban ko murmusa ba don nawa dariyan zai kona mata rai fiye dana saura.
Kaima Adnan aikika kenan a bangaren maza a yau don Allah ku kula suka amsa da yes sir sai ya kallo inda nake yana fadin u Sahiba you will be with my family i mean my mother and my sister and others take care of their needs please kada ki yarda ki daga a inda muke komai taro zaki saje a cikin mu tare damu kamar yar family din kike kina saka ido a kan mu.
Felix yace baby girl ke nan dai ya watsa mai harara kafin ya fara fada yana fadin ka kula ba aikin wasa nake so ba don nasan akwai makiya a wurin dole zai kasance da hatsari a wurin sosai don kaga wanan taron yafi na wanda mukayi a baya cika sosai .
Ya amsa da zai kula kudi ya fito dashi ya mikawa kowa wrafer yana fadin a samu na badawa kunsan komai na bayerabe kudine shi don haka ya bamu namu rikon .
Kowa ya mike nima haia ya juyo yana fadin Sahiba go inside now zaki samu mahaifiyana tare da yan uwanta suna shiri kufito tare.
Gabana ne ya fadi lokaci daya idan na shiga wazance dasu nake amma a fili yes sir na amsa mai ban ko juyo gun yan uwa ba ma sakai na shige ciki.
Cikin babban wurine sosai mai dakuna da yawa a ciki akwai kuma katon falo maidan girma daga ciki din na samu wuri na zauna bancewa kowa komai ba ina kallon zirga zirgan su da kowa keyi na shiri.
Sautin wani waka ana salati na fara ji haka yasa nasan zasu fito daga cikin zuwa wurin taron ke nan son nasan komai akan taron na tashi naga anayin sa tun ina karama kuma duk wankan da zasuyi na iyasa sosai nima.
Na mike na gyara na fara dan takawa na shige cikin su muka jera tare zuwa waje a falo muka sameshi nan ma tare da wasu yagama ya tako zuwa gaban uwan shi ya duka ta dafa kanshi tana mai addua sauran masu kurciya a wurin duk suka kai duke ana fadin Amin amin amin ya Allah.
Lokacun da aka mike din ne na samu kustsawa nakai kusa dasu na tsaya har aka fito inda za a shiga mota motocine bakake wul dasu tunda zamu shigo an wankesu sai walkiya sukeyi suna sheki da daukan ido.
An bubudesu da sauri ya nuna wanda mahaifiyar nasa zata shiga suka nufi wurin alokacin naja na tsaya ya kalloni da sauri nabi bayan su nima.
Kowa ma yabi don ga masu kirarin su nan suna kirari har muka isa wurin motan suka shiga suka zauna uwar da kanwarshi a baya sai ya bude gaban a zaton kowa a wurin shine zai zauna sai juyo yana fadin in shiga gaban motan.
Na shiga na gyara aka rufe ya koma baya tare da mahaifiyar shi suka saka kanwarshi a tsakiya sauran yan uwan su suka shiga sauran motocin dake wurin.
Idona na lumshe tare da ajiyan zuciya lokacin da naji motan ya tashi ya fara tafiya damu zuwa wurin taron ke nan.
Sha,aban waye wanan daka hada mu da ita ban gane ba mahaifiyar tasu ta fada abinda yasani bude idona ke nan lokacin.
She is my new sectrary ya fada wanan karamar yarinyar haka aini na dauka ka hakkura ka samu wace kake sone yanzu but wanan ai tayi karama sister shi Aisha ta fada.
Stop dat Aisha ya fada a kausashe ya zama dole sai ta kasance damu ke nan mahaifiyar su ta tambaye shi.
Aikintane ta kula damu a wurin shine dalilin zuwa da mukayi tare ita don ta kula damu a wurin ya fada yana kawar da kai gefe daya.
Shiru motan yayi har lokacin da muka isa wurin taron addua inda wani filine babba da aka ware dan shagulgula a garin banyi tsamanin taron zai tara jama,a irin haka masu yawa a wurin.
Saigashi indama zamu aje mota ya zama aiki a wirin saida kyar felix suka samu a can ciki aka shiga da motan muka samu muka sauka.
Dakyat suka samu kaiwa inda aka tanadarwa su iyalin shi don bayan su yan dakin su su biyu akwai wasu mata biyu da mahaifin nasa ya haifa mahaifiyar su yan yare dayane da mahaifin nasa.