Showing 369001 words to 372000 words out of 382072 words

Chapter 124 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28377

mu sha karshen abin.
Duk da a yanzu na fahinci sabon matsalanki shine da zaran mun kebe dani dakene kike shiga wanan halin kenan haka na nufin akwai abindake faruwa dake a wani wurin yanzu kuma.
Kallon mamaki nake mashi don jin kusan yasan komai dake faruwa dani a yanzu saidai ta yaya yasan da hakan ke nan ?
Kada ki damu ya fada yana kai hannunshi saman kafadana ya rugumoni zuwa jikin shi idona na lumshe lokaci guda don jin saukan hannun nashi da nayi a jikina lokacin.
Yana kuma fadin nikaina nasan matsalan ki tun farko sanina dake sahiba bayan haka kuma ina bibiyan komai sannu a hankali nasa daga ina zan fara da matsalan nan naki tun yanzu.
Hawaye naji yana zo min wanda bansan kona meye ba a lokacin gwaggo hari ashe tana da gaskiyanta wazai ga ramin maciji da rana yazo da dare ya taka bakin ramin da kafanshi.
Babu mai hakkuri da wanan irin matsalolin nawa danima ya sameni da rana tsaka tunda da farko ba haka nake ba nima ai.
Hada jikinshi yayi sosai da nawa ta yadda har nake iya jin saukan numfashin shi a lokacin a cikin gangan jikina har banyi aune ba naji saukan hannayen shi saman jikina yana yawo a hankali.
Jikina na kankameva wuri daya tare da kara runtse idanuwa da suke rufe a lokacin don jinda nake kamar ana watsa min ruwan zafi masu zafi nake ji a lokacin.
Banyi aune ba naji yana kokarin kwantar dani saman gadon a cikin wani irin karfi da bai taba tsamanjn jinshi gareni ba kasancewata yar firit dani ga idonshi.
Yasa yayi saurin jada baya yana zuba min ido tare da kallon yadda jikina ya dauki rawa lokaci guda saina fara jin ina zuwa baya suuu lokaci guda idona yana kara rufewa
Kafin hankalina ya karasa gushewa ina iya dan jiyo sautin karatun daya fara yi shi kadai zan iya karaswa a lokacin wanda naji a lokacin.
Nidai a karshe na bude ido na ganni wujuga wujiga kwance saman gadon dakina da sai warin hayaki dake tashi ko ina na dakin ga baki daya.
Yunkurin tashi nayi zaune bayan nagama bin ko ina na dakin da kallo lokaci guda na yunkura na mike zaune murya hjy su uncle ce dake zaune da a gefena tare da kanwarta.
Sannu yar nan suka kara fada lokaci guda sannu kinji sannu da fama wanan abu haka yaki guda tun safe ana abu guda.
Ai Allah ya kawo saukin abin nata mabiyan manyane fiye da wa yannan da aka turo matasu yanzu gashi sun fada da bakinsu cewa sarki ya tare wuri yana wahalal dasu da basu azzaba.
Aini jikina duk ya mutu idan ba ko aikin aljani ba har yaushe yar nan tasan wa yannan labarun data bamu a yanzu ?
Bashi bama ba abinda yafi ban mamaki shine kamar wai yadda zancen gonan gadon su yaran nan ya fito a bakin wanan yar har take bamu labarin shi tas kamar a gabanta akayi komai alokacin.
Jinsu kawai nakeyi don ina son kewayawa bandaki a lokacin kuma suna zaune a dakin nawa haka yasa ina mikewa suke tambayana da turanci nayi magana na fito daga dakin suna ganin haka a zatonsu bana cikin hankalinane yasa nake kokarin fita daga dakin gashi sai wani irin zufa nake tarsowa a jikina lokacin na wahala.
Ina zaki tafi gaba dayan su suka fada lokaci guda na dan juyo na kallesu ina fadin zan shiga bathroom ne aiga kofa nan dakin Fatima zan shiga na fada.
Jin hakan yasa sister ta tashi da sauri tabi bayana zuwa dakin har na kewaya na fito sallah nake kokarin yi a lokacin haka dai na daure nayi sallah dake kaina a lokacin.
A nan na kara kwanciya don banson hayaniya ido na lumshe duk da ba barci nakeyi ba lokacin amma saika dauka nayi barcine a lokacin yadda na lafe.
Kokarin bude kofan da akayine yasani bude ido shine ya shigo tare da wani tsoho sosai mai farin gemu gajere da dogon tasbaha a hannun ga warin turareshi yasa kaina hawa na fara jin wani iri lokaci guda.
Da sauri uncle mukhatar yazagayo zuwa inda nake ya tallafoni lokaci guda na fara shakuwa ina gyatsa duk lokaci guda ga hamma da nake sakewa ba kakautawa .
Kai tsohon ya fara kadawa tare dan matsowa inda muke din zaune sai kokarin kankame jikina nakeyi don kada ya kara tabani.
Ido sosai tsohon ya kafa nan ya fara karatu yana tofa min tare da umartan uncle da yadafe min kaina sai girgiza kai nakeyi hawaye na zuba min a idanuwana.
Ya dan jima yana karatu kafin ya fara fadin wanan babban kayane a kanta sai baki gasunan sunsha fama sai sun shiga jikinta suma amma hakan bai yuyuwa .
Karatu yaci gaba dayi abin mamaki yaren su na farayi na kanuri ina fadin abar karatun nan nan muka zuba yare dashi nan abinda naki fada a farko na fada cewa anturosune su hanani zaman aure da mijin wata.
Sai sukai rashin sa,a sarki mai karfin iko yana jikina do haka ba wani wanda ya isa ya rabeni a wanan lokacin su kuma sunyi alkawari har sun amshi jini a matsayin hadayansu ko.
Salati dakin ya dauka daga can kofa muryan sister ne ke fadin waya turoku wanan aikin haka gareta wani kallo aka watsa mata kafin ace wace ta turosu ta riga datafi karku dukkan ku banda wanan godiyan da aikin mu baya iya tasiri a jikin ta ko kadan.
Mun gwada ko wani hanya bamuyi nasara ba ga hakan gashi kuma yanzun ana kona mu ba zamu yafe ba dole mu koma jikin wanda ya aikomu zuwa wurinta.
Sai wani Ihu da kowa dake wurin ya razana da hakan dajin ihun maishi yana wahala a lokacin an dauki lokaci ana wanan yakin kafin su ce sun fice su tafi nayi lankwas kamar bani da rai a wurin.
Allah ya taimaka tunda nayi barci ban falkaba sai washe gari na tashi da ciwon jiki da kasala haka yasani kwanciya ko falo ban iya lekowa ba a ranan.
Yayinda shi kuma yake ta faman sintiri dayin hayaki da shafa abubuwa a jikina hardasu shakawa haka sunin ranan suka wuni dani da dare kuma tare dashi din muka kwana duk da akwai mutane a gidan da dole suzo su zauna dani din.
Ranan kan ba abinda ya faru bayan kunyan hakan da nake danji duk da ina kwance ba lakka a jikina hakan bai hanashi gwada rungumana ba a Darren kamar yadda malamin yace su gwada hakan a gani.
Dole haka ya barni ya koma don dama zuwan banana shirin bane yazone ya dan Kwan daya sai gani gani kwana uku don Lauren daya sameni bayan Susan nasa din.
Fabian morrow nake ina kallon kaina yarda na rame na nayi duhu don abinda ya faru din dani lokacin a wurin Fatima nake jin abubuwan daya faru dani lokacin naji komai daya faru dani daga bakinta bata boye min komai ba.
Yanzu kunne aka kasa ashe don sun ce zasu koma gun wance ta turosu su zo gareni su bata min jin dadin aure da farin cikina da sauran sheri .
Na daina ji nauyin shi da kunya ayanzu don yakan bugo waya mu dauki lokaci muna hira har yakai na dan fara sakewa dashi sosai yanzu din.
Ina da wata daya da kwana biyu a garin maiduguri muna kuma zaune lafiya da kowa kullun kuma ina waya da umma har Ammar ina jin lafiyan su sai hakan yazo min da sauki don kamar muna tare a gari dayane dasu sai kewan nasu ya rage min a raina lokacin.
Kwatsan ya fado muna kamar wancan zuwan saidai wanan zuwan na safe yayi muna tunda ya shigo yayi wanka bai leko falon ba.
Don hakane muka samu daman yin aiyukan mu wanda nida kaina na tuka mashi tuwon amala miyan ewedo da tantakwshi sai kuma naman dana watsa kamar yadda mukeyi a can.
Bayan mun gama an shirya komai wanka nafada yi na fito na gyara jikina tsab cikin wani shadda kamfala milk colour dake ta maikon sabontaka a jikina.
Part din nasa na nufa a kwance na sameshi ringine ya kwanta ya dora hannu daya a goshin shi kamar me tunane jin sallama na yasa ya dan dago daga yadda yake.
Yana kallona na karaso ina fadin good day sir how was your jorning saida ya dan dago tare da mikon hannun shi zuwa gareni na karasa takowa a hankali har Inda yake kwance din jawoni nayi na fada a saman jikinshi.
Ya maida hannun shi ya rufe yana sauke ajiyan zuciya lokaci guda sam wanan karon banji komai da nake ji ba a lokacin shima sai ji nake yana dan sake ajiyan zuciya na dan lokaci.
A haka yaso wasan ya canza lokaci guda amma sai nayi saurin mikewa ina fadin your food is ready na barshi a kwance .
Murmushi yayi ya bini da kallo yana fadin ya kamata by now a tausaya main hakana a barni naji dumin amaryana ko zan samu relief a zuciyana.
Nima dan guntun murmushin na sake cikin kunyan shi nace ai ko yanzu kaji dimin jikin nawa me kuma ya rage a yanzu din.
Ohh realy ban iya bashi amsa ba Allah ya taimakeni wayanshi ta dauki kara haka yasa na samu na fice daga dakin zuwa nawa dankin.
A gaba mirrow na tsaya ina kallon kaina tare da sake ajiyan zuciya ina bawa kaina shawaran abinda zanyi a lokaci don kawai na nunawa wanda ke bina da sheri a kan auren sherin shi baicini ba.
Yaji dadin abincin sosai har yana rokon aje mashi ya kakara da dare gidan hjyn shi ya tafi bayan fitan shi mun zauna da fatima a dakina muna hira tana ta kara nausar dani yadda ya dace na dinga yi idan yana gari wanda sai kallonta kawai nakeyi ni.
A ranan kan komai ya wakana tsakanin mu saidai kafin hakan ya faru shi kanshi yasan abinda ya taba don bani kadai bace naji jiki gaba dayan mu kowa ya ji nasa .
Abubuwane dake dukkan bangaren mu sai dai da taimakon ubangiji har aka samu kadarin abin ya karye inda a wani bangare kuma faruwan wani abu ya faru don the massage back to sender now.
Badon komai ba sai dan yawan alherun mu da tsare ibada da bada sadaka da Allah ya hore munayin shi gaba dayan mu nida shi duka.
Wanan yasa duk wani sherin da mugun nufi da aiken sheri na sihiri baya tasiri a kaina gashini alherina gun kananan yarane da bukata na sosai haka zan aiki yaron dake zama damu ya bi hanya yabawa mabukacin daya hadu dashi alheri ko nasaka aimun kosai da manja ko na sayi gishiri mai yawa na bayar akaiwa mabukata unguwar tallakawa .


ZAINAB IDRIS MAKAWA

ANA DARA, , , , , , , , ,

BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , ,

1️⃣1️⃣2️⃣

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM, , , , AL,BAQI

YAR UWA KIJI TSORON ALLAH KI DAINA FITAR MIN DA NOVEL DON KIN BIYA KI BARI WANI YA BIYA SABODA ALLAH👋👋

Duk yadda yaso na sake jiki dashi da safe naji kunyar hakan kwana shi biyu ya juya ya koma daga sunan zuwa ghana aiki ya kwasheshi kuma zuwa Australia daga can sai a waya mukai magana dashi.
Haka naci gaba da rayuwa ni da fatima sai yan abokan arzikin da a yanzu muka samu a garin dake dan zagayo ana mu,amula arziki dasu.
Ba fita mukeyi ba don haka bamu da labarin komai dake faruwa sai wani shigowa da sister tayi a wurinta muke jin labarin ashe hjy falmata bata da lafiya kusa wata biyu ke nan duk labari har ya baza gari muna cikin gida bamu sani ba.
Ba tare da jin komai ba nayi mata faran samun lafiya na canza topic din hiran mu saboda ban dauki zancen a komai ba har a zuciyana.
Mun wayi gari da mumunan labarin da anty Amarya ta bugo muna tunda safe cewa an kama ya mustapha a kasan waje tare da wasu abokan harkallahshi su shiddah.
Wanan labarin sai baimun dadi ba sam danaji amma sai naga ita Anty kamar ma murna rakeyi da hakan don tana fadi tana kwasan dariya a lokacin.
Haka na wuni ranan a cikin damuwa don wanan labarin daya riskemu maradadi ga ya mustapha din a ranan ina jin yadda Fatima take waya da aibanta shi .
Nakira umma munyi maganan amma nace ta kyale idan ba gwagwo hari ta kirata da kanta ta fada mata ba don kada su dauka muna bibiyan bayan sune saboda mutum wuyan sha,ani gareshi.
Dole muka daiyi Dan zance kan abinda ya shafi zancen kafin my kashe wayan cikin tausayawa a halin da abin ya shafa ballema da take dan son ga iyayyen shi kasancewanshi shi kadai a garesu.
Ba anty ba kawai had Faiza data kirani iron abinda take fada min me nan cewa wai asirin shi ya tuno dama yana wandaka da kudi son ranshi, ashe kallar sana,an da yakeyi ke nan.
Gashi yanzu asiri ya tonu gwaggo hari tana cikin tashin hankali tana bin manyan kasan su taimaka afito mata dashi suna fama kashin kudi.
Don babu Wanda zai iya fito dashi akace son laifin nasa babbane sosai na katseta da fadin har in baida laifi ba zasu sakeshi ba ?
Yana da laifi kan don ashe dama sana,arshi kenan sayar da kwaya ga anty Nabila dake faman jiranshi taki kula kowa akanshi yanzu.
Kuma shi yace baya sonta dan dama dama Fatima gwaggo hari kuma ta hana halakan shi da Fatima din wai bata hada zuri,a da anty Amarya don ba mutanen kirki bane.
Tay tayin maganganu da dama nidai said umm nake amsa mata had zuwa lokacin da muka gama wayan da ita hankalina ya tafi ga zancen ta sosai.
Yanzu na yarda da cewa kowa kanshi yasani a fannin ubanne na don na fahince su tsab kowa basu bari ba me nan don' ai ba anty amarya kawai ta haifi Fatima a gaskiya camfinsu yayi yawa sosai wallahi.
Wasa wasa wanan maganan har ya kai gwaggo hari ta kirani da kanta kan case din tana kuka take fada min na taimaka mata nayiwa uncle magana ya tsoma baki ko Allah zaisa a sako ya mustapha din don shi yana hurda da manya sosai.
Nayi mata alkawarin zan mass magana na kuma jajanta mata kan matsalan tana godiya muka gama wayan na kashe ina fadin olesi, olopopo.
Yanzunne tasan ina da rana run ranan da suka tafi bata kirani taji lafiyata garama in na kirata a lokacin ina masu yaya hanya har sau biyu.
Na kira umma na sheda mata yadda mukayi da gwaggo hari din tace idan ba matsala nayiwa uncle din waya na sanar dashi halinda ake ciki koda akwai taimakon da zai iya mata a kan case din.
Banki ba nayi sa,a ranan ya kira waya saboda haka nake kwance jiki ba lakka said ga kiranshi bayan sallah la,asar na dauka muka gaisa dashi jin muryana da yayi wani iri yasa yake tambayana meke faruwa ?
Dan jim nayi kafin na amsa da babu komai yace your voice sound like kamar baki da lafiya na danyi murmushi kafin nace dashi kawai dai iam not in good mood ne yau din.
Ya tambaya da sauri akan me fa nace kawai labarin wani cousin brother din mune ya samu matsala sai naji yace wanan da aka kama a abroad ?
Cikin mamaki na tambaya kasan da zancen ne yace kwarai kuwa nasan komai saidai laifin ai babbane sosai don hakane kowa baya son saka kanshi ciki.
Amma aiba laifin shi bane asalima kayan da ake tunanen nasane ba kayan shi bane sheri akai mashi kuma sunki bari yayi bayani.
Yaya kikasan da hakan ke ya tambayeni Dan murmushi na sake tare da fadin na sanine mana haka zancen yake yanzu haka wa yanda sukai mashi sherin suna kokarin barin kasan ta ruwa .
Nan na kara mai bayanin komai tare da rokonshi a kan ya taimaka muna please son case din ya zo da sauki da sauri yace ta yaya zan jefa kaina a wanan case din mai karfi haka ?
Akan mutanen da har gobe nasan ba sonki sukiyi ba fatima tareshi nayi da fadin koda basu sona sune dai yan uwan nawa dana sani kuma nake bearing din sunan iyayyena a yanzu.
Dan ajiyan zuciya ya sauke yana fadin yanzu ya kike son ayi ke nan don dole risk zan dauka na jefa kaina a cikin wanan case din don ba karamin case bace tunda ba a Nigeria aka kamashi ba.
Bayani nayi mai yadda zai gane yayi shiru yana saurarena har saida na gama kafin yace anya kuwa Sahiba ba kina ganin har hanji ba ?
Wanan irin bayani haka kamar a


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login