Showing 1 words to 3000 words out of 382072 words
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM DUKKAN GODIYA DA YABO YA TABBATA GA ALLAH SARKIN KOWA DA KOMAI MAI SAMAU MAI KASAI DA ABINDA KE CIKIN SU.
YA ALLAH MUNA GODIYA DAKA NUNA MUNA WANAN LOKACIN LAFIYA UBANGIJI ALLAH YADDA KA BAMU DAMAN FARAWA LAFIYA KA NUFE MU DA GANI KARSHEN LABARIN NAN LAFIYA ALLAHUMA AMIN.
YAN UWA ZOMU ZAUNA ZO MU SABA MUYI HAKKURI DA JUNA GA DUK WANDA ALLAH YABA IKON GANIN KUMA YA SHIGA GROUP DON ALLAH MUYI HAKKURI DA JUNAN MU, , ,
YAR UWA LITTAFI DAI NA KUDINE DARI BIYAR NE KACAL DON ALLAH KI DAURE KI BIYA KAFIN KI KARANTA DON GUJEWA SHIGA HAKKIN WANDA BAKI SANI BA, , , ,
Misalin karfe biyar da rabi na yamma amma kuma yanayin garin ya juye kamar karfe bakwai da rabi na dare zuwa takwas.
Don gagarumin hadarin daya taso a lokacin ya hade garin ga baki daya baka ganin komai sai masu abin hawan dake gittaiya da masu sauri a kasa don kada ruwa ya fado a lokacin.
Cikin hakane kuma wata katuwan jeep dark blue sai sheki takeyi ta keto titin da gudun gaskeda alama mai shi sauri yakeyi ya kai inda zai tafi kafin ruwan dake barazanan fadowa ya sauko
Titin shiru don unguwan ko ba hakan bai faye yawan mutane sosai ba wani gida a layin motan ta tsaya tana horn sai maigadin gidan yayi saurin bude mashi kofan.
Motan ta tsaya a daidai inda ake parking din motoci a gidan wani dan dattijo ne ya taso shima da saurin shi zuwa inda motan ta tsaya yana faman duke duke tun na cikin motan bai bude ba ya farayi mashi sannu da zuwa.
Wani kyakyawan matashin saurayine ya fito daga motan ya zuro kafab shi daya bayan ya bude motan ya daukan wani abu a cikin motan.
Wanan dattijon cikin girmamawa a gare shi yake fadin sannu da zuwa Alhaji karami barka da hanya.
Karasa fitowa yayi gaba daya yana dauke da yar wata jakka dake nuna na laptop ne tare da wasu muhinman takardun shi a ciki.
Shekaru shi zaikai kimanin ashirin da bakwai zuwa takwasa yana saye da wandon jeas blue na maza sai riga mai kwala fara da dan ado kadan a tsakiya ga kamshi na tashi ta ko ina duk da iskan dake kadawa alokacin.
Kallon mutumin daya nace da gaishe shi yayi yana fadin malam mudi baka samu wuri ka labewa ruwa nan ba har yanzu kada fa ka jike kajawa kanka ciwo kasan ruwan sama yana tafiya da dan sauri yake magana da wanan mutumin .
Dan jakkar da ya riko din mutumin ke kokarin amsa daga hannun shi ya dakatar dashi da fadin No ka bar shi kawai ya shige cikin gidan.
Kamar ana jiran shigan shine aka sako da wani irin ruwan sama mai karfi lokaci guda abinda yasa garin ya kara yin tsit kenan Allah yana nasa ilon a lokacin.
Yana shiga babban falon gidan ya dauke hanya zuwa part din shi kai tsaye duk da yana jiyo dan hayani a falon alaman akwai mutanen dake zaune falon lokacin.
Babu abinda ke tashi sai kida duk da ruwan saman da akeyi a lokacin ya ja tsuki ya nufi dakin nasa yasa key ya bude ya shige ciki kai tsaye.
Ruwan saman da ake zugawa a lokacin bai hanashi shiga wanka ba don dan tafiyan da yayo daga jos zuwa kano a mota.
Ya fito wanka da alwalan shi duk da yasan akwai sauran lokacin sallah magariba kwanciya yayi saman kujera yana bin dakin da kallon yadda ummin su tasa aka gyara mashi dakin sai kamshi ke tashi don tasan shi din ma,abocin son kamshi ne sosai a rayuwan shi.
Mikewa yayi da niyar zuwa dakin hjyn nasu daidai lokacin wayan shi da yai saiitin lokacin sallah ya dauki kara.
Ba zai iya fita masalci ba a lokacin don haka ya tsaya daki ya tayar da sallah har saida yai isha,i yayi abinda zaiyi ya nufi dakin mahaifiyan nasu don su gaisa don ba wanda yasan ya dawo gidan a lokacin.
Har lokacin kannen nasa suna zaune a falo ba wanda ya mike don zuwa sallah sai dararakun su da sukeyi a wurin.
Kwatsan lokaci daya suka ganshi tsaye a kansu kamar an jefoshi daga sama nan suka dan shiga kame kame cikin rawan murya suna gaida shi da dawowa.
Wani tsawa ya daka masu hadi da zazzare masu idon shi wanda kan firgitasu dashi don sun san inya juye idon ba wasa a wanan lokocin yaya ashe ka, , ,
Yace shut up tsupid girls ana ruwan ma ba zaku natsu ba anyi sallah kuma duk kuna zaune .
Mai dan girman tana da dan kama dashi a cikin sune tace wallahi yaya yanzu nake, , , ,
Shiru tayi don yadda ya watsa mata kallo a wurin yana nuna masu hanyan dakunan su da hannun shi haka yasa kowan su mikewa da sauri suka bar falon yaja tsuki ya shige auri ummi din.
Zaune take saman sallaya yayi sallama ya shigo tana ji ta dago tana fadin yanzu na gama tunanen ka ai.
Na dauka wanan hadarin ya hanaka tasowa da wuri don nasan ka da tafiyan dare .
Zama yayi yana fadin mun dawo tun dazun ai ummi don na tsaya sauke abokin tafiyane ne har iskan nan ya taso ban karaso gida ba ina hanya amma ai nan ruwan ya sameni ina shigowa.
Ka dai daina wanan tafiyan daren na fada ma yanzu hanya baida kyau ko kadan kowa na tsoron hakan.
Wai ummi meyasa baku sakawa yaran nan ido wurin ibadane ace wai yaran nan duk ruwan nan da akayi har magariba yayi suna zaune falo suna shan kida kamar gidan yan coci damu .
Kai uwar ta kada tare da fadin kai Allah ya sawaka da halin yaran nan na dauka sun tafi daki yin sallah tun dazun ai.
A dai saka masu ido don su yanzu babu a binda ke ransu sai duniyanci da shakiyanci Allah dai ya shirya muna su uwar ta fada.
A dai kula mami ya fada za a akulan ta sake fada a cikin rashin damuwa da abinda yake fadi din akan yan uwan shi din.
Yaushe ne zaka koma lagos ta tambaye shi ya nisa tare da fadin sai idan daddy ya dawo daga tafiya ya bata amsa.
Amma idan bai dawo karshen satin nan ba zan tafi hakana ba tare da mun hadu din ba amma naso ka bari ya dawo ku hadu don wanan damuwan da yake ciki ko zaka gano abinda ke damun shi a yan watannin nan.
Na rasa me yasa Alh ya koma hakan kamar bashi ba ga daya ya canza ya daina walwala da mu,amula da kowa a cikin mu har yaran nan duk ya daina sakewa dasu a yanzu.
Kaita dago tana duban dan nata da yai zurfi a cikin tunane yana nazarin abinda mahaifiyan nashi ke fadi game da mahaifin su a lokacin.
Kafin wayan shi dake aljihun shi yayi kara alaman kira ya shigo mai a lokacin ya dan dago da sauri yana daukan wayan tare da karawa a kunnen shi yana sauraren abinda ake fada mai.
Bayan ya gama saurare ne yake fadin tomorrow morning in sha Allahu i will be in lagos sai mu duba shi.
Bayan ya gama wayan ne ya nisa yana mayar da wayan cikin aljihun gaban rigan dake jikin shi ummi din ta dago tana fadin gobe ke nan zaka koma lagos din ashe ?
Fuska ya bata kafin yace dole hjy kin san aikina ba nazama bane ya zama dole gobe inbi jirgin safe zuwa lagos din abinci fa mahaifiyar ta tambaye shi ?
Fuska ya bata kafin yace sanyin nan ba zai bari na danci wani abu zan sha tea kafin in kwanta kadai kula da cin abinci ta fada.
Yace insha Allah zava tsare ummi sun dan taba hira kafin ya fito yayi mata sallama don goben ba lalai bane ya samu ganin ta da safen kafin ya fita don asubancin da zaiyi a goben.
Ya fito zuwa part din shi don hankalin shi naga wayan da akai mai gaba daya hankalin shi ya koma can.
Bai zauna ba ya fara shiri ko tea din da yace zai sha din bai samu sha ba biyar da rabi na asuba ummi taji fitan shi gidan an bude mai get ya fita.
Addua tayiwa dan nata na Allah ya tsare ya kare mata shi da sauran yan uwa a lokacin don ganin kakanta shi ga aikin da yakeyi a yanzu din.
Wanda a gaskiya sai take ganin shekarun shi baikai ya fada wanan aikin ba haka don aikin nasu akwai kasada sosai a cikin sa.
Karfe goman safe jirgin su ya sauka a filin jirgin inda abokan aikin shi ke jiran shi don daga nan zasu wuce inda suke son zuwa din don basu da wadattacen lokaci don kamar ma sun dan makara a lokacin.
Kafin su gama da can su dawo karfe biyu saura ga ruwan sama daya sauko a lokacin ba tare da wani alamun hadari zai zubo ruwa ba kamar yadda nan arewa yakan tsaya nuna muna alaman zuwan shi.
Ga wani irin go slow da ya cika hanyan sai hasken fitalan motoci kake gani da mutanen dake zirga zirga a kasa da sauran abin hawa don su haka bai damesu ba sun saba da hakan a rayuwan su .
Tana tafe da sauri har tana tuntube don dan yayafin da aka fara tasan ruwane ke shirin saukowa a lokacin.
Amma haka bai hanata sauri ta nufi titi mafi kusa inda tasan zata samu mutane a wurin .
Saidai kafin ma takai titin ruwa mai karfi ya gwauce haka ta dinga tafiya ta hango jerin motoci da ke saman titin sun jera dogon layi don go slow din ya hadu a lokacin .
Haka ta fara bin motocin tana bara tana neman taimako gana Allah da wanda yaji kyanta ya bata don Allah a cikin wanan ruwan.
Glass din motan shi ta gefen shi yaji ana kwankwasawa ya dan dago daga abinda yakeyi da sauri yana kallon wurin.
Mace ya hango a tsaye duk wanan uban ruwan tana cikin shi hankali kwance wanda suke tare ne yace dashi a cikin harshen turanci wa yan nan mutanen ne yan bara .
Bara a cikin wanan ruwan haka yace kana mamaki ne su ai damane ya samu masu ga wanan lokacin yadda aka hafa go slow din nan haka.
Dayan gefen ta koma tana kwankwasawa a hasale ta miko hannu ta inda aka dan bude din tana fadin Wahidu oga .
Give me something oga even small Allah will reward you with , , , , kai innalillahi wanan mutanen suna da kaskantar da kai wallahi ya fada a hasale.
Ta kara mika hannu tana fadin Wahidun Oga give something to eat a hasalw zai rufe glassa din na tare dashi yace a, a yana bude wani wuri yace bari mu bata don in ba bata mukayi ba haka zasu damemu da wanan baran .
A lokacin ya dago kai yana kallon ta tana sharce ruwan daya kwanta mata a fuska da alama karfin ruwan yana damun ta itama a lokacin dubu biyu yayi niyar zarowa sai ya zaro kusan hudu haka takai hannu ta wafta duka a hannun mutumin tana jiyawa da sauri bayan godiyan da tayi mai .
Binta da kallon mamaki yayi kafin yace innalillahi wanan yarinyace karama da wanan halin banza iri sune ma yan iskan gari.
Dan murmushi na gefen shi ya sake yana girgiza kai tare da fadin indai wanan erea din ne zaka sha mamakin su ko wani yare zaka samu a nan tundai hausawan ku yan arewa sun fi yawa ga wanan harkan na bara yaja tsuki yana kawar da kai.
Tare da jin haushin hakan a zuciyar shi ga yarinya har yarinya amma ta tsaya tana wanan kazantar sana,an dayafi tsana ko a arewan su.
Balle lagas da yake ganin hanyoyin sana,a sun fi a kirga ga neman kudi idan mutum ya tashi nema din.
Har suka kai gida a na sheka ruwan sama a lokacin suka fito daga motan a cikin ruwa hakan yasa suka dan jika kayan jikin su din.
Kallon kudin dake hannun ta taji wani irin farin ciki ya kamata da sauri ta juya don barin wurin har tana dan hadawa da gudu gudu don tunawa da tayi tun safe basuci abinci daga ita har kanin ta Amar da duk suka dogara da ita a yanzu.
Tun daren jiya batayi barci da dadi ba idan ta tuna babu abinda zasu ko karya dashi a gidan haka yasa bata kaunan komai nasu ya kare.
Tasan wanan din zasu samu su danyi amfani dashi har zuwa dare in yaso sai ta fito ta nema masu abinda zasu ci.
Da sauri ta karasa wani shago mafi kusa ta sai duk abubuwan da zasu buka mai saukin ci sai a lokacin ne ta kula ashe kudin yafi yadda take zaton ta samu.
Wani irin shu,umin murmushi ta sake lokaci guda nan ta kara sayen komai wadatace da zai ishe su har karshen jibi da safe .
Har ta isa gida ba,a kare ruwan saman da akeyi ba haka tsamo tsamo ta samu ta isa kazamin unguwan nasu da babu abinda ke tashi banda warin kwata da bola a lokacin.
Cikin rashin damuwa da hakan saboda sabo da tayi da hakan a yanzu yasa bata ji kazantar komai ba a lokacin
Kowa na gidan yana dakin shi ya labe ganin yadda yawancin kayan gidan suke iwo a cikin ruwa ganin haka yasa ta tuna da dakin su dake zuban ruwa sosai ga mahaifiyar su ba lafiya duk kwanakin nan wanda tasan ba komai bane ya kawo hakan sai aikin wahalan da takeyi kullun don saman masu dan abinda zasu kaiwa cikin su.
Da sauri ta tura kyauren dakin, dakin ya bude can ta hangosu a takure wuri daya ga yan tsumakaran su duk sun jike da ruwan da ke diga daga saman kamar indararo a dakin.
Da sauri ta karasa inda mahaifiyan nasu take labe tare da dan kanin su karamita dauko wani babban bargo suka kare kansu su ukun gaba daya a ciki.
Duk da halin da sule ciki haka bai hanata dauko masu abinda ta sawo suci ba a takure a wurin suka ta mike ta dauko ledan pure watar daya daya rage masu a dakin ta kawowa mahaifiyar nasu da kanin ta su sha, .
Kai mahaifiyan ta kada tana fadi da kyar kusha keda dan uwan ki ni zan dan samu ruwan saman nan da akayi insha.
Wallahi Umma ba zan sha ba don ban ma jin kishin ruwa a yanzu din ta fada don hankalin uwar nasu ya kwanta tasha ruwan ta sauke wani irin ajiyan zuciya ta juya ta kalli uwar nasu tana mata sannu umma .
Muryan mahaifiyar ne ke fadin kece da sannu da ubangiji ya hore mune ke kike samo muna abinda zamu sakawa cikin mu a cikin karfin ki.
Sahiba ban da kwankwanto a kanki don nasan irin tarbiyan dana taso maki dashi tun farko naki dogara da karfin ki ki tallafi kanki ba sai kin zubarda mutuncin ki da kimarki ba ga maza a karshe ki koma abin kyama a garesu .
Sahiba yadda kike muna Allah ya biyaki da mafificin alherin sa a rayuwan ki Allah ya baki masu rama maki irin abinda kikai muna.
Kin kula dani da kanin ki tun kina mitsitsiyar ki har zuwa yanzun duk wani wahalan mu da dawainiyar mu duk a kanki yake yanzu Sahiba.
Allah kadai zai iya biyan ki don Allah yasan komai daya jefa rayuwan mu a cikin wanan halin da gatan ku a duniya kun koma mabukata karfi da yaji kan wani dalili nasu can na rashin imani.
Da sauri yar ta dago kai ta kalli mahaifiyar nata don wanan ba farau din ta bane wurin fadin da gatan su amma wasu sunyi dalilin komawan su hakan.
Duk da nasan Allah ba zai kyalesu ba suma a kan wanan abin da suka aikata muna a rayuwan mu na shiga kunci da wahala irin haka a yanzu .
Ina alfahari da samun ku a matsayin yaya a gareni Sahiba don da wuya a wanan zamanin a samu ya data fiki tausayin iyayyenta da yiwa mahaifiya biyayya irin haka.
Sahiba a kullun ina maki adduan Allah ya baki kyakyawan sakamo arayuwan ki don a yau in munci munsha duk a dalilin kine Sahibat a duniyan nan.
Hawaye suka silalo a hankali daga idon Sahiban dake sauraren uwarta kan ta na duke a kasa .
A hankali ta lumshe idon ta tana tunanen yadda