Showing 282001 words to 285000 words out of 557259 words
tashi ki dubamin cikin gidanku,daga parlor din matar gidan har bedroom dinta,akwai qannenta da sukazo,ki fara karbamin wayar hannun babbar,minti goma kuma nace ki qara musu su taso ki biyosu har sai kin kawominsu gidannan".
"Angama ranki ya dade" Ta fada tana miqewa da hanzari har dankwalinta yana faduwa,duk da ranta a bace yake ainun da irin tsawar data daka matan.
Parlor ta duba na farko dana biyu duka ba kowa. A kitchen ta samu ma'u tana juye mata kunun a flask gudun kada yayi sanyi jin shuru bata dawo ba.
Ido suka hada mau ta dauke dubanta a wajen. Haka kawai jininsu baizo daya da zuwairan ba,duk da ma'u bata nuna mata komai,saidai ita zuwairan cike take da haushin ma'un ganin yadda sabreen din ke mu'amalantarta sama da yadda take sakar mata.
Ko ina na gidan ta duba,tana shirin fita farfajiyar gidan ta duba can sai ga laila ta shigo afujajan
"Ina matar gidan?" Lailan ta tambayi xuwaira.
"Ban sani ba nima" Ta bata amsa cikin jin haushi zuciyarta tana raya mata itama aikin dubata ta bata.
Dole data gama dube dubenta ta dawo parlor din,daidai sanda ma'u ta kammala komai tazo ta rabesu tana ficewa abinta ba tare da tace da kowa komai ba.
Dukkansu qoqarin kiran maamah suke don kowa ya fara shaida mata yadda ake ciki. Laila ce ta fara samunta,cikin tsananin biyayyar data sanya zuwaira sakin baki tare da tunanin ko wani sabon makircin shiga jikinta suka qullo ta tsaya tana dubanta
"Maamah kaman bata gidan nan fa?". Wata zazzafar zufa ce ta karyo mata,taji kamar gudawa zata tsinke mata. To amma yaushe suka shigo da har za'ace basa cikin gidan?.
"Kun duba ko ina da ina?" Kai laila ta girgiza tana duban hallway din
"Banda bedrooms dinta"
"Me kuke jira?,ku dubamin har can" Ta bata umarni a tsawace har sai da wayar hannun lailan ta kusa faduwa.
"Zan shiga na duba" Lailan ta fada tana duban zuwaira. Wani kallo ta watsa mata tana samun daya daga cikin kujerun ta zauna tana tabe baki.
Da karsashinta ta soma nufar dakunan,har cikin ranta tana jin dokin shiga taga dakunan ya suke?,tunda koda hallway din bata taba takawa ba bare akai ga shiga ciki.
"Alhamdulillah" Ta samu kanta da furtawa lokacin dame napep ya ajiyesu a qofar gidan. Sai a sannan hankalinta ya dawo jikinta,ta tuna bata riqo komai a hannunta ba.
"Don Allah dan yi haquri,bari a karbo maka kudinka,fitar ce ba'a tsanake ba" Ta fada tana dubansa. Bai wani damu ba sam,saboda yanayinta kadai ya tabbatar masa idan bai samu qarin abinda ya kamata a bashi ba to tabbas ba za'a rageshi da komai ba. Waiwayawa tayi ta kalli su huda
"Ku shiga ciki ku karbomin dubu biyar wajen titi". Huda ce tayi gaba suka bita a baya. Basu jima ba nadra ta fito da kudin ta miqawa sabreen din,ta karba ta bashi sannan suka wuce cikin gidan a tare.
Tana sallama aishatu ta fara gani,tana duqe tana wankin uniform dinta daga can bakin famfon da akayi musu saboda hidima irin wannan. Tadan zubawa yarinyar idanu farinciki yana ratsata. Ko a iya aishatu kawai idan ta kalla tana jin wani farinciki da sassauci yana ratsata,kamar ba aishatun da aka debe tsammani da rayuwa da ita ba,kamar ba aishatun da idan ka fita ba zakayi tsammanin zaka dawo ka sameta a raye ba. Sai data dago don yin shanya suka hada idanu,ta watsar da uniform din,ta rugo da gudu tana kiran sunanta
"Adda sabreeennn" Ta maqaleta da kyau,sai itama ta tsugunna tana rungumeta cikin jikinta qwallar farinciki na sauka a idanunta.
"Aishatu......haka kika koma?......alhamdulillah" Ta fada tana shafa sumarta me santsi.
"Adda na warke.......na samu sauqi adda" Ta fada itama tana kwantar da kanta a kafadarta.
"Ki barta ta qaraso ciki mana aishatu" Muryar titi ta ratso kunnuwansu tana dubansu cikin murmushi,daga nesa kuma tana kallon yadda sabreen din tayi wani irin kyau,fatarta ta qara tsananin haske da wani irin murjewa,sai glowing takeyi duk da tadan fada kadan qibarta ta ragu.
Tana riqe da hannun aishatun suka shiga parlor din titi. Duka sauran yaran falon suka miqe don basu fahimci ita ake magana ba.
Dukkaninsu suka baibayeta suna qoqarin kiran sunanta,sai ta zame kawai ta zauna tana rungumesu cikin jikinta gaba daya tana kiran sunansu daya bayan daya.
Ruwa da lemon zobo da titi din ke saidawa ta dire musu tana zama gefanta. Sai a sannan yaran duka suka tashi suna ficewa don basu sarari.
"Banyi zaton sake ganinki nan kusa ba" Titi ta fada bayan sun gama gaisawa da gaske farinciki yana nunawa saman fuskarta,duba da sanin babban mutumin data aura. Murmushi sabreen din tayi wanda yakai mata har zuci,musamman data tuna daga rana irin ta yau ta nesanta maamah din da rayuwar qannenta kenan,nesantawa ta har abada
"Me zai hana titi?,ban fara fita bane kawai" Ta amsata tana gyara zamanta
"To ma sha Allah,ubangiji ya sanya alkhairi,ya bada zaman lafiya ya kade fitina". Bata amsa duka wadannan addu'o'i na titi din ba,sai tace da ita
"Alfarma nazo nema titi don girman Allah" Kallonta titi takeyi wani yanayi yana bin fuskarta
"Haba sabreen.....haba don Allah,aike din kifi qarfin alfarma......saidai bada umarni kawai" Murmushi ta saki tana girgiza kai,har yanzu suna mata wani madaukakin kallo.
"Su huda na kawo miki,inaso kuma ki riqemin su zuwa wani lokaci,don Allah titi ko nan da qofar gida bana so su leqa idan zai yiwu bare sukai ga fita waje.......akwai gagarumar matsala da take tunkararmu gaba daya,akwai masu bibiyar rayuwarsu,ki kulamin dasu don Allah". Sosai maganar ta shigi titi,saita girgiza kai tana fadin
"Aiko su din ba jininki bane sabreena sai inda qarfina ya qare......ba abinda bakiyi mana ba,banda ke da Allah ya jefo mana da yanzu bansan a wanne bigire rayuwarmu take kai ba......zan kula miki dasu fiye da yadda kike muradi"
"Na gode titi......kina da tsohuwar waya da bakya amfani da ita?"
"Banga abun godiya a nan ba,hasalima kamar wajibi na na aikata.....akwai wayata da kika canzamin sanda zamuyi tafiyar nan......bari na dauko miki ita"
"Idan zan samu da wata wayar daban zanyi kira" Ta fadi tana qoqarin hada numbers din momma a kanta.
Banda tana da kaifin basira da saurin riqe abu ba yadda zata iya hada number wayar momma din,saidai cikin ikon Allah ta hadasu tsaf ta kuma kira zuciyarta na bugawa da fatan ta kira daidai.
Bugu uku aka daga,muryar momma ta mamaye speaker din tana amsawa da sautin da yake kama sak dana ummensu,sautin da har tata mutuwar ta risketa ba zata manta dashi ba.
"Mom......momma" Sabreen din ta kirata bakinta yana rawa idanunta suna cika fal da hawaye.
"Sabreena?.......kun dawo?,yaushe kika dawo?"
"Daga ina?" Ta tambayi momma din a mamakance qwallar idonta suna tsagaitawa.
"Tafiyar da kukayi mana ke da me gidan.......ko sanda zan koma ai naso haduwa dake dole sai hannun surukarki nabar qannenki.......saboda dole sai passport dinsu ya zama ready.....duk dama dai munyi magana tana ta iya bakin qoqarin ta,kuma kusan kullum sai munyi waya da yaran". Mamaki ya sandarar da sabreen,sai ta bude bakinta a hankali
"Momma me ya faru?,ban fahimta ba,ita ta nema ki bata su?"46
"Eh kusan hakanne,don naso ganinki ban samu ganin naki ba......tafiyar tawa bata shiri bace......abbansu ne rashin lafiya ta taso masa,dole kuma ana buqatata a kusa,a yadda na tsara zan jira passport din nasu da komai ya kammala,amna dole na tafi saboda jinyarsa,saidai ba inda zan barsu don ban aminta da hannun kowa ba. Randa nake wannan tunanin saiga surukarki Allah ya jeho ta. Ita ta roqeni na bata yaran zata sanya mai gidanki yayi magana don a kammala basu komai da wuri,tace kuma zata turosu ko ta kawominsu da kanta,to amma lokacin da nayi tsammani ma sai gashi har ya gota. Kawai abinda yake kwantarmin da hankali duk sanda mukayi waya da yaran alamu suna nunamin basu da matsala ko damuwar komai". Kai kawai sabreen ke jinjinawa tana sake girmama kaidin maamah din. Ta tabbatar ita zata kawo tsaiko a samun fasfunansu,wataqila ma kuwa an samu ta riqe ne taqi gayawa momma din. Tanason ta yiwa momma bayanin da zata fahimceta,amma kuma bataso ta daga mata hankali. Tana ji a jikinta zata iya komai,kuma wannan lokacin kamar wata dama ce da Allah ya ara mata akan maamah din
"Momma"
"Na'am sabreen"
"Komai da kike kallonsa a haka yanzu a zahiri ba'a haka yake ba........abinda zance rayuwarsu tana cikin hadari babba........basa hannunta yanzun suna wani hannun na daban,saidai bana son ki gayawa kowa,don Allah mommma......koda ta kiraki kiyi kaman bakisan abinda yake faruwa ba.......in sha Allah nan da kwanaki kadan zan turosu su biyoki". Shuru momma din tayi tanaji a jikinta ba lafiya
"Amma sabreen me yake faruwa?".
"Ba wani mummunan abu bane momma,kada ki tashi hankalinki.....kawai dai komai kiyishi kamar bakisan anayi ba" Kai ta jinjina bawai don hankalinta ya kwanta ba sukayi sallama.
Tana ajiye wayar ta sabule zobunan hannunta guda biyu na gold,ta kama hannun titi ta zubasu tana kallon idanunta.
"Yanzu bani da contact na kowa.....inaso ki saida wannan,ki nema mutumin da ya muku visa na fita india ya yiwa su huda duka su ukun komai,inaso kada su wuce sati biyu a nan don Allah titi". Zobunan ta kalla sannan ta maida dubanta ga sabreen
"In sha Allah.....zanyi duk yadda zanyi na miki abinda kikeso". Kai ta jinjina tana jin wata nutsuwa tana saukar mata. Murya ta daga ta kira huda,ta shigo ita daya,abinda ya sanya titi miqewa don basu guri.
"Ina wayar hannunki?" Ba musu ta dauki wayar daga kan cinyarta ta miqawa sabreen din. Saita karbeta tana juyata a hannunta. Waya ce me asalin tsada da kyau wanda kusan sai wane da wane. Idanunta ta maida fuskarta tana kallonta
"Huda baki dago komai ba?,bakiji komai ba game da matar da aka kira da sunan uwar mijina?" Tayi mata tambayar kai tsaye tanason samun wani abu daya danganci maamah. Shuru hudan tayi,tana qoqarin recalling komai,tun daga ranar farkonsu cikin gidan kawo yau.
Siririyar ajiyar zuciya ta sauke,a hankali ta maida dubanta ga sabreen
"Inajin kawai batamin ba.....duk kirkin da take gwadana mana sai nakeji jini na da nata kaman bai hadu ba.......sannan yadda take mana kirki kaman ba haka dabi'arta take ga masu aiki qarqashinta ba" Hudan ta fadi abinda da gaske haka takeji a zuciyarta take kuma hasashe.
Wani siririn murmushi sabreen ta saki tana saukar da kanta qasa gami da juya wayar hannunta. Anzo daidai gabar da tafiso.....anzo daidai wajen da zata gwadawa maamah shege......anzo daidai gurin da zatayi wasa da hankali da kuma tunaninta kamar yadda mage kanyi da qadangare ko bera a duk sa'ilin da yayi gigi ko kakambar shiga hannunta.
Daukewa murmushin fuskarta yayi lokaci guda,ta maida kallonta kan hudan
"Ina fata ba wani abu na cutarwa data taba muku......idan kuma akwaishi ko da da mugun kallo ne ina saurarenki". Kai ta girgiza tana kallon addar tata,tanason kuma fahimtar dalilin da yasa taketa mata tambayoyi haka
"Babu kwata kwata adda......saidai kawai nidai hankalina ya kasa nutsuwa da ita... Musamman da ya zamana kusan ko yaushe tana mana alqwarin zata kawomu wajenki sai kuma ta gaza cikawa.....har sai da mijinki yazo.....shi yace ta barmu muje". Jinjina kai take tana duban huda dake bayani,fuad ne kenan.......me yasa yace suzo din?,shima akwai yiwuwar yana da nashi boyayyen manufar?.
"Kinsan garkuwa tayi daku?,kidnapping a fakaice?" Tambayar ta zowa huda a bazata,ta zaro idanunta waje tana dafe hannunta saman qirjinta.
"Kidnapping fa adda?" Kai ya gyada mata gami da lumshe idanunta,sai kuma tace
"You are free in sha Allah.....zaku bi momma mali soon......abu daya nakeson na gaya miki ko bayan kun tafi......be smart as much as you can.......ki dinga amfani da kwanyarki da basirarki.....ki kula da nadra da Haneefa,ki zame musu garkuwa kamar yadda na zame muku.....sannan......ki zama mara saurin yarda da mutune,walau maza ko mata,a family yake ko a wajen family......saurin yarda tushen kowacce rushewa ce" Ta qarasa maganar tana nunata da yatsa.
Iska ta zuqa sosai sanda take cikin napep din sannan ta furzar da ita waje,tana jinta kamar mutumin daya dauki dutsen dala da gauron dutse yau Allah ya 'yan tashi ya samu saukeshi daga saman kansa. Sakayau take jinta,wani farinciki yana ratsata gami da iskar abun hawa wadda ta manta rabon data ratsata. Ta ware idanu sosai tana kallon titi.....Don yaushe rabonta data fito?,ko fitarta ta qarshe cikin rufaffar mota ne qarqashin kulawar jami'an tsaro.
"Sabreena Ahmad AKA MUHSEENA" Sunan da taji an ambata kenan saitin kunnenta. Ko daga bacci ta tashi tasan waye?......wannan wata shaidace kuma stamp ne daya kasance nasa shi kadai. Mashkur....ta gayawa kanta da kanta,don haka ta tattara dukka nutsuwarta da qarfin halinta ta maida sashen da sautin ya fito.
Shi dinne,zaune a seat din driver,ya dafe dukka hannuwansa saman steering din motar yana jifanta da wani zazzafan kallo. Duk da yadda haushinta da wutar son daukar fansa ke ruruwa a ruhinsa.......amma hakan bai hana shaidan harbawa zuciyarsa wutar matsananciyar sha'awarta ba. A yadda yake hangen wani lafiyayyen kyau a tattare da skin dinta......wani irin kyau da abaya fatarta bata sameshi ba,sai yakejin burinsa ya ninku zuwa gida biyu,YA DAUKI FANSA sannan kuma YA KASHE QISHIRWAR SHA'AWARTA A RANSA. Dadaddiyar qishirwar data maidashi sakarai kuma shashasha a kanta duk da tarin tsananin wayonsa.
"Damn it!" Ya furta da qarfi yana dukan steering din motar tasa gami da cije lips dinsa gami da kashe mata idanu guda daya. Salin alin ta dauke dubanta daga kansa,tana jin wani matsanancin faduwar gaba yana saukar mata. Faduwar gaban da bata taba ji ba a kansa ko akan wani d'a namiji ba idan ka dauke fu'ad din
"To ko wannan shine haqqin aure da kowacce mace kejin nauyinsa a kanta?" Ta tambayi kanta da kanta tana jinjina girman abun. Kafin ya sake cewa komai traffic light ya sakesu,motarsu ta riga tasa yin gaba. Cikin mamaki sai ta samu kanta da addu'ar kada ubangiji ya bashi ikon ganinsu har ya biyosu yaga gidan da take,duk da ta sani......gidan su zai wahala ya zama wani boyayyen gida da zai wahalar da za'a iya ganoshi.
*MUHAMMAD FU'AD*
Basuyi nisa can can ba ya tuna yabar file dinsa a gida,wanda file ne dake da muhimmanci ya dubashi a yau ya tura da bayanan cikinsa ga company din da suka nema sanya hannun jarinsu a kamfanin. Ba kasafai ya fiya son yin alqawari ba tare daya cikashi ba,idan har hakan ta kasance ta tabbas baida yadda zaiyi ne,don haka ya sanya su saddiq sukayi gaba,shi kuma suka juya da wasu motocin suna dawowa gidan.
Wuri wuri zuwaira tayi ta shiga raba idanu sanda taji dirin shigowar motocin nasa harabar gidan. Raba idanu ta shiga yi sannan ta furta kalmar
"Na shiga uku!" Bayan ta tuna gargadin da yayi mata a ranar daya fara ganinta. Yadda tasan halinsa ta kuma haddaceshi bata haddace fuskarsa haka ba,ta tabbatar yazo ya sameta a sassan kamar yadda ya gargadeta shan ruwanta a gidan ya qare. Wani abu guda daya da bata qaunar ya faru......zaman gidan yafi mata zaman ko ina......zaman gidan cike kuma yake da 'yanci,ba kyara ba tsangwama,hakanan ba nauyayen aikace aikace a cikinsa,sabanin gidan maamah din da yake cike da tsarabe tsarabe kala kala.
Wuf tayi ta miqe tana dosar qofar da zata sadata da sassansu kamar zata ci da baka,cikin ranta cike fal da Allah ya qarawa laila tare da fatan ubangiji ya hadata dashi yaci zarafinta har fiye da tunaninta taga yadda abun zai kaya.
Da nutsuwar nan tasa ya shigo cikin falon,idanunsa suna kan inda ta tsaya a dazun sannan ta waiwaya tana komawa ciki. Ya janye lumsassun idanunsa yana wucewa parlor na biyu,daga nan ya doshi qofar da zata sadashi da hallway da kuma stairs dinsa.
Saurin ja yayi da baya kaman yadda itama taja da baya da sauri. Ya zuba mata idanu yayin da ita kuma kwarjininsa yaso bugar da ita. Bata shirya ba amma sai gata tana rusunawa gami da gaidashi
"Barka da safiya hamma.....ya aiki?"
"Kece laila?" Ya tambayeta yana dinke girarsa tsaf saboda yadda yaga abun ya masa wani iri. Ta yaya zata ratsa privacy dinsu ta shigo har nan wajen?,wani irin rashin hankali ne da ita matar gidan zata bari haka ya faru?. Shi din wani irin mutum ne me tsananin son privacy,kamar yadda yake da iyakoki akan komai daya shafi rayuwarsa.....kuma kowanne mutum da nashi iyakar.
Murmushi ta saki tana wani karyar da wuya gami da rolling idanunta a kansa
"Eh hamma.....nice.....baka gane ni ba?,nazo ne duba.....ammm.....ammm sabreen,maamah nason magana da ita da gaggawa,so kuma unfortunately sai na duba ko ina na gidan amma babu ita.....infact ma ta fita.....".
Banbarakwai yaji maganar kamar da wani yare daban take magana. Ta fita?,zuwa ina kenan?,sannan da izinin waye ta fita?. Ajiye duka maganganun yayi gefe guda yana dubanta
"What I have told you tun ranar farko?.....so ki