Showing 378001 words to 381000 words out of 557259 words

Chapter 127 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

519

yana sallama don sanar da anni da amna dake dining suna magana shigowarsu.

"Wa'alaikumussalam......marhaba da matafiya" Anni ta fada da murmushi saman fuskarta tana saukowa daga dining area din tana nufosu.

Tun bata qaraso ba maamah ta fara qare mata kallo,tayi kyau cikin super embellished me asalin tsadar. Kwanciyar hankali nutsuwarta da riqonta da ibada sun sanya wani irin kwarjini akan fuskarta gami da fidda ainihin quruciyarta,kai bakace itace uwa ga saddiq da farouq ba.

Tako ta ina sai take ganin annin ta fita samun duniya ne,wannan shine sirrin wannan kyan da take gani tattare da ita. Dom ta sutura tana sanya sama da suturar dake jikin annin a yanzu.

"Barkanku da zuwa.....saddiq ku dauki luggage dinta zuwa daki......me babban suna ya akayi baka bada exact time din da zaku sauka ba?" Anni ta fada tana dauke kai daga irin duban da maamah ke mata

"Na sha'afa ne anni.....amma gamu mun iso alhamdulillah" Yayi maganar yana shafa sumar kansa,gaba daya hankalinsa yana wajen amna yana tunanin ganin sabreen tare da ita.

"Alhamdulillah.....haka akeso ai.....bismillah Mariya mana kunata tsaye?" Anni ta fada tana jifan maamah da murmushi. Idanu maamah ta janye a kanta,tana jin wani abu yana tokare mata wuya. Yau ita akewa tayin zama a gidan d'anta?.

"Da baki gaggawa ba ameenatu,zama kam nina cancanceshi" Ta fada tana son maida maganar cikin yanayi na wasa wasa. Sosai maganar ta samu muhalli a zuciyar anni,ita kuma ta sani bawai da wasa mariya ke maganar ba,saidai koma meye ta shiryama zama da mariya din albarkacin muhammad fu'ad din.

"Zo mana amna" Anni ta fada tana kiran amna dake zaune kawai. Haka kawai takejin batason rabar matar......bata son yanayin kallon da take binta dashi. Qarasowa tayi inda annin take,ta sani sarai anni na iyayi mata fada don haka ta rusuna tana gida maamah data fidda mayafinta ta aje gefe da bawa kowa na wajen tabbacin tazo gurin data isa ne. Kaman yadda ta saba amsa musu gaisuwa haka ta amsawa amna.

"A gabatar mata da ruwa....sun sha hanya ita da hammanki".

"Karki kawomin zallar ruwa,lemo nake buqata da wani abun tabawar bawai dangin ruwa kadai ba" Daga amnan har anni ba wanda ya nuna yaji abinda tace,illa anni ta dubi amna

"Ki duba fridge kiyi warming pizza da samosa ki hado dashi". Kai amna ta gyada a sanyaye tana nufar kitchen din. Har yanzu ta kasa aminta da gamsuwa matar wai itace mahaifiya ga hammansu.

Gefe anni ta samu ta zauna tana gayawa kanta da kanta. Maamah ta cancanci kawaicinta kawai saboda fu'ad din. Sam sabreen bataji shigowar amna ba sai data gama hada kayan zata fita sannan ta riqota tana cire earpiece din kunnenta.

"Ki cewa anni an kammala,sai meye za'a dora mata?". Kai kawai ta gyada mata ta fice,tanason ce mata hamman ya dawo amma kuma yanayin sanyin jikin data tsinci kanta a ciki ya hana mata.

Sake daga kansa yayi cikin matuqar zaquwa yana sanya ran ganin fitowarta a kitchen din tare da amna. Saidai a yanzun ma amnan kawai ya gani ta fito. Iska ya zuqa sosai yana fesarwa

"Me take buqata dashi ne?,hauka take so ya fara gwada mata tuburan?" Ya tambayi kansa yana jin zuciyarsa tana quntata waje daya.

Sheqeqe maamah tabi tray din da amna ta shiryo,ta tabe baki wanda muraran duk wanda ya kalleta zai gani. Baya amna taja tana gayawa anni saqon sabreen,abinda yasa ruwan da maamah ta kurba yayi mata cak a maqogaro.

Juya zancen takeyi tsakanin rai da zuciyarta. Me haka yake nufi?,kyakkyawar alaqa tsakanin sabreen din kena da ameenatu?,yarinyar ke niyyar zame mata qadangaren bakin tulu ko.kuma ameenatun?,waye ainihin matsalarta a cikin su biyun?.

Ta bangaren fu'ad din sai ya dinga ji ransa yana sake baci....dole ya sake tabbatar mata ita mallakinsa ce,dole ya sake tuna mata muhammad fu'ad mijinta ne.....mijin da bazai juri qaurace masa ba.....mijin da bazai juri bada umarni tasa qafa ta take ba saboda raini.

"Kice ruwan zafi kawai zata dafa......ta fito ga baqi sunzo tazo su gaisa". Anni ta fada tana duban amna. Baisan ya miqe tsaye ba,shidai yaji yana gayaw anni

"Bari na samo warm water.....nasha sanyi a haram da yawa" Yayi maganar yana jin wani magnet yana jansa zuwa kitchen din,ba tare da ya tuna waye da waye a wajen ba.

Ajiye cup din hannunta maamah tayi tana binsa da kallo sanda yake takawa hankali kwance zuwa kitchen din. Tuni amna ta wuce dakinsu don ba zatayi gangancin komawa kitchen din ba tunda can hammansu ya nufa.

Wani mamaki yake kashe maamah tana daga zaunen. Ita din ba yarinya bace haihuwar jiya ko yau,ta sani sarai ita yabi....sabreena yabi bako shakka. Daga yanayin fu'ad din kawai tasan akwai abinda ke jansa zuwa can din,wani dakiya da shariya ta gani tattare dashi wanda bata taba ganin irinsa ba. Yadda yake tafiya zuwa kitchen din hankalinsa kwance kaman ba wani idon kunya a wajen?.

Sanda tayi nisa da binsa da kallo a lokacin anni itama tayi nisa da qare mata kallo da kuma fahimtar rudewarta da kuma canzawar yanayinta lokaci guda.

"Ya rabb......kasa addu'ar dana bata tsahon dare ina yinta ce ka amsa.....ubangiji ka sanya wannan mummunan qullin ka juyar dashi zuwa kyakkyawa". Anni ta sake jaddada addu'arta can qasan zuciyarta wani murmushin nishadi yana subuce mata.

"Tabbas kina dab da ganin yadda ubangiji ke jujjuya al'amura......kina kuma dab da samun ciwon hauka muddin akan Sabreen da fu'ad ne" Anni ta sake fada qasan ranta.

Ba jiya yau ko shekaran jiya ba take karantar duk wani motsi na fu'ad ba.....me babban suna ya canza gaba daya.....ya shiga wata gawurtacciyar koma ta soyayya wadda tayi imani shi kansa baisan girman abinda ya fada a cikinsa ba......karantar irin wannan yanayin kuma sai uwa ko gawutaccen masoyi.

"Zan shige daki na shirya.....naga magarib tana dab da isowa.....ga masaukinki can,a huta lafiya" Muryar anni ta dawo da ita daga rudanin data shiga. Bata sake cewa maamah din komai ba,saidai ta barta da kallon murmushin dake kwance akan fuskarta. Ita ba zata bari fu'ad ya fito ya sameta ba ballanta yaji kunya ko ya raga daga soyayyar da yayi niyyar nunawa matarsa ba.....ta barwa maamah ta fara kallon sample kafin anihin abun ya bayyana a idanunta gaba daya.

Idanunta ciki ciki tabi anni da kallo har ta isa dakinta.

"Ta ina kuma ameenatun ta sake bullomin?" Ta yiwa kanta tambayar zuciyarta cike da kokwanton murmushin data gani saman fuskarta.

_turqashiπŸ˜‚πŸ˜‚,anya maamah nan din gidan zamanki ne kuwa?_

_maji ma gani dai_



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 92



92


A hankali ya tura qofar kitchen din sannan ya maidata ya rufe a nutse bayan ya karanci earpiece ne a kunnenta,sai ya maida bayansa jikin qofar kitchen din,ya goye hannayensa a qirji yana qare mata kallo.

Ta fidda hijabij jikinta ta saqaleshi a hanger na kitchen din don tafi jin dadin yin aikin,bata da damuwa kan musaddiq ko saddiq,dukkaninsu idan zasu shiga wani guri cikin gidan saisun tsaya daga waje sunyi sallama. Sassalkan gashinta da amna ta kame mata su da hair clips masu kaloli da shapes daban daban jelarsa ta baje sosai a bayanta. Baqi sidik ne yanata shining saboda ko da can ita din bame wasa bace da gyaran jikinta ma gaba daya. Idanunsa ya lumshe yana bin sauran sassan jikinta da kallo,qugunta ya bude sosai ta cikin skirt din dake jikinta,shape dinta ya fita sosai da duk wani sura na kyau da Allah ya bata.

"Ya salam" Ya furta qasan ransa saboda wani irin magnet dake fusgarsa zuwa gareta. Wani sashe na zuciyarsa ya raya masa inda wani tsakanin musaddiq da saddiq ne ya shigo a haka zai ganta?. Raba jikinsa yayi da qofar ya fara takawa a nutse yana dosarta.

Dukan hankalinta yayi nisa wajen killace plates din data wanke. Kwata kwata bata kawowa ranta wai dawowarsa ba ballantana shigowarsa kitchen din ba. Ta gama jerawa tayi taku biyu baya don matsawa daga wajen,santsin man daya diga a qasan tiles din ya kwasheta,tayi baya zata fadi a matuqar tsorace. Hannayensa ya sanya duka biyun ya tarota,take ta samu masauki a faffadan qirijinsa.

Gam ta sanya hannu tana riqeshi ba tare data fahimci a jikin wanda take ba,tunaninta duka ta samu wani abunne ta kama.

Fadowarta jikinsa ya bashi daman qarewa kyakkyawar fuskarta kallo. Karon farko da wannan tsiwatacciyar fuskar ta fito a matsayin matsoraciyar fuska. Sauke idanunsa yayi saman qirjinta dake sama da qasa alamun tsoro muraran da kuma yawan adadin bugun da zuciyarta ta qara. Cikin qasa da second ashirin hankalinta ya fara dawowa jikinta bayan ta tabbatar batasha qasa ba,ta zuqi numfashi sosai wanda hakan ya taimaka mata wajen isar lallausan qamshinsa qofofin hancinta ya kuma isar da saqon waye me turaren cikin kwanyarta.

Idanunta ta ware da sauri,take suka fada saman fuskarsa dake dab da tata,sukayi wani zuzzurfan musayar numfashi daya hautsina masa tunani karon farko. Kyakkyawar fuskar nan tasa dake shimfide da wani irin kyau da ba kowacce fuskar d'a namiji ke da baiwar irinsa ba.....wani irin kyau me cakude da kwarjini musamman cikin narkakkun idanunsa da kallon cikinsu yasha banban da idanun kowacce d'a namiji data taba kalla.

Cikin sauri ta tura qirjinsa baya tana zamewa daga jikinsa,saidai ya gwada mata halittar sam ba daya bane ta hanyar miqa hannunsa ya damqota. Wata kyakkyawar runguma yayi mata ta baya gana matseta cikin jikinsa,ya aza fuskarsa saman kafadarta,sannan ya motsa labbansa da wani irin nannauyan numfashi.

"Am back.....am home.......but......" Ya fada yana dagata gami da juyo da ita gaba daya tana fuskantarsa sosai. Raina kanta tayi sosai ganin yadda ta koma 'yar qarama a gabansa,ya kuma ritsata da wannan kallon nasa yana duban duka qwayoyin idanunta kafin ya jefa mata tambayarsa.

"You break my rules hajjaju.....don't blame me indai na tashi hukuntaki" Yayi maganar cikin nuna mata da gaske yake yana miqa hannunsa zai shafi gefan fuskarta. Baya taja da sauri,abinda ya sanya ya tsaya ya zuba mata ido. Da gaske take batason koda yatsarta ya taba.....ko yaya ya kusanta kanshi da ita saitayi wani abu da zai nuna bataso.

"Ya kamata kabar kitchen din nan kafin wani ya shigo ya ganka" Ta fadi masa tana qoqarin maida hijabinta. Taku uku ya isa gabanta,ya sanya hannu ya fusge hijabin yana kuma jawo kujera dab da ita ya zauna ranshi a hade yana fadin.

"Wace irin mace ce ke?.....bakiyi kewata ba?" Yayi tambayar da gasken gaske tun daga qasan zuciyarsa,yana fatan ko sau daya yaji tace tayi kewarsa.

Wani kallo ta watsa masa sannan ta janye idanunta,ta taka tana kashe gas din sannan ta soma tafiya a nutse zuwa bakin qofa. Iya hakan ya bashi tabbacin ficewa zatayi,ba kuma zaka kulashi ba kenan. A zafafe ya miqe yana wurgi da hijabin nata,ya sake shan gabanta yana mata wani duba nakai tsaye. Ko ba'a gaya mata ba zuwa yanzu tana saurin gane abinda ya taba zuciyarsa. Sauyawar yanayinsa wani abu ne da yake saurin razanata.

Soma hade tazarar dake tsakanin su yayi yana duban idanunta sosai.

"Na tsani nuna halin ko in kula......na tsani wannan attitude din.....Please behave.....or I'll have to take disciplinary action" Yayi maganar har zuciyarsa yana nufin abinda ya fada din soft lips dinta masu kalan red dake motsawa kadan kadan alamun tsiwa na cinta suna fusgar hankalinsa. Yasha imagination na sanda zata mallaka masa su ba gardama ba tare daya qwata da qarfi ba......bama iya su kadai bama.....dukkaninta yakewa wannan fatan da kuma burin. Lallausan tafin hannunta ya matsa yana sauraren Jin muryarta. Muryar data zame masa abokiyar hirarsa a mafarki tun waccan ranar data amsa wayarsa a garin makka.

Idanunta ta jjanye daga kanshi,har yanzu batajin zata iya kulashi din......duk sanda ta kalli fuskarsa fareeda take gani kwance cikin qirjinsa.....duk sanda ta kalleshi munanan maganganunsa a kanta take tunawa.....muguntarsa da musguna mata da mugayen maganganu,don haka ta taka zuwa side din hagunsa da nufin rabeshi ta fice.

Cak ya dagata ya azata saman kitchen cabinet din ba tare da tunanin tayi kusa da qofa ba,ko kuma jama'ar dake gidan ba. Hannayensa ya sanya ya zagaye bayanta dasu,ya hana mata kowacce dama da zata raba jikinta da nasa,ya kuma yi kane kane a fuskarta ya hanata matsawa ko kadan,da wannan daman ya samu ya riqe lips dinta da suke tsone masa idanu ya fara aike mata da wani irin tattausan kiss. Ba wannan zafin ba kuma wannan hanzarin,wani irin sarrafata yakeyi da wani irin sanyi da salo daya soma zare mata duk wani kuzari da takeji da kuma zafin da takeji a kansa.

Duk wani tunani nata ya tsaya cak tun daga sanda ya wuce cikin kitchen din. Wani abune da yazo mata a bazata wanda bata taba tunanin zai faru ba. Yau fu'ad ne a gabanta ya tsallake yabi mace kitchen da zummar zai samo ruwan dumi?.

Cup din hannunta ta ajiye tunaninta yana komawa baya,ta saita dukkan idanunta da hankalinta akan qofar kitchen din tana lissafin mintuna nawa zaiyi kafin ya fito. Falon yayi shuru saboda wucewar kowa sai ita daya data rage,ta dauke kanta tana duban agogon hannunta bayan shudewar mintuna biyar din data tabbatar ko dafa ruwan za'ayi wadannan mintunan sun wadatar. Kujerar da take kai din sai takejin kamar ta mata nisa da bakin qofar. Miqewa tayi tsam tana canza kujera mafi kusa da bakin kitchen din tana sauke wani zazzafan huci,tanata qoqarin hana zuciyarta ci gaba da hasashen abubuwa daban daban da zuciyarta ke saqa mata.

"Da gaske yarinyar nan 'yar bariki ce.....da gaske bariki takeson gwadamin?.....wai uban me yakeyi a kitchen din?,da gayya ta tsareshi kenan don ta gwada mata iyakarta?" Wadannan tunane tunane su sukaci gaba da kai kawo tsakanin zuciya da kwanyar maamah. Sake matsawa tayi kujera ta gaba tana sake zurfafa jinta da kuma idanunta akan qofar kitchen din,amma bata iya jiyo komai,abinda ya sake assasa baqincikinta. Wai wanne tsautsayi ne ya hanata tsaiwa a nigeria tasa ayiwa fu'ad da sabreen din mummunan farraqu?,irin farraqun da ko me irin sunanta zai tsani ballantana ita da kanta.

Maida idanunta tayi ga agogo tana duba adadin lokutan da aka shafe. To badai dafa ruwan dumi ba....ko dan mutum za'a dafa a wannan gabar yaci ace ya dahu wani irin tsalle zuciyar ta keyi,wani sashe na zuciyar na bata shawarar shiga kitchen din da kanta taga qaryar rashin kunya. Sau uku tana miqewa sai ta koma ta zauna cikin shakka da kokwanto. Batasan ya zataji ba idan taje ta tadda daidai da abinda tunaninta yake bata. Qaqqarfan motsin da taji daga kitchen din ya qarasa tunzura zuciyarta,ta miqe da wani irin gaggawa ta durfafi kitchen din.

Baya fahimtar komai sai sabreen din dake gabansa......kowanne sashe na jikinsa karbar saqo yakeyi iyaka,baisan wanne irin kebantaccen shauqi yakeji haka a kanta ba. A yadda yakejin kansa a lokacin yana jin kamar duniyar ma tayi musu kadan shi da ita. Ya sake zurfafa harshensa cikin bakinta yana sake zare mata duk wani kuzari nata. Qwace masa numfashinsa ya dinga yi yana kamoshi da qyar,a daidai wannan lokacin maamah ta qaraso bakin qofar kitchen din cikin zaton zata samesu tsakiya ko qarshen kitchen din.

Tamkar an juya kwanyarta daga sama zuwa qasa haka taji. Wani irin shock jikinta ya dauka na tsakanin mamaki da kuma tsoro,jikinta da qafafunta gaba daya suka dauki kyarma,saita juya da matsanancin sauri tana jin juwa na shirin kayar da ita. Tana juyawa yana zare bakinsa a nata,baiganta duka ba,amma yaga wani sashe na rigarta. Zazzafan numfashi ya furzar yana cure hannun sabreen dukka cikin kasa hadi da kifi fuskarsa a bayan hannuwan nasu yana qoqarin daidaita numfashinsa.

"Maamah" Ya fada can qasan ranshi,kwata kwata ya manta ya barta a parlor,amma yayi tsammanin yadda anni ta wuce daki itama dakin ta nufa. Daga fuskarsa yayi data sauya launi yana zubesu saman tata fuskar. Fuskarta ta kawar tana qoqarin dauke hawayen dake shirin zubo mata. Ya gansu,don haka ya sanya hannu da nufin dawo da fuskarta saitin nasa,saidai ta rigashi ta hanyar ture hannuwan nasa. A wahalce a kuma kasalance yace.

"Na jima ina baki wannan shawarar......zanci gaba kuma da maimaita miki ita....kada kice zaki gwada raba kanki dani......zaki wahalar da rayukanmu ne kawai......don fu'ad bai shirya rabuwa da duk macen data sanshi a d'a namiji ba......fu'ad bai shirya rabuwa da sabrrrr ba" Yana kaiwa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login