Showing 138001 words to 141000 words out of 557259 words

Chapter 47 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

543

daga kowacce kafa ta gashi dake jikinsa. Gangar jikinsa yakejin kamar ba tashi ba ballantana ayi batun qafafunsa su samu daman iya daukansa,don haka sai kawai ya sulale ya zube ragwab a wajen yana jin kamar numfashinsa zai qwace masa.

Meye ma zaiyi ne?,ihu ko kuka?,hauka zaiyi ko mene?,kudade maqudai?,kudadenma kuma na kamfanin jadda?,kudaden da akansu yau suke lissafi zasu kuma gama lissafinsu a gobe?. Shin waye ya aikata hakan?,waye yake da alhakin aiwatar da hakan?. Yaushema abun ya faru?,wa zai soma kira ya tambaya bayan daga bakinsa ya kamata a fara ji?,wai yaushe ma abun ya faru ne?.

Ko sanda ya duba time na faruwar abun,da sanda John ya fara kiransa sai kawai ya saki wayar ya dora hannu saman kai yana fadin

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Da qarfin gaske,wanda kalmar ma sam batazo bakinsa ba sai sannan. Yana dire kalmar farko hawaye suka fara bin kuncinsa. Daidai sanda kuma kira ya shigo wayar tasa abinda ya sanyashi zabura kafin yakai dubansa ga wayar.

Sir sadiq daya gani a rubuce ya sanya fitsarin dole kubce masa duk kuwa da yadda yaso ga riqeshi. Ya shiga uku ya lalace,yasan tunda yaga kiran saddiq din magana ya gama isa kunnen boss. Da wanne baki zai kare kansa?,idan suka buqaci kuma ya biya a ina zai samu?,ta ina zai samosu?. Yayi imanin koda danginsa zai siyar bazai hada wadannan kudaden ba.

Zuciyar dake da Allah a cikinta......hakanan zuciyar dake da yawan ambaton Allah ce kadai ke samun nutsuwa a sadda bala'i ya durfafo ta,don haka dukka wata dabara da kuma nutsuwa sukayi qaura daga gareshi.

Ya dinga zirya yana kai kawo,ya kasa aiwatar da komai,ya kuma kasa kamo bakin zaren komai. A haka lokutan sallah duka suka shude masa,hakanan qarar kiraye kirayen mutane suka yita shiga kunnuwansa suna fita ba tare daya iya rabar inda wayar take ba.

Duk wani kira da zai shigo wayar tsoro yake bashi,baya qaunar koda rabar inda wayar ma take gaba daya.

Sai kusan bayan sallar ishai ya iya fusgo tunanin baiyi sallah ba,ya miqe yana hada hanya ya nufi toilet don cire jiqaqqen wandon jikinsa daya jiqe da fitsari ya dauraye jikinsa ya kuma daura alwala. Har a sannan sam tunaninsa bai kawo masa sabreen ba,ya mance sam sam da itama saboda tsananin rudanin daya shiga.

"Don't call him again......ka barshi,inason naga iya gudun ruwanshi......kafin sannan ni na gama nawa" Fuad yace da sadiq wanda ke shirin sake kiran mikail din karo na biyu

"Okay" Ya amsawa fuad din yana maida kansa ga titi.

Ring na wayarsa ya katse shurun daya gilma cikin motar. A hankali ya maida kallonsa kan screen din. Anni ce,sai a sannan ya manta bai kira ba bai kuma sanya an kirata ba wunin yau. Zuciyarsa tadan saki daga quntatar da take ciki,ya daga wayar yana sanyata a kunne.

Kusan tare suka yiwa juna sallama ita dashi,sai suka amsawa juna sannan tace

"Nace dai Allah yasa lafiya......daga ku har abbanku yau duka kunyi dare a waje"

"Lafiya lau anni.....ayyuka ne suka riqemu,wasu al'amura kuma suka taso wadanda su suka shagaltar dani daga kiranki"

"Babu komai......kada ka damu,tunda dai dukkaninku kuna lafiya to alhmdlh......farouq yace min kuna tare da musaddiq ko?"

"Eh muna tare anni"

"To Allah ya tsare,ya dawo daku lafiya"

"Ameen ya hayyu ya qayyumu" Ya amsa mata zuciyarsa na sake cika fal da qaunarta da qarin ganin kimarta. Tana taka muhimmiyar rawa qwarai da gaske wajen cike musu wawakeken gibi da ramin dake zukata da kuma rayuwarsu.

Tun da aka kirayi sallar magariba ta gama shirya komai,sannan ta sallami masu aikinta kamar jiya. Tsaf ta shirya cikin embroidery holland gold atamfa da keta sheqi da nuna ainihin tsadar sutturar. Tayi kyau abinta,kai ba zakace itace ta haifi zabgegen saurayi irin muhammad fuad da musaddiq ba. Ita din ba baya bace wajen iya kula da jiki da tattalin fatarta da dukkan abinda zaya qara mata lafiya da kuma quruciya.

Parlor ta koma tayi zaune bayan ta kunna tv ta kuma saita tashar da take ra'ayi. Ta kame saman daya daga cikin sofas din falon tana kallon hagunta da damanta. Kujerun take kallo,a ranta tana wassafa ranar da zatayi gwanjonsu. Duk da tsadarsu da kudaden da aka kashe wajen mallakarsu sam ita bata tuna wannan. Abu daya dake sake tsaye mata a rai shine,labarin katafaren ginin daular data samu cewa yana yi cikin garin abuja. Batasan ainihin wacce unguwa bace,amma me kawo labaran ya shaida mata cikin jerin unguwanni mafi daraja da tsada a garin abuje yake ginin,kamar yadda yakejin qishin qishin din yana nan yana tamfatsa wani a lagos.

*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 75


K'aramar qwafa taja,muddin da gaske wannan villa din yake ginawa.....indai da gaske hoton da me dauko rahotonta ya nuna mata fuad dinta ke ginawa.....to kuwa koda zatayi yawo tsirara ba zata taba bari ameena da hamza su sanya qafafunsu cikin wannan daular ba.

Wayarta ta dauko ya kira hajja harira,a nan suka bata lokaci me tsaho suna sake tsara yadda komai zaya kasance.

Batasan ma lokaci yaja haka ba sai da suka gama waya da hajja harira din. Ta kalli agogo tana mamakin rashin shigowarsu gidan,fargaba na saukar mata na kada fa yau ma a maimaita abun jiya?.

Bata samu fuad ba,amma ta samu musaddiq,ya amsa mata da zasu shigo,don shima baisan fuad din ya gama shirya yadda zasu cinye daren a waje ba.

Ci gaba tayi da duba lokaci mintuna bayan mintuna,saidai duk sanda ta kalli agogon sai ranta ya sake baci,haka ta sake jawo waya da xummar sake trying number musaddiq amma ta kasa samunsa.

Ranta ya sake baci qwarai,dama ta sani samun number fuad ba abu bane me sauqi,sau tari xaka iya kiransa ka kasa reaching dinsa,saboda ba da gama garin wayoyi yake amfani ba don dalili na tsaro da kuma matakin rayuwa da yake kai dole yana buqatar tsari akan komai nashi.

Dukka number dinsa taci gaba da gwadawa,number ta qarshe data kira taji alamun kiran ya soma tafiya,saita samu gefen kujera ta zauna tana furzar da iska me zafi daga bakinta ranta yana tafasa.

Kaman jira ake ya gama wayar wani kiran ya shigo. Kamar ko yaushe bayyanar sunanta saman screen din fargaba da kokwanto yake sanyashi. To amma ba yadda ya iya,dole ya daga kiran ya mata sallama kaman yadda yake a dabi'arsa.

"Wa'alaikumussalam.......me yasa har yanzu baku shigo bane fuad?,ka manta da alfarmar dana nema kenan?" Ta fadi tana qoqarin tausar zuciyarta ta yadda kalaman zasu fita da taushi daga bakinta.

Komai qanqantar motsi tsakanin anni da maamah sai yaga tarin banbance babance. Da fari anni lafiyarsu kawai takeso taji kafin komai......amma ita nata uzurin su shigo suci abinci shi ta fara gabatarwa,abincin da ta tabbatar koda basuci a wajenta ba zasuci ako ina nema,amma kuma lafiya fa?.

"Ayyukane suka tsaremu yau dukkaninmu,yanzu haka ma wani guri zan qarasa......amma in sha Allah i will do my best". Shuru ta danyi wuta tana dauke mata,yanzun qarfe tara harda rabi na dare,yaushe yaje wani waje,yabaro gurin kuma yazo wajenta?.

" Okay,ina jira" Abinda ta fada kenan tana jin kamar ta bude masa abinda ke ranta. Bala'i da masifa takeson lullubeshi dashi,to amma ko dazun suna waya da hajja harira sai data gaya mata

"Me garaje ba kasafai ya fiya cin nasara ba a dukka lamuransa,saikin saka haquri juriya da kauda kai kaman bakiga komai ba". Wayar ta cillar gefe,ta hada tafukan hannayenta cikin fuskarta.

Wata irin tsanar anni da alhaji hamza tana mata masauki a zuciya tana kuma qara samun hauhawa cikin ranta. Inama ace yau zata budi idanu taga babu su cikin rayuwarsu?,da kowacce dama tazo mata yadda takeso.

Iya tafiyar da sukayi cikin motar bawai zaman shuru kadai yayi ba,zuciyarsa ta gama nisa akan matsalar iya balla shingen asusun ajiyarsu har kuma a debi wani abun?. Ba shakka koma waye ya aikata hakan yana da alaqa me qarfi da kamfaninsu,yana kuma da alaqa ta kusa kusa da mika'il. Dole ya zamana yana da alaqa da mikail.....ko shi kansa mikail din ma gaba daya.

Dalili......dukan abinda zai basu daman yin kutse kai tsaye da samun nasara haka a sauqaqe yana tare da mikail din. Dazu dazu ya danqa masa komai,cikin qasa da awa biyu kacal kuma ace komai ya faru?.

"Muje gida" Ya bawa driver din umarni,wanda ba wanda ya binciki dalili tsakaninsu ukun suka sauya akalar tafiyar tasu.

A tsaitsaye ya leqa anni sannan ya wuce zuwa sassanshi. Ya samu sassan nasa neat kamar ko yaushe kaman kuma yadda yake buqata. Ba duhu ba kuma haske me yawa sai matsakaicin hasken da bai fiya takurawa idanuwa ba. Ko ina qamshi yake fiddawa da wani irin moderate yanayi.

Takalmanshi ya sabule daga bakin qofa yana sauya wasu lausasan flip flops,daya daga cikin hadimansa ya sunkuya ya daukesu yana adanasu cikin wani qawataccen ma'ajiyar takalma me daukan hankali.

"Ku ajiye komai ku tafi,na sallami kowa.....sai da safe" Ya fadi musu yana takawa zuwa hanyar da zata sadashi da wani dan corridor da zai bashi daman isa bangaren dakunan baccinsa.

Daga zuciyarsa har gangar jikinsa basu da wani karsashi ko qwari,to amma kasancewar zuciyar jaruma ce ya sanya bata gaza ba,sai daya tabbatar yayi wanka yayi sallah ya sauya kayan jikinsa sannan Kai tsaye ya dawo falon da babu kowa a cikinsa,saidai ya tabbatar security tako ina suna kai kawo cikin gidan dama wajen gidan.

A nutse yake ratsa falon hannunsa zube a aljihun boxers din daya sanya tamkar wanda ya boyeshi saboda jin sanyi ko baya buqatar aga hannun nasa. Light blue kalan kayan sun masa wani irin kyau,saidai kuma fuskarsa tadan fada kadan wanda baya rasa nasaba da stress din yau daya tsinci kansa a ciki.

Dining ya wuce kai tsaye,komai yana shirye cikin tsafta. Bayajin a duniya bayan anni akwai wanda yakai ameh sanin tsarinsa akan abinci.

Yasan duk abinda ya bude cimarsa ce,kuma abinda yakeso ne,saidai kuma bayajin akwai wani sauran space da cikinsa zan dauki abinci,wannan ya sanya ya bude royal glass bowl din da tun bai bude ba yana iya ganin abinda yake ciki.

Lafiyayyen fruit salad ne da aka samar dashi daga dukkan nau'in kayan marmari na nan qasar dama wanda bamu dasu a nan din. Baya rabo da fruit sam,don haka masu shirya masa store da fridge dinsa sunsan duk inda zasu samar masa da nauin fruit da cimar da yakeso din.

Yadan diba da yawa,sai ya sauka a hankali ya duba ma'ajiyar shayinsa.

Bayashan coffee sai idan dole ta kama,amma yasan sirrin shan black tea da ake masa hadi na musamman da abubuwa masu amfani ga lafiya irinsu cinnamon cardamom scent leaves da sauransu.

Da kansa ya shirya komai saman tray ya nufi wata yar kyakkyawar books shelves ta ainihin gogaggen katako dake bangon gabas na parlor din. Hannu daya ya sanya ya murza wani abu da ba lallai ka iya lura da zamansa jikinta ba,sai ya sakeshi yasa hannu ya juyashi take qofa ta bayyana daga baya abinda ba zaka taba tunanin samuwarsa a wajen ba,ya taka ya shiga a hankali yana maida qofar yadda take.

*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 76


Daki ne da yakan jima bai shiga cikinsa ba sai muhimmin aiki irin haka ya taso. Saidai duk da haka komai a tsaftace yake.

Wani irin table ne na musamman ya jawoshi gaban main table dake dauke da nau'ikan na'urorin computer iri daban daban,ya aza tray din hannunsa a kai,ya taka a hankali ya kunna kowanne lantarki dake dakin,ya bada haske sosai. Komai na dakin bisa tsari yake,da nau'o'in kalolin green masu qarawa idanu qwarin gani.

Idanunsa saman systems din daya kunna guda biyu yana jiran su gama saituwa. Kadan kadan kuma yana kurbar black tea din da qamshinsa ke qara masa nutsuwa,kafin ya ajiye ya soma shan fruit salad din,daidai sanda komai na system din ya daidai ta,sai ya sake jawo kujerarsa gaba yana bata dukkanin hankalinsa.

Cikin tsananin nutsuwa da qwarewa yake bin komai. Ya kusa kashe a qalla awa biyu cikakku kafin ya dakata,ya tura kujerarsa baya yana zubawa allon computer idanu yana duba abinda ya samu a tsahon zaman da awannin da ya kashe.

Iska kawai yake furzarwa daga bakinsa,mamaki yana sake cikashi da samun bayanan duk da bai qarasa samun ragowar baya nan ba,amma ko iya wadannan bayanan da zaman da zaiyi da mikail sun isheshi samun kan komai. Ya dinga murza tafin hannunsa cikin na juna tamka ma jin sanyi,kanshi yana sake cakewa.

"Jibril usman" Ya maimaita sunan idanunshi nakan sunan da bai samu damar samun ainihin fuskar me sunan ba. Tabbas ko wayeshi din mayen computer ne,kuma qwarrare a sanin fanninta,saidai duk da haka qwarewar tasa akwai saura,don akwao gurare da abubuwa daya gani wanda shi Jabril din da ya samu rufesu to ba shakka shi kansa yanzun bazaikai ga isa ga bayanan ba. Qaramin masanin computer zai iya saluting jibril,amma shi da mutane ire irensa zasuyi murmushi ne kawai,a karon farko kuma su fahimci saura taqi kadan yakai inda ya dace yakai din.

Gefe daya ranshi ya sake ninka baci,duk wanda yaga aka zare kudin zaiyi tsammamin manyan hackers gagarumai wanda suka gagari duniya system dinsu ta hadu dashi......wannan kadai ya isa ya sake zaburar dashi lallai lallai yana buqatar yin garambawul wa security team dinsa,amma kafin sannan mikail shine mutum na farko daya dace ya dauki mummunan mataki a kansa,saboda shi da kansa ya yiwa tsaron company dinsu aiki,ya saka abubuwan da duk qwarewarka idan ba samun wani information mutum yayi ba zai wahala ya samu isa ga inda suka samu isa din.

"Ina yaje?,waye ya bawa sirrinmu?" Wadannan sune tambayoyi guda biyu da yake buqatar ji daga bakin mikail din. Kodai yaci amanar company......ko an nemi rayuwarsa an masa barazana....kota dalilin sakacinsa bayanan sun fita.

Washegari kaman kullum,yabi tsarin jawadalinsa na kullum tun daga gida har zuwa office. Qarfe shida da rabi yake kammala motsa jikinsa ya wuce wanka,idan ya fito yakan dan bar bathrobe jikinsa ya karbi newspaper da magazines ya duba,yadan duba saqonnin email da WhatsApp dinsa ya hada da shan ruwan duminsa ko dafaffiyar madarar shanunsa me tumeric. Sai bayan kammala dukka wadannan hidindimun sannan yake shiryawa,yayi breakfast ya wuce office.

Kamar ko yaushe yau dinma bakwai da rabi ya fito daga toilet daure da bathrobe dinsa. Yanaso yau ya fita da wuri ne fiye da yadda ya saba fitan. Don ko da safe daya tashi ya sami missed calls din maama din kusan guda goma,wanda ya tabbatar tun na daren jiya ne.

Yawan kiran nata kadai da takeyi yana sake bashi tabbaci ne a kanta. Ya jawo wayar ya turawa musaddiq text akan zuwa takwas ya shirya zai aikeshi wani guri,sai ya cire toilet slippers din ya sanya wasu tausasan rufaffun takalma ya soma takawa yana fita don riskar parlor ya duba newspapers din yau.

Ba kowa parlor din sai ameh daketa zirga zirgar shiryawa ogan nasa dining,sai me sunan malam dake zaune saman lallausan turkey carpet din da aka qawata tsakanin kujerun. Me sunan malam din na daya daga cikin amintattunsa da basu da shamaki wajen samun daman isowa parlor dinsa.

"Good morning sir" Ya fadi yana rusunar dakai

"Morning me sunan malam.....mun tashi lpy" Ya amsa masa yana zama saman wata sofa guda daya data banbanta da sauran duka kujerun parlor din yana

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login