Showing 438001 words to 441000 words out of 557259 words

Chapter 147 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

502

yasha madara yayi fari sol,da kanta anni ta zuba mata a mug ta saka sugar dan daidai sannan ta miqa mata.

Karba kawai tayi tana wassafa yadda zata sanya a bakinta,kai.anni ta jinjina mata cikin son bata qwarin gwiwa,wannan ya sakata kai mug din bakinta.

Kurba uku kawai tayi ta dire,annin bata matsanta mata ba ta dauka kawai ta rufe ta bata ruwa. Kurba daya shikam ta ajjiye,saboda batajin zai zauna a cikin ta. Bakinta ya saba da zartsin zartsi na taste din zam zam. Annin ta fahimci haka,don haka ta qwalawa ma'u kira tace ta duba store ta ciro zam zam babban roba. Ba jimawa ta dawo dashi,annin ta bude ta tsiyaya ta bata.

Wannan karon anci sa'a,tas ta shanyeshi ta ajiye cup din,hakan ya yiwa anni dadi,saita matsa ta dauki counter tasbaha ta maqala mata a yatsunta

"Hasbunnallahu wa ni'imal wakil,wallahu galibun ala amrih sau ba adadi" Kai ta gyada a hankali tana jin hankalinta yana karkata ga addu'a maimakon kuka da bala'in tashin hankalin da takeji.

Sai da anni taga ta kama sannan ta miqe a hankali ta nufi qofar ta fita tana rufe mata da nufin dawo dasu huda ciki su tayata zama.

Fitar anni da second talatin kadai wato rabin minti taji kamam muryar musaddiq cikin kunnuwanta. Sakin counter din tayi ta miqe qirjinta na wani irin mahaukacin bugu,cikin sanda kaman barawon daya shirya gagarumar sata ta nufi qofar,ta kamata ta bude a hankali,sai muryar musaddiq din ta fito tas.

"Muje ka gayan me ya faru,koma meye banaso sabreen taji" Taji anni tana fada.

Sakin qofar tayi a hankali ta fara takawa tana biye da bayan annin,duk da cewa akwai ginin hallway daya rabasu basa iya ganinta amma ita tana iya jinsu sosai,cikinta hautsinawa yakeyi sosai,tana cike da tashin hankali da fargabar abinda zataji daga bakin musaddiq din.

Hannun musaddiq kawai anni ta kama kai tsaye ta ajeshi saman kujerun da suke matsakaicin falon,tashin hankali da rudani sunaso suyi galaba a kanta amma tana cinyewa.

"Gayamim musaddiq......ina fu'ad.....ina me babbban suna?" Shuru ya danyi,yana juya yadda zai bata incomplete information,saidai shirunsa zaifi zame mata damuwa sama da amsarsa

"Sun harbeshi" Ya fada a hankali kaman bakinsa bayason fada.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Anni ta shiga maimaitawa. Wani irin bugu maganar ta yiwa sabreen,abu na farko daya fara zuwa kanta shine SUN KASHESHI.

Nutsuwarta da hankalinta ne gaba daya suka fara gushewa,sannu sannu saita fara daina jin abinda musaddiq yaci gaba da fada.....duhu ya fara gilmawa idanuwanta,ta suma sulalewa a wajen ta zube saman rug din.

"Harbin farko ya kauce basu sameshi ba,ya hangi maharbin sai yayi nufin binsa shine ya sameshi a harbi na biyu dana uku......suna tare da yaa farouq,tare ma suka yunqura suka bishin,amma yanxun ba'a ga ya farouq ba,ba'asan ina yayi ba.....shi kansa hamman da jordan dinma ba'asan ina akayi dasu ko yaya akayi dasu ba" Ya qarasa fadawa anni maganar zuciyarsa tana girgiza.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Taci gaba da maimaitawa tana jin zuciyarta na wani irin jijjiga kaman zata ballo daga qirjinta ya fado.

"Musaddiq ina abbanku?" Ta tambaya saboda tana jin duk wata jarumta tata da dabararta ta qare,tana buqatar tallafin abban a kusa.

Kaman yasan shi take nema sai gashi ya sako kai,kai tsaye ta miqe ta nufeshi,bata kuma tsaya bata lokaci ba ta fada qirjinsa hawaye yana sauka daga idanunta,wani abu da bata taba yi ba gaban yaran tsahon shekarun.

"Ya isa ameenatu.....kiyi haquri.....duk inda suke da halin da suke ciki za'a samosu in sha Allah,karki daga hankalinki da yawa,idan hakan ya faru ita kuma sabreen muyi yaya da ita kenan?". Kiran sunan sabreen din ya ankarar da ita,ta janye jikinta daga abban gabanta yana faduwa. Sai sannan ta tuna tayita maimaita innalillahi da qarfi a dazun,wanda zai wahala baikai cikin dakin da sabreen din take ba.

"Bari na dubota abba" Ta fada tana juyawa da sassarfa tana nufar ciki.

Tuntuben da tayi da ita shi ya sakata taja baya da sauri,kasa jurewa abinda idanunta suke gani tayi,sai kawai ta saki qara tana kiran sunan abba a gigice.

Shima ya kadu da jin qararta,wani abu da bai taba ji ameenatu tayi ba komai girman jarrabawa,don haka da sauri yayo hanyar dakin musaddiq yana biye dashi.

"Maza jeka kira mommanta.....kada ka bari yaran su biyoku" Abba yace da musaddiq saboda a yadda anni ta gigice yasan ba zata iya riqe sabreen ba.

Ba shiri momma data tayar da sallar la'asar din da bata samu daman yi ba sai sannan ta sallame tabi bayan musaddiq. A gigice ta duqa gaban sabreen tana dagata,saidai ba wani alamun numfashi a tattare da ita.

"Nutsuwa zakuyi ku taimaketa ta hanyar daukota mu wuce asibiti da ita" Abba yayi qoqarin dawo musu da tunaninsu jikinsu.

Kaman gawa haka suka dagata,suka wuce kuma kai tsaye bakin farfajiyar shigowa gidan,don tuni musaddiq ya sanya an matso da mota gaban ginin.

Makeken private hospital dinnan da babu kamarsa kaf Nigeria suka nufa da ita wato Noor hospital. Idan ka shiga zakayi tsammanin kana qasashen qetare ne bawai a Nigeria ba kuma gida kanon dabo.

Asibiti ne da yake mallakin Muhammed fu'ad jadda.....amma a sirrance mallakar ta kasance,ba kowa bane yasan da hakan. Duk wani kalar kayan aikin da bamu dashi sai a qasashen qetare ya kawosu ya zuba don hana masu kudinmu fita neman magani waje. Donsu din kawai dama yayi asibitin,don babu wani me qaramin qarfi da zaiyi gigin kai kanshi nan. Saidai kuma kusan duka kudaden da ake samu ta asibitin ana tafi dashi ne ta hanyar hidimar al'umma,don baya ci ko karban ko sisi a ciki,saboda baida buqatarsu.

Dr hajar da Dr mubeena ne suka karbeta,don ba wani likita namiji da yayi kuskuren zuwa inda take,duk da dama kusan haka tsarin asibitin yake,mata likitoci mata ke karbarsu,maza kuma likitoci maza.

Cikin qwarewa suka shiga bata taimako don maido numfashinta kan saiti gudun rasa abinda take dauke dashi,sun samu nasara saidai sun mata allurar bacci saboda ta sake samun nutsuwa sosai,don ta shiga shocked ba kadan ba. Sunyi duk wasu gwaje gwaje daya kamata,harda su scanning da basu tsaya anyi a madeena ba,saidai abinda scan din yaketa nuna musu ya sanyasu a mamaki.

Hankalinta kwance take cikin dakinta tana ninke lace din data siya jiya naira dubu dari tara da tamanin,ta kuma budeshi don ta tabbatar shi dinne. Zuciya cike da saqe saqe da taraddadin cikar mission dinta da tafiyarsa daidai?,ko kuma akasin hakan wato FADUWA wanda ko sunanta bata qaunar taji.

Har yanzu zuciyarta tana mata susa idan ta tuna fattatakar da bokan yayi mata,sam yama qi saurarenta,wanda ita bataga dalilinsa naqin sauraron nata ba bayan tana cika masa aljihu da kudi. Ta dora kyakkyawan zato akan hajja....duk da tasan mutum ne shi da ba'a sakashi ba'a kuma hanashi......amma tana da zato me girma akan hajja din,wannan ya sauya akalar tunaninta na taci gaba da riqon laila.

Zuwa yanzun lailan ya fara zame mata kaya,don ba wani abu da zata iya aiwatarwa na qashin kanta saita tambayi maamah din. Daidai da cin abinci wannan sai data fatattaketa,tace kada ta qara tambayarta don zataci abinci,taci ko kada taci wannan ya rage nata.

Ko yanzun da akayi mata knocking sai data ja tsaki,tasan bazai wuce laila din ba,don cikin masu aikinta ba wanda ya isa ya qaraso nan wajen sai idan ita ta nemi ganinka.

"Waye?". Ta tambaya cikin 'yar qaramar fusata.

" Laila ce".lailan ta fada jiki da muryarta dukka suna rawa. Har ta bude baki zata koreta,sai kuma taji kaman akwai raunana a muryarta don haka tace

"Meye kuma?,kinsan banason damu ko?".

"Kiyi haquri.....wani abu ne ya faru nazo nuna miki,nima yanzu naga an sakashi a page din jaridar breakers".

"Shigo" Ta bata dama kai tsaye tanason jin me tazo dashi.

Sanda ta shigo jikinta yana rawa ta miqa mata wayar hannunta. Hannu ta sanya ta karba cikin yamutsa fuska sai kuma ta waro idanunta dukka waje.

"AN KAIWA SHARARREN MATASHIN ATTAJIRIN NAN FARMAKI A FILIN TASHI DA SAUKAR JIRAGEN SAMA HARI WATO MUHAMMAD FU'AD JADDA.....HARMA ANA KYAUTATA ZATON BACEWARSA.....YANZU HAKA BA'ASAN INDA YAKE BA". Sake qarewa rubutun kallo tayi da kyau,ta maimaita rubutun ta sake maimaitawa sai kuma murmushi ya subuce mata duk da zulumin daya cika wani sashe na zuciyarta.

"Lokacin tarwatsewarki ameenatu yayi.......tabbas wannan itace dama ta ta farko a kanki kafin na isa ga dama ta biyu na qarasa murqusheki.....na kuma jefa rayuwarki data ahalinki cikin halin ni 'yasu" Tayi maganar a sararin tana jin dadin samun wata gwagwgwabar dama da ta sameta ta sassauqar hanya.

Idanunta ta zube akan laila dake kallonta kawai.

"Kina da hanyar da zaki hadamin 'yan press?,ina da buqatar gabatar da taron 'yan jarida.......ya kamata na fara gwadawa ameenatu nawa salon da kuma ainihin kalata" Kai laila ta girgiza.

"Bansan yadda zamu kirasu ba.....amma ina da qawa da take aiki gidan radio.....zan shaida mata sai suzo din".

"Hakan yayi.....gobe da sassafe nake buqatar su hallara a harabar gidan nan,bayan gida radio dinsu ina buqatar ta qara da gayyatar wasu kafafen yad'a labaran dama na jaridun......zan biyata akan wannan aikin gayyatar" Maamah tayi maganar tana lalubar number musaddiq,can qasan ranta baqincikin yadda musaddiq ya kasa kiranta a matsayinta na mahaifiyarsu ya shaida mata abinda ya farun sai a rariya ta gani.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 120



https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX



120


Dab da zata tsinke ya daga,kafin yakai ga gaidata ta amshe

"Duk tsiya tuwo dai sunansa tuwo.....kuma.basai kayi hakan ba zaka tabbatar min ni ba komin komai bace a wajenku.....abu ya samu dan uwanka musaddiq saidai naji labari a wani wajen?,yanzun kuna ina?". Tafin hannunsa ya sanya ya riqe goshinsa saboda yadda kansa yake sarawa......ta dage ita kuma still saita qara masa wani ciwon.

"Muna asibiti" Ya amsa mata a taqaice.

"An ganshi ne?" Ta tambaya yana fargabar bayyanarsa kafin ta qullawa ameenatu jakar tsabar data shirya qulla mata.

"Adda sabreen ce....."

"Tayi bari?" Ta qarasa masa da abinda zuciyarta ke fatan ya kasance. Sai daya janye wayar a kunnensa yana dubanta kafin ya maida cike da mamaki.

"Wanne asibiti ne?" Ta tambayeshi tana kauda waccan tambayar ganin bai bata amsa ba.

"Noor hospital" Iya abinda dama takeson ji kenan,tana kuma da buqatar zuwa idan barinne sabreen din tayi ta karbi barin da hannunta ta taho dashi nan ta bawa karnukansu su cinye su shanyen jinin,ta kuma aikawa sabreen din video din ta yadda zai zame mata wani mummunan ciwon.

Sharp sharp ta shirya,ta kuma kira driver ya fidda mota suka wuce noor hospital kai tsaye.

Masifa ta dinga yiwa driver din,tana ganin kaman baya sauri.....kamar ba zai isa akan lokaci ba. Cikin qasa da minti arba'in sai gashi cikin noor hospital saboda uban gudun data sanyashi ya dinga zubawa.

"Scanning din da mukayi mata ya kasa bamu ainihin abinda mukeson gani.....saidai mun samu nasarar ganin two embryos,hakan yana alamta akwai d'a biyu cikin mararta.....iya abinda muka gani kenan,mararta akwai nauyi da aiki fiye da marar me dauke da yaro guda daya....so that dole ta dinga kiyaye wasu abubuwan.....bacin ranta.....aiki me wahala da nauyi da duk abinda zai sanya mata stress.......babies din suna lafiya......amma idan ba'a basu kulawar data dace ba.....komai zai iya faruwa" Bayanin likitan kenan da dukkaninsa ya sauka a kunnen maamah data shigo dakin da qarfinta,saidai ta samu annin da dr mubeena tana mata bayani a parlor din dakin da sabreen din take.

"Za'a kiyaye in sha Allah Dr...." Anni ta fada jikinta yana sanyaya,tana sake girmama hukuncin ubangiji da girman qudurarsa da zatinsa.

"Allah kaine Allah,baka da abokin tarayya Allah.....yadda ka samar da wadannan halittu naka a mahaifar mahaifiyarsu cikin wani salo da hikima irin naka.....Allah ka fidda mahaifinsu ka kiyayeshi daga dukkan hadari" Anni tayi adduar da take har zuciyarta ba tare da tasan da wanzuwar maamah a wajen ba.

Duk da taso tazo ta samu gudan jinin yaron a leda amma saita samu akasin haka.....daga tunanin yaro daya ya koma biyu....bugu da qari ma kuma ana bata tabbacin raunanniyar lafiyar da suke da ita.....to amma har yanzu tana da sauran abinda ya rage wanda zata girgixa duniyar anni.....a yanzu zata gudanar da plan A......plan B din kuma ta ajewa kwanakin da suke zuwa a gaba.

"Zaki gama munafuncinki tsaf.....da duk wata munafukar addu'arki ki gayamin inda kika kaimin d'ana.....ni dama nasan za'azo wajen.....ko ba dade ko bajima dole sai kinyi yunqurin salwantarmin da yaro saboda ki handame abinda ya mallaka......to wallahi baki isa ba......ni mariya nice uwar FU'AD,bazan kuma qyaleki ba idan yarona ya salwanta". Cak anni ta dakata daga buda qofar ainihin dakin da sabreen ke ciki,waiwayowa tayi a nutse cike da mamaki tana duban maamah din

"Mariya?,kinsan abinda bakinki yake fada kuwa?". Wani kallo maamah ta watsawa anni,cike da alfahari da samun tabbaci akan qudurinta.

"Na sani mana ameena.....kina tunanin ba'a hayyacina nake ba?.....UWAR RIQON MUHAMMAD JADDA TAYI KIDNAPPING DINSA SABODA NEMAN KUDIN FANSA......A HALIN YANZU BA WANDA YASAN INDA TA BOYESHI....ya kikaga taken wannan labarin a gidajen rediyoyin Nigeria africa dama duniya gaba daya?" Har tsakiyar kanta anni taji wani abu ya tsarga mata

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"

"Dama ki riqe abarki zuwa gobe.....don kuwa goben warhaka bana tunanin kina cikin masu cikakken 'yanci kamar haka". Ta qarasa fada tana takawa hankali kwance tana wucewa dakin da sabreen din take.

Duk wata jijiya ta kanta ta gama tashi saman goshinta,ba abinda qirjinta yakeyi sai bugawa da wani irin matsanancin fushi. Kowacce kalma data fita daga bakin maamah a kunnen sabreen ta sauka wadda ke zaune ta jingina da fuskar gadon tana kokawa da kanta ta samu tasha tea din ko babu yawa.

Zubawa maamah ido tayi sanda take shigowa dakin,qasan ranta cike da damuwar yadda ta samu sabreen din zaune sosai.....ba wani alamu na fitar hayyaci ko jigata a tattare da ita.

Kallon kallo sukewa junansu,yayin da kallon da sabreen ke ajiye mata ya kasance wani qazamtacce kuma wulaqantaccen kallo da bata taba ganin irinsa ba a kanta. Hakan bai sage mata gwiwa ba,taci gaba da takowa har ta qaraso dab da gadonta sannan ta janye dubanta daga kanta ta maidashi kan ledar ruwan da aka gama qara mata.

"Inda zan baki shawara ki dauka......da zaifimiki kyau salin alin ki kwanta a zare miki cikin nan cikin girma da mutunci......"

".......idan ba haka ba zaki sanya a kwantar dani a kasheni sannan ki qwaqule abinda yake marata?" Lafuzzan suka fita da wani irin fushi da yaja hankalin maamah din zuwa gareta.

Wani zazzafan kallo take sauke mata tana kuma ajiye mug din hannunta.

"Eh ina nufin abinda na fada din......kina zaton don kin aikata hakan zai bani mamaki?" Ta jefa mata tambayar tana dage dukka girarta sama,sai kuma ta girgiza kanta.

"Ko kadan bazanyi mamaki ba......matar data zabi duniyarta akan lahirarta?,.....matar data zabi salwantar yaranta ta tsira da qazantar duniya wato kudi!......ke nake zargi......ke nake zargi da harbin FU'AD!......ke nake zargi da batarmin da MIJINA UBAN 'YA'YANA......" Ta qarasa maganar tana dora hannunta saman mararta,wasu zafafan hawaye suna taruwar mata.

Sosai maganar ta zowa maamah a bazata,amma bata dauketa da wani muhimmanci me yawa ba tunda tana ganin sabreen din bata da wani power hujja ko damar da zata iya aiwatar da komai a kanta.

Girarta ta dage duka tana yiwa sabreen duban mamaki,wani qaramin murmushin rainin wayo yana fita akan fuskarta

"Ko?......sannu tattabara uwar aure.... Sannu me miji,to idan nidince fa?,sai yaya?". Idanu sabreen ta zuba mata kafin wani kwantaccen murmushi ya sauka saman fuskarta,abinda ya soma sanyawa maamah dawowa hayyacinta. Ba jiya ko yau ba,ta sani murmushin sabreen din bashi da dadi

"Kina daukan abun da sauqi ne har haka ko?.....haihuwar muhammad da kikayi hakan bazai qareki da komai ba a sanda kike qoqarin rabani dashi......haihuwarsa bazai qareki da komai ba a sanda kike qoqarin tabamin shi....lafiyarsa hankalinsa ko dukiyarsa........ko waye yayi gigin tabamin DUNIYATA sai inda qarfina ya qare........ciki kuwa harda ke......ke mahaifiyarsa wadda tayi rainonsa na shekara sha hudu kawai......fu'ad DUNIYATA ne.....duniyar da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login